Showing 117001 words to 120000 words out of 397328 words

Chapter 40 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70033

shakaf, hakan shi ya fi komai hargitsa masa lissafi, dan yakan yi wuya ya kwanta har gari ya waye bai ji yana son kaɗaici da mace ba, to amma fa...

Shi yana kallon mafi aksarin mata ne da wasu idanu na daban, wato indai ka ce zaka gauraya rayuwar ka da su, to fa shakka babu kullum ranka yana ɓaci ne da kuma hauhawar jinin ka, ya riga da ya san mata sune abokan rayuwar maza, kuma sune jin daɗin mazan, sai dai mata irin na *da* ba na yanzu ba, a gwagwarmayar sa ta rayuwa bai shiga sha'anin mata, amma mata sun farmake shi tare da yin dambe duk a kan shi da ko kulasu baya yi, sannan yana da abokai, yana da ƴan uwa, duk yana jin ya rayuwar su take tafiya da matan su, wasu ma budurwa ce za ta nemi zautar da kai kuma wai ka rasa ya zakayi da ita dan iskanci. Shi kam sam wannan bidi'ar ce ba ya cikin ta, a gidan nan nashi idan aka tilasta masa zama da mace ba tare da shi ya shirya hakan ba, to tabbas akwai iya shamakin ta dan ba ko ina za ta shigar masa ba ma bare ta shiga rayuwar sa.

Shirun da ya yi yawa ne ya sa Aba faɗin "Ka yi shiru ba ka ce komai ba?"

Muskutawa AA ya yi yana sauke numfashi cikin ladabi yace "Aba, ban da matsala da mace ko ɗaya, shi ma auren lokaci ne, idan lokacin ya zo Aba zan yi in sha Allah, kar ku damu."

Ƙara gyara zama Aba ya yi kamar zai faɗo saman jikin AA a dole shi sirri yake so su yi yace "Kana ji son, idan kana jin wani abu ne a jikin ka ba damuwa ka sanar dani, ni fa mahaifin ka ne kuma namiji, ba ka da wanda za ka sanar wa da damuwar ka sama da ni, ka faɗa min idan irin kana jin haka dai kamar..."

Ƙara ranƙwafowa Aba ya yi yace "Ba ka jin haka jikin ka wani iri, ka ji kamar baka sha'awar mace kwata-kwata? Idan kana jin haka ka faɗa min Aswan, sai na nema maka magani kaji ɗan albarka, idan kuma mafarke mafarkai kake yi cikin dare irin na miyagu, duk ka sanar min zan taimaka maka in sha Allah."

Galala AA ya yi da baki yana kallon Aba ya kasa cewa komai tunda ya fara magana mamaki da zulumi ya ishe shi, Aba fa nufin shi ko bai da lafiyar dokin shi ne kenan? Ko kuma irin abun nan da ake cewa aljana ta auri mutum, yana nufin shi yanzu aljana sai ta aure shi? To! Ya san ba ta inda Allah ya rage shi a rayuwa kam, amma dai aljana ma ai b za ta yi gigin yi masa wannan haukan ba ita ma, rashin lafiyar Aswan kula da Aba ke masa zato, ai ko shi mai nemawa kan sa lafiya ne idan da haka ɗin ne tunda burin shi na gaba bayan kammala aikin nan shine ya je wata islamiyya haka ya samo ƴar budurwa mai hankali da sanin ta kamata ya aure, to idan ya bar kansa ba magani ya zaiyi da ƴar mutane kenan? Kai La'ilaha illalah! Wani sa'ilin ma sai ya ga kamar mutum karan kan shi ne sheɗani wallahi ba wani ba, idan ba haka ba wane irin tunani ne wannan Aba yake yi masa?

Girgiza kai ya yi a sanyaye yana mai sadda kan shi ƙasa yace "Aba bana jin komai, lafiyata ƙalau wallahi."

Da irin tuhuma Aba yace "Ka tabbata?"

Ɗaga kai ya yi ya kalli Aban yace "Allah kuwa Aba, kowane dare fa ina fama da kaina, juriya ce kawai da rashin saka abun a rai, ba ka ga har na fara ramewa ba?"

Ƙura masa idanu Aban ya yi kuwa kamar mai son gano ramar, kuma kam sai ya ga tabbas ɗan shi ya ɗan faɗa saboda abincin da suke ci prison ai ba ɗaya bane da na gida, jinjina kai ya yi yace" E gaskiya ne kuma, to amma dai baka kauce hanya ko? Jikan Anza bana so ka yi abinda ni da Kakan ka bamu yi bane, sannan ka dubi ƙanin ka Humed, yana ashirin da huɗu a lokacin yana tsaka da karatun shi ya kalleni ya ce Aba aure nake so na yi, da fari nace a'a karatu ka ke yi, ina ce kai ya sama da maganar ka min magana a bar shi ya yi aure yana buƙatar hakan ne? Shin da muka aurar da shi ba a wata tara cif da kwanaki matar sa ta haihu ba? Da mun hana shi kana ganin da ba banzar alaƙa zai ƙulla mana a waje ba?"

Ya Allah! Maganar nan ta Aba ta fara hawa masa kai, sai magana Aba yake dake saka shi hasko wata ƙaniya jama'a, shi fa bai ce ba zai yi ba, zai yi amma dai yana jiran wani abun ne, sannan mutane nawa ne suka bar duniya ma babu auren? Har manyan tabi'ai da masu bi musu ke akwai, saboda auren yan da nasa rikicin basu yarda sun haɗa neman ilimin su da aure ba, haka suka gama rayuwar su sai neman ilimi da yaɗa shi a faɗin duniya. Kanshi na sunkuye dai amma bai ce komai ba, Aba kuma tsaf ya fuskanci maganar ta fara damun sa, sai kawai yake jin to zai fara nema masa maganin miyagun wataƙila sharrin su ne, dan sune idan aka yi maganar auren sai ran mutum ya ɓace, cikin nutsuwa ya gyara zaman shi ta hanyar jingina a kujerar yace "Shikenan, kwana uku da suka wuce uncle ɗin ka ya zo yana son ganin ka sosai, ka samu ka je ka gan shi."

Jinjina kai ya yi yace "In sha Allah, zan fara kiran shi dan na fi so na same shi gida."

Yunƙurawa Aba ya yi ya tashi tsaye haka ma AA dake aje towel ɗin hannun shi da abun ruwa, ya so ya takewa Aba baya, amma sai Aba ya dafa kafaɗar shi suna tafiya yana cewa "Kwanaki kaɗan nan ake sanar da ni an ga mai kama da kai a babban prison, shin akwai wanda ka sani da zai iya yin kama da kai ne kuma a can?"

Wani kallo AA ya ma Aba sororo da mamakin yau rigimar da Aban yake ji, sai kawai ya girgiza kai yace "Aba ta ya zamu san duk wasu da sukayi kama da mu? Amma wa ya faɗa maka?"

Kamar kuwa Aba yasan me sanar da shi wanda ya faɗa masa ɗin zai janyo sai kawai yace "Shikenan kawai, na ɗauka ko kai zaka san shi, tunda miyagun mutane ai duk abokan harkarku ne."

Girgiza kai ya yi yana jin lallai sai ya san wanda ya faɗawa Aban sa wannan maganar, ko ma wanene yana kyautata zaton ya san shi, kuma an faɗawa Aban ne dan a karkata masa hankalin sa can ya gagara samun nutsuwar yin aikin da ya kai shi, kuma ko ma waye to yana kyautata zaton imma wanda ba ya so ya ci gaba da aiki? Imma wanda ba ya son zaman lafiyar Aban sa ne kawai, dole cikin biyu a samu ɗaya.

Haka dai ya raka Aba har waje inda su Sk suke sannan suka wuce shi kula ya dawo yana ta jinjina maganar da suka tattauna da Aba ɗin, yana shigowa kai tsaye ban ɗaki ya nufa dan yin wanka da rakiyar su Mim da Angel, saida ya shiga ban ɗakin kaɗai suka tsaya anan kamar masu gadin shi.



*BILAL YUSUF*


Tun da ya ji horn ɗin motar ta ya tabbatar ita ce ta dawo, dan haka ya zabura ya miƙe ya shiga saka doguwar rigar sa da takalmi ya fito daga ɗakin nashi zuwa ɓangaren aunty Intisar ɗin... Ita kuma tana fitowa daga mota da takon ɗaiɗaya na rashin kuzarin da ƙaramin cikin ta ke haifar mata take takowa har ta shigo falon nata da sallama dan tasan mijin nata yana nan bai fita ba kamar yadda sukayi zai jira ta dawo.

Yana kwance kan kujera yana kallon ball a tv ya amsa sallamar yana miƙewa zauna ya zuba mata idanu cike da so da ƙaunar ta, tun kafin ta ƙaraso ta shiga warware lafayar ta ta aje haka ma ƙaramar jakar hannun ta da makullin mota, kyakyawar surar ta ce ta bayyana gaban shi cikin wani riga da siket na atamfa ko ɗan kwalin su babu a kan ta, miƙa mata hannayen shi ya yi ya jawo nata hannayen cike da kulawa yace "Ya dai *my*? Har kin dawo?"

Da yanayin shagwaɓa da ta ƙware a cikin ta ta narke akan cinyar sa tare da ɗora kan ta a kafaɗar sa murya a tausashe tace "Na dawo my, na barka kai kaɗai ko? Sorry."

Haɗa fuskar shi ya yi da ta ta fuskar kamar za su sumbaci junan su cikin raɗa yace "Ba komai tawan, da fatan kin yi nasara? Dan ina so ɗan Hajia ya bar min ke da my unborn ku huta."

Murmushi ta yi tana wasa da fatar kunnen shi tace "Bari na kira shi ma a waya na faɗa masa duk abinda na samo yau, kafin ya fara min zarya a falo."

Murmushi ya yi ya riƙe ƙugun ta sosai yace "Kin samo duka bayanan ta?"

Cikin sanyin jiki da jimami tace "Da ƙyar, sai dai labarin ta cike yake da abun tausayi."

Ƙara naniƙe mata ya yi sosai a jiki yana shaƙa daddaɗan ƙamshin jikin ta yace "A bon! To ki faɗa masa ai..."

Sallamar da Bilal ya rabka musu a falon bayan shigowar sa ta sa su dukan suka zabura dan basu shirya zuwa wani ba a lokacin, ko yaran su suna makaranta kuma lokacin tashin su bai yi ba. Haɗe fuska sosai Yaya Mubarak ɗin ya yi yana kallon shi kamar ya zage shi saboda shi bai so tashi daga nan ba idan ba gadon girma zai hau ba ya wani katse masa jin daɗi. Intisar kuma kunya ce ta kamata sosai dan gaskiya ba sa irin haka gaban kowa, kuma da ma kusa da juna ne ya same su ko kan mijin ta a cinyar ta ko ita nata kan a jikin shi ko ƙafar ta ko tashi, a hankali ta sulala ta zauna kan kujera tana gyara zaman ta sai sinne kai take.

Amma shaƙiyanci irin na Bilal tsaf ya murje idanu kamar bai tarar da komai ba ya ci gaba da shigowa yana faɗin "Aunty Inti kin dawo shine ko ki kirani na zo na ji bayani? Kinsan yadda na ke ta dakon jiran ki kuwa?"

Wata uwar harara Yaya Mubarak ya sakar masa, hakan ya sa yayi murmushi ya tsaya turus yana kallon Intisar yace "Aunty ko zamu fita waje mu ƙarasa maganar mu? Kinsan idan aka katsewa mutum hanaarin sa har mari yakan iya yi."

Cikin ɓacin rai Yaya Mubarak yace "Bilalu ban son iskanci, fita waje za ta same ka."

Dariya Bilal ya yi yace "Kin gani ko aunty? Shiyasa nake so na yi auren nima, wallahi sallah ma sai ka bubbuga min ƙofa zan fito."

Taɓe baki Yaya Mubarak ya yi yana ɓoye sirrin shi da ya fara bayyana yace "Idan kana so ma zaka iya ajiye musuluncin daga baya sai ka koma."

Duk wannan bidiri da suke Intisar ba ta ce musu ƙala ba, sai tashi da ta yi ta nufi inda ta aje lafayarta ta ɗauka tana ɗaurawa sannan ta dawo ta zauna, kallon Bilal ta yi tace "Zauna."

Zaman ya yi yana satar kallon Yayan nashi da ya sake wurga masa harara, saida suka nutsu dukan su kafin ta fara da "Bilal, kamar yadda ka sani sunan ta Yusrah Abdul-Hamid Turaki, ba ƴar kowa bace ita face jajirtaccen mahaifin da sai ya fita ya nemo yake kawo musu su ci, basu samu gatan yin karatu a makarantun kuɗi ba sai na gwamnati, tsananin rayuwa da ake ciki na yau a ci gobe ba'a ci ba ya sa Yusrah dagewa wajen karatu dan burin ta shine ta taimaki mahaifin ta wajen ɗawainiyar gida, bata kula samari ko da sun zo inda take, ba ta kula ƙawaye sai ƙawar ta ɗaya Maryam da suke da nisa da juna, amma kullum suna tare a makaranta, Yusrah ta yi nasarar cikar burin ta har ta fara stage a asibiti inda muka fara haɗuwa da ita, sai dai yanzu haka da nake maka magana Yusrah ta zama marainiya gaba da baya, ina ce dukan ku kun ji rushewar gidaje da aka samu a unguwar gangare a labarai?"

Ta yi tambayar tana mai kallon kowanen su, duk jinjina mata kai sukayi har Bilal ya ƙara gyara zama yana tsare ta da idanu yace" Tabbas, mun ji aunty, har yanzu ba'a bar maganar ba ai a labarai."

Lumshe idanu tayi tace" To har da gidan su Yusrah wannan abu ya faru, ita da ƙanin ta kaɗai suka tsira wanda shi muka ji a ranar tana haukan za ta je neman sa, amma mahaifin ta, mahaifiyar ta da kuma Yayar ta, duk tare suka rasu a wannan haɗarin, ƙanin ta kuma da ta bari hannun Kakar su ta tafi neman kuɗin yi masa magani, sai ta dawo ta tarar baya nan wai an tafi da shi, shine dalilin da muka kasa gane mata a ranar, kuma wannan ne ya janyo ta fita da har yanzu babu wanda ya sake ganin ta a asibitin ko kusa da haka, wannan shine labarin da na samo wajen nurse Sakina da kuma gidan limamin unguwar su, dan har can naje, kuma sun ce tun ana zaman makokin iyayen ta da suka gan ta har yanzu ba su sake ganin ta ba, amma dai liman ya ce cikin yaran shi akwai wanda ya ce ya ganta kwana kusan bakwai haka ta fito daga gidan da jakar kaya, shiyasa nake ta zulumin Allah ya sa ba duniya Yusrah za ta shiga ba, ba wanda ya san ina take ko ƙanin ta."

Ta ƙarashe maganar da share ƙwalla da ta cika mata idanu da yatsar ta, Bilal da ya kusa suman zaune suka ji yana faɗin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil."

Sai kuma ya miƙe yana faɗin" Aunty bara naje unguwar na sake tuntuɓar su, ba za'a rasa wata makamar ba in sha Allah, zan duba ko da cikin gidajen ƴan uwa ne, wataƙila can ta tafi, amma Yusrah ba za ta shiga duniya ba."

Duk ya yi maganar ne yana fita daga falon kamar wani mahaukaci, ba wanda ya dakatar da shi dan su kan su a zunɗume suke da wannan lamari.

Da gaske Bilal na fita bai zame ko ina ba sai unguwar su Yusrah, sai dai bai samu sakin jiki daga gurin liman ba da ya yi tambaya dan yana son jin ƙarin bayani daga bakin shi, ba dan komai ba sai dan sanin yadda duniya take yanzu, kuma yarinyar nan tana wani hali ne yanzu da babu mai tsaya mata sai Allah, dan haka bai tarbi Bilal kamar yadda ya tarbi matar da ta tafi daga wajen shi ba jimawa ba (Intisar), saida ya nemi sanin wani dangin ta haka kaɗai ya masa kwatance da gidan Goggo Hindatu.

Daga nan ma kai tsayen gidan Goggo Hindatu ya nufa, kuma bai sha wahalar gane gidan ba dan ko da ya faɗi sunan nata gidan *Hinda sana'a goma* aka kaishi har ƙofar gidan. Daga ita sai kishiyar ta ne a gidan lokacin yara na makaranta sai dai suna daf da tasowa dan rana ta yi, dake kuma a soro ta same shi ta gama kalle motar da yake ciki, sai ta sa wa ranta babba ne kuma ɗan babban da zai iya mata kyauta irin ta matar da ta mata jiya.

Bayan duk sun gaisa ne ya faɗa mata sunan shi da sunan mahaifin shi, kafin ya faɗa mata Yusrah yake nema dan Allah ba su da labarin ta? Da mamaki mai ƙunshe da takaicin wai Yusrahn nan wacece ne wai? Me take aikatawa ne a waje da basu sani ba ta dube shi tace "Yusrah kuma? Lafiya ko?"

Da ladabi ya amsa da "Lafiya lau Mama, kamar yadda na faɗa miki sunana Bilal, na fara haɗuwa da Yusrah a asibiti ne kafin wannan iftila'in ya same su, kuma magana ta gaskiya ina son ta ne da aure, shine nake so na ji ko kuna da labarin ta."

Taɓe baki Goggo ta yi a ɓoye, amma a bayyana sai ta washe baki tace" Ayya, ai yaro rashin sa'a kayi, jiya zan iya ce maka warhaka Yusrah tana gidan nan, tana gidan wata Hajia ne, amma ba zan faɗa maka komai akai ba gaskiya har sai ta sake dawowa na ji daga gare ta, ai ka ce sunan ka Bilal ko?"

Amsawa ya yi da e da kuma ɗorawa da" Goggo kenan Yusrah tana zuwa nan? Amma kamar yaushe zan iya dawowa dan na gan ta?"

Wani sakaran kallo ta masa dan ita ba Yusrah ta hangowa Bilal ba face Safiya ƴar ta, kafin ya dawo za ta sa malam ya basu ko da kwalli ne da Safiya za ta yi aiki da shi, da ya dawo suka haɗa idanu ya ji ita yake so ba Yusrah ba, dan ita yanzu bata ma yarda da tarbiyyar Yusrah ba gaskiya.

Da irin yanayin rashin kunya Goggo tana murmushi tace "E to, da ma dai ina da waya ne, yanzu kuma yara da nace su kira min lamba za ka ji ana cewa ba kati na kawo a saka, kasuwar kula yanzu sai a hankali wallahi, da sai nace ka bani lambar ka kawai yadda tana zuwa zan kira ka."

Wani abu da Bilal ya fahimta game da matar nan shine akwai abinda take nufi da maganar ta, dan haka ya nuna mata a aikace zai iya komai akan Yusrah, da ladabi yace" Ina zuwa Mama?"

Motar sa ya je ya buɗe ya ɗauko kuɗi ƴan jaka biyar guda takwas tare da katin shi, yana zuwa ya bata yace" Gashi Mama, wannan ɗin a sa kati, wannan kuma katina ne dan Allah da ta zo ku kirani."

Hannun ta har yana rawa ta karɓa tana ayyana _" Wane irin arziƙi ne wannan ke bibiyar Yusrah?"_ Kuɗin da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login