Showing 369001 words to 372000 words out of 397328 words

Chapter 124 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70101

fasa, kin ga ki yi nesa dani dan ina iya ɗaukan mummunan mataki a kanki, mutane dama gayyarki ne ai, sai ki watsa, ina ji ina gani ba zan cuci yaron da nake yiwa kallon ɗan cikina ba, bari ki ji da ace za'a koma baya da na fasa aurenki nima dan kuwa babu abinda aurenki ya haddasa min sai taɓarɓarewar tarbiyyar ƴaƴan da kika haifa da cikinki, ke sai in rasa wace riba to kike son ci a duniya? A yanzu na kula ke ba ma wannan ne a gabanki ba, tana da manema ai ki tistiyeta tabbas tana da manema."

Daga haka ya kama hannun Aswan da yayi mutuwar tsaye suka juya suka nufi mota, Nabihat kuwa ta ringa zunduma ihu uwar na rufe mata baki ta jata ƙiiiii suka yi falon gidan ta ringa kifa mata mari tana kuka tana faɗi " Sai da na miki faɗan wannan wautar, sai da nace ki tabbatar da an sauke vidion nan da sunanki, sai da na faɗa maki su waye mijin da zaki aura da kuma wanda yake ubanki, amma kika ƙi yarda, faɗa min uban waye saurayin naki ko in matse maki wuya in yi kason ki?"

Nabihat na kuka kanta na juyawa cikinta na hautsinewa da neman yin amai, ƙanen ta na ƙoƙarin riƙe mamansu aman nan ya kubce mata, ta duƙa tana sheƙawa a nan tana kuka, da ƙyar ta iya faɗin" Mama Imran ne, Imran ne ƙanin mijin aunty Intisar."

Da uwar da ƙanen nata duka ɗif suka yi suna kallonta, mai bi mata yace" Wai dama da gaske soyayyar kike yi? Soyayyar ma da Imran? Imran ɗin nan dai na gidan su Mubarak? Lalle ke kam kin wulaƙanta mu, yanzu ke da kike da AA a hannun ki kika wulaƙanta kan ki? Mama in dai Imran ne ai ki binciketa kawai dan gaskiya ɗan hayahaya ne, mayen ɗan nanaye ne, shi fa baya soyayyar aure, ya yi auren ya ajiye a gida saboda mamansa yake cewa, cewa yake yi yanzu kuma love yake ci, ni kam ba ruwana."

Jikin uwar ya sake ɗaukan rawa ta nufi Nabihat ɗin zata maƙureta ta tambaye ta, Nabihat ta miƙe da gudu ta rufta sama tana zaro ido juwa na kwasarta tana faɗin" Wayyo! Na shiga uku yau asiri ya gama tonuwa ina zan saka kaina, na shiga uku."

Da gudu gudu ita ma ta bi bayan ta bata kuma zame ko ina ba sai ɗakin Nabihat ɗin wacce ta kile shi, bubbugawa ta shiga yi a haukace tana faɗin "Za ki buɗe min ƙofar ko in kira mahaifin ki ya ɓalla min ita? Kinga ki rufawa kan ki asiri ki buɗe ɗakin nan, Nabihat kar ki kaini bango fa."

Nabihat na ihu da kururuwar kar ta mata komai ga jirin dake ta kwasar ta kamar zai kifar ta taso ta buɗe ƙofar, hankali tashe maman ta maida ƙofar ta rufe tana ƙare mata kallo, sai kuma ta fizgi hannun ta suka ƙarasa gaban gado ta zaunar da Nabihat ɗin a kausashe tace "Dan uban ki faɗa min gaskiya, kin dai ji an ce shi... Uban wa ye ma sunan shi? Ɗan iska ne na gaske ko? Gaya min yaushe kuka haɗu da shi?"

Nabihat ta yi tsuru tsuru da idanu tana dafe kanta da hannu biyu tace "Mama ba'a jima ba fa, ko wata bamuyi ba har yanzu."

Da kakkausan kallo na harara ta sake hayayyaƙo mata tace "Kun taɓa haɗuwa ne? Kuma ya taɓa taɓa jikin ki?"

Nan ma wurƙil tayi da idanu ba ta bata amsa ba, saida ta daka mata wata tsawa tare da kashe fuskar ta da mari tace "Za ki buɗa baki ki min magana ko sai na halakaki? Dan kutumar uban ki baki san abinda ke tunkaro mu bane daga ni har ke? Auren ki fa ya dakatar, idan har ya zauna kan bakan shi ina zamu saka ran mu? Ki faɗa min gaskiya dan nasan ta inda zan ɓullowa lamarin?"

Cikin matsanancin kuka Nabihat na matsar ciki da kuma murzar idanu tace" Sau...sau kaɗan ne Mama, wallahi kaɗan ne."

"Kaɗan ɗin uban ki, kaɗan ne me? Ya taɓa ki ko kuka haɗu?" Ta faɗa tana sake dangware mata kai, a rikice Nabihat tace "Muka haɗu Mama."

Dafe ƙirji ta yi ta ɗan rusuno kusa da fuskar Nabihat ɗin tace "Ya miki lalata? Ya taɓa jikin ki ne kuma?"

Da rashin gaskiya Nabihat ta ɗaga kai alamar e, hakan ya sa maman rabka salati da salallami tana tafa hannaye har tana juyawa, sai dai take wani tashin hankalin ya ƙara ziyartar ta sa'ilin da Chef ya banko ɗakin ya shigo, yadda duk suka dube shi rashin gaskiyar su ta sake bayyana sosai, dan babu wacce ba ta yi tunanin ya ji wannan magana ba.

Saida ya ƙare musu mummunan kallo sannan ya kalli Nabihat yace "Yadda kika sa aka wa baiwar Allah ba ta ji ba bata gani ba, to ki sani kema idan jibin ta zo cikin masu gadina zan samu ɗaya na haɗa ki da shi, idan ya so in an ɗaura auren ki gudu ki shiga duniya ko ki zauna, ke kuma..."

Ya faɗa yana kallon Maman ta yace" Ki samu ki lallaɓata ki bata shawara ta ma zauna a gidan ta, dan ko ta shiga duniyar ba da kyau za ta gani ba, idan kuma kika kuskura kika sake min hauka, wallahi ba ni ba ke har abada."

Zai juya ya fita kenan Nabihat ta fashe da wani irin kuka ta yi gaggawar riƙo ƙafafun shi ta jimƙe gam gam tana cewa" Na tuba Aba, dan girman Allah kar ka bayar dani sadaka, wallahi Aba zan maka biyayya amma kar kayi sadaka dani, Aba Imran yana sona sosai nima kuma ina son sa, dan Allah ka kira shi sai kuyi magana ka aura masa ni, Aba na tuba dan Allah ka yi haƙuri..."

Fizge ƙafafun shi yake yi amma ta riƙe gam ta ƙi saki, wannan surutan tayi ta yi da har suka saka Chef yin jim tare da tunanin girman soyayyar da take wa Imran ɗin ne ta kai har ta kasa yin kawaici da kunya a gaban su take faɗin irin wannan maganganun? Ko kuma dai tashin hankalin da take ciki ne? Idan kuwa haka...Maman ta ce ta katse mata tunani bayan ta marairaice ta fuskance shi tace "Alhaji, dan Allah ka tausaya mana, duk abin nan da ya faru har da rashin zaunawa a tattauna, Alhaji kar ka dakatar da auren ta dan Allah, ka yi haƙuri ka yafe mana, tunda shima Aswan ɗin ai ya ce k..."

Kallon ta ya yi shima ya katse ta da cewa "Aswan fa kike magana a kai? Ai na faɗa muku ko bayan raina bai isa ya aure ta ba, wallahi id..."

Cikin matsanancin kuka da fitar hayyaci Nabihat tace "Aba ni na yarda ma idan ba zan auri Aswan ɗin ba, ni dama yanzu ba son sa nake yi ba na fi son Imr..."

Da wani irin takaici maman ta ta buge mata baki da ƙarfi, wanda hakan ya sa ta ƙwala ihu tare da sakin ƙafafun Chef ta rufe bakin ta, wani murmushin takaici Chef ya yi yana sauraron maman ta na masifar" Shashashar banza, ke in baki auri Aswan a duniya ba ai ban ga anfanin zuwan ki duniyar nan ba, burin da muka ci tare da alwashi kike so ki rusa mana? Imran ɗin banza da wofi, wa ye uban sa? Me yake da shi me ya tar..."

Ita kanta bata hayyacin nata shiyasa har ta dinga wannan maganganun, sai da ta kusa kai aya ta tuna da Chef na gaban su ashe, shiyasa ya yi murmushi yana kallon ta yace" Niyyar ku ce ba mai kyau ba tun farko, shiyasa Allah ya tseratar da shi daga kaidin uwa da ƴar ta, na kuma tabbata wacce ya samu yanzu ita ce alkairin sa, shiyasa Allah ya bashi... Hmmmm! Allah ya kyauta."

Kallon Nabihat ya yi yace" Imran ne ko wanene? Ba ruwana da harkar shi in gaya miki, idan shi kike so ba zan hanaki auren shi ba in har ya nema a wajena, dan nayi alƙawari ba zan sake hana ɗa da abinda yake so ba bare har ta kai ga na kore shi, na rufe wannan aƙidar har abada da izinin Allah."

Yana gama faɗin haka ya fice ya bar musu ɗakin cike da tashin hankalin rasa madafa, Maman Nabihat kuma tsugunnawa ta yi gaban ta ta zuba tagumi tana matso ƙwallar da bata ma san na me ye take yi ba.


*AA MENSION*



Da wannan gurɓataccen yanayin na halayen ƙaramar yarinyar da suka girgiza shi ya shigo gidan wacce da take daf da zama matar sa, duk da yana halin jin salama a zuciyar sa na kuɓuta daga auren ta da ya yi, amma hakan bai hana shi shiga damuwa da tunanin kuma ya su Aba za su ɗauki lamarin?

Ya so ya ganta tun a falo ne ta tarbe shi da fara'ar ta, kwalliyar ta da kuma ƙamshin jikin ta dake saka masa nutsuwa a kowane lokaci, sai dai bai san me ya sa bai same ta a falon ba duba da zuwa wannan lokaci ta jima da gama abincin ranar ta sai dai ta kasance mai jiran shi, amma saboda yau da gobe sai Allah sai ya fara zarcewa madafar tunda ya san ba masu aiki gare ta ba, masu taya ta gyaran gida ne suma da sun kammala suke tafiya sai kuma washe gari, yana shiga madafar daga bakin ƙofa ma ya juyo ya fito dan bata nan, dan haka kai tsaye ya nufi ɗakin ta.

Yana tura ƙofar bayan ya buɗe digital ɗin tsaf idanun shi suka sauka akan ta a ƙasan lallausan carfet kwance duk ta takure wuri ɗaya gashi ta lulluɓe cikin hijabin da yake kyautata zaton sallah ta yi da shi dan shima har ƙasa yake sosai.

A tunanin shi bahagon yanayin nata ne ya sauko da za ta yi ta takura kanta, idan ya tambaya kuma ta ce ba komai ya sauko mata, haka dai ya dake ya ƙarasa yana ɗan yin sallama akan laɓɓan shi, shiru ba ta amsa ba kuma bata motsa ba kamar dai mai bacci, yana zuwa bai yi ƙasa a guiwa ba ya zauna ƙasan shi ma ya tanƙwashe ƙafafun shi sannan ya fara kiciniyar buɗa fuskar ta da hijabin.

Hakan ya tashe ta a bacci marar kan gadon da ya ɗauke ta mai daɗin gaske ta ɗago kan ta, suna haɗa idanu ta ɗan mitsika idanun ta muryar ta da alamar bacci tace "Wai, wai har ka dawo? Sannu da zuwa."

Ba yabo ba fallasa ya amsa mata da "Me ye haka? Ki ta kwanci a ƙasa salon sanyi ya kama ki?"

Yunƙurawa ta fara yi dan ta tashi zaune tana mai cije leɓen ta cike da dauriyar ciwon kan da take ji mai tsanani tana faɗin "Ban san baccin ya ɗaukeni bane..."

Ta yi maganar ne shi kuma ya shiga taimaka mata wajen tashi zaunen tare da yaye mata hijabin yana faɗin "Ba kya jin zafi ne? Kuma ma ko ac ba k..."

Maganar sa ce ta katse saboda jin zafi a jikin ta da ya saka gaban shi yankewa ya faɗi tare da ƙura mata idanu kamar ta yi laifi, da sauri ya gyara mata zamanta ya ɗauko ta cimak ya ɗora saman ƙafafun shi yana ci gaba da taɓa wuyan ta da goshin ta yace" Jaanu, baki da lafiya ne? Jikin ki zafi sosai."

Langaɓar da kai ta yi ta ɗora saman ƙirjin shi ta yi shiru abun ta, tunanin maganar ta da Nawal take ɗazu a waya, wai anjima zasu kawo mata ɗinkin da Anna ta sa a mata wanda ya dace ta saka ranar da za'a kawo amarya, duk da ba gida ɗaya bane amma da yiwuwar za su haɗu da amarya a daren ko dan shi ya musu nasiha matsayin sa na shugaban su, za ta iya cewa tun lokacin ne ta rikice ta rasa me ke mata daɗi, sai kuma ta ji jikin ta gaba ɗaya ya ƙiya irin dai yanayin marasa lafiya, ita kam idan har maganar nan ce ta kaita ga kwanciya haka ai ta jima da shiga uku, to a ya ya za ta yi rayuwa da abun nan kenan?

Wannan tunanin da take yi da kuma shafa jikin ta da yake yi yana sake tambayar ta "Ki min magana mana *mai ɗakina*, baki da lafiya ne? Taɓa jikin ki fa ki ji..."

Wata shasheka ta sauke saboda kawai sai ta ji zuciyar ta ta karye kukan kaɗai za ta yi ta samu sauƙi, tallaɓo haɓar ta ya yi da hannu yana kallon fuskar ta, ganin abinda ba ya so wato hawaye yasa ya gyara hannayen shi sosai akan fuskar ta ya tallabe yana faɗin "Please, please my lady ban da yanzu, lafiyar ki a yanzu ita ce gaba da komai a gareni, dan Allah faɗa min idan ba kya jin daɗi ne muke clinic? Please..."

Bai sani bane duk maganar da yake yi ƙara karyar da zuciyar ta take, dan haka yanzu ma da ta tsurawa fuskar sa idanu tana kallo, sai sheɗan ke ta hasko mata nan da rana irin ta yau ma har sun yi sabo fiye da haka da amaryar sa, zai zama ita ma yana kula da ita kamar dai haka, yana ririta ta tare da shagwaɓata, zai taɓa ko ina na jikin ta a sanda ya so a kuma lokacin da ya ga dama, sannan ita ma bata da shamaki da duk wani sassa na jikin shi, zai haɗa bakin shi da nata ya tsotsa kamar yadda yake yi mata, zai kafa bakin shi akan ƴan biyun ta yayi yadda yake so, daga ƙarshe wannan mijin nata mai ƙarfin dokin da har yanzu bata daina jigatuwa da zuwan shi ba indai ta fannin gado ne, mijin ta da kowane lokaci bai ƙi a ce yana kanta yana sukuwa ba, mijin da take alfahari da Allah ya bata shi saboda soyayyar da yake nuna mata zahiri da baɗini, mijin ta dai da ita dai a wajen ta babu ta inda ya ragu, sai kawai ta wayi gari da shi yana ɗakin watan ta ba ita ba. Ya Allah! Ina za ta kai wannan lamari mai girman gaske a rayuwar ta? Ta ya za ta fara jurar haka bare har ta saba da shi? Ta...

Kukan da ya sake kubce mata yasa ta ƙamƙame shi tana girgiza kai a cikin ƙirjin shi sai shiɗewa take neman yi, hankali tashe ya shiga daddaɓa bayan ta ya rumgume ta tsam a jikin shi ya shiga yi mata raɗa a kunne "Ki fitar, ki fitar da abinda yake ranki baby, idan ba haka ba za ki ci gaba da cutuwa, Yusrah ke ma kina sona ko? Kishi kike ji a zuciyar ki saboda zan yi wani auren? Idan hakane ki faɗi abinda kike ji a ran ki, sannan kar ki ɗaga min ƙafa ki min irin *dabancin* da kika min a waccen ranar a PG, zan ɗauka my lady, wallahi zan ɗauki duk haukan da zaki min, shin baki ga yadda na kawo ki gidan nan ba saboda kishin ki? Sannan yau ma na mari wani banza saboda ya kira min ke ƴar daba, alhalin ke *ƴar dabata* ce, ni kaɗai kike wa dabanci kuma ina son haka, dan Allah ki murmure ki min ko za ki saki ran ki, kin ji *mariƙiyar jikan Anza*."

Ya subhanallah! Ya Hayyu ya Qayyum! Hankalin ta a tashe yake, zuciyar ta a ɗugunzume take, amma wa Billahillazi maganganun shi suka sakata ɗago kanta daga ƙirjin shi tana mai gasgata tabbas idan yau ba ta faɗa masa ba to za ta mutu ne nan kusa, a ƙarshe ta barshi da wacce ba ta so ɗin su more soyayyar su, bayan kuma a yanzu dai kam ta sake yarda mai raba ta da bawan Allahn nan ɗan Aliyu jikan Haidar sai Allah wallahi.

Sai kawai ta ɗaga hannun ta na dama ta ɗan kashe fuskar shi da irin marin nan na zolaya da soyayya, saida ta jera masa haka har sau uku tana ƙara rushewa da kuka sannan ta yi ƙarfin halin buɗa bakin ta tana faɗin "In dama zan iya ne, da na kashe ka AA, bana so, wallahi bana so ko kaɗan, ka min rai, ka min rai Rohi kar ka haɗa min kan ka da kowace mace a duniya, ina...ina...in...amai...amai zan yi Roh..."

Ba ta gama faɗa ba ta jirkice daga saman jikin ta ta fara kwarara amai kamar ruwan sama, kusan duk abinda ta ci a wunin saida ta maido shi, hakan ya sa ya tausaya mata sosai tare da kamata suka shiga ban ɗaki ya cire mata kayan jikin ta, fanfon dake kawo ruwan zafi ya kunna mata ya tabbatar yadda jikin ta zai iya ɗauka ne sannan ya watsa mata a jikin ta, jim kaɗan suka fito ya saka mata doguwar riga da hijab sannan ya ce maza su wuce clinic a duba ta, ba ta masa musu ba tana biye da shi suka ɗauki hanya, kafin su isa kuwa jikin ta ya sake ɗaukan zafi sosai har suka isa.

Nurse Dr. Siddik ya sa ta duba ta har ta nemi kwantar da ita dan ta saka mata ƙarin ruwa, sai kuma Dr. Siddik ɗin ya tambaye ta ta mata awon ƙwaƙwaf na jini ko fitsari? Amsa ta bashi da "A'a Dr, na dai duba ƙarfin zazzaɓin ne da kuma silar zazzaɓi, kamar dai yanayi ko wani abun daban ya haifar mata da zazzaɓi."

Da kulawa sosai yace mata "Ki mata awon fitsari to, amarya ce, kinga kar a zo da shigar ciki ki mata traitement ɗin da ita ko abun cikin ta zai gaza ɗauka."

Da girmamawa ta amsa shi sannan ta dawo wajen Yusrah, fitsarin ta da ta buƙata ya sa gaban Yusrah faɗuwa da tambayar ta lafiya? Ta dai faɗa mata dr ne ya saka ta ita ma, bata sake mata gardama ba ta shiga ban ɗaki ta yi fitsari sannan ta fito ta kawo mata, abun awo babba ta saka da take yake nuna komai, ai kam kamar jira ake ta ga da shigar ciki a tare da ita na kusan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login