Showing 18001 words to 21000 words out of 397328 words

Chapter 7 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70002

surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*6*



Saida suka gama cin abinci kafin suka ɗauko kayan karatun su kafin shigowar Baba da sun san yana shigowa maganar da zai musu kenan, hatta da Hannah dake ta sauri ta gama wankin kayan makarantar ta da na ƴan uwan ta da ta ɗauko, ita ma daga nan take bitar haddar ta saboda sanin Baban su bai da sauƙi game da lamarin da ya shafi karatu.

Suna haka Baba ya yi sallama, kusan duk a tare suka amsa mishi tare da yi masa sannu da shigowa, kan tabarmar ya zauna shi ma yana kallon Safwan yace "To babban su, ya karatun naka? Ka haddace dai ko?"

Kallon Yusrah ya yi sannan ya kalli Baban yana murmushi yace "E Baba, na iya duka."

Jinjina kai Baban yayi yace "Ma sha Allah, to matso mu fara da kai."

Matsawa ya yi tare da rufe littafin shi hizib biyar lokacin da Hannah ta zo ta zauna ita ma, cikin nutsuwa ba ɗar ko inda inda ya fara karatun shi, duk shiru tsakar gidan ya ɗauka suna sauraren karatun yaron da bai fi shekara shida zuwa bakwai ba har ya dasa aya. A tare Mama da Baba suka furta "Allahu akbar."

Sai Baba da ya ɗora da "Ma sha Allah, babban su, kana ƙoƙari fa sosai."

Sai kuma ya gyara zama yana karɓan littafin dan ɗora mishi yana sake cewa "Ka ci gaba da haka kaji ko, in sha Allah za ka zama babban mutum."

Da jin daɗi Safwan ya kalli Yusrah ya ɗan yi mata gwalo cike da hura hanci, ɗan hararan shi Yusrah tayi tana murmushi, cikin nutsuwa Baba ya sake ɗora masa wani tare da nanata masa har ya riƙe kafin ya sallame shi ya koma gefe, Yusrah ce ta matso ita ma ta rufe Alƙur'anin hannun ta sannan ta fara da a'uziyya da kuma basmala sannan ta ci gaba da karatun ta.

Saida dukansu suka gama sannan Baba ya dube su dukan su yace "Alhamdulillah, tabbas kuna ƙoƙari, ku ci gaba da kasancewa haka, kuma dama ubangiji ya yi alƙawarin sauƙaƙawa duk wanda ya ɗauri niyyar karatun littafin shi mai tsarki, Allah ya muku albarka, Allah ya baku zuri'a ta gari, Allah ya ci gaba da dafa muku a dukkannin lamarin da kuka saka a gaban ku."

A ladabce suka amsa da" Ameen Baba." Daga nan ya ɗora ma Yusrah sannan Hannah, kafin daga bisani Mama ta kalle su tace" Ku tashi kuyi shinfiɗa ku kwanta ku huta."

Miƙewa Hannah tayi sai Yusrah da ta langaɓar da kai tace" Mama ni kam da waje mukayi shinfiɗa, ya fi sanyi wallahi."

Kallonta Mama tayi tace" Yanzu Yusrah aka ce ki kwana a wajen nan sai ki kwana? Jiya fa kwana akayi ana ruwa yaf yaf yaf, yau ma kusan sau uku ana yayyafi, ƙasa a jiƙe take ba zata kwantu ba ai."

Ba ta ce komai ba ta nufi ɗaki, nan ta kamawa Hannah sukayi shinfiɗa tare da yin duk abinda suka san ya zama wajibi kafin suka kwanta, Hannah da Yusrah ne a yaloluwar katifa d aya, sai Safwan dake gefen su akan bargo.



*AA ANZA*



Wunin yau ɗin sam ba mai daɗi bane a gare shi, haka ya yi shi ba wani armashi sai tarin tunani da ɓacin rai, sallah kaɗai ke fitar da shi daga gidan, har saida ya yi sallah isha'i sannan ya kira Chef ya faɗa masa yana son ganin shi, ko ba maganar aiki ba Chef ya san Aswan mai zuwa gidan shi ne kai tsaye, dan haka ya bashi izinin zuwa kai tsaye.

Cikin wani tsadadden yard ash color ya shirya da takalmi flat ƙirar India sannan ya fito yana zuba ƙamshin turaren Creed, Meem da Angel na ganin shi suka fahimci shirin shi na fita nesa ne kuma wuri mai mahimmanci, dan haka tiryan tiryan suka biyo shi har bakin mota, yana buɗewa ya shiga ya zauna suna tsaye suna kallon shi saɓanin fitar da ya yi ta safe, irin kallon da suke mishi ya sa shi ɗaga musu hannu yana murmushi yace "My baby's, yanzu zan dawo, saboda ku kawai."

Jan ƙofar ya yi ya rufe sannan ya fara baya baya, har lokacin suna tsaye suna kallon shi sai Meem da ke ta ɗan kukan nan irin na mage can ƙasa ƙasa irin dai ba ta son rabuwa da shi, saida ya fice daga gidan kafin suka koma ciki duk babu mai karsashi a cikin su kamar wasu mutane dai.

Babban gida ne da sojawa ke gadin gidan, sanin wa ye shi a sojawa da kuma matsayin sa a gurin Chef ya sa suka sara masa a ladabce sannan suka buɗe mishi ya shige, kai tsaye Chef dake ya san da zuwan shi kuma ya san magana mai mahimmanci ce ta kawo Aswan gidan shi, ƙaramin office ɗin shi dake ɓangaren shi suka shiga suna ƙara gaisawa.

Chef na fuskantar shi tare da karantar yanayin shi yace "Boy, ya ake ciki?"

Ɗan muskutawa Aswan ya yi yana duban Chef ɗin da girmamawa, amma kafin ya yi magana sai aka ƙwanƙwasa ƙofar ofishin, Chef dake ya san ya umarci uwar gidan shi da ta sa ɗaya daga cikin yaran shi wata ta kawo abun sha yace "Shigo."

Buɗe ƙofar aka yi, inda matashiyar budurwat ta buɗa bakin ta a nutse tana faɗin "Assalamu alaikum."

Nutsuwar muryar ta sa Aswan kan shi ɗan juyawa ya kalli mai shigowar, *NABIHA* ce ɗauke da faranti jere da ababen sha, sanye da doguwar rigar atamfa ɗinkin mai kyau, iya ɗan kwalin atamfar ne kawai a kan ta ta masa ɗaurin ture kaga tsiya, a ƙalla Nabiha za ta kai shekara 20 a duniya ko ma ashirin 21, kyakyawa ce kuma fara hakazalika doguwa, murmushin dake kan fuskar ta a lokacin ya sa Aswan ɗn zuba mata idanu, sai kuma ya ɗauke kan shi cike da rashin nuna ko in kula ya bayar kan teburin dake gaban su.

Nabiha kuma na ƙarasowa da wannan fara'ar tace "Yaya AA ina wuni?"

Ba tare da ya sake kallon ta ba kuma ba tare da fara'a ba ya amsa da "Barka."

Ba tare da damuwa da yadda ya amsa mata ba yace "Barka Yaya, ina twins? Da Abrar?"

Ɗan jim yayi yana ƙurawa Chef idanu dake ta doka murmushi, Abrar, shi wallahi sai sunan ma ya so ɓace mishi, ashe fa ƴar gidan su ce, ƴar matar nan ko? To me ke haɗin shi da ita? Jin bai bata amsa ba ga kuma Abban nata da ya mata godiya ya ce ta bar shi ba sai ta zuba ma ya sa ta juya tana faɗin "Yaya, Mom ta ce na faɗa maka saura kayi halin naka wai."

Yanzu kam kallon ta ya yi, dattijuwar nan akwai kamala tana kuma birge shi, ya kuma gane me take nufi da kar ya yi halin, wato kar ya tafi bai je suka gaisa ba, ɗan murmushi kawai yayi wanda Nabiha ma bata san ya yi ba dan har ta fice, Chef dai ya gani yana sake jadadda masa ƙorafin da ya baro tana yi na rashin shigar shi idan ya zo.

Kwalbar lemu ya ɗauka irin masu tsadar nan zai buɗe Aswan ya mishi alamar a'a, sannan ya ɗan ɗauki na gwangwani Shwimpess ya ajiye gaban shi alamar ya ishe shi ma wannan, dan haka Chef ya sake tsura masa idanu yace "Uhm! Ina jin ka my boy?"

Numfashi ya sauke a nutse yana ɗan mamatsa tafukan hannayen shi yace "Chef, hukuncin da kuka yanke min ya min tsauri dayawa, dan Allah ku sassauta min ko da ta hanyar dawo da watanni ne zuwa wasu kwanaki."

Ɗan zaro idanu Chef ya yi yace "Aswan, ka san me kake faɗa kuwa? Hukuncin wata biyar kake so a dawo da shi wasu kwanaki?"

Tsurawa Chef idanu yayi yana kallo, hakan ya sa Chef girgiza kai yace "Ba zai yiwu ba Aswan, da zan iya yin wani abu da na yi tun ranar da abin nan ya faru, ka gane wani abu ɗaya, abun nan ya faru ne gaban idanu dayawa, da a ce da ka shaƙe Col. Garba daga kai sai shi ne haka ta faru, da zan iya sulhuntaku ba sai maganar ta fiya ba, to amma fa sai da ka ƙwace shi a hannun ka, kowa ya gani kuma ya bayar da shaida, sannan a gaban wasu manya aka yi haka, dan haka kayi haƙuri Aswan, ba zan iya yi maka komai ba akan maganar nan."

A raunane Aswan ya sake duban shi yace" Za ka iya Chef, sai dai idan baka yi niyya ba, kai ne babba a wurin nan, idan ka ce ka dawo da ni nan da wasu kwanaki ba wanda zai kalle ka ma bare ya ɗaga maka murya."

Kafe shi da idanu Chef yayi tare da jingina a bayan kujerar yace" Kuma kai ka yarda mu karya dokar aikinmu?"

Ƙurawa juna idanu sukayi, sai kuma ya sake cewa" Ko kana so mu zama ɗaya daga cikin wanda basa bin dokoki ne? Sannan mu zama ɗaya daga cikin mutane azzalumai? Ba ma wannan ba Aswan, idan nayi haka nima ba za'a barni ba, za'a iya kai ƙarata a na gaba da ni saboda ƙiri ƙiri mun tauye doka, za'a ga haka a matsayin dan kana ɗan aminina ne, ko kuma dan mahaifin ka na da ƙarfin iko a ƙasar nan, daga ƙarshe ni da kai zamu iya rasa aikinmu gaba ɗaya."

Nauyayyar ajiyar zuciya Aswan ya sauke yana mai gasgata duk abinda Chef ɗin ya faɗa, kafin ya sake kallon shi a tausashe yace" To yanzu Chef ya zan yi? Ba zaku gane irin ɗacin da nake ji a zuciyata ba saboda yau na tashi ga kaki gabana amma ba zan iya sakawa naje inda ya dace da shi ba, ba zan iya lamuntar wannan rayuwar ba har na wata shida."

Cike da tausayawa Chef yace" To ka karɓi ɗaya daga cikin aikin da mahaifin ka ya baka zaɓi mana?"

Da sauri ya kalli Chef ɗin, ba abun mamaki bane dan yasan da maganar, girgiza kai yayi yace" Ba zan iya ko ɗaya daga ciki ba, sannan da Dad ya lissafa waɗannan ayyukan, idan ka cire na kamfanin shi duka fa sauran na gwamnati ne, kenan za'a tunɓuke wanda yake aiki akan wurin ni na hau? Ko kuma zan hau ne saboda kawai ni ɗan wani ne?"

Murmushi Chef ya yi yana kallon shi yace" To yanzu ni wane irin taimako zan iya yi maka?"

Kallon Chef ɗin ya yi, sai kuma yayi shiru yana tunanin abubuwa da dama wanda ya wuni yau yana tunani a kan su, jin zuciyar shi ta gamsu da abu ɗaya yasa yayi saurin gyara zama yayi gyaran murya da" Ugyhemmm!" Sannan ya ɗora da" Chef, kaga ai kowane soja da inda ya fi ƙwarewa a kai, wane aikin shi daga wannan daji zuwa daji ne, wani kuma iyakar shi cikin gari, wani bakin boda ne, wani ma a harkar daƙile nakiya ya fi ƙwarewa, Chef, wani kuma sojan sama ne, wani sojan ruwa, wani kuma soja ne da ya fi ƙwarewa a harkar bincike, to kamar dai haka, Chef za ka iya taimaka min?"

Ƙanƙance idanu Chef ya yi yace" Akan me zan taimaka maka ɗin Aswan? Sojan ruwan kake so ka zama yanzu? Ko sojan sama?"

Murmushi Aswan yayi ya girgiza kai a tausashe yana ɗaga girar shi ɗaya yace" Na bincike dai Chef."

Tsai! Chef yayi yana kallon shi, ba zai tambaye shi zai iya ba? Saboda ya san zai iya ɗin, idan yayi niyyar aiki ko ya saka abu gaba da bin ƙwaƙwafi yake kai shi ƙasa, sai dai matsalar anan an dakatar da shi, bashi wannan aiki yanzu taka doka ne shi kuma dole sai da sahalewar wasu na ƙasa da shi, sannan sai sun yi rubutu sun tura sama...

Haɗe hannaye Aswan yayi alamar roƙo yace "Please, kar ka ce min ba zaka iya ba shima *Abuh*."

Kallon shi dai Chef yake yi kafin ya numfasa yana gyara zama a tausashe yace "Aswan abin da kake nem..."

Katse shi yayi da "Na sani Abuh, abu ne mai wahala, amma na san zaka iya yi min, ko dan ƙaunar da kake min."

Kallon shi dai chef yake yi kafin ya ɗan jinjina kai yace "Ko haka zai fari Aswan dole sai dai idan zaka zama jami'in bincike na sirri ne, sannan nayi haka ba tare da sanin na ƙasa da ni ba, sai dai kawai na tura takarda a sama."

Da jin daɗi Aswan yace "Yess! Abuh za ka iya yin haka ma, ni kuma ba zan baka kunya ba."

Jinjina kai Chef yayi ya miƙe tare da faɗin "Shikenan, ina zuwa?"

Da kallo ya bishi har ya fita sannan ya sauke wata irin bazawarar ajiyar zuciya, yanzu ya fara jin sanyi na ratsa shi saboda ya samu tabbacin ba bar aikin soja ba. Ya kuma minti talatin zaune Chef bai dawo ba, dan daga sama ne ya kira shugaba mai mulkin jami'iyar dake mulki wacce ta zama abokiyar hamayyar jam'iyar da mahaifin Aswan ɗin ke takara, ɗan siyasa kuma yana so ya ga lagon abokin hamayyar shi, dan haka ba ɓata lokaci aka ba Aswan damar yin wannan aiki ko ba komai za'a riƙe hakan a matsayin abinda zz'a zunguri ɗan takara na gaba da shi.

Chef na shigowa ma rubutu ya fara yi kan kwanfutar shi kafin ya gama ya tura shi a sama sannan ya jinkirta dan a dawo mishi da amsa da sa hannun shugaban, bai fi minti goma ba dake dama an san da maganar aka turo saƙon sannan ya kwafi takardar ya tura ta a wata na'ura take ya cirota a takarda, alƙalami ya ɗauka shima ya saka sa hannun shi daga ƙasa sannan ya miƙawa Aswan yana faɗin "Aswan Ali Anza, dosarmais tu seras un officier militaire, mais un agent secret en enquete, ce document contient la signature de monsieeur le President e ma signature aussi pour te permettre d'entrer ou tu vex, a condition que tu fasses attention a notre etat, si tu continues ton comportement de rupture la loi dan la communautes, alors vous serez complètement renvoyer dan l'armee (Aswan Ali Anza, daga yanzu ka zama jami'in soja amma na sirri akan bincike, wannan takardar na ɗauke da sa hannun mai girma shugaban ƙasa da ni ma na lamunce maka ka shiga duk inda kake so, sai dai ka kula da sharaɗinmu, idan ka ci haba da halin ka na karya doka a cikin al'umma, to za ka zama sallamamme daga soja gaba ɗaya)."

Da wani irin farin ciki Aswan ya miƙe ya karɓi takardar yana sarawa Chef sai godiya yake ta yi mishi da alƙawarin ba zai saɓa dokar ba in sha Allah, wannan farin ciki ya sa ya fice bai ko bi ta kan shiga cikin gidan ba, Chef ma dke ba tare suka fita ba nan ya barshi yana waya da bayar da tabbacin ya fa bashi takardar, sai fatan nasara kawai.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*7*





A gaggauce YUSRAH ta shirya suka fito tare da Hannah da Safwan suka nufi bakin titi, sai da suka ƙarasa ne kowa ya ɗauki hanyarsa domin shi auta makaranta zai nufa, Hannah kuma University, YUSRAH kuwa asibiti wajen aikin ta.

Tunda ta zo asibiti yau a kan ƙafafuwansu suke sunna aiki ka'in da na'in, ba ji ba gani ba kuma kama hannun yaro, domin asibitin ɓangarori ne musamman su dake ɓangaren kula da mata masu ciki da haihuwa, ta shafi duk wani abinda ya shafi haihuwar dan kuwa ba wai iya haihuwar bace ake amsa a wajen dukkan wani kula a nan ake ba mace da jaririnta na dangin lafiya, ga lokaci ne da zaka ga a ƙalla kafin a tashi an karɓi haihuwar mata fiye da ashirin a rana guda, tamkar harda na wani garin ake karɓa , koda yake na ƙauyukan dake kusa da garin sukan shigo nan ɗin dan su haihu.

A hankali ta furzar da hucin numfashi, zuciyarta cike da saƙe saƙen abubuwa kaɗan kaɗan da take tsintar waɗanda basu yi mata ba, suka fara kaiwa ƙwaƙwalwarta tunani kala kala


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login