Showing 381001 words to 384000 words out of 397328 words
haka kuma da kan ta ta shiga kasuwa ta yo wa Yusrah siyayya irin su zogale, makani (gwaza), masara da sauran kaya irin dai wanda ta san da wuya mai ciki ta ce a'a, ai ko Yusrah har da ƴar ƙwalla an mata kyautar abinda ta jima tana marari, musamman ma masara da take so ta ga ta gasa ta ci, wannan ma bai wani birge shi ba sai dai bai hanata ci ba.
Abinda ya saka shi saukowa shine, wani ɗan kasuwa ne yake neman auren Goggon, sai kuwa ta murje fuska ta ce ai ya je ya nemi auren ta wajen ɗan ta, idan ya amince ita ma ta amince, in ko bai amince ba to ma'assalam, AA na gidan shi aka ce ana masa sallama, da ya fita ya kuma ji uzurin mutumin ba ƙaramin suman tsaye ya yi ba, ya tambaye shi Goggo fa? Ya tabbatar masa e, ya sake tambaya ita ta ce ya zo? Ya kuwa ce e, take kawai ya yi murmushi ya ce wa mutumin ba laifi zasuyi shawara sai ya neme shi, nan sukayi musayan lamba ya dawo ciki, wajen Yusrah ya karɓi lambar Goggon ya danna mata kira, ita ma dake bata da lambar bata san waye ba ta ɗaga tana sallama, saida ya amsa ne ta gane wa ye.
Da irin dai kunyar nan dukan su yace _"Ammm... Dama wai dan nace ne, ɗazu nayi baƙo, amma ban bashi ba, na ce sai nayi shawara, ina fata ban yi laifi ba?"_
Da jin daɗin kiran da ya mata Goggo tace _" Au, ya zo kenan? Ba wani laifi da ka yi, ai kaine wakilin uwar taka."_
Ƴar dariya ya yi yana gyara zaman shi da kyau saboda Yusrah dake tahowa, yasan da ta zo kuma a jikin shi za ta yi masauki ko ta ajiye masa farantin hannun ta akan cinyoyi tunda ta riga dai ta gama raina shi, ba tare da ya daina murmushin ba yace _" Ni jikan Anza, a sassauta min na fara aurar da ƙannan mana, kuma ni da za'a ji ta tawa ma da saurayi na samowa uwata."_
Dariya ta yi ita ma ta amsa da _" Kaii! Kar ka so kan ka dayawa mana, tsohuwa dani me zan yi da saurayi yanzu? A'a gaskiya ban shirya sake dawowa gaban *Annarmu* yin zawarci ba, so nake idan na tafi na tafi kenan."_
Wani sahihin murmushi ya yi na jin daɗin yadda ta kira Anna sannan yace _" *Momma* da gaske zan iya samo miki saurayi, amma ban san girman son da kike ma wanda ya zo ba, zan bincika ko shi wa ye, idan na gamsu da halayen shi zan amince masa, hakan ya yi?"_
Amsawa ta yi da _" Ya yi *ɗan Tidin*, sai mun ji sakamakon."_
Daga haka sukayi sallama, inda ya dinga duban wayar tashi yana jin wani shaƙat haka a zuciyar shi kamar ba shi ba wata damuwa dai ta gidan duniya, inda ɗaya hannun shi ke shafa tun daga ƙirjin Yusrah har zuwa kan cikin ta da tubarkallah ya shiga wata na huɗu ya turo riga, wannan shine mafarin shiryawar shi da Goggo sannan komai ya wuce kamar ba'a yi shi ba, yanzu haka idan ya shigo gidan Goggo na nan Anna ta ga ko ta ji suna wasu zancen sai ta bisu da kallo kawai, mamakin yaushe suka fara haka ke kamata? Ƙasan zuciyar ta kuma farin ciki ne kamar zai sumar da ita, da ta sanarwa da Aba sai ya yi murmushi kawai yace "Ba abinda ban sani ba tsakanin su, ban taɓa magana bane saboda nasan wannan ranar za ta zo, ko shakka babu Aswan na hushi da ita ne saboda yadda take ɗaukar ki, idan nace zan mishi magana akan ya daina nasan zai bari, amma kuma na tauye shi saboda ke kika haife shi, dole ya so ki fiye da yadda zai so ni ma, ita kuma ai ba yarinya bace da zan zauna na ce mata ta dinga girmama ki, a gidan ki take zaune, dan haka na sani ne ko bayan raina dole akwai wani abu da zai ɗinke ɓarakar da ta shiga tsakanin ku, wannan shine dalilina na zuba muku idanuwa dukan ku, abu ɗaya da na sani shine Aswan bai isa ya rainata a gabana ba ko bayan idanuna, haka kuma ita ma bata isa ta miki rashin kunya a bayan idanuwana ba bare gabana, duk kuma wanda ya yi ƙoƙarin yin haka sai na saɓa masa, faƙat."
Da wannan ne gidan su yanzu farin ciki ya sake yalwata, dan Nabihat kan ta dake zaune gidan yanzu kunya ma ce ke hanata rawar gaban hantsi, gashi ba damar ta koma gidan su dan Maman ta yi take kamar za ta kashe ta, duk wani motsin ta haushin shi take ji, har ta fi jin sauƙi ma daga wajen Chef dan shi kam ya ɗauki duniya ne kasuwa, ka ci ka wuce kawai.
Yusrah ma rainon cikin ta take yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk da ta koma aikin ta wanda ya ƙara mata kyau da haiba, amma kular da take samu daga wajen mijin ta ya sa take cikin ƙoshin lafiya a kowane lokaci, ga zirga zirga da take ƙara yi mata yawa yanzun na bukukuwan nan dake ƙaratowa, amma kuma a haka idan ta je ta dawo yake bata kulawar sa dake sakata dawowa hayyacin ta, shiyasa kullum jikin ta ke yin gaba ba baya ba, kullum fara'ar ta ke ƙaruwa, nutsuwar ta ke bunƙasa, soyayyar ta ga mijin ta ke nunkuwa sau ninkin ba ninki.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕??❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*97*
Matsaloli sun gama mamaye rayuwar Goggo, a yanzu ciwo sosai ya gama danneta na damuwa da tashin hankali, a kwanakin da suka shuɗe da faruwar wannan fitina ta matsuguni ya zamo babu kalar ciwon da bai nemi kawo mata farmaki ba, sai dai ikon Allah mutuwar ita ta ƙi ziyartarta kamar yadda ta ringa fata a jiya da aunty Khadija ta dawo mata jina jina ta sha kuka har ta gode Allah a bakin masallacin da suka samu suka raɓe suke rayuwa ta sanar mata sun je wajen sarakuwarta saboda su roƙi alfarmar ta bada dama ta kai su gidanta ita da mijinta domin mijinta ya amince ɗari bisa ɗari har ya nuna yana iya komawa gidan abokinsa dake kusa wanda bai yi aure ba har a ga yadda hali ya bada ya kama musu haya su zauna, tashin farko ta nuna bafa zai yiwu ba, ba zai yiwu a kawo mace da ƴaƴa a jibge a gida shi ya koma zaure ba, kuma maganar kama gida ma gaskiya ba wannan maganar saboda samunsa ba wani bane kuma abubuwa da yawa a kansa, dan kuwa shine ke ciyar da su su ɗin ma da kuma kuɗin hayarsu, ƙarshe ma a gabanta ta nuna masa in dai ya ce zai zagaye yayi bata yafe ba, su dukansu hankalinsu ya tashi sosai, aunty Khadija ta yi ta kuka yana bata haƙuri da faɗin in sha Allah zai san yadda yayi ya rarrashi mamansa, sai dai ita da kanta ta san ba wannan maganar mahaifiyarsa magana ɗaya take yi kuma bata dawowa kan maganarta ko waye kai dole zaka yi biyayya, a daddafe ta kwaɗa masu kwaki ta nufi inda suke zuciyarta cike da ɗacin rashin madafa.
Goggo ta mayar da kai ta soke, duk irin jikin nan na Goggo gaba ɗaya ya tafi ta zabge ta yi wata irin rama na tashin hankali, kuka ba dare ba rana shi take yi, abubuwan ne da suka tashi zuwan mata bata yi zato ko tsammani ba, sun diro mata ta inda bata taɓa tunani ba, an kawo mata kuɗin ta million ɗaya an kore su daga gidan nan sun fito suna neman agaji maƙota na ji suna gani suka ƙi tallafa musu, ko da yake ita a lokacin da ta zauna wa ta tallafawa? Wa ta duba? Wa ta zauna lafiya da shi? Wa ta ragawa? Wa ta tausayawa? Waye ya zo neman taimako ta masa magana mai daɗi balle har a kai ga taimakawa? Ko abinda take siyarwa ka zo siya iya kuɗin ka iya shagalinka, bata san gyara ko ta ba almajirai ba, idan tukunya nawa zata ɗora almajirai ba zasu samu siɗin tukunya ba, tun suna naci da bara a gidanta da kansu suka ba kansu lafiya suke zagaye gidanta su nema a maƙota, Goggo bata san in an yi maka haihuwa, rasuwa ko zaka aurar da ɗa ta yi maka dan ihsani ba, idan ma ta je ɗin ai da kyau, mijinta da kishiyarta ne kawai suka san wannan, takan yiwa kanta taken babu abinda zai kaita gidan talaka yi masa hidima dan kuwa ta san da ba ranar da zaya rama mata, takan ce da kuɗin ta babu wanda zai wahalar da ita, babu wanda zata jira ya bata, takan ce ai mai kuɗi ya fi ƙarfin talaka, ita ce ake cewa Hajia Hinda kowa katan, wato ta yagaka baya ce mata komai, ta wulaƙanta ka baya ce mata komai, a kan kuɗi kuwa ko wanene kai sai ta wulaƙanta ka.
Wannan dalili ya sa ko da aka kore su daga gidan nan tun da kwanaki kaɗan maƙotanta suka rufo ƙofa, duk inda aunty Khadija ta je ta roƙi alfarma sai a kawo mata da jajen rayuwa a nuna mata ba'a da wannan dama sai maigidan ya zo, masu gidan kuwa kamar haɗin baki babu wanda ya bi ta kan zancen, to aka kai inda ta je ta yada zango? Daf da masalaci ne cikin wata yar rumfar mai tuyar masa, da farko sam ƙiyawa matar ta yi sai da liman ya roƙi alfarmar nan bayan aunty Khadija ta roƙe shi sannan matar ta barsu, shi da kansa abin dan ya fi na rai ɗaya ne ya kasa ɗauka, domin shi ma talaka ne, bashi da shi sai wanda Allah ya aiko, haka kuma matansa babu wacce ke ga maciji da Goggo, har gida ta taɓa zuwa ta ci musu mutunci ta zazzage su tass, ya tabbata idan ya kaita gidansa da ƴaƴanta dan a taimaka mata sai dai ya ɗaukarwa kansa wani zunubi daban, gwara a nan ɗin duk abinda Allah ya hore masa na taimakawa zai taimaketa da shi abinda ya shafi abinci ko gidan sauro dai da sauransu, ya zamo Goggo ba cen ba nan sai ikon Allah, domin kuɗin nan aunty Khadija na faman a kama haya nemansu aka yi aka rasa, sama ko kasa ba'a gansu ba, har Safiya ta tuhuma ita kuwa ta murje ido ta ce bata san zance ba kuɗi bata gansu ba a dole suka zubawa sarautar Allah ido suke duban rayuwa, ga ciwon auta ƙafa idan aka ɗagata sai an kakkaɓe tsutsa, yaron ya rame ya rame sosai, ciwonsa ya fi komai ɗagawa Goggo hankali, ta yi kuka ta yi kuka ta gode Allah, ta rasa inda zata saka ranta, idan ta yi kiran uncle Sulaiman tun tana shiga har ta fasa shiga, sam bata shiga, Safiya kuwa wani lokacin tafiyarta take yi ta kwana wani wajen da basu sani ba, sai da safe ta zo ta zauna nesa da su tana haɗe rai cike da jin haushin kowa.
Nisawa Aunty Khadi ta yi tana duban Goggo murya a shaƙe sosai ta ce" Mama, zamanku a nan bashi da anfani, gashi mai masa jiya ta ce min ita fa a bata waje saboda sana'arta na son ja baya, cewa ake yi in an zo siya wari wajen ke yi, kar haka ya sa ta rasa masu siyan masarta bayan da ita take rufawa kanta asiri tana ciyar da ƴaƴanta, ina tsoron ta zo rana tsaka ta kore mu a wajen nan Mama."
Goggo ta sake sauke ajiyar zuciyar dake ratsa ƙahon zuciyarta, domin duk idan ta zo kwanciya zuciyarta ke tokarewa ta ce bata san zancen ba, ita da kanta ta san zuciyarta a kumbure take a irin wannan lokacin, ƙwarai ta san zuciyarta ba lafiya sai dai bata da yadda zata yi.
Murya na rawa sosai ta ce" To idan muka fita daga nan ina zamu je Khadija? Ai in muka fita daga rumfar nan shikenan sai dai mu ringa kwana a titi Khadija, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un."
Ta ƙarashe tana jan yagaggen hijabinta ta rufe fuskarta ta saka kuka mai tsananin gaske, aunty Khadi ta sadda kai ita ma hawayen wani na korar wani, tana tunanin ya ya zata yi? Gaba ɗaya kuɗin sana'arta babu ta ɓatar saboda buƙatun su Goggo, a yanzu mijinta ne ke nemowa ya bata na abincin da zata kawo musu da kuma abin hawa domin suna da nisa sosai da juna, ta buga ta buga amma sai a hankali, kowa yana ta kansa jama'a rayuwa ta yi zafi, da ƙyar ta samu rancen ƴan kuɗaɗen da ba zasu yi mata maganin matsalar ba, su ɗin ma da ta kai auta asibiti da su ko ganin likita basu isa ba aka kuma tsoratata cewar ƙafarsa fa ta lalace, wannan abu shi ya gigitata ya zamo ta ƙara tsorata da rayuwa, duniya kenan, wani yare ne bata anfani da shi dan ta ganar da mahaifiyarta? Sai dai Goggo macece mai sakin baki, tunda ta buɗi baki ta ja maganar da ta tsoratata cewar in ta kuma shiga zata tsine mata sai ta yi gum take faɗawa Allah ya shirya tun kafin a je gare shi.
"Me zai hana a je wajen Yusrah?" Muryar Safiya ta sa suka ɗago gaba ɗayan su suna kallonta, aunty ta langwaɓar da kai tana girgiza kanta a hankali ta ce" Safiya, yanzu idan aka ce a je wajen Yusrah ke sai ki je? Da wace ƙafar, da kuma wani idon? Da wani yaren za'a jewa Yusrah ace mata me? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, rayuwa kenan, shi yasa ko me zaka yi ka ringa tuna cewar wanda ya yika na sama yana kallon ka, ko dan kanka da kanka sai ka kiyaye wasu abubuwan domin shi sarki ne mai gaskiya, yanzu Safiya a je a cewa wacce aka kora aka zaga, aka wulakanta, aka zalunta a kan dukiyarta a lokacin da ta fi buƙata ta fi buƙatar taimakon nan, bata zo ta ce a yi mata kyauta ba, ta roƙi a bata a nata, aka kawo nata ɗin aka raba aka bata rabi, sannan aka koreta, wacce ta rasa uwa, uba, ƴar uwa aka ƙyamaceta aka wulaƙantata, a barta ta kwana ma aka ƙi yi mata wannan alfarmar sai duniya ta je suka amsheta, yanzu a je ace mata me? Anya kuwa bayan shiga uku da muka yi har ba mun ƙara shiga ukun ba? Ai ido ba mugu bane ya san kunya." Aunty khadi ta ƙarashe tana ɗauke kanta ranta na son ɓacewa.
Safiya ta ce" Aunty, ai hannunka baya ruɓewa ka cire ka yar, Yusrah a yanzu tana iya riƙe anguwar nan ba wai iya mu ƴan uwanta da Goggon ta ba, bayan wannan ita Goggon nata da ta wulaƙanta ta ai sai su yi tsakaninsu amma ki duba ki ga ƙafarsa, ita ce ke warin nan fa, ki duba ki gani fa, in kuwa kina da wata hanyar bi to sai ki bi, ni dai zuwa yanzu na gama gane cewar in ba ita ɗin ba babu wani da ya rage mana a duniya, babanmu ba'a san inda yayi ba, uncle Sulaiman ya saka mu a black list, ni na fita na buga na buga wallahi babu, dan nan da kika ganni babu hanyar da ban bi ba gaskiya sai dai a baka ƴan kuɗaɗen da basu kai suka kawo ba in aka gama da kai, gaskiya a je ɗin ya fi."
Aunty Khadi ta zuba mata ido a tsorace tana kallonta, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, kenan in ta fita abinda take zuwa ta yi kenan? Wayyo Allah sun shiga uku sun lalace, Goggo ta ɗago muryarta na rawa sosai ta ce" Khadija, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri Khadija, kin ji? Na san duk halin da muke ciki nice sanadi, na ɗauki *WATA TAFIYA* na ɗorawa kaina mai nisan gaske bayan bani da tabbacin me gobe zata kaya, Khadija ki taimakeni ki rufa min asiri idan kina da kuɗin adaidaitar ki kaini in nemi yafiyar yarinyar nan, na tabbata shigata tashin hankalin nan haƙƙnta ne, wallahi ni ba ma dan ta bani wani abin ba, da kunya in nemi wani abu a wajen wacce ni na hana mata nawa na kuma ci nata da ƙarfi dan ina ganin na fi ƙarfin ta bata da yadda zata yi da ni, mu je ki kaini in roƙi yafiyarta dan Allah Khadi kin ji?"
Aunty Khadija ta rasa yaya zata yi, a dole ta nemi adaidaita ta tsayar ta ɗauki auta bayan ta naɗe masa ƙafar