Showing 174001 words to 177000 words out of 397328 words
ma tana ƙara ƙure fuskarsa da ido kanta na neman ɗaukan zafi sanadiyar hasaso mata mutumin da ta yiwa kanta alƙawarin haɗuwa goma jigatawa goma, da sauri ta kori tunanin ta ce" Sir, a damtsen hannu ake yi masa dexa ɗin ko a cinya? A ɗan taimaka a buɗe min in masa kar ya tashi a firgice."
Ɗan jan iska ya yi ta bakinsa sannan ya ƙaraso wajen nasu bayan ya mayar da file ɗin ya ɗan duƙa a nutse yana ɗan ambaton sunnan yaron nasa, ya ɗan janye masa abin idon shima dan ya tashe shi, amma Safwan sai barci yake yi yana luu luu da idanu murya a shagwaɓe na abin barcin nan yana maƙale kafaɗa can ciki ya ce"Dad."
Aswan ya riƙe shi da kyau bayan ya buɗe ya ɗora shi a ƙirjinsa bayan ya zauna da kyau a saman kujerar a hankali ya furta" Shiiiiiii my boy, bari a yi maka allurrar ka sai ka ci gaba da barcin ka ka ji? Yanzu za'a gama ba zafi."
Da ƴan yatsunsa ya mata alamun ta yi, ita kuma mamakin ƙaton ɗan take da sangarta, ya naanuƙe fuska a ƙirjin uban sai iya shege yake zubawa, uhum ƴaƴan masu kuɗi dai wasun kamar ka tuɓe su ka ɗauraye masu jiki alƙur'an.
A nutse ta soka allurar bayan ta goge wajen da auduga sannan ta matsa ruwan allurar, barcin nasa ne ya sake shi saboda shigar allurar da ruwan allurar ya ɗago da sauri ya kalli likitar zai fashe da kukan shagwaɓa ya zaro ido yana kallonta a lokacin da ta ɗan ja baya da ƙarfi saboda bugawar da ƙirjinta ya yi, Safwan ma da ya ƙara sauri ya gyara kwanciyar sa a jikin Aswan ya ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
28/05/2024, 14:40 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*45*
Safwan ma da ya ƙara sauri ya gyara kwanciyar sa a jikin Aswan ya ce" *Aunty Yussy*?"
Yusrah a rikice tana nuna shi ta ce" *Safwan*? Saffff..."
"Lah, Dady aunty Yussy ce." Safwan ya faɗa da ɗan ƙarfi da alamun mamakin ganinta har yana miƙewa zaune ya ɗora da faɗin" Dama a cikin jirgi kike shine kika gudu kika bar ni?"
Hankalinta neman gushewa yake yi, a birkice ta dubi Aswan da ya yi mutuwar zaune ta kalli Safwan, sai kuma ta wangale baki tsabar farin cikin ta na bayyana sosai da mugun sauri ta durƙushe tana tara masa hayyane tace" Zo Safwan ɗina, zo babban gidan mu, dama kana raye? Ni na san d..."
Riƙe shi da Aswan ya yi tamau a jikin shi yana mata wani kallon me ye haka? Ya sa ta kalle shi da mamaki, amma a lokacin sai ta hango wannan fuskar tashi da ta gani a can ta shaye shaye, hakan ya sa ta miƙewa tsaye ta nuna shi da] ar yatsarta dake yi mata rawa ta ce" Dama ƙanina ya na wajen ka? Kai ne ka sace min ƙanina? Kai wai ba kai bane wannan ɗan balaja'un fitananne na prison?"
"To fa." Aswan ya furta ƙasa ƙasa yana miƙewa ya mayar da Safwan saman kujerarsa a tausashe ya ce" Look at me hero?" Safwan ya dubi Baban nasa lokaci ɗaya kuma ya na son karkatawa ya kalli Yusrah da ita ma ke duban shi, hakan ya sa Aswan tallabar fuskar sa ya tsayar da duban nashi ga fuskar shi kawai.
A tausashe ya ce ma" Ba na son in sake jin ka buɗe bakinka, ka koma barcin ka ka ji ko? Maza boy ɗin Dady a yi barci, bana so in ji ka kirayi sunan kowa, ko waye ka ji?"
Yusrah ta kama ƙugu tana leƙen ikon Allah ta ce" Ban gane ba? Kai a wa za ka faɗ..."
Aswan ya ɗago a ɗan hautsine ya ɗora yatsarsa saman le;ensa yana ɗan fito mata da idanuwa ya ce" Shiiiiiiiii!"
Yusrah ta sake zaro ido ta zagaye shi tana ƙoƙarin sake tayar da Safwan, duk da ba ya son haka ma na faruwa da shi da mace amma saida ta tilasta masa ya damƙi hannunta na dama ya jata ƙiiii ya nufi kicin ɗin cikin jirgin da ita, suna shiga ya saketa yana haɗe rai sosai ya nuna ta da yatsa ya ce" Dama ke ce Yayarsa ta sa?"
Yusrah ta gyaɗa kai da sauri hankalinta duk a birkice ta ce" Eh ni ce, wallahi ni ce, ni ce yayarsa, wayyo Allahna bawan Allah, kai ne ka sace min ƙanina?"
Haushi ya kama shi, ya zabga mata harara ya ce" Eh nine, kuma kar ki saki in ga kin raɓar min ɗana, kin ji kunya ke kam."
Takaici ya turnuƙeta, lokaci ɗaya ta yarda tabbas wannan shine na prison ɗin nan, ta ƙaraso gabansa ta kama rigarsa ta riƙe taf rai ɓace ta ce" ɗanka? Babu abinda ya haɗa ka da ƙanina, yanzu zaka bani ƙanina mu tafi, kuma idan kai ne na prison ka sani ba zan taɓa yafe maka ba macuci mai yiwa mutane ƙazafi."
Takaici ya ƙara turnuƙe shi, ta wani shaƙe shi kamar sa'anta wai shi Aswan? Sai da ya dan kalli kicin ɗin da kyau duk da ya san ba kowa amma saboda tsaro kar a zo wani ya ga sanda ta ci kwalar sa haka da haushi haushi ya ce" Eh ni ne na sace shi, ki kai ƙarata in za ki iya, kuma maganar prison sai na ji dama sharrin da za'a ɗaure ki na maki tunda ke baki da tausayi ba kya jin tsoron Allah, ki tafi ki bar yaro cikin mawuyacin hali yanzu har kina da bakin kiransa ƙanin ki? Cika min riga ko in sumar da ke nan wurin in wurga ki waje kowama ya huta, mahaukaciya kawai."
Hargagin da ya yi mata na ƙarshe sai da cikinta ya nemi juyawa, amma ta yi tam da rigar tasa idanuwanta na cika da hawaye tana daf da fasa ihun kukan tashin hankali da ƙarfin halin da take ji idan bata yi da gaske ba a yanzu to daga ita har Safwan wataƙila ɓatar da su ma zai yi.
Muryarta na rawa ta ce" Sai dai ka kasheni amma ba zan sake ka ba, ba zan sake ka ba, ka bani ƙanina sannan ka gaggauta dakatar da jirgin nan mu sauka, wai wani ɗanka ko kunya ba ka ji, to kai babanmu ne da mamamnmu? Su kaɗai suka haifi Safwan ɗina, Safwan ɗina ne ka bani ƙanina nayi nesa da kai."
A ransa sai ya shiga shakkun to kar dai aje ciwon ya motsa? In ba wannan ba ihun nan da ya mata ai ya tsorata ƙarti da yawa idan ya masu da shi, to ta ya ita ta masa ƙiƙam ne haka? Ta yi raf da shi kamar ta riƙo ɓarawon ta, shi kam ya ya aka yi hanyarsa ke haɗuwa da wannan sha taran? Yanzu ya ya zai yi da ita kenan?
A nutse ya ɗaga hannayen shi ya riƙe duka wuyan hannayen ta dake kan rigar sa, amma fuskar sa a kausashe ya dinciki hannayen nata da ƙarfi tare da hankaɗata baya ya tura ta, hakan ya sa Yusrah yin baya sosai ta ƙarasa danganewa ga chauffage ɗin dake kicin ɗin haɗe da wani desk... Ƙarfin hali ya sa ba ta ko kula da buguwar da ta yi a guiwar hannun ta ba ta sake yunƙurowa da azama za ta sake cakumar shi, sai dai tuni shi ma ta kaishi bangon da ba ya son ya kai ɗin, hakan ya sa ya riga isa gare ta yana matse mata wuri tare sa nunata da yatsar sa manuniya a kausashe sosai duk da kusancin da suka samu yace "Saurareni da kyau, aiki na ɗauko ki kiyi min kuma biyan ki zan yi, bayan wannan bana son wani abu ya haɗani ko ɗana da ke, Safwan ɗana ne a yanzu kuma halataccen ɗana da yanzu shari'a ta tabbatar min da shi, ba zan ɗaga miki ƙafa akan abin da ya shafe shi ko rashin lafiyar sa ba, dan haka ki iya bakin ki ba komai zaki saki baki kina faɗa min ba musamman ma a gaban ɗana, kin fahimta?"
Ƙyaƙyafta idanu Yusrah ta yi hakan ya sa hawaye sake silalo mata, duk da zuciyarta ta jima da karyewa kuka take so ta yi sosai, amma haka ta daure da ƙarfin hali ta kalli tsakiyar idanun shi masu girma da zurfi tana shanye duk wani kwaejinin su da wutar bala'in da take gani a ciki da rawar muryar kuka tace "Kai a wa za ka faɗa min haka? Safwan ƙanina ne kuma duniya ma ta shaida haka, kai ba Babanmu bane da har za ka bani umarni na bi, aikin ka kuma na fasa kawai ka bani ƙanina yanzun nan zamu rabu da kai da rayuwar ka gaba ɗaya."
Ba tare da ya matsa daga kusan ta ba yana kausasa duban shi a kan ta yace" Saboda yanzu ni ne uban Safwan, idan baki shiga hankalin ki ba kuma tsaf zan rab tafiyata dake ta hanyar loda miki kayan laifin da zasu bayar da damar riƙe ki a filin jirgi daga nan kuwa sai prison."
Zai aika, tabbas zai aikata, bashi da imani ai, wannan karon hawaye ne sosai suka ɓalle mata har ta sa ɗan hijab ɗin ta tana sharewa tana faɗin" Allah yana gani bamu cutar da kai da komai ba, ƙanina da ya rage min kawai nake so ka bani, ka san wahalar da na sha wajen neman shi? Kasan adadin tashin hankalin da na tsinci kaina saboda rashin sa? Idan ma za ka kaimu ne ka siyar wallahi zan rufa maka asiri idan ka ban Safwan babu wanda zai ji, dan yanzu na gama ji a jikina wani shirin kake shiryawa a kanmu, shiyasa duk ka taramu a nan, dan Allah ka ban ƙanina ka ji Alhaji."
Ta ƙarashe tana durƙusawa kan guiwoyin ta tana haɗe hannaye almar roƙo ta sake cewa" Na roƙe ka da girman Allah ka bani Safwan ka ji, wallahi yanzu ina da kuɗi da aiki mai kyau da ahalin da zasu tsaya min wajen kula da shi har ya warke, na maka alƙawari ba zan bari ka sake ganina ba idan ma ni ce baka son gani a duniyar da kake rayuwa a cikin ta."
Kallon ta Aswan yake yi yana ƙarawa ya rasa ma mamaki ne take bashi ko tsoro, amma sai ya shanye komai ya ɗan ja baya sannan ya ranƙwafo daidai da tsayin ta yana wani murmushi irin na lalaci yace "Oho! Wato kin tara kuɗi ko? Na gane, wato kin gudu kin barshi ne saboda kina ganin nauyi ne shi a gare ki? Shiyasa kika yi watsi da shi akan titi ba tare da tunanin komai ba dan kawai ki ji daɗin rayuwar ki, ke wace irin marar imani ce? Wace irin zuciya ce a ƙirjin ki? Wai ke wace irin macece eeeeee?"
Yadda ya ƙarashe maganar da tsawa sosai ya sa ta ɗan tsorata ta yi baya, amma da ta ga ba neman su rabu lafiya yake ba sai ta miƙe tsaye tana haɗe kukan ta fuska a haɗe ta nuna shi da yatsa tace" Kai saurara ka ji, ni ban gudu na bar Safwan ba, neman kuɗin aikin sa na tafi na kuma bar shi hannun Iya, idan akwai wanda ya gudu ya barshi Iya Abu ce, dan haka wallahi in jirgin nan zai sake lulawa sama ta bakwai ne Allah sai ka bani ƙanina, dama fa na gama fahimtar ka ba kirki ne da kai ba, kuma a yanzu na ji ban yarda da kai ba gaba ɗaya, ina kyautata zaton yadda kake safarar bindigu haka kake na mutane cikin sauƙi."
Mamakin yadda babu shakkar sa ko wani tsoron sa tare da ita shi ya fi damun sa, kafin ya ce mata wani abu aka shigo kicin ɗin, a tare suka dubi ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgi sai dai wannan namiji ne ɗauke da faranti a hannun shi da abun sha. Dan son tabbatarwa kan shi wai shine Colonel Aswan Aliyu Anza? Ko kuma dai kwarjinin nasa ne ya gama zubewa a idanun jama'a ya sa ya dubi namijin nan da ya ƙare musu kallo yace "Da wata matsala ne anan yallaɓai?"
A ɗan tsawace Aswan yace "Babu, maza fice daga nan ka rufe min ƙofar?"
Da mugun sauri ya rusuna alamar girmamawa ya amsa da "Ok sir, sorry sir."
E tabbas yana nan dai a yadda yake, to amma me ya sa ita wannan ba ta nuna hakane? Sai kawai ya ji bari ya ƙyaleta a haka da alama ita ma ciwon nata ne ya motsa tunda wasu suna jin jiri idan sun shiga jirgi ai, wani malalacin murmushi ya yi kawai ya juya yana gyara zaman rigar sa da ga duk ta canza masa zaman gugar sa yana jan tsaki... Amma sarautar Allah sai ya ji kamar ana bin a baya haka, amma sai bai kula ba har saida ya fito daga kicin ɗin wanda hakan ya yi daidai da tahowar wata hotes, da girmamawa hotes ɗin ta rusuna mishi tace "Sir, ina fatan komai lafiya?"
Ta ƙarashe maganar tana satar kallon Yusrah dake share hawaye, a hankali ya juya ya ga tabbas Yusrah bin bayan shi take yi, kallon da ya mata na mamakin me ye kuma na bin shi haka uwa wutsiya ya sa ta cike da tabbaci tace "Wallahi idan ka ga na bar bin sawayen ka to tabbas ƙanina ka bani, sai kuma idan mutuwa ce ta ɗaukeni."
Wani sakaran murmushi ya yi ya kalli hotes ɗin ya girgiza mata kai yace "No, ba komai fa, ciwon ta ne ya tashi, na yi fata ma ina na taho da Dr. da zai dubata."
Yana faɗa kawai ya wuce Yusrah ta sake bin bayan shi tana ayyana _"Ka faɗi koma menene a kaina zan ɗauka."_
Safwan na ganin su ya gyara zaman sa a kujera ya langaɓe kai, hakan ya sa Aswan ya tsuguna ya shafi kumcin sa a tausashe kamar mai raɗa yace" Ya dai jikan *Haidar*?"
A marairaice Safwan yace" Dadyy, aunty Yussy ce, ka yarda na mata magana ko ƴar kaɗan ce?"
Saida ya ɗan haɗe rai sai kuma ya saki fuskar sa yadda yaron ba zai fahimci wani abu ba yace" Boy, kenan ba ka ji maganar Dadyn ka ba?"
A raunane yace" Na ji Dady, ka yi haƙuri to."
Murmushi ya sakar masa yace" Na yi to, yanzu ka yi bacci ka ji, naji zafin jikin ka ya sauka, uhumm?"
Jinjina kai ya yi yana satar kallon Yusrah dake tsaye sannan ya rintse idanu gam gam alamar baccin zai yi, ranƙwafowa Yusrah ta yi kamar zata yi ruku'i tace" Safwan, ni ce fa, aunty Yussy, Yusran ka Safwan, zo ka ji ƙ..."
Ganin bai buɗa idanun shi ba ya sa Aswan miƙewa daga tsugunnon da ya yi a zafafe y ja rigar ta ta likitoci ya nufi wajen zaman ta da ita, saida ya kaita kan kujera ya zaunar da ita yana sake nunata da yatsa yace" Kashedi na ƙarshe da zan miki idan kina so mu je lafiya, kar ki sake ƙoƙarin ɗagawa yarona hankali ko saka masa wani banzan tunani, me kike nufi? Bayan kin jefar da shi zai rasa yadda zai yi ne har yunwa ta kashe shi? Ko kuma ya fara bara a bakin titi dan ya samu abinda zai ci? Ke a ganin ki shine ya zama miskini kenan? To ahir ɗin ki da sake kiran ɗana da ƙanin ki."
Juyawa ya yi ya koma kan kujerar shi ya zauna, yana tsaka da maƙala belt ɗin shi da niyyar ya rufe idanun shi nutsuwar sa ta saukar masa kawai ya sake ganin ta tsaye a kan su tana shirin daddaɓa Safwan da har yanzu ya ƙi buɗa idanun shi. Ya Allah! Ya Arrahaman! Ya rahim! Wai yau wace irin jaraba ce ya haɗu da ita jama'a? Yarinya uwa aljana sai liƙe masa take yana rabuwa da ita, jama'a wannan wace jaraba ce haka? Kamar wata ƴar tauri ko baƙauriya? Duk irin firgicin da yasan yana tsorata maza ma bare mata ya mata, amma dan masifa ta ƙi tsorata saboda shi bai ma san haukan nata a wane mataki yake ba, gashi baya so ya yi abinda ɗan da yake so ya ga shaƙuwar shi da shi ta fi haka ya fara kallon sa da tsoro.
Da mugun azama ya riƙo lallausan hannun nata da ta kai zata taɓa Safwan bayan ta wanka masa harara ta kira sunan Safwan ɗin, bai tsaya komai ba saboda ganin Safwan ɗin zai juya inda ya ji an kira sunan shi ya fizgota ta biyo ta gaban Safwan sannan ta isa gaban shi shima, kafin duk ta ankara da wannan abu ya zaunar da ita kusa da shi yana sake matsowa kusa da Safwan ya zaunar da ita sosai saboda kujerun idan a tafiyar takura ce zasu ɗauki mutum biyu musamman ma su da suke vip. Yana tabbatar da ta zauna sai kuwa ya mata wata matsa