Showing 120001 words to 123000 words out of 397328 words

Chapter 41 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70111

matar nan ta bata ta jiya har yanzu bata taɓa sisi a ciki ba, ga wasu sun sake isketa a zaune ba cinikin kwabo, e lallai ma dole ta ɗaurexa Safiya wannan saurayi tamau yadda za ta ja shi kamar raƙumi da akala.

Haka sukayi sallama ya tafi ita ma ta shiga ciki tana mita da sababin wannan neman jaraba da ake ta ma wata Yusrah kamar ƴar gwal ya fara damun ta, yanzu haka kwana huɗu kenan ba ta ɗaukar kiran ƙanin nasu wato kawun su Yusrah saboda jarabar sa ta girmi shekarun ta, ita ce babba amma tsaf sai ya zageta yanzu nan akan ɓatan yaran, haka kawai ya dinga yi mata masifa a waya kamar ya haifeta saboda ta ce ba'a san ina suke ba ita da ƙanin ta, wai har wani nanatawa yake _"Ƴaƴan ɗan uwan nawa?"_ Kamar ita ba ƴaƴan ɗan uwan ta ba, koma menene ai Yusrah ita ta so haka ta kuma zaɓa, yanzu haka data gareta a waya ta sati da ta sa aka mata, amma wallahi saboda tsoron Suleiman sam ta ƙi buɗawa ta yi harkokin gaban ta, kai tuni ma ta fara tunanin canza layi dan kar ta ga lambar shi. Ko da yake jiya Baban Safiya na ce mata sun yi waya har yana ce masa wai yana nan shigowa sati na sama in sha Allah, to ya zo mana, ai dai ba dukan ta zai yi ba, ita masifar sa ce ta fatar baki bata iya wa wallahi, dan duk faɗan ta ya dame ta ya shanye tsaf, shiyasa take tausayawa wacce zai aura nan gaba. Dan Iya Abu ma ƙaramar matsala ce, haka ita ma ta zo gidan nan wai tana neman Yusrah, kwana biyu ta yi gidan ta kafin ta nuna mata ba fa wanda zai ce ga inda Yusrah take, dan haka zai fi ta tafi idan an ji labarin ta sai ta sanar da ita, ba dan ranta ya so ba ta tafi amma ita bata damu ba, dan gaskiya ba zatayi ta zama mata a gida ba akan wacce ba'a san yaushe kuma ina za'a ganta ba.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*32*




Tun daga farfajiyar gidan ya gane Goggon sa na nan saboda motar da ta ɗebo ake kuma tuƙa ta a ciki saboda alfahari, bai yi mamaki dan ya san yadda take sakin jiki tayi hira da uncle Hamat da matar sa bata yi da iyayen sa haka, to ita ma dai matar uncle Hamat ɗin ba wani faran faran bane suke da juna, tun wata rana da ya zane babbar ƴar ta akan idanun ta saboda yarinyar tana wa mai yi musu wanki rashin kunya, to fa shi dai tun daga ranar ya ga ko haɗuwa sukayi sai ta haɗe fuska kawai suyi gaisuwar ƴan mota, sai shi ma ya yi gefe da ita yake ci gaba da harkokin sa, dan ba ƴar ta ba wallahi ko ita tayi abinda bai masa ba sai ya zaneta tunda gaba yake da ita a shekaru.

Yana nan zaune cikin motar ƙafar sa ɗaya waje uncle Hamat ɗin ya fito daga cikin gidan, yana kusan ƙarasowa saboda girmamawa da ƙaunar uncle ɗin nasa ya fito gaba ɗayan sa yana murmushi, shi ma da murmushin ya ƙaraso yana buɗe hannayen shi alamar rumgumar juna zasuyi yace "My son, har ka iso? Ya kuma baka shiga ciki ba?"

Murmushi dai ya yi har suka ɗan rumgumi junan su uncle Hamat ya bubbuga bayan AA ɗin, bai bashi amsa ba gaskiya dan ba zai iya ce masa kallon raini ne baya so daga matan nan guda biyu da ya tabbata suna ciki, gaisawa sukayi daga nan tsaye kafin uncle Hamat ɗin ya kama hannun shi yace "Mu shiga ciki to?"

Baya so ya mishi gardama, dan haka ya bi bayan nashi suka nufi ƙofar da za ta sada su da falon uncle ɗin, acan suka zauna kuma ba laifi sun taɓa hira sosai kusan minti talatin kafin ya mishi sallama dan daga nan asibitin su yake so ya je ya ga ko Mani dreba ya dawo? Daga nan kuma ya yi sallah magriba ya sake komawa wajen ɗan sa su yi ta farin cikin su.

Rako shi ya yi suna tunkarar motar AA ɗin aka yi oda alamar za'a shigo, da sauri mai gadi ya buɗe ƙofa wata jibgegiyar mota irin mai numfashin nan ta shigo cikin gidan, kallo ɗaya AA ya ma motar ya ɗauke kai bai sake duban ta ba, amma fa a wannan kallo ɗayan ya gane wanda ke cikin motar, Muntari Buza ne, kuma saida ya girgiza a sirrance da ganin ya shigo gidan uncle ɗin sa kai tsaye haka, sai ya shiga tunanin to me ya kawo shi? Me ye wai tsakanin su haka? Wace alaƙa ce ta haɗa su bayan auren Goggon sa da aka faɗa masa yana nema?

Haka ya shiga motar shi bayan sun yi sallama da uncle ɗin ya rufe motar amma ta madubin gaba yana kallon yadda Sani dreban uncle ya buɗewa Buza ƙofar mota ya fito sai fadanci yake masa, haka kuma ya ga uncle ɗin yana tunkarar sa da fara'a a fuskar shi alamar dai e suna ganewa juna kuma ma ya san da zuwan sa ko? Da wannan tunanin ya bar gidan ya je asibiti, amma abun haushi shine wai har yanzu Mani bai dawo ba, tafiya ce ya ce zasuyi mai tsawo amma ba mai nisa ba, kuma tare da oga ya ce, ma'ana *uncle Hamat*, to ga uncle ɗin a gida shi kuma yana ina? Me jimawar ta sa take nufi ne?

Haka ya ciro wayar sa tun a hanya yana kiran lambar Mani amma shiru bata shiga, da takaicin nan har ya isa asibiti wajen Safwan ya samu Anna sun fito ita da Nawal zasu tafi gida, da mamaki yace da su "Amma Anna ya akayi kuka jima haka? Kuma daga ku sai dreba fa."

Murmushi ta yi tace "Wallahi tsayawa nayi jiran Intisar da ta ce mana za ta zo duba ɗan naka, sai yanzu Mubarak ɗin ya kira yake sanar dani wai yanzu ma ya ɗaukota daga clinic ƙarin ruwa aka mata ita ma ba ta jin daɗi."

Da kulawa sosai yace "Subhanallah! Me ya same ta?"

Saida Anna ta kalli Nawal dake ta sunkuyar da kai da ladabi a gaban shi kafin tace "E, ina ga zazzaɓi ne."

Jinjina kai ya yi yace "Allah ya bata lafiya, zan kira in sha Allah na mata sannu."

Anna ma jinjina kai ta yi tace "Hakan na da kyau, mun wuce mu saida safe."

Murmushi ya yi yace "Sai na shigo dai Anna."

Murmushi ita ma ta yi ta amsa da to sannan suka shige mota suka bar asibitin, shi ma kuma ciki ya shiga yana neman lambar Intisar ɗin.

*Ba* Intisar ba hatta Mubarak da ya miƙo mata wayar saida ya nutsu, uwa uba ita da ta sake gyara zama ta yi gyaran murya tun kafin ta ɗaga kiran kamar wacce ke tsoron yi masa laifi, ɗaga wayar tayi tana faɗin "Assalama alaika Akhi?"

Daga inda AA yake ya yi wani murmushin rainin hankali saboda ya san fa suna kiran shi da AA ko Chairman wani lokaci ma Oga, amma wai a bayan idanun sa suke faɗa har Humed ma, amsa sallamar ya yi suka gaisa sosai kafin ya tambayi jikin ta, da jin daɗin kulawar sa gare ta ta amsa da "Jiki Alhamdulillah Akhi, ai na ma ji sauƙi sosai, in sha Allah ina so ko zuwa gobe na zo naga yaron mu."

Murmushi ya yi kamar suna gaban juna ya amsa da "Ki bari har jikin ki ya yi yau, my boy kuma gashi na baki ku gaisa a waya, idan kin warware da kyau kin zo."

Da fara'a tace "To shikenan Akhi, a bani shi ɗin."

Miƙawa Safwan wayar ya yi yana masa raɗa da "Auntyn ka ce, ita ma ƙanwata ce."

Sallama Safwan ya yi tare da ɗorawa da "Ina wuni aunty?"

Da kulawa sosai ta amsa da "Lafiya lau boy, ya jikin ka?"

Amsa mata ya yi kafin su ɗan gaisa ya miƙawa AA wayar, yana karɓa shi ma ya mata sallama da cewa ta gaida yaran da kuma ɗorawa da "Ina mijin ki? Yana lafiya?"

Kallon Yaya Mubarak ta yi daya tsareta da idanu tace "Lafiyar sa ƙalau Akhi, gashi nan ma."

Cike da tsare gida yace "Ki gaishe shi." Daga haka ya kashe wayar Intisar kuma ta sauke ajiyar zuciya tana aje wayar, kallon Yaya Mubarak ta sake yi tace "Yana gaishe ka."

Da fara'a yace "Ya kamata fa naje na kwashi gaisuwa wajen Yaya Chairman tun kafin a sakani baƙin jadawali."

Murmushi ta yi tana gyara zaman ta tare da jingina a kujera ta lumshe idanu dan ta samu damar yin tunanin abinda za ta ci wanda ko babu shi zai siyo mata kamar yadda suke hirae kafin kiran AA ya katse su.



*YUSRAH*



Suna shiga Maryam murya a karye ainun ta ce" Yusrah."

Yusrah ta juyo ta zuba mata ido, bata san me zata iya cewa da Maryam ba, bata san in har zasu iya yin maganar nan a yanzu ba, abu ɗaya dai ya ɗan tsayeamata a rai a lokacin da ta je gidan su Maryam ƙwarai ta so ace mahaifiyarta ta je asibiti, balle da ta ga yanayin da take ciki, amma shi ma ba zata yi mata maganar ba, gwara ta yi shiru tunda bata je dan kanta ba ai ba abin cewa kuma, gaba ɗaya kwanakin nan da ta yi a killace tare da Hajia wani neman jin haushin kowa take yi da ya yi sake a lamarinta, a lamarin Safwan ɗin ta, hum! Rayuwa kenan, dama haka ne in Allah ya tsaga maka zaka tashi daga mai kowa zuwa wanda bashi da kowa.

"Dan Allah ki min magana, ki yi haƙuri." Maryam ta sake faɗa tana haɗe hannayenta.

Yusrah ta ce" Na haƙura."

Daga haka ta nufi bayi ta kwaɓe ta shiga wanka, magariba ce ta sanyo kai dan haka ta ɗauro alwalarta, tana fitowa ta gansu saman sallaya dan haka ta ƙarasa jikinta a mace ta ciro doguwar riga ja mai ratsin baƙi ta saka ta saka pant ta ɗauki hijabinta ta zura ta tayar da sallar ita ma zuciyarta cike da tabbacin dabarar da ta yi wacce zata bata damar tafiya.

Suna gama sallah Maryam ta nuna tafiya zata yi, da sauri Yusrah ta ce" A'a, ki bari mu ci abinci mana sai mu raka ki."

Maryam ta nuna dare fa na yi, Fatila ita ma ta saka baki cewar dan Allah ta yi haƙuri su ci abinci sai su rakatan.

A dole ta haƙura bayan ta yi kiran mahaifiyarta ta tabbatar mata gatanan zuwa tana tare da Yusrah ɗin ne.

Bayan sun yi sallar isha'i da ƴan mintuna kafin a kawo abincin aka yi sallama da Fatila.

Fatila na fita Yusrah ta miƙe tace da Maryam su je ta rakata. Maryam ta kalleta shatakai cike da tunanin lafiyarta kuwa? Ta ce ta tsaya su ci abinci, kuma yanzu za'a kawo abincin basu ci ɗin ba ta ce ta tashi su je? Ba ta yi mata musu ba ta miƙe ɗin ta ce bata yiwa Hajia sallama ba.

Yusrah ta waiga ɓangaren ɗakin hajiyar ta ɗan sosa kai ta ce" Hajia bata fitowa da wuri idan ta yi sallar isha'i, in jiranta zaki yi kina iya kaiwa ƙarfe goma yau a gidan nan."

Maryam ta zaro ido ta ce" Kai? Mu je gobe zan yi kiran ki ki bani ita in sha Allah koda ban same ki ba sai in yi kiran Fatila da yake mun amshi numbar juna."

Yusrah ta gyara kanta, a nutse suka juya, har sun fita ta dawo ta ajiye farar takardar da ta rubuta ta rintse ido tana jin kamar bata kyauta ba, sai dai tuna cewar in fa ta zauna tabbas gaba za'a ji haushin juna balle irin yadda Hajia take da hawan jini, in Tasneem ta ɗaga mata hankali matar Jafar take, amma ita fa? Da wahala ta zo ta shiga layin masu ɗagawa Hajia hankali, ba zata taɓa iyawa ba.

Suna fitowa ta nunawa Fatila zata je rakiya, har Maryam na tsokanar Fatilar ita ma tana ɗan ramawa sannan suka fice a gidan.

Bayan sun fito a sanyaye Maryam ta dubi Yusrah ta ce" Besty, kin tabbata baki yi fushi da ni ba?"

Yusrah ta sakar mata ɓoyayyan murmushi ta ce" Ke dan Allah ki bari, fushin me wai? Kin ga ɗan sahu can mu tsallaka daga can mu tsayar."

Ai kam suka koma ɗayan gefen suka yi jira har ya zo suka tsayar, sun gama magana Maryam ta shiga suka kama hannun juna suka yiwa juna murmushi Maryam ta nuna mata alamun su yi waya, daga haka suka yi sallama mai adaidaita ya ja da Maryam ya tafi.

Ita ma mai adaidaitar ta so tsayarwa bayan ta tabbatarwa kanta asibiti zata je yanzun, sai dai me, tana duba jikinta babu kuɗi babu alamunsu, sai a lokacin ta tuna kuɗin ta suna ɗakin fatila cikin sif ajiye, tabbas dan takardun makarantar ta da katin ta da takardun gidan su tana sane ta baro su dan kar ta ɗauko abinda za'a gane ta, shiyasa ta taho da waya yadda za ta kira su idan hankali ya kwanta ko dan saboda takardun ta masu mahimmanci, amma kuɗin kam shaf ta manta da su saboda suna ɗakin Fatila ne ajiye.

Sai da kanta ya sara, domin daga ita sai wayar hannunta da hijabinta ta fito, ta juya ta kalli hanyar gidan ya fi a irga, ta tabbata zuwa yanzu ko da baƙon Fatila bai tafi ba yana daf da tafiya, idan ta koma ta yiwu ta tarda Fatila ta ga takardar nan, ko kuma ta tarda baƙon zai tafi, daga nan ta san ko me zata yi ba zata samu fita ita kaɗai ba.

Idanuwanta ta rintse cike da jin takaicin kanta, ta yiwu du wannan tafiyar da take yi tana komawa baya laifinta ne, ta yiwu ita ce bata komai a tsare yadda ya kamata, ta yiwu ita ce ke saka kanta a matsala, ta yiwu ɓatan Safwan laifinta ne ba na kowa ba! Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! A dole ta juya ta ɗauki hanyar da zata kaita asibiti, wacce ta tabbata ko da zata kwana a hanya yau sai ta je asibitin nan.

Ta koro da tafiya kusan minti goma sha biyar kiran Fatila ya ringa shigowa wayarta, sai da gabanta ya faɗi haka kuma tsoro ya kamata, nan da nan ta yanke shawarar canza hanya dan kar aje a biyo doguwar hanyar nan a ganta a hanya, a lokacin kuma an jima da gama sallah isha'i ya zamo jefi jefin samari kaɗai ka ke hangowa sai motoci da babura dake kai kawo.

Bayan ta shiga layin shi ma babban layi ne, saidai sosai a cen ƙarshen layin, haka kuma wajen baya rasa mutane jefi jefi, dan haka ta shiga tafiya bata jin gajiya ko kaɗan dan burinta ta je can yau ita da su sai dai a ga waye ya fi wani gaskiya domin ba zata karɓi uzurin kowa ba, docter kuwa dama nemansa take yi, a kan Safwan sai ta tsinke fuskarsa da mari ba ruwanta da shekarunsa.

Ta yi nisa da tafiyar kiran bai daina shigowa ba dan haka ta lalubo wayar dan ta kasheta domin ta kula Fatila ba zata daina kiranta ba.

Kashe wayar ta yi ta ɗago dan ta mayar da ita cikin hijabinta ta ɓoye, sai dai tana ɗagowa ta ga samari biyu sun sakata gaba suna kallo.

Gabanta ya sake faɗuwa da ƙarfin gaske, domin kallon tamkar na mahaukata haka suka sakata a gaba.

Da sauri ta so juyawa, sai dai ɗaya a cikinsu ya ciro wuƙa a jikinsa ya nuna mata ya ce" Ke, idan kika yarda kika gudu sai mun sassara ki yau in muka kama ki, ki rufawa kanki asiri ki biyo mu wancen lungun in ba haka ba abinda zamu maki ko uwarki ba zata shaida ki ba!"

Kana jin muryarsa zaka gane ya gama sha ta kai masa wajen da baya gane komai sai cutarwar, hankalin Yusrah ya yi mugun tashi, lokaci ɗaya hawaye ya ɓalle mata, tana ƙoƙarin haɗe hannayenta dan ta masu magiya ɗaya ya tankaɗa ƙetarta sai da ta yi tangal tangal ta duƙe dan hankaɗar da gasken gaske ya yi mata ita.

Tana ɗagowa bata tsaya wata wata ba ta ari na kare ta daɓa a guje tana ihun a taimaketa, basu tsaya wata wata ba suma suka mara mata baya domin anguwar Yusrah ita ce bata sani ba dama anguwa ce marar kyau, ƙwarai take da hatsari anguwar ko ga saurayi namiji balle ƴar budurwa, ɓata gari sun yi yawa a layin dan kuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login