Showing 348001 words to 351000 words out of 397328 words
ta ta ya yi cike da tausayawa, sai kuma ya kama hannun nata ya jawota a hankali kamar baya son motsa ta yar ta zauna... Sai dai bata san zaman ba daɗi bane a gareta a wannan lokacin, take ta yi baya za ta koma ta kwanta a rashin bazatan haka zata ji zafi tare da ƙamƙame hannayen shi ta rintse idanuwanta ta furta "Washhhhhhh!"
Da sauri ya jawota jikin shi ya rumgume bai barta ta koma ta kwanta ba, bayanta ya dinga shafawa a hankali a hankali murya ƙasa ƙasa kamar mai raɗa yana cewa "Sorry, sorry baby, ki gafarceni kin ji? Ban san ba haka ake yi ba, gashi...na raunata ki fa."
Duk da ba fuskar ta yake kallo ba amma haka ta saki murmushin ƙarfin hali numfashin ta na fita sama sama tace "Ba...komai fa *my*..., damahh an ce mana haka yake fa...ruwahhh, kar ka damu, na ji daɗi da...ban..., ruwa, taimaka min da ruwa."
Da sauri ya miƙe ya fita yaje ya ɗauko mata ruwan a fridge ya dawo ya kawo mata, da kanshi ya buɗe mata ya kafa mata a baki tasha sannan ya rufe ya aje, kallon fuskarta ya yi da duk ta jeme yace" Na kiran Annan ne???"
Girgiza kai ta yi tace" Um um, kar ka min haka, zan iya na faɗa maka."
Yunƙurawa ta sake yi a karo na biyu ya yi azamar taimaka mata, sanin ta na likita da kuma shekarun ta ma ya sa sai ita ce take faɗa masa abinda take da buƙata yana kuma kawo mata, har ruwan ɗumi saida ya kawo mata sannan ta saka liquide toilet na bagaruwa da na kanunfari da duk Anna ta tanadar mata su a toilet ɗin sannan ta shiga ta zauna, riƙeta ya yi ta zauna sosai a hankali a hankali har ta daidaita cikin ruwan.
Da ya ga dai tana daddafawa tana yin komai da kanta sai kawai ya fito ya shiga gyaran gadon da kan shi yana yi yana murmushi tare da hasko komai da ya faru a saman gadon nasu mai matuƙar daraja, tana fitowa sanye da rigar wanka ta nufi wajen kayan ta ɓangaren kayan ta na bacci, shi kuma ya ɗauke wannan zanin gadon ya shiga da shi ban ɗakin, rigar bacci ta saka marar nauyi iya guiwoyin ta ta shafa turare, a daddafe ta dawo kan gadon kawai ta yi kwance dan duk abinda ta yi ƙarfin hali ta yi dama, zanin rufar ta jawo ta rufe duka jikin ta dan da gaske zazzaɓi take ji na son rufe ta ga kuma sanyin acn da take jin ya mata yawa yau, iya kanta kaɗai ta bari a buɗe ta lumshe idanun ta wani bacci mai ni'ima na son fizgar ta duk da tana jin motsin shi irin dai wankin zanin gadon yake yi, amma wallahi ba za ta iya yin komai ba a yanzun nan sai dai ko zuwa da rana ko yamma.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
03/07/2024, 20:37 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*88*
Da ya same ta kwancen nan saida ya ji tsoron ko dai ba lafiya ba? Amma da ya taɓa jikin ta ya ji zafi ne sai ya kawo mata magani tasha sannan ta sake komawa ta kwanta, ba jimawa bacci ya yi gaba da ita shi kuma ya kwanta gefen ta yana kallon ta da tunanuka fal a ran shi, musamman ma akan auren sa da Nabihat da har ga Allah sam ba ya jin abun a zuciyar shi, yanzu kuma sai yake tunanin anya zai iya jarumtar haɗata da wata mace a duniyar nan ma? Anya zai iya ɗaukar rigimar ta kuwa? Anya zai iya jurar ganin damuwar ta bare har ta kai ga zubar hawayen ta? Anya zai iya kuwa shi Aswan? Dan ya jima da fahimtar Yusrah ta masa illar da ya ɗauki shekaru yana guje ma, ta gama shigar masa hanci tunda har yanzu yakan iya haɗa tunanin ta da na wasu sabgogin sa masu mahimmanci, hasalima wani sa'ilin yakan sako damuwar ta ne a gaba da muhimman abubuwan shi.
Da wannan ya musu oder abinci, bayan an kawo ya tashi ya karɓo ya biya sannan ya shirya wajen cin abincin da kanshi, saida aka fara kiran sallah ya tashe ta shima ya nufi masallaci, ko da ya dawo ya same ta tana aunawa kanta zazzaɓi da ya sake rufeta ruf a lokacin, zaune ya yi ya zuba mata idanu yana kallo yayi tagumi yace "Oh ni jikan Anza, matar jikan Anza hala dai na ɓarkaki dayawa?"
Ɗan murmushin yaƙe ta yi ta girgiza kai alamar a'a a sanyaye tace "Kawai dai yanayi ne."
"Da rashin sabo kuma ko?" Ya faɗa yana tsareta da idanu, gyaɗa kai ta yi alamar e sannan ta mayar da abun awon cikin akwatin ujilar sannan ta ɗauko allura ta fara haɗawa, ɗan waro idanu ya yi yace "Allura za ki yi?"
A hankali ta amsa da "Um, idan ba haka na zafin ba zai sauka ba."
Da kulawa sosai yace "Allura fa? To kinga ki yi min ni, nasan za ki samu sauƙin."
Kallon shi tayi tana murmushi tace "Ta ya ya kenan?"
Saida ya sumbaci kumcin ta sannan yace "Sai na sake tittila miki ruwan jikina mana, kinga maganin zai riske ki."
Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi ta ci gaba da haɗa allurar, tana gamawa ta saka doguwar roba ta ɗaure damtsen ta sosai dan tayi saurin samun jijiya, tana samu ta daidaita allurar tana fara sokata cikin jikin ta saita runtse idanu ta ɗan ɗora kanta a kafaɗar shi har saida ta gama sannan ta cire tsinin allurar ta jefar a saman akwatin ujilar ta sake shigewa jikin shi tana sauke numfashi... Shi kan shi idanun shi a rufe suke tunda ya ga za ta soka tsinin saida ya ji sautin jefa allurar da tayi sannan ya buɗe idanun shi ya kalle ta, ko da ta lafe a jikin shi ya ƙara rumgume ta yana shafa ta, kamata ya yi suka fito falo ya zaunar da ita kan kujera sannan ya ɗauko abincin nan ya aje, gyarawa ya yi ya fara bata da kanshi a baki tana karɓa a hankali ba dan yana mata daɗi ba.
*Haka* wunin bayin Allahn nan ya kasance, ya zama duk wani motsi nata AA yana kula da shi ne tamkar wanda aka bashi assingment akan ta, idan ta motsa kuwa ƙa'ida ne ta kan tambaye ta ya dai? Me take so? Har yanzu da ciwo ne? Bayan sallah la'asar kuma sai ya kasance mai sake sosa mata ciwon da ya ji mata, dan salo iya salo ya dinga yi mata da yasa ta manta da raɗaɗin dake jikin ta, har saida ta kai dan kanta tana tambayar kanta _"Dama haka Aswan yake? Dama ba iya kaushi da tsaurarawa da bala'i kaɗai ya iya ba? Har tarairaya ma ya iya da tausasawa? Amma me ya sa su Manal ke masa gurguwar fahimta haka?"_
Ita kam a wannan wunin za ta iya cewa gaskiya babu kamar mijin ta, dan ya nuna mata asalin wa ye shi a zahiri da baɗini, ya nuna mata shi babban ƙwaro ne ta kowane ɓangare na rayuwa, ya nuna mata shi ɗin *uban gidan ta* ne kuma *jarumin ta* wanda za ta kasance mai alfahari da shi har ƙarshen rayuwar ta.
*ANZA MENSION*
Murmushi Abrar ta yi tana kallon motar mahaifiyar ta har ta ƙarasa wajen ajiyar su, da fara'a ta kalli Mukhtar da yau ne ranar shi ta farko da ya zo gidan da sunan zance wajen ta tace "Akhi, ga Momma nan ta dawo."
Murmushin ƙarfin hali ya saki yana sake kafe motar ta da kallo, a ranshi kawai yake ayyana lallai fa ya ɗebo ruwan dafa kan shi, matar nan cikin siyasa take tsundum, bugu da ƙari ƙanwa ga Elhaj Aliyu Anza, dole kam kaga motar ta kamar tana magana idan tana tafiya, amma Alhamdulillah yana da arzikin shi daidai gwargwado, duk da ba lallai ne ta karɓe shi saboda yasan mata ce da son nuna ita wata ce da son fantamawa da arzikin ta, ba zai sare ba ko ya ji tsoron haɗuwa da ita saboda yana son Abrar, ba kuma zai bari ta raba shi da ita cikin sauƙi ba.
Miƙewa sukayi shi da Abrar suka tunkare ta tana tahowa dan shiga falo ba ta ko kula da inda suke zaune ba, saida suka tareta ne shi ya durƙusa dan gaishe ta ta amsa ba yabo ba fallasa, Abrar kuma ta kwantar da kanta a kafaɗar ta cikin shagwaɓa tace "Momma, ga Yaya Mukhtar, dama ya zo ya gaishe ki ne."
Kallon shi ta yi daga sama har ƙasa, shigar shi, surar shi, haibar shi da cikar zati duk bata ga makusa ba, amma saboda bata son harkar ɓata lokaci nan take ta yatsina fuska tace "Mukhtar ko?"
Ɗan ɗaga kai ya yi yana amsawa da "Hakane Hajia."
Ɗan taɓe baki tayi tace "Mukhtar, wa ye mahaifin ka? Sannan a ina ka ke? Kuma wane aiki ka ke yi?"
Murmushin ƙarfin hali ya saki tare da sadda kai da girmamawa yace "Mukhtar Abbakar, kuma ni ɗan garin nan, lauya ne ni, ina kula da harkokin mutane da dama sannan yanzu haka ina aiki da banki wajen kula da harkar shiga da fitar kuɗin da suka bayar bashi, kuma akwai wasu harkokin ma da muke taɓawa ni da mahaifina."
Gaba ɗaya ta ma fuskar ta irin yanayin gajiya da jin zancen nashi, to amma tunda ba wata makusa tare da shi, kuma ita ba burin ta bane dama mijin da Abrar za ta aura ya zama shahararren mai kuɗi, saboda ta gama sakankancewa kuɗin da take samu ita kanta ai aiki za ta ba kanta idan ta ce sai Abrar ta samo mijin da ya kere ta a kuɗi bare kuma a zo ga taƙadarin nan AA ko uban shi, abu ne marar yiwuwa, kuma ta ga shi kan shi Yayan nata ai ba ya tsayawa zaɓe wajen aurar da yaran sa, tunda Mubarak bai kai yadda yake yanzu ba sanda ya aura masa Intisar, amma yanzu gashi nan yana ta ƙara haɓaka shi ma.
Irin a barikancen nan ta dubi Abrar ta ɗan tallabo haɓar ta tace "Baby, kina son shi ne?"
Kunya ce ta saka Abrar rufe fuska tace "Kai Momma..." Sai kuma ta juya da niyyar shigewa ta bar su, riƙe hannunta tayi tana murmushi tace "Come on baby, ki bani amsa mana, idan kina son shi ban da matsala da haka ni, zan sanar da dangin mahaifin ki ne kawai, idan kuma ba kya so, yanzu zan wa tufkar hanci."
Ƙara dawowa ta yi jikin ta ta lafe tayi shiru, ƙyaran kallon ta take yi daga nan tace" Uhum! Kina son shi?"
Jawo ɗan yalolon gyalen maman ta yi tace" To mama ni kunyar amsa miki nake."
Ƴar dariya ta yi sannan ta kalli Mukhtar da har lokacin yake durƙushe yana ta shafa kai da murmushin jin daɗin Abrar bata ce a'a ba tace masa" *Ɗan lele*, ka yi farin ciki babyna tana son ka, dan haka zan fara yi wa manya maganar, duk yadda mukayi za ka ji daga gare ta ko kuma ni da kaina, ka fahimta?"
Da jin daɗi ya amsa yana ta mata addu'a, Abrar kuma turo baki tayi a shagwaɓe tace" Momma, ɗan lele kuma?"
Kallon ta tayi tace" Yes my baby, alƙawari ne nayi idan kika kawo min mijin da ba Aswan ba dama, to zan so shi na kuma ƙaunace shi kamar dai ke, dan haka daga yau ɗan lelena ne."
"Momma." Abrar ta faɗa, juyawa ta yi za ta wuce ciki tana amsa sai anjimar da Mukhtar yake mata, Abrar na kallon shi ta ga ya zuba mata idanun shi kamar zai haɗe, xike da kunya tace "Ya dai?"
Sai kuma ya ɗan harareta yace "Wato ma hassada kike min saboda belle mere ɗita ta saka min suna kuma ta ce za ta ƙaunace ni?"
Ajiyar zuciya Abrar ta sauke cikin gurguwar hausar ta tace "Ko kaɗan Akhi, fatana bai wuce Momma ta so ka kuma ta fahimci girman ka a zuciyata ba, da zan iya ƙara maka daraja da kima a idanun ta to da nayi hakan, saboda ita ce duniyata, kai kuma mai daɗaɗa wannan duniyar tawa, idan ba'a samu fahimta tsakanin ku ba kamar yadda ba sa jituwa da Akhi AA, ban san ina zan saka kaina ba, dan haka na fi ka farin ciki, kawai dai ina mata burgar nan ne."
Dariya ya yi da jin daɗin hakan daga bakin ta sannan suka juya dan komawa mazaunin su yana faɗin" Ki bani labari, me ya kawo rashin jituwa tsakanin belle mere da wannan ɗan iskan?"
" Akhin?" Ta faɗa tana zaro idanu, harara ya cilla mata yace" A gare ki ba, ni ai aminina ne."
Jinjina kai tayi da zolayar nan tace" Idan fa ya hanaka aurena?"
Da sauri yace" Kar ki fara buzuwata, kar ki fara nuna masa za ki bi umarnin sa, idan ba haka ba zan shiga uku a gurin shi, yanzu dai na janye kalmar tawa a kan shi to, bani labarin?"
Numfashi ta sauke tace" Gaskiya ban san komai ba, dan ko da na girma haka na gan su ba sa ga maciji, ban san me ya sa ba? Na tambayi Momma ta ce kawai ya rainata ne, shi kuma Akhi ina tsoron sa ba zan iya tambayar sa ba."
Jinjina kai ya yi yace" Kar ki damu, zan masa maganar sannan na shirya tsakanin su in sha Allah, wannan alƙawarina ne a gare ki, dan ba zan yarda yana babban abokina ba kuma yana gaba da sarakuwata ba."
A tausashe tace" Gaskiya da naji daɗi idan ka yi haka Akhi." Da haka suka ƙarasa kan kujerun su suka ci gaba da hirar su cikin nishaɗi da ƙaunar juna.
*Falo* ma dai wani bidirin ake sha sakamakon kiran da uncle Sulaiman ya ma wayar Manal, Nawal da neman rigima ta fizgo wayar tana son nunawa Anna tana cewa" Anna duba? Dubi ki gani uncle Sul ne yake kiran ta, amma da anyi magana sai ta ce ba komai."
Rai ɓace Manal ta figi wayar ta tana yanke kiran ta zabga mata harara tace" Ina ruwan ki to? Nawal bana son shishigi wallahi, zan zubar miki da haƙoran gaba."
Da halin ko in kula Nawal tace" Na ji dai, wallahi Anna soyayya suke yi a ɓoye ita da uncle Sul, baki ga tun yana nan ba sai ya yi ta kiran..."
A tsawace Anna tace mata" Ina ruwan ki wai Nawal? Bana son shiga abinda bai shafeka ba fa, ke ma ki je kiyi soyayyar mana, wa ya hana ki?"
Zama Manal ta yi kan kujera tana cewa" Ƙarya ma take Anna, ni ba komai tsakanina da shi, me ma zan yi da tsohon nan?"
Kallon sama da ƙasa Anna ta mata, sai kawai ta yi murmushi irin na babba da yaron nan tace" Sulaiman ɗin ne tsoho? Tsaran jikan Anza ne fa, kenan dai mun cuci Yusrah da muka haɗa ta da shi?"
Turo baki ta yi tace" Ni dai ban ce ba Anna, amma ni bana wani soyayya da shi, duk samarina?"
Jinjina kai Anna ta yi tana satar kallon ta tace" To, ko ma dai menene ki hutar da kan ki, shi fa yana da mata da aka masa kamu tun kafin ya bar ƙasar nan, yanzu ma dai ina ga bai wuce ɗan kankani lokaci ya rage ba a dai yadda ya faɗa mana, kinga kenan shi ma ba abinda zai yi da ke."
Kallon Anna ta yi, irin kallon nan na ban gane ba amma kuma ba ta ce komai ba, sai Nawal ce ta gyara zama tace" Haba dai, kenan Anna shima ya kusa yin aure?"
" In sha Allah, nan da ina ga bai fi wata huɗu zuwa uku ba, ai har hoton yarinyar ya nuna mana a zuwan shi na farko gidan nan, shiyasa Aban ku ai ya ɗauki nauyin gyaran gidan sa, kuma kinga an kusa kammalawa." Anna ta yi maganar tana ta satar kallon Manal dake ta wani damƙe wayar ta a hannu tana jujjuya ta sai maƙoshin dake shafe sumul ke yin ƙasa da sama, miƙewa Nawal ta yi tana faɗin" Bari na ɗauko wayata na kira uncle Sul ɗin na masa tijara, ya manta ni ce babbar aminiyar sa da bai faɗa min ba ko me?"
Ɗakin su ta nufa tana faɗin" Jama'a kowa sai aure yake, ga bikin Maryam ma ya zo daf shi ma, ga komen da aunty Fatila za ta yi gidan mijin ta jibi, ga sis Abrar can yau ta gayyato Yaya Mukhtar dan su gaisa da Goggo, da fa ta amince shikenan ita ma za ta fara ƙamshin amarci."
Zabura Manal ta yi ta bi bayan ta da sauri, suna zuwa kan matakala bata gama hayewa ba ta riƙeta a rikice tace" My half, please je ki tambaya min