Showing 48001 words to 51000 words out of 397328 words
dake Anna ta fi komai mahimmanci a rayuwar sa, ta zubar da hawaye a gaban shi akan tashin hankalin da ta shiga da ta ga yadda cousin ɗin ta sigari ta illata shi ba kaɗan ba, har ta zama silar kasa samun haihuwa da ya yi har ya rasu, sai kawai ya ɗaukar mata alƙawarin dainawa ta har abada.
Gyara zama ya yi yana fuskantar mutumin yace "Ka san wani abu? Magana na zo muyi da kai."
Kallon AA ya yi, yanayin fuskar shi a lokacin sai ya saka gaban shi girɗewa ya faɗi, amma sai ya yi jarumtar ƙaƙaro murmushi yace "Yallaɓai magana? Da ni kuma?"
Ba tare da ya rusuna kallon shi gare shi ba yace "Rana irin ta yau da dare sosai, ka je asibitin Saddi Ja ka ɗauko ɗaya daga cikin motar ujila na asibitin nan, da ka ɗauko motar ina ka kai ta?"
Ya tsorata matuƙa da jin wannan bayani, sai dai kuma ya yarda koma wanene wannan mutumin to a shirye ya zo masa ta yiwu kuma ya san abubuwa da dama, basarwa ya yi yace" Anya kuwa yallaɓai? Ko dai wani ka ke nema ba ni ba?"
A wata irin kakkausan murya yace" Ba na son rainin wayo, ban da lokacin ɓatawa anan, ka bani amsar abinda na tambaye ka."
Da yanayin rashin gaskiya mutumin yace" Wall..." Da sauri AA ya dakatar da shi da cewa" Kaga malam, kar ka wahalar da kan ka wajen rantsewa, so ka ke na nuna maka hujjar da ta tabbatar min da kai nake maganar nan?"
Aje butar shayin hannun shi ya yi ya share gumin da ya fara fito masa a goshi, da inda inda yace" Yallaɓai, dan Allah dan girman Allah, dan soyayyar da ka ke wa mahaifiyarka yallaɓai ka bar maganar nan, abinda na sani ƙalilan ne akan abinda ka ke tambayata, faɗin shi kuma zai iya zama barazana gare ni da rayuwata, dan Allah ka bar maganar nan."
Wani shashashan kallo ya mishi a daƙile yace" Ban fito daga gida da wannan manufar ba, ka sanar da ni abinda nake so na sani, na baka tabbaci ba abinda zai same ka, ka na cikin kariyar ubangiji da kuma tsarona in sha Allah."
Wani huci ya feso yana ɗan jujjuyawa bayan shi da gefen shi, ganin wanda ya tafi siyan sigari na tahowa ya sa ya kalli AA yace" Ɗauki lambata yallaɓai, zan faɗa maka inda zamu haɗu sai muyi magana, amma anan ba tsaro."
Da ƙasaita AA yace mishi" Faɗi lambar."
Da mamaki ya fara duban shi ganin bai ciro waya dan ɗaukar lambar ba kuma ba abun rubutu a tare da shi, amma dake wannan na kusantowa sai kawai ya shiga faɗa masa, sarauta da miskilanci ya sa AA ko maimaitawa bai yi ba haka ya miƙe ko sai anjima bai ce masa ba ya nufi motar sa. Sai mutumin da ya kawo masa sigari ya bishi da sauri ya kai masa, karɓa ya yi yana kallon ta da tunanin yaushe rabon da ya riƙe ta haka? Sai yau dalilin aiki, saida ya shiga mota ya zauna ya buɗa wata ma'ajiya ya aje ta sannan ya ciro kuɗi ya ma mutumin kyauta da faɗin "Na gode." A taƙaice sannan ya rufe motar, wayar sa ya ciro daga aljihu ya shiga rattaɓa lambobin da mutumin nan ya zayyana masa tsaf dama ya riƙe su akan shi, yana gama sakawa ya saka mishi harafin *A* yadda zai yi saurin nemo lambar idan ya tashi kira sannan ya tafi.
*BILAL YUSUF*
Duk hidimar da ake ciki ta haihuwar Zahra'u da yadda mata ke shige da fice saboda haihuwa ce tamkar yau aka fara, kuma hakane suke kasancewar suna da abun da ake kira kuɗi, shiyasa duk wacce ta haihu ko haihuwa ta nawa ce a cikin gidan ake bidiri tamkar ranar aka fara haihuwa, wannan bidirin bai hana Bilal tattaki har ɓangaren aunty Zahra'u ba ya sa aka ma Intisar magana.
Da fari ba ta yarda da aka ce shi yake kiran ta ba, amma da ta same shi tsaye bakin ƙofa sai ya so bata dariya, murmushi ta yi ta ƙaraso da hausar ta wacce kana gane ba asalin bahausa bace tace "Ƙanin mijina, ya ake ciki?"
A raunane ya kalle ta yana ciro hannayen shi daga aljihu yace "Aunty Inti, wai ya haka? Kin ce na bar komai a hannun ki za ki dubo min yarinyar nan, wallahi aunty da gaske nake ina son ta, amma naga ke kawai wasu abubuwa ne ma a gaban ki ba ta ni kike ba."
Aunty Intisar dai dake gwanar murmushi ce yanzun ma abun da take ta yi masa kenan har ya dasa aya sannan tace" Matsalata da kai Bilal gajen haƙuri, ni fa na gaya maka zan samo maka bayanan yarinyar, ko ba ka yarda da ni bane? Sanin kan ka ne ina zaune a gidan nan idan na so za'a iya shigo min da rahoton kowane ma'aikaci dake asibitin nan, bare ma ga sister Halima, ga Docter Rabi'a, ga su Sakina da dai sauran su, kiran waya ɗaya fa ya wadatar."
Sai kuma ta gyara tsayuwa da kyau sannan ta ɗora da" Kana ji, ni da abinda na so yi maka shine, idan na samu bayanan ta to zan je har gidan su da kaina na tabbatar ba ta da wani tsayayye, ka ga sai na nema maka izinin fara zuwa wajen ta daga gurin iyayen ta, hakan zai ƙara maka kima da daraja a idanun su har ma su gamsu daga babban gida ka fito, saboda ba ka yi son ran ka na tare musu ƴa a titi ba."
Wani salihin murmushi ya yi mai cike da kunya yana sosa ƙeya yace" Aunty Intisar, wallahi shiyasa kike birgeni na ke kuma yi miki addu'a Allah ƙara danƙon soyayya tsakanin ki da Yaya *Mubarak*, wallahi yanzu na ji hankalina ya kwan..."
Sallalamin da suka jiyo daga ɗakin Zahra'u da kuma kukan ita Zahra'u ya sa hankalin su tashe suka rankaya ɗakin da gudun su, musamman ma Intisar da gaban ta ya yi mummunar faɗuwa saboda tunanin da ya zo mata a rai na ko ƴar ce ta koma saboda tun jiya take fama da muguwar majina irin ta gaban nan sosai da sosai har take hanata numfasawa da kyau.
Suna shiga suka samu kuwa baby Yusrah ce ke ta kakkafewa tana fizgar numfashi, ganin duk mata sun zuba idanu sai salati da jimami wasu ke yi ya sa Bilal tallabar babyn a nutse ya rumgume a jikin shi, ba ɓata lokaci ya juya da gudu ya fita da ita, aunty Intisar ce da Yayar Zahra'u da aunty Bilkisu suka rufa masa baya dan sun san asibiti zai kai su, Zahra'u na shirin saka hijabi ta bi su Mahaifiyar ta da sauran matan suka riƙe kan ta yi haƙuri za su kula mata da ita. Haka suka tafi asibiti ita kuma tana ta kuka a gida wanda Maman Bilal ɗin bata so haka ba tunda ai yarinyar ba komawa ta yi ba har yanzu.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*15*
Tunda garin Allah ya waye suke cikin rigimar Safwan, kuka yaron ke yi na zafin ciwo da kuma rigimar mamansa, duk da Safwan ba wai yaro ƙarami sosai bane, amma yanayin nan da ya faɗa lokaci ɗaya ya saka ya kasa fahimtar abinda yayarsa ke son fahimtar da shi, domin sau huɗu tana zama ta riƙe hanayensa ta sake faɗa masa cewar dan Allah ya yi haƙuri su Mama basa nan sun yi tafiyar da ba dawowa sun rasu amma ita gata nan, ai ya san rasuwa, Safwan fa har maƙabarta suna zuwa idan aka yi rasuwa a anguwa tare da yara daidai shi, shine yanzu zai tada rigimar da ba zata fitar da shi ba ya ƙi ji ya ƙi sauraro so yake yi sai ya fama ɗorin da aka yi masa, ga babban ciwon bayan da ya hana masa sukuni, gashi har ƙarfe tara ce ta yi shiru ba'a zo aka bashi magungunan da ya dace ace tun ƙarfe bakwai da rabi an masa na safe.
Iya Abu ce ta kalli Yusrah ta ce" Yusrah, sake shi, sake shi kar ku kifa ki ɗauki abinci ki ci, ke kuwa sai yunwa ta shige ki ta yadda zaki kasa tsayawa? Ki yi ƙoƙari ki ringa ci da ƙarfi koda ba kya so, kin ga nima matafiya ce kin san lalurar baffanku ya zamana yanzu idan aka barshi shi kaɗai a waje sai dai a zo a neme shi a rasa, baya zama, ya sha ɓacewa da ƙyar da roƙon Allah mu ka samo shi, kin ga ina da buƙatar in ga kin kama jikin ki sosai saboda in san ko ba komai da jajirtacciya na tafi na barshi a *WANNAN TAFIYA*."
Yusrah ta zauna ƙasa ɗabas ta kai hanayenta wajen fuskarta tana mamatsawa tamkar wacce ke masaging ɗin fuskar, bayan hanayen ne kawai ke taɓa fuskar , zuciyarta ta shige cikin matsanancin tunani da wasi wasin ƙwaƙwalwa.
Tsoro ke son kamata na abinda ke yi mata kai kawo. Anya waccen azzalumin ba maganar da ta faɗa cewar ba zata yarda da sharuɗɗansa bane yake son hawa kai ya zauna? Idan kuwa hakane ai ta shiga uku, yaya zata yi kenan? Yaya zata yi da ciwon Safwan?
Kokon ta samu mai zafi ta zauna ta sake riƙo Safwan a jikinta da dabara da ƙyar ta samu ya sha, sai itama ta zauna ta sha tana kallonsa, kamar ma Safwan fushi yake yi mata, domin duk idan tace su Mama sun rasu hanayensa yake kawowa ya doke hannunta dake daf da shi, kuma sai turo fuska yake yi ko abin kumburin ciwo ne?
*B. YUSUF*
Zaune suke su biyu suna cin fruits, ko in ce ya samu mahaifiyarsa na ci ya zauna suka shiga ci tare suna taɓa hira.
Da kula mamansu ta ce" Bilalu, Ni kam ƴaƴan yanzu daga yaro ya fara rashin lafiya fitttt sai su warta su kai asibiti a yi ta kashe kashen kuɗi kamar ba gobe, a jariri ina abin riƙewa har da kwana jama'a saboda mura? Da ace zasu bani in mata murzar ƙirji da abinda zan fitar masu daga ƙirjin ƴa sai tsoron Allah ya kama su, amma sun tafi an samu ƴan hannaye an huda sai ƙara danna mata ita ake yi cikin ƙirji ana waftar kuɗinsu, ga duka ga tsinka jaka haka kawai dan wani tashin hankali, hum Allah shi kyauta."
Bilal ya yi dariya yana kallon Mama ya ce" To wai ni abinda ban gane ba, ina faɗan ya dosa ne Hajiata."
Mamansa ta kalle shi sheƙeƙe sai kuma ta ɗauke kai tana sake tura tufarta a baki ta ce" Duk kwana ɗaya ka san nawa Yayanka yace min kuɗin ɗakin nan da na titsiye shi?"
"To magajiya wasa ce?" Ya faɗa yana kallonta, ta haɗe hannayenta a dunƙule ta watsa masa ta ce" Ƙaniya dai ba magajiya ba, ku dai ƴaƴan yanzu baku da kara a kan ƴaƴanku, kuma kai kamar ka fi yayunka dan kana gaba kuna yawace yawacen kashe kuɗin wa mata, ni kam kamar ƴaƴana matansu sun fi ƙarfin su, ko da yake kai baka yi ba auren tukunan, amma ka ga Mubarack? Kamar jira yake Inteesar ta motsa zaka ga ya motsa ne."
Me Bilal zai yi ban da dariya, har riƙe cikinsa yake yi da mamaki yana kallon mamansu, kai! Wato Hajia mama an fara koyo halin sakawa sirikai ido ko? Yana dariyar ya ce" Yanzu Hajia mama aikin nan waye ya koya maki? Fisabililahi mutum da matarsa to in bai kashe mata ɗan abun buƙata ba ina zata je a kashe mata? Hajia mama wanda ya koya maki wannan lamari gaskiya bai kyauta mana ba ina."
Ita ma dariyar ce ta kamata dan yadda ya tare yana sallalami, ta miƙa hannu ta ɗauki maficinta dake daf da ita saboda ana yanayi na yawan ɗaukewar wuta musamman idan aka fara ruwa komai kaɗan ɗin su, da an ɗauke ita kuma sai ta shiga fifitu ba za'a tada inji ba sai in dare ne, cewa take yi rayuwa a ringa yi ana dubawa kashe kashen kuɗi ya zama a kan kowani motsi sai a ringa kashe kuɗi ba'a ɗan daidaitawa, bayan rayuwar ta yi tsada.
Jefa masa maficin ta yi dan ya ɗaga da sauri ya yi gaba da gudu yana dariya, ta ɗan ɗaga murya ta ce" Ja'iri, idan ka tashi tafiya asibitin ka zo ka ɗauki abincin su , ni ba zan samu zuwa ba yau." Da to ya amsa da ɗan ƙarfi shima ya tafi ɗakin sa dan ya dan huta kafin ya fita.
*Washe Gari*
Ƙarfe goma sha biyu kenan take daf da cikewa, wanda cikar ta ke neman zuwa da sake fita Yusrah a hayyacinta, sanadiyar irin kukan da Safwan ke yi mata, da ƙyar ta samu Iya ta bashi pain killer har zafin da yake kukan yana ji ya ɗauke, har ya yi shiru da kukan amma kuma mita bai daina ba har sai da magariba ta tardo su, Iya ta sake bashi wani maganin barci ya kwashe shi sannan Yusrah ta samu ta fito ta nufi wajen da ta tabbata zata samu Sakina, sai dai zuwanta biyu aka sanar mata Sakina bata nan a dole ta koma ta sake ɗaura wata alwallah ta haye salayya bayan ta sake shan wani kokon domin ƙarfi da yaji koko ya zama abincinta dan bata iya tauna komai, kokon kansa idan tana sha tamkar magani take ci haka take ji, ga kuma abinci ba laifi ana kawo musu daga gida.
Sallah ta yi, tana gamawa ta yi ta addu'a tana kaiwa Allah kukanta har dare ya tsala sosai da sosai ta silale a hankali ta kwanta hawaye na bin kumatunta, gaba ɗaya idan tace zata yi tunanin inda kuɗi zai fito mata ƙwaƙwalwarta ke dakatar da ita a kan bata da wata hanya, bata ajiye ba, bata ba wani ajiya ba, iyayenta basu yi rayuwar ajiye kuɗi wajen wani ba balle ta je tace a bata, bata da wata hanyar da ta wuce komawa wajen docter, dan haka ta samu ƙarfin yin barcin dan ta samu abinda zata faɗa masa ta tabbata zai yarda ai in sha Allah.
*LAHADI*
Wajen ƙarfe goma na safe da ya kama kwanan su uku yau da faruwar wannan lamari ta nufi office ɗin Docter kanta tsaye dan ta tabbata yanzu ya zo harma ya gama ganin mararsa lafiyan da yake gani.
Tunda ta nemi izinin shiga gabanta ke dokawa, sai dai ta sani ne ba gudu ba ja da baya zata fuskance shi a yau, sai da ya ga dama dan kansa sannan ya bata damar shigowa.
Tunda ta shigo yake bin suturar jikinta da kallo, kayan nan tunda aka kawota da su sune dai a jikinta, ta yiwu ko wanka bata yi balle ta cenza ... yake ayyanawa a cikin zuciyarsa.
A sanyaye ta dawo ta zauna a kujerar da ya nuna mata kanta a ƙasa muryarta a matuƙar sanyaye ta ce" Yallaɓai, na dawo kan batun jinyar ƙanina ne..." Ta ɗaga a hankali tana kallonsa, muryarta a sanyaye sosai ta ce" Ka min alfarma, ka taimakeni, a bashi dukkan kular da ta dace, idan yaso sai na maka aiki adadin lokacin da zai biya kuɗin kashe kashen da aka yi mana, wallahi ba zan shiga hurumin kai da kawon asibitinka ba, bakina inda aka ajiyeni in
yi aikina har in gama wa'adin lokacin da ka ɗaukar min."
Ta ajiye maganar tana sauka a kan ƙafafuwanta ta haɗe hannayenta ta ce" Dan girman Allah ka min rai, bani da hanyar kuɗin nan a yanzu, a yi masa dukkan abinda ya dace."
Kai ya ɗauke daga fuskarta dake matuƙar birge shi a rayuwa ya juyar da fuskarsa gefe ransa na ɓaci da naci irin nata da kafiya, wannan yarinya bai san wace irin yarinya ce ba, duk irin abinda take ciki kenan ba zata sauko ta ji sanyi ba? Lalle.
Miƙewa ya yi ya ɗauki agogonsa yana ɗaurawa ya ce" Loook Yusrah, ki yi haƙuri kawai, kin san ai babu kalar ma'aikatan da bani da su a nan, zuwanki nan aiki ke na taimakawa ba wai dan na rasa mai min bane, ba zan shiga hurumin asusun asibiti ba gaskiya, ki je kawai ki ɗauki ƙaninki ki kai shi wata asibitin, ni ina da tafiya a gabana tashi ki tafi kawai."
A firgice ta zuba masa ido, ya yi kicin kicin da fuska tamkar zai kifa mata mari, dan sassaucin da take gani a fuskarsa wasu lokutan ma yanzu ya ɗinke tsaf babu komai, gaba ɗaya