Showing 207001 words to 210000 words out of 397328 words

Chapter 70 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70100

Anna kuma sai ta kalli Bilal da Anna ƙarama ke kusa da shi yana riƙe da hannayen ta tace " Bilal manyan gari, shikenan tunda su Uka suka bar ƙasar nan fa bana jin na sake ganin ka?"

Murmushi ya yi yana shafa kanshi da irin kunyar nan bai ce komai ba dan kusan hakane gaskiya, sai Aba dake shirin miƙewa dan ya watsa ruwa kafin a kira sallah isha'i dan zuwan su kafin su zauna saida kowa ya yi sallah yace" Kika sani ko aure ya yi? Hakane Bilal?"

Girgiza kai Bilal ya yi da jin kunya yace" A'a Aba, muna jiran lokaci dai."

Ƴar dariya Intisar tayi ta kalli Anna tace" Anna, Bilal fa ke ce mai bashi ƴa, auren Yusrah yake nema ai."

Da shi Bilal ɗin da Yusrah matsananciyar kunya ce ta rufe su musamman ma Yusrah da ta kalli Intisar ɗin baki buɗe da mamaki sannan ta soke kai cikin ƙafafun ta, sauran na ɗakin kuma kowa murmushi ya yi ba ma kamar Anna da tace" Iyeah, kuma shine baka zo ka kawo min gaisuwa ba? Da gaske kuma kana so na baka ƴata ɗin?"

Bilal dai dake ta murmushi ya sosa kai yace" A yi haƙuri Anna, daga yanzu za ki fara ganina?"

A tausashe aunty Intisar tace" Dole za ka faɗi haka mana, tunda Yusrah za ta dawo hannun Anna."

" Dady hancina." Safwan ya faɗa saboda cokalin da Aswan ya nufi hancin shi da shi madadin bakin shi. *Duk* maganar nan da ake yi jin su dai yake yi suna bashi wani irin haushi da takaici, da fari Bilal ya kalli, yadda yake jin kunya da wani noƙewa da yake yi sai ya ji kamar ya gaggaura masa tafi, shi yanzu yaron nan aure yake so ko me? Shi yanzu ya yi hankalin kulawa da mace? Macen ma... Wannan mai iskokai.

Sai ya taɓe baki yana jan tsaki a zuciyar shi ya ɗan karkata idanun shi ya fara da kallon ƙafafun ta, a hankali ya cira duban shi sama har zuwa fuskar ta, a dole dai bata so ya fara yarda da lamarin ta, tunda gashi nan daga yin maganar aure wai har da duƙar da kai irin kunya take ji, kawai sai ya saki gajeran tsaki da haushi haushi ya dubi Safwan da ya yi maganar hancin shi, sai kawai ya aje robar creame ɗin ya sa tissue ya goge masa hanci sannan ya miƙe gaba ɗaya ya nufi hanyar barin falon yana jin idan fa aka takura sa zai dawo ne ya zane kowa a gurin nan idan aka cire Anna da Aba, tomm! Ya za'a zauna gaban yara ana wani maganar aure, su kuma suna noƙewa mutane kawuna wai su masu son su yi aure ko? Ko yaushe aka haife su dukan su.

Saida ya kai ga ƙofar ya juyo ya dubi Intisar dake ta shafa kan Uka dake saman cinyar ta, cikin wata kakkausan muryar da ba mai iya dakatar da shi a lokacin yace mata "Anan za ki ci gaba da kwana, har sai na waiwaye ki."

Da sauri ta jinjina alamar ta amsa, inda Anna ta dube shi haka ma Aba da yake ayyana _"Kai! Kai jama'a!"_

Sai kuma ya maida duban shi kan Yusrah da ita bata gane me zancan shi na ta kwana anan yake nufi ba dan haka ita ma shi take kallo tana ayyana _" Wai shi haka yake ne?"_

Da wani irin yanayin bayar da umarni yace mata" Kinsan da babu abinda kika ci ko? To ki ci sannan ki kwanta."

Hmmmmm! Ajiyar zuciyoyi wasu suka sauke, kusan dai daga ƙarshe babu wanda bai gane karatun nashi ba, Bilal ma sarai ya fahimta, dan haka kafin wani tsautsayin ya ritsa da shi a ce shima anan zai kwana sai ya saki hannun Anna ƙarama ya kalli Intisar yace "To, aunty Inti ni zan wuce, sai goben ko?"

Da wani irin kallo Intisar ta bishi dake nuni da _"Ayya! Ayya Bilal! Gobe fa?"_

Da kulawa Aba ya kalle shi yace" Bilal, ka yi haƙuri ka ji, ka san halin Yayan nata da zafi, yanzu idan muka ce ta tafi ba da izinin shi, to ina tabbatar maka zan je har gidan ne ya ɗaga muku hankali, dan haka kayi haƙuri ka tafi ka ji, idan ka je ka ba Hajiar haƙuri, ni kuma zan kira Mubarak ɗin da kaina na sanar da shi."

Da girmamawa Bilal ya sadda kai yace" Ba komai Aba, in sha Allah zan gaɗa musu, saida safe aunty."

Ya faɗa yana tashi tsaye sukayi sallama, kallon Aba Anna ta yi ƙasa ƙasa tace" Kuma yanzu ka yarda ta kwana ɗin? Ba fa haka ta yo daga gidan ta ba ko?"

Shi ma ƙasa ƙasa yace" To ya zan yi? Kina so ya je ne can gidan ya musu ba daɗi?"

A hankali ta girgiza kai alamar a'a, dan haka yace" to mu yi haƙuri, na tabbata dai zai shigo anjima ko dan yi mana saida safe sannan ya ga ɗan sa."

Ko sanin zasu mishi maganar nan ne ya sa yau ko gidan bai dawo da daren ba, sai Aban dai ya kira ya tambayi Safwan da a lokacin ya yi bacci tare da Yusrah dan ta dinga kula da shi, sannan ya bashi Anna ma ya mata saida safe, ba wanda ya ɗaga masa maganar suka bar shi a haka a zuwan ai akwai safiyar gobe in sha Allah.


*DR. HAMAT*



Bai yi ƙasa a guiwa ba yamma na yi ya yi tattaki ziwa asibiti wajen Dr. Siddik, amma tun daga yadda Dr. Siddik ɗin ya tarbe shi a oficce ɗin shi da wani zama da ya yi yana juyawa akan kujera irin an zo wajen kan nan kai ma ya fara jin kamar fa zai ɗuɗɗura ashar, amma haka ya zauna bayan sun gaisa ya kalle shi yace "Siddik, na kira ka a waya ranar, amma sai na ji kana min magana kamar baka gane wa ye ni ba, shine na zo mu haɗu fuska da fuska, Siddik ina son lamba ko adreshin Yusrah ne saboda wani muhimmin abu da ya taso."

Da irin izza izzar nan raini raini Dr. Siddik yace" Abu muhimmi Dr.? Me ye shi? Ka sanar da ni mana sai na faɗa mata idan ta zo?"

Ɗan rintse idanu ya fara yi ya danne leɓen shi ya saita nutsuwar shi sannan ya sake duban shi yace" Siddik, magana ce fa mai mahimmanci tsakanina da ita, magana ake ta ƙanin ta da take nema, ya kake nema ka maida abun wasa?"

Da murmushi a fuskar Siddik yana juya kujerar nan yace" Ba wasa nake ba Dr., gani nayi yanzu Yusrah ni mai gidan ta ne, zan iya karɓar mata duk wani saƙo."

Garara jurewa ya yi ya miƙe a hassale yana buga teburin yace" Kai Siddik, kar ka ce za ka rainani dan ka ga na zo inda kake, me kake taƙama da shi da har za ka wulaƙantani? Ka san ko wa ye Dr. Hamat Anza kuwa? To ka sani idan na so zan iya ɓatar da kai, kuma kaf dangin ka ba wanda zai iya tambayar inda ka ke, dan haka ka taka a sannu."

Sai kuma ya nuna shi da yatsa yace" Magana ta ƙarshe tsakanina da kai, za ka bani lambar Yusrah ko a'a?"

Cak Siddik ya dakatar da juyawar kujerar ya ɗora hannayen shi akan table ɗin shima a dake sosai yace" Ba zan baka wata masaniya akan Yusrah ba, idan ka damu da sanin inda take ka yi bincike, ba kana da iko ba? Sanin adreshin wata ƙaramar yarinya ne zai gagare ka, sannan ya zama na ƙarshe da za ka zo har oficce ɗina sannan ka ce za ka min barazana, nima likita ne."

Kamar zai yi kuka ya jinjina kai yace" Ok fine, haka ka ce ko? Ok."

A fusace ya juya ya fita daga ofishin, Dr. Siddik ya bi bayan sa da harara yana taɓe baki sannan ya gyara zaman shi.

Saida dare ya ƙara yi ncle Hamat ya shirya bayan ya nutsu sosai daga gidan nan nasa ya nufi gidan AA, dan burinsa ya je ya ganewa idanuwansa shin yaron ƙanin Yusrah ɗin ne da gaske ko kuwa? Dan idan shi ne zai mayar da shi asibitin sa ne dan a duba shi a can, ya tabbata duk inda take da kanta zata kawo kanta har ma ta nemi alfarmar ya kula ta, wannan tunani ya saka shi nufar gidan da karsashinsa.

Da ya je ya taki sa'a tafiyar Barista Mukhtar kenan, AA ɗin na falonsa yana waya da Chef kan maganar aikin su, shigowar uncle ɗin sa kai tsaye ya saka shi yiwa chef ɗin sallama yana duban uncle ɗin nasa da ya zo har inda yake fuska ɗauke da fara'a tamkar gonar auduga yana yi masa sallama da faɗin " Son? Ni ban ma san ta inda zan fara ba, ace ka yi tafiya, tafiyar ma mai mahimmanci ban da labari? Yaushe zaka faɗa min na yi jika? Yaushe za'a ce yaron bashi da lafiya amma ba nine ke kula da shi ba? Tell me."

Da ƙyar AA ya iya hana kansa fallasa abinda yake zuciyarsa, sai dai duk da haka uncle ya fahimci wani abu sakamakon ɗan gimtsewar da ya yi da farko kafin ya saki ya yi ɗan murmushi yana ɗora hannayensa a jikin kujerar da yake zaune a tausashe ya ce" Uncle, ina yini?"

Uncle ya ɗan yi turus da tarin zubar da ya ɗauko ya ɗan zubawa yanayin AA ido, A hankali ya ce" Lafiyar ka ƙalau kuwa? Me yake faruwa ne?"

Basarwa AA ya yi yana sake dannar zuciyarsa ya ɗan yi alamun maganar da zai faɗa da gaske yake ya ce" Na gaji ne sosai Dady, ban samu barci ba ko kaɗan, jikan ka ya hana min barci, amma Alhamdulillah yanzu da sauƙi sosai."

Ɓoyayyar ajiyar zuciya uncle ya sauke ya miƙe yana nufar ɗakin AA ya ce" Sorry hero, ina abokin nawa yake ne? Yana ina in ganshi?"

AA a nutse ya ce" Yana gidan Aba da nurse ɗin sa, gobe dai za'a kai shi asibitin in sha Allah."

Uncle Hamat bai kawowa kansa wata asibitin za'a kai yaron ba, shi yasa ya kwantar da hankalinsa ya saka a ransa ai gobe ya ga yaron, ya dawo ya zauna suka shiga ɗan zantawa sama sama, amma firar sam ba daɗi dan har wani barci barcin gangan AA ke yi, har sai da ya ga cewar yau fa da gaske yaron nasa ya gaji sai kawai ya masa sallama ya tafi.

Yana tafiya ya yi kiran shugaban security ɗin gidansa, yana zuwa a nutse ya ce" Nan gaba, idan ba Anna ko Aba, ko Safwan Aswan suka zo a irin wannan lokacin ba, kar ka bar ko ma waye shigowa kai tsaye, ka fahimta? A nemi izinina idan na bada sai a shigo."

Sara masa ya yi ya tafi, AA kuwa ya jima zaune yana cizar leɓe da tarin takaicin ga nama amma ba damar ya ci, a dole zai haƙura ya yi jiran lokaci, ƙwafa ya yi ya miƙe ya shigewarsa ciki dan ya kwanta domin ba zai koma ba yau gidan sai goben in sha Allah.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
01/06/2024, 21:12 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*53*



Zuwan Yaya Mubarak da wani kawun shi ya sa Yusrah da su Manal da suka zo gaishe da Aba basu wuri a falon, tana bayan gidan ma AA ya shiga suka gaisa, a dole ya zauna saboda Aba ya umarce shi dan ya saurare su, amma shi wajen ɗan sa ya so tafiya ya ga ya jikin shi ya kuma ya kwana?

Yana sauraran su dukan su kaf suka gama maganar su da Yaya Mubarak ɗin sa kawun na shi, da ya ɗaga kai zai yi magana sai ya dubi Intisar da Anna ta kira yace "Ke, shiga ciki."

Miƙewa ta yi da ladabi ta fita daga falon na Aba, Yaya Mubarak ya bita da kallo yana ayyana _"Da gaske wai biye ma wannan Yayan nata za ta yi? Yau ga jaraba! Dan kai baka san daɗin mata ba sai ka hana wasu zama da nasu matan?"_

Amma a zahiri sai ya sake kallon AA da tsantsar ladabi duk da ba shekaru ne tsakanin su ba sai surukantaka, AA kuma Yaya Mubarak ɗin ya tsare da duba yace" Ka san mutumci ya sa mu kanmu muka yi shiru yara ƴan mata suke hannun ƙaramar ƙanwar ka, sannan Intisar ta yi muku karar da ta fi ƙarfin ƴaƴan ta su tozarta wajen zuri'ar ka, akan me za ka nuna mata fin ƙarfi akan ƴaƴan ta? Ta haifi abun ta ba tare da taimakon kowa ba, ta rene su har suka yi tasawar da za ta iya cin moriyar su, sai kawai ka rabata da su suyi tafiya mai nisan gaske tsakin ta da su, kuma a haka ma babu kyakyawar kulawa, Mubarak wacece ƙanwar nan taka? Mijin ta ɗan gidan uban wa ye shi? Ka sani zan sa a dawo da su ƙasar nan ko basa ma Allah, kuma wallahi sai muyi shari'a da su akan cin zarafin yaran nan, dan ina raye wani ɗa da ya fito daga tsatson Anza ya fi ƙarfin wulaƙanta, na cire maka yanayi na rayuwa, amma sai in da ƙarfina ya ƙare da izinin Allah."

Tsit ɗakin ya ɗauka sai numfashi kawai da ake saukewa, kawun Yaya Mubarak ne ya ƙara tausasa murya yace" Hakane, mun sani ba'a kyauta ba, amma ba wanda ya tsammaci Hawa'u za ta iya aikata haka wa yaran ɗan uwan ta da suka fito ciki ɗaya, ka duba lamarin dan Allah ka sassauta masa shima ba da sanin sa haka ke faruwa ba, yanzu haka ita kan ta mahaifiyar tasu ji hushi take da shi tana ganin ya goyi bayan ku ne, ita ma yanzu daga nan can gidan zan nufa dan in sanar da ita komai ko ta dawo hayyacin ta, amma dan girman Allah ka bar maganar ƙarar nan, zumunci ne mai ƙarfi a tsakani yanzu tunda har zuri'a ta riga ta haɗa, a yi haƙuri dan Allah."

Shiru ya yi yana ɗan duba wayar sa sannan ya kalli kawun yace" Shikenan, amma dai Intisar za ta ci gaba da zama anan har sai nayi tunani akan lamarin ta, magana ta gaskiya sai naji hankalina ya kasa kwanciya da zaman ta a gidan, kasancewar ita ce mai sanyin gidan mu, sai nake jin an ya kuwa ba'a cuta mata ƙin faɗa ne take y...yi."

Gyaran murya Anna ta yi amma saida ya gama dire maganar sannan ya kalle ta da mamakin _" Me na yi kuma Anna?"_

Kallon gargaɗi Anna ta masa sannan ta ɗauke kan ta, sai kawai ya miƙe yana soka wayar sa aljihu yace" Anna bari na ga jikin yarona."

Yaya Mubarak kaɗai ya bishi da kallon ka dawo ka tausaya min wallahi, idan ba haka ba nima zan dawo gidan nan, Aba ne ya shiga tausar su da nuna musu baya so ya ce zai bayar da umarni ne kai tsaye saboda shi ma kamar uba yake gare su, amma su ɗan masa uzuri ya huce kwana biyu, in sha Allah idan ma bai waiwayi lamarin ba shi da kan shi zai kira Mubarak ya zo ya ɗauki matar sa. Haka ma Anna ta ƙara da basu haƙuri kafin su yi musu sallama su tashi.

*Yusrah* na farfajiyar gida ita da Safwan suna ta zagayawa akan kujerar shi tare da Anna ƙarama, kallon ta ya yi yace "Aunty Yussy yunwa nake ji, kamar ban ci komai ba."

Murmushi ta sakar masa tace "Dole ne Safwan, amma ka yi haƙuri, ba'a cin abu mai nauyi ne saboda bayan gari kar ya wahalar da kai wajen yunƙuri, hakan zai fama ciwon ka, ama bari na je na ɗauko maka cake ɗin ka da yaghourt."

Saida ta daidaita masa zama a kujerar sannan ta tafi riƙe da remonte din dan bata wasa da lamarin kula da shi ɗin sam, Dadyn shi ma take jira ta ji yaushe zasu kai shi asibiti ne a ci gaba da kulawa da shi a can? Ta ƙofar baya ta madafa inda ma'aikata ke shiga ta bi, AA kuma ya fito ta ƙofar falo, bata jima ba ta ɗauko ta fito sai kuma ta biyo ta falon ita ma saboda hangen su Yaya Mubarak, dama basu gaisa ba da suka shigo, dan haka ta taho da fara'ar ta tana faɗin "Yaya Mubarak ina kw.aaa."

Ba ta ƙarasa faɗa ba saboda da ya juyo damuwa ƙarara ta karanta a fuskar shi har da ma ɗan ƙyalli ƙyallin ruwa a idanun shi, amma da suka kalli juna sai ya sa tissue yana goge idanun, ƙarasowa tayi jiki a sanyaye da kulawa tace "Yaya Mubarak lafiya? Me yake faruwa? Ina aunty Intisar ɗin?"

Murmushin da ya mata ko yarinya ce ita za ta gane kawai an dai yi maka ne amma ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login