Showing 147001 words to 150000 words out of 397328 words
anan kar ta tafi da ita, ita kan ta tana son zama da mu fa, ko Yusrah?"
Zuba ma Yusrah idanu aka yi har da aunty da ta tallabo haɓar ta tace" Kina so na tafi ba da ke ba Yusrah? Ba zaki bini ba kema?"
Kamar za ta fashe da kuka muryar ta na rawa tace" Aunty, ina so na zauna tare dake, saboda nasan idan ina tare dake kamar ina tare da Mamanmu ne, komai naku ɗaya ne da na mamanmu, sai dai a yanzu aunty ba zan iya tafiya ba tare da nasan ina Safwan yake ba? A wane hali yake ciki? Sun yi alƙawarin taimaka mana wajen tsaya mana ko da ma za'a nuna mana fin ƙarfi ne da rashin gata, ki bari mu ga Safwan kin ji aunty?"
Girgiza kai aunty Fureira ta yi tana ɗauke kai daga Yusrahn irin dai bata yarda ba ita gaskiya cikin taushin murya tace" Ta ya zan tafi na barki a hannun yara Yusrah? Dama Hajia ce ta dage akan sai na barki da zan iya barin naki."
Murmushi Yaya Mubarak ya yi haka ma Hajia da tace" Fureira, ai ba su kaɗai bane a gidan, ga mahaifiyar su su dukan su, na tabbata za ta kula ta kuma saka ido akan komai, in sha Allah nasan ba zata bari wani abu marar kyau ya faru ba, ki yarda dani, ni kaina ina so Yusrah ta zauna kusa dani, amma na ga rigimar wannan tafi ƙarfin kaina..."
Ta faɗa tana kallon Intisar tare da dorawa da" Wataƙila rigimar da biyu take yin ta, saboda ba ita kaɗai bace yanzu, kuma zan goyi da bayan a bata Yusrahn nan mu huta haka ma ɗana ya samu saukin rigimar shi ma."
Dariya kowa dake ɗakin ya yi musamman ma Yaya Mubarak da ya ma Intisar data sinne kai cike da kunya alamu na Hajia ta fahimce shi kenan? Amma aunty Fureira ita bata ga alamar Yusrah za ta samu kulawa daga wannan tsohuwar ba gaskiya, saboda fuskar ta ma babu annuri kamar na Hajia, sannan tun bayan gaisuwa bata saka bakin ta a maganar ba idan ba Goggo da ta kora ba, hakan ya nuna ita ma bata da haƙuri ko ta ce mai zafi ce.
Ɗaga kai Intisar ta yi tace "Aunty, idan ma kina jin kamar baki yarda damu bane, ga mijina sunan sa Mubarak Yusuf, ɗa ga margayi Alhaji Yusuf bagobiri, idan kika tambaya ko a cikin gari sananne ne, ni kuma sunana Intisar Aliyu Anza, mahaifina ma ba ɓoyayyen mutum bane, ina da ahali kamar dai haka ɗin nan, mahaifiya, ƙannai guda uku, Goggo, kawu, Yaya, ƴaƴa, duka, idan kina so aunty zaki iya tashi mu je gidan namu suma ki gan su ki tabbatar da abinda nake faɗa, dan Allah ki bamu Yusrah aunty, ita kanta tana buƙatar ta ga likita duba da tunda haɗarin ya faru bata lafiyar ta take yi ba sai ta ɗan uwan ta."
Nauyayyar ajiyar zuciya aunty Fureira ta sauke tana jin yanzu kam za ta iya barin su, Aliyu Anza? Tabbas ba a garin nan take ba, amma ta san shi sosai dan tana jin labarin shi, kuma mutumin ma dake neman kujerar shugaban ƙasar nan, yanzu kam za ta iya barin Yusrah, ko wani abu ya faru ta san waɗanda za ta nema, baya ga haka ma tabbas yanzu ta ji Safwan ba zai ɓoyu ba a doron duniyar nan face sun zaƙulo shi sun kuma hukunta wanda ya ɗauke shi ya ɗauki alhakin su.
*Saɓanin* Yusrah da ta ji kamar tashin hankali zai baibaye ta, Aliyu Anza? Elhaj Aliyu Anza dai da ta sani? Wanda ta fara stage a asibitin sa? Wanda kuma Safwan ya ɓace a asibitin sa saboda rashin imani na ma'aikatan asibitin? Sannan Yaya ga Dr. Hamat? Likitan da ko yanzu da za ta ganshi babu abinda zai hanata tsinke fuskar shi da mari? Kenan kawun Intisar ne? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Ya haka kenan? Me ke shirin faruwa kenan? Idan ɓatan Safwan da sa hannun Dr. Hamat, shin za su yarda su taimaka mata har ta nemo ɗan uwan ta? Me zai faru kenan idan ta zauna da su?
Muryar aunty Fureira ta katse mata tunani sa'ilin da tace "...
*_SAJEERAH_*??️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*39*
Muryar aunty Fureira ta katse mata tunani sa'ilin da tace "Shikenan, ya zan yi? Tunda kun fini yawa masu son ta zauna, ai sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi, ba damuwa, za ta iya zaunawa har Allah ya sa a ga Safwan, amma ke kuma..."
Ta yi maganar tana kallon Intisar da farin ciki ya gama mamayeta kamar ta ƙurma ihu dan daɗi, da sigar zolaya aunty tace" Kar fa idan aka ga autan nawa kuma ki ce za ki haɗa duka ki riƙe dan ba zan yarda kin ji na faɗa miki."
Dariya wasu sukayi har Intisar ɗin ma ta girgiza kai tace" Allah aunty ba zan miki ba, sai dai na yi ta addu'a Allah ya sa Yusrah ta samu miji anan ta yi aure, kinga dole zaki kawo mana ita garin nan da kan ki."
Dariya aunty ta yi tace" Wannan dai akwai rigimammiya ko?"
Sunkuyar da kai ta yi, sai a lokacin kaɗai Yaya Jafar yace" To Alhamdulillah, mun gode sosai aunty da kika bar mana Yusrah anan, ko da ba gidanmu za ta zauna ba kamar dai tana tare da mu ne, dan haka ina ga yanzu ai komai ya ƙare, sai kuma muyi fatan Allah ya sa a ga Safwan cikin ƙoshin lafiya."
Wani irin kallo Yusrah ta mishi, idan ana faɗin a ga Safwan sannan ana danganta Safwan da maganar lafiya, sai ta ji zuciyar ta na ƙoƙarin raya mata idan fa masu satar mutane ne? Anya Safwan ɗin ta yana raye? La'ilaha illalah! Nan aunty Fureira ta fara kiciniyar ciro wayar ta a jaka tana faɗin "Karɓi nan Yusrah, ki saka min lambar ki wacce da na kira zan same ki, tunda na samu jiya an gyara min wajen cajin wayar."
Da tsantsar birgewa Yaya Mubarak ya kalli aunty Fureira, ga ta dai ba wasu shekaru ne da ita sosai ba, amma a cike take da dattako da faɗan abu yadda ya zo. Alama ya ma Intisar ta matsa kusa da shi, ba su san me ya ce mata ba suka ga ta miƙe ta fita, Yusrah har ta saka ma aunty lambar an fara taɓa wata hirar, sai ga Imran ya sallamo falon sai lokacin ne zai fita ya shigo gaishe da mahaifiyar ta su, sosai ya gaisa da kowa duk da bai san su wa ye ba, kafin ya zauna ƙasa kusan ƙafafun Maman sukayi gaisuwa irin ta ɗa da uwa, nan ya kalleta yace "Mama baƙi mukayi ashe?"
Ba yabo ba fallasa Maman tace "Umm! Baƙi mukayi."
Shiru ba wanda ya sake cewa wani abu, shi dai har ya miƙe ya mata sallama da sauran mutanen ɗakin sannan ya fice, fitar sa ke da wuya Intisar ta dawo da wata leda a hannun ta haka mai ɗauke da kwali, Yaya Mubarak ɗin ta bata sai ya mata alama da ta ba aunty Fureira, dan haka ta ƙaraso kusan auntyn ta bata shi kuma Yaya Mubarak ɗin yace "Aunty, wannan sabuwar waya ce, ina ga kamata ya yi mu haɗaki da sabuwar wayar da kai tsaye zaku dinga magana ta WhatsApp da Yusrah, hakan zai sa hankalin ki kwanciya idan kina jin lafiyar ta a kai a kai, amma idan kira ne daga can zuwa nan wasu lokuta akwai matsala ta network."
Kallon shi aunty Fureira ta yi ta girgiza kai tace" A'a gaskiya, kar muyi haka da ku kuma, abun ai sai ya yi yawa, ga ɗan mutum da za'a riƙe maka ko da na kwana ɗaya ne bare ba wanda yasan adadin kwanakin, ga kuma wata ɗawainiya?"
Da wani irin kallon takaici Maman Mubarak kamar ta yi hira ta karɓe wayar ta ce to shikenan take kallon kwalin tana so ta ƙiyasta adadin girman wayar da kuɗin ta duk da bata da sani akan haka, Yaya Jafar ne yace" Aunty ai kawai ki karɓa, abinda na yi tunanin yi miki ne yanzu idan muka fita daga nan ya yi, dan haka ki karɓa kawai, kinga har Hajia ma da ita kan ta madame ɗin (Intisar) ai duk ya kamata ace yanzu kina da lambobin su."
"Gaskiya ne wannan." Cewar Aminu yana murmushi, haka aunty Fureira ta sa hannu biyu ta karɓa tana godiya sosai, Fatila ce ta karɓi wayar tana buɗewa ta ga tanfatsetsiyar waya ce babba mai rai da lafiya, ya siye ta ne saboda tunanin tafiya da take daf da samun shi, yana so ya ware wayar aiki da kuma ta ganawa da ahalin shi, to tunda an yi haka anjima idan ya fita ya siyi sabuwa kawai. Nan Fatila ta shiga saita ma aunty wayar da saka mata lambar Hajiar su har da ta Maman Mubarak duk da bata so haka ba ita, dan ba ita ta bayar da lambar ba ma Mubarak ɗin ne, sannan ta karɓi ta Intisar da kuma Yusrah. Daga nan zaman su ya ƙare inda Intisar ta ma aunty alƙawarin jibi idan za ta koma kamar yadda ta faɗa in sha Allah zasu je su mata sallama tare da Yusrah.
Suna nan farfajiya su Hajia har motar su ta fita a gidan Intisar ta kama hannun Yusrah zasu juya Bilal a fito daga ɓangaren shi cikin shirin fita yana ta baza ƙamshin turaren shi fucking fabulos, saida ya yi wani sororo daga tsaye sanda ya sauke idanun shi kan Yusrah...
Yana ƙarasowa Intisar ta ja hannun Yusrah dake ta sinne kai saboda kallon da yake mata tace "Muje ƙawata, wanda ya damu da ke ya same ki inda kike."
Da dai ya tabbatar ita ce ba mafarki ba, ai da sauri ya bi bayan su yana kiran aunty Intisar, harara Yaya Mubarak ya ƙwala masa yace "Marar mutumci, yaushe rabon da ka je inda take? Wato kai ka samu dahir tunda ka riƙe Goggon ta ko? To yanzu haka Goggon ta sallama ma duniya ita har abada."
Da mamaki yace "Yaya Mubarak kamar ya? Ban gane ba? Wai da gaske Yusrah ce? A ina kuka same ta? Yaushe ta zo gidan nan?"
Shi ma bai faɗa masa komai ba ya shige ya bar shi nan yana cewa "Sai ka je ka lallaɓa auntyn taka, idan ta ga dama ku shirya, idan ba ta so ba kuma ka ƙyale min babyta ta huta."
Tsaye suka barshi ya rasa me zai yi, sai kawai duk ya rufa musu baya shima zuwa ɓangaren nasu dan jin ya aka yi haka wai? Da ƙyar ya rarrashi Intisar ta sauko kafin ta faɗa masa duk abinda ya faru daga daren shekaran jiya da suka samu Yusrah zuwa yanzun nan, haba ai murna wajen Bilal ba kama hannun yaro, haka yake ta maimaita yanzu Yusrah ta zama ƴar gidan nan kenan? Ya so ganin ta amma Intisar ta ce ya haƙura ba yanzu ba, kar ya fara takura ta da shishigi hakan zai sa ta ƙi sakewa da kowa, amma ya bata lokaci nan da kwana biyu ta saki jikin ta.
*Ba* ƙaramar tirjiya Yusrah ta so yi ma Intisar ɗin ba da ta ce zasu je asibiti, haka take ta marairaicewa tana faɗin "Wallahi aunty Intisar lafiyata ƙalau, babu abinda nake ji a jikina."
Ita kuma sai ta girgiza kai tace "Ban yarda dake ba Yusrah, mutum ce fa kema, duk wanda ya shiga yanayin da kika shiga a ƙasa da sati uku Yusrah dole a same shi marar lafiya, kawai dai baki fahimci haka bane ko ba kya so ki faɗa."
Yaya Mubarak ne ya tuƙa su har wata babbar Clinic ta wani cousin ɗin shi kula abokin shi, nan suka sanar da shi duk gwaje gwajen da suke so a yi mata, ai kam Yusrah ta ga sarautar Allah, tun daga tafin ƙafar ta zuwa kan yatsar ta na hannu, da ƙoƙon kan ta zuwa duk wani sassa na jikin ta saida aka ɗauke shi a na'ura aka duba, kafin aka shiga tattaɓa jikin ta dan a gano ko da inda ke mata ciwo, wani wurin ma har wani ɗan abu mai kamar katako ake sakawa ana bubbuga jikin ta, kai dai ta ga sarautar Allah.
Bata taɓa yarda zasuyi nasara ba, sai da nurse ɗin dake mammatsa jikin ta ta danna bayan ta sai ta ji ta ɗan zabura haka, take likitan dake tsaye yana kula da yanayin ta ya fahimci haka ya sake ba wa nurse ɗin umarnin ta ƙara danna bayan ta. Ashe dai ciwo ne danƙare a bayan Yusrah, dan tun nurse ɗin na dannawa a hankali har ta fara saka mata ƙarfi, daga bayan ta zuwa wajen ƙugun ta ciwo ne da ya jiya yana buƙatar a duba amma bai samu wannan gatan ba, sai yanzu da ake taɓawa ya riga ya yi tsami sai ga Yusrah na sharar hawaye, dan haka aka sake duba bayan nata zuwa kumkumi.
Nan ya tabbatar musu da ta bugu ne a bayan nata, sannan ya rubuta manyan maguna take Yaya Mubarak ya siyo su anan Pharmacie dake kusa ya kawo sannan aka nuna musu yadda za ta sha, daga haka suka sallame su da cewa zasu dawo wata ɗaya, idan kuma kafin lokacin ta ji babu wani sauyi to su gaggauta dawowa, tunda a matsalolin ta har da alamu na tension ma'ana (debut) ɗin shi, shi kam wani magani ne ya bata duk wuni sau ɗaya za ta sha, sai ƙa'idojin kiyaye ci gaba da ciwon da ya faɗa musu, hatta idan sun samu tana barci to kar a tasheta da daddaɓawa irin ta gaggawa, a nutsu kafin a tashe ta ɗin, rashin yin haka zai sa sassan jikin ta su amsa har zuciyar ta ta shiga bugawa da sauri.
Da haka suka koma gida, da niyyar Intisar daga nan ya aje su wajen su Anna su gaishe su, amma da ta ji yanayin jikin na Yusrah sai ta ce su je gida kawai sun je nan da kwana biyu idan ta fara shan magungunan ta, yadda ta ce haka ya yi ya aje su sannan ya ɗan fita gari shi ma.
Ko da suka dawo gida kai tsaye ɓangaren Zahra'u suka shiga, ita ma faran faran ta tarbi Yusrah da tuni ta ɗauki little Yusrah tana mata wasa, da fara'a Zahra'u take duban Yusrah tace "Yusrah ina kika shiga? Nan Bilalun Mama ya ɗaga mana hankali wajen neman ki."
Ƴar dariya kawai Hafsat ta yi amma ba ta ce komai ba, sai Intisar ce tace "Bari kedai ƴar uwa, tun jiya take nan ai, gidan nan ta kwana ma, kuma daga yanzu za ki dinga ganin ta har sanda zan mata aure na miƙawa Bilalu."
Da sauri Yusrah ta kalle ta sai kawai ta yi murmushi, Zahra'u kuma da mamaki tace "Kai haba? To me ya faru?"
Murmushi kawai Intisar ta yi tace "Zan faɗa miki, yanzu zamu shiga da ita ciki ne ta samu ta yi wanka, daga asibiti muke da ita."
Da kulawa Zahra'u tace "Asibiti? Wani ne ba lafiya? Ko Yusrahn?"
Saida Intisar ta miƙe tace "E wallahi, kinsan tunda aka samu haɗarin ita ba ta ma zauna asibiti ba bare a bata kulawar da ta dace, shine muka tafi yanzu."
"Ba dai wata matsala ko?" Cewar Zahra'u, girgiza kai ta yi tace "Ba wata matsala in sha Allah, bayan ta ne kawai kuma an ɗorata a magani."
"To Allah ya sawaƙe." Cewar Zahra'u, miƙewa Yusrah ma ta yi da little Yusrah a hannun ta tana ƙara ƙamƙame ta, ganin haka ya sa Intisar yin dariya tace "To su Yusrah, ki aje babyn ko da ita zaki tafi?"
Langaɓe kai Yusrah ta yi tace "E aunty, in tafi da ita sai in dawo da ita anjima."
Kallon juna sukayi ita da Zahra'u sukayi dariya tace mata "To ke kin ji, kin yarda?"
Da fara'a Zahra'u tace "Sosai ma, dama wanka zamu shiga yanzu da mai tsaro, dake ba kowa a wurin har muna tunanin miƙa ta wajen Mama dama."
Ai da azama Yusrah ta gyara ma babyn zama a jikin ta inda Zahra'u ta ɗauko duk abinda zasu iya buƙata na yarinyar kafin a dawo da ita sannan suka tafi, Intisar dai kallon Yusrah take tana dariya har suka shiga ɓangaren nasu.
*BAYAN KWANA BIYU*
A yau bayan Mubarak ya gama cin abinci ya nemi ganawa da Yusrah kan maganar aikinta, domin tace bata son asibitin uncle Hamat, shi kuwa yana da aboki wanda suka yi karatu tare Dr. Siddik, tuni ya masa maganar ta whatsup ya nuna masa ba damuwa suna iya haɗuwa a asibiti, ko da takardar da ta karanta sunnada ma'aikata irinta da yawa zai iya ɗaukan ta domin suna yiwa junna alfarma sosai, shine aka kirawota ta sake tabbatarwa eh gwara a sama mata wani wajen.
Intisar ta dubeta ta ce" Yusrah, why ba zaki yi aiki a