Showing 6001 words to 9000 words out of 397328 words
sake maida duban shi kan wayar ya sa ta fahimci abinda yake mai mahimmanci ne, tana ƙarasowa da wata matsakaiciyar flask mai kyau ɗauke da haɗin shayin da take dafawa Dad ɗin da ganyen shayi irin na asalin bugaje ta aje kan wani ɗaramin desk mai kyau da ƙyalli kamar madubi tana faɗin "Mon Excellence, lafiya dai, kamar ina ganin damuwa a fuskar ka?"
Duk da hausar ta ta ba sosai take fita ba saboda buzanci ya fi ƙwacewa, amma dai sarai ya gane me take nufi, dan haka ma ya fuskance ta sosai yana sauke numfashi yace "Mutumin ki nake kira, amma wai wayar kashe?"
Ita ma nauyayyan numfashi ta sauke tare da waina idanun ta, takawa ta fara yi ɗaya bayan ɗaya tamkar wata ɗawisu, dama a jiƙe rayuwar ta ta taso cikin kuɗi, dan haka kamar wacce ta gaji sarauta haka komai nata take yin shi a nutse, uwa uba kuma ƙibar dake gare ta musamman ta baya (mazaunai) ta ƙara sabbaba mata tafiyar nutsuwa, saida ta zauna bakin gadon Dad ɗin dake tsakiyar ɗakin kamar zaiyi magana, a hankali take sauke numfashi tana kallon mijin nata da ta rasa gane irin ƙaunar da yake ma Aswan ta sa ya manta da yanzu shi ba yaro bane, sannan aikin sa ba inda ba zai iya kai shi ba na kuma kwanaki ko satittika ko ma watanni. Cikin tausashiyar murya tace "Mon Excellence, me ya sa zaka damu to? Kamar ba ka san aikin Aswan ba?"
Shima da ta shi nutsuwar da izza ya matsa kusa da ita ya zauna kan wata lafiyayyar kujera irin wacce mutum idan ya zauna yake jinginar nan sosai har yana ɗan lilawa bayan ya miƙe ƙafafun shi yadda yake so sannan yace" Na sani, amma kin san indai yana gari bai cika jimawa haka ba."
Cike da gamsuwa tace" Hakane, amma dai yanzu ga shayin ka nan ka sha, sai ka taso mu kwanta, wataƙila ma yana gidan shi fa, ta yiwu ya yo dare ne kawai bai leƙo nan ɗin ba."
Shiru yayi yana ƙan ɗora maganar ta a ma'auni, kafin daga bisani ya jinjina kai a tausashe yace" Shikenan, zuba min."
A nutse ta miƙe ta nufi flask ɗin tare da wani kofi kamar na zinariya ta fara zuba mishi, ita kaɗai dake tsayen nan take murmushi, ba dan komai ba sai dan ganin ita matsalar ta da Aswan duk ta girmi wacce mahaifin shi yake da da shi, ƙwarai tana so ya bar aikin soja saboda bai dace da shi ba, sai dai duk son da take masa da barin aikin nan bai kai na aure da take so ya yi ba, ta yi maganar ta laluma da nasiha, ta kwatanta masa shekarun sa ƙara tafiya suke yi saboda yanzu haka yana 34 ne, kai har misali ta bashi da ƙannan shi *Humed* da ko yanzu aka ce matar sa ta haihu ba zasu yi gardama ba bayan suna da wani ɗan, ga ƙanwar shi *Intisar* da ta jima da yin auren ta duk da manyan burikan ta, yanzu haka yaran ta biyu a haka ma dan tana saka dogon hutu kafin ta haihu, ƴan biyu dake da shekara 20 ne yanzu a gaban su, tana da buri a kan su na ganin sunyi karatu sosai sannan su samu wani gwagwaɓan aiki, amma duk da haka daga ƙarshe aurar da su zatayi, amma Aswan, wanda ƙannan shi ke masa alkunya da *chairman* wani sa'ilin kuma suce *oga*, abokai da abokan aikin shi ke masa kira da *AA Anza*, duk sanda ta masa maganar ya yi aure amsa ɗaya zuwa biyu yake bata.
"Zan yi Anna." Ko kuma yace "Akwai abinda nake jira, idan na gama zan yi." Sama da shekara huɗu yake faɗa mata haka, amma har yanzu ɗin bai yi ba, ba irin ƴan matan da basu dinga jawo su a jikin su ba ko Allah zai sa a dace, amma daga ƙarshe ma shi ko fuskarsu ba ya gama shaidawa.
Ba ta san menene burin shi ba? Bata san me yake shiryawa ba? Ba ta san menene harin shi na gaba ba? Sannan ba ta san yaushe ne ya tanadarwa kan sa dan samun abokiyar rayuwa ba? Abu ɗaya da ta sani duk ranar da wannan damar ta zo, to ba zata ɓata lokaci ba wajen ɗaura masa aure ta huta, dan a duniya ba abinda take tsoro da fargaba kamar AA ya saka kan sa harkar neman mata, har yanzu ba ta shaidar sa duk da ta haife shi, amma dai abinda ta sani na zahiri da baɗini game da shi, ta san baya kula mata.
Haka daren nan ya shuɗe ba tare da Dad ya rintsa idanun shi da kyau da sunan bacci ba, saboda shi dai a duniya ba abin da yake so sama da ɗan nashi na farko, a kan Aswan ne ya fara sanin daɗin soyayar ɗa, dan haka ba ya tamtama gaba ɗaya soyayyar sa a kan sa ne, akwai abubuwa da ya sani game da AA da komai rintsi ba zai iya canja ra'ayin shi a kan su ba, misali duk yadda zai ɗaga hankalin mutane a gidan nan ya fita ran shi É"ace, duk in da ƙarfe 10:00 zuwa 11:00 sukayi, to zai zo gidan nan ya musu sai da safe sannan ya wuce na shi gidan, kuma ma duka bai fi shekara ɗaya da rabi da ya yi gidan nan ba ya tare a can saboda kawai ya ce suna yawan yi masa maganar aure da kuma barin aikin da shine rayuwar sa. Hakazalika duk gaggawar da yake yi da safe ba ya tsallake unguwar nan sai ya zo ya gaishe su da safe sannan ya wuce uzirin shi, sannan duk ranar alhamis da litinin a gidan yake cin abincin dare saboda azumin nafila da yake yi, sannan duk ƙashen wata in dai yana garin nan to safiyar da ta kama ta ƙarshen wata ya kan je gona tun safe sai yamma yake dawowa, Aswan yaro ne mai baiwar gaske, tunda ya taso Allah ya masa nasibin duk irin da zai shuka to a kwana ɗaya zuwa na biyu zai fito da izinin Allah, hakan ya sa ma bayan ya mallaki hankalin shi saida ya fara karantar harkar noma da kiwo, duk da matsayin da shi mahaifin shi ya taka a rayuwa, daga ciki har da kasancwar mai neman shugabancin al'umma duk da dai shima jawosa ne akayi ta ƙarfi a harkar, amma ba ya ganin zai iya samun abinda bai samu ba kafin yanzu ta dalilin siyasa, sai dai kamar yadda aminin sa chef ya faɗa ne, zai iya shiga siyasa ko dan ya kawar da hankalin al'umma da suka fara ƙiyasta masa dukiyar sa da kuma tamtamar ta inda yake samun ta. Duk da wannan Aswan bai yada noma da kiwo ba, kusan sune abu na biyu da ya fi so a rayuwar sa bayan aikin soja, ga kuma irin albarkar da yake samu sanadiyar haka ɗin, ma fi yawan arziƙin da ya mallaka na ƙaashin kan shi duk wannan noma da kiwon ne yake kawo masa shi. Kallon Anna yake dake baccin ta a nutse, sai dai shi ya gagara samun haka saboda yawan farkawa da yake yi sannan tunanin AA ya sake diro masa a kai.
*WASHE GARI* Tunda garin Allah ya waye bayan ya dawo daga masallaci ya kasa komawa barcin da yake yi na safe ya zauna a falonsa da waya a hannunsa yana sake gwada kiran numbar Aswan, amma amsar ɗaya ce a kashe, shi kuwa ya nace kan sai an amsa shi. A hankali ya ɗaga dubansa jin tafiyarta a lokacin da ta gama jan carbi ta ga shiru bai shigo kwanciya ba sai ta miƙe ta sauko, a nutse ta zauna gefensa tana kallonsa ta ce" Mon excelence kana da sarkafa da Aswan, plz ka ɗan sanyaya mana, ka san shiru na nufin lafiya, da ace da wani abu da tuni an neme mu ko."
"Ki gane baya kashe wayarsa ko ina yake, idan wayarsa a kashe ba zan taɓa yarda cewar lafiyarsa ƙalau ba." Ya faɗa a tausashen shima yana jin har kansa na sarawa dan baya haɗa damuwar ƴaƴan sa da kowa bale Aswan da ake ganin ya fi sonsa cikin ƴaƴan sa. Ita ɗin ma sai ta ji hankalinta na neman tashi, har ga Allah ita ta ɗauki shirunsa matsayin sun yi rigima da uban jiya shi yasa ya kashe wayar dan uban ya neme shi yace ya haƙura ya yi aikinsa, sai yanzu da ya tuna mata ko me za'a yi baya kashe waya kuma a rasa shi ɗif sai ta ji itama hankalinta na neman tashi.
A tausashe ta ce" Ka yi kiran Chef mana mu ji ko ya fita aiki bamu da labari ne?"
Miƙewa Alhaji ALIYU ya yi ya shiga haurawa yana faɗin "No! Bari in je da kaina."
Jin haka ita ma sai ta nufi nata ɓangaren ta shiga kimtsawa da gaggawa, dan ba zata iya zama ya tafi shi kaɗai ba, yanzun ne hankalinta ke neman tashi a kan yaron nata, ko da sun yi rigima da babansa ai ita babu abinda ya haɗa su marar daɗi ko?
*YUSRAH TURAKI*
Kasa aiwatar da komai Yusrah tayi tun da aka ambaci wai tiyata, matar da ke daf da haihuwar ce za'a ma tiyata? Abun ya ɗaure mata kai, gashi kuma duk wanda zata iya tambaya ya fahimtar da ita tuni aka shiga shirin kai matar nan ɗakin tiyata, kafin daga bisani Sakina ta fito sanar da ahalin ta halin da ake ciki.
A duba na tsanake da Yusrah ta ma ahalin, sai ta fara tunanin ko dai dan suna masu hali ne ya sa za'a mata tiyata dan a karɓi kuɗin? Idan ba haka ba ita kambata ga wani dalili ba, amma kuma asibitin nan ai tafi ƙarfin a ce za'a yi haka dan kuɗi kawai... Muryar Sakina ce ta dawo da ita hayyacin ta tana faɗin "Karɓi mana Yusrah, gaggawa fa ake, mijin nata ya saka hannu."
Zabura tayi kamar wacxe aka gaurawa mari ta kalli Sakina a tsorace, sai kuma ta kalli abinda Sakinar ke miƙo mata, abun aski ne da wasu abubuwan tana umartar ta taje ta yiwa matar nan, karɓa ta yi a sanyaye sannan ta bi bayan Sakina dake ta zabga sauri saboda zuwa ambulance ɗin da zata ɗauki matar zuwa ɓangaren tiyata na masu kuɗi.
Ba ƙaramar godiya ga Allah Yusrah tayi ba da bata samu wani dattin da zata aske a jikin matar ba, dan kuwa ruɗanin da tale ciki da ace sai ta mata askin nan, to shakka babu da sai ta yanke ta da abun askin nan mai masifar kaifi.
Su uku ne mata masu taimaka ma likitan nan, kowace na aikinta yadda ya kamata, amma Yusrah da mamakin kamannin dattijon ke bata mamaki ta kasa yin nata aikin.
Ya ɗauki sakanni da tara hannun shi bayan ya sanar ta bashi wani ƙaramin almakashi, jin babu alamar za'a miƙo masa ya sa ya ɗago kan shi, ganin Yusrah tsaye ta zubawa kan shi dake luf luf da gashi idanu ba ƙaramin ɓata masa rai ya yi ba, a mugun tsawace yace "Ke! Mahaukaciyar ina ce? Tun yaushe nake faɗin ki bani almakashi?"
Tunda ya kirata da ke ta zabura tare da juyawa inda farantin kayan aikin yake, jikin ta na rawa rawa ta ɗauko ta miƙo mishi ba tare da tace uffan ba, karɓa ya yi tare da kwaɗa wani wawan tsaki ya furta" Shirme kawai."
Lumshe idanu ta yi cike da jin ba daɗi wa ita da matar da ake ma aikin nan, ita kam tasan wannan matar an mata tiyata ce dan wata manufa amma ba dan ta kasa ba ko wata matsalar, a ɗan zaman ta asibitin nan ta ga abubuwan mamaki, amma bata ga fiye da na yanzu ba gaskiya.
*A* sanyaye sosai ta fito daga ɗakin zaman su bayan ta gama shirin tafiyar ta gida dan yau ba aikin kwana za ta yi ba, da tausayawa sosai ta kalli Ahalin matar nan dake ta murna anyi aiki lafiya, hatta Sakina kasa yi mata ban kwana ta yi haka ta tafiyar ta da tunanin ta yi sallar magriba a gida, amma a yanayin da take ciki game da lamarin asibitin nan bazata iya anan ba.
*Tun* a ƙofar gida da adaidaitawa sahu ya ajeta ta samu Baba dake zaune ƙofar gida kan tabarma tare da maƙwabcin su, har ƙasa ta durƙusa cikin sanyin jiki tace "Ina wunin ku Baba?"
Maƙwabcin nasu ya fara amsawa da "Lafiya lau Yusrah, an sauko daga aikin?"
Da kulawa da kuma farin cikin ganin ta dawo lafiya bayan ya ɗan fara tunanin ko lafiya ta kai magriba ya amsa da "Lafiya ƙalau Yusrah, sai yanzu? Me ya tsayar dake? Bayan kin faɗa mana yau da yamma za ki tashi."
Cikin muryar jimami tace "E Baba, har na shirya zan taho sai aka kawo mai naƙuda, dole na tsaya har aka gama mata tiyata."
Da tausayawa suka jinjina kai suna addu'ar samun lafiya ga matar sai Babab Yusrah da ya ɗora da "Ku kuma Allah ya baku ladar aikin."
"Ameen Baba." Ta faɗa tana miƙewa ta shiga ciki, da sallama ta shiga gidan, saidai ba kamar yadda ta saba yi kullum ba, Safwan ne ya fara amsawa da murna yana tarban ta.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨??👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*4*
Bayan ta shirya ta ɗaya falon ta ratso ta shiga falo na biyu har zuwa ɗakin cin abinci da tasan wannan lokacin mutanen gidan suna can dan karyawa su tafi sabgogin gaban su, haka kuwa aka yi ta samu wasu daga ciki zaune suna karin kumallo cikin, duk da ba wata hira suke yi ba amma dai fuskokin su a sake suke, ba wai rashin tsari bane ya sa ko mutanen gidan basu taru ba suke cin abinci, kowa da aikin shi ne hakan ya sa idan dai ka zo table ɗin to kawai za ka ɗibi abinda kake so ne ka ci, Anna da Dad ne kaɗai ko wanene kai za ka je har inda suke ku gaisa sai kayi tafiyar ka. Cikin tafiyar nutsuwa ta ƙarasa wani haɗa makeken table dake ɗakin cin abinci wanda wasu labulaye shara shara kalar bleue suka ƙawata wurin, tana ƙarasowa mutanen dake saman kujeru da alama duk ita suke jira, da fara'a ta ƙaraso tana jan kujera cikin harshen buzanci ta musu sannu, matashin saurayin dake zaune da shekarun shi zasu kai 28 ya fara sakar mata murmushi sosai yana aje wayat hannun shi kan table ɗin yace "Sannu da fitowa *Anna*."
Cike da kulawa ta kalle shi tana murmushi ta amsa tare da ɗorawa da "Ina ɗan rigima?"
Ƴar dariya ya yi yace "Har na fito basu tashi ba, dake yau ba su zuwa makaranta."
Da kai ta amsa mishi alamar gamsuwa, sai ƴan mata biyun da ɗaya cikin ladabi tace "Anna ina kwana?"
Ɗayar kuma ba yabo ba fallasa tace "Ina kwana *Aunty*."
Da sakin fuska ta amsa mata duk da dai bata jin daɗin yadda *Abrar* ɗin har yanzu ta kasa kiran ta da sunan Anna, tunda a ganin ta ai ta cancanci wannan sunan, dan kuwa a gidan nan ƙanwar mijin nata ta haifi cikin ta, bata nuna mata wani banbanci tsakanin ta da ƴan biyun ta ba, amma haka ta tashi tana banbanta sunan ta da na mahaifiyar ta. Ba ta zauna ba saboda ta zo su gaisa ne dama sannan ta jira fitowar Excellence su wuce tare, tana kallon Abrar ɗin duk dan ta fi nuna kulawar ta akan nata ƴaƴan cikin harshen hausar ta da ba sosai take fita ba, hasalima ga mai sauraro bai cika ganewa ba tace "Ina *Nawal*? Bacci take ko?"
Da sakin fuska Abrar ɗin tace "A'a ta tashi, tana fitowa yanzu, waya take."
Da mamaki ta kalli Abrar ɗin sosai tana shirin tambayar ta waya kuma? Yanzu da sassafen? Sai kawai *Humed* dake zaune ya kalleta fuskar shi a ɗan haɗe da tashi hausar da ma gwara ta uwar yace "Dwa take wayya yanzu (da wa take waya yanzu)?"
Shiru Abrar ɗin tayi sai kallon Nawal take da ta fito sanye da Italy abaya kalar pink da ta mata kyau, tubarkallah ita da ɗaya daga cikin ƴan matan dake zaune wato *Mannal* kamar su ɗaya tak tak, da fara'a take tahowa, amma kallon da Humed ya sakar mata ya sa ta sunkuyar da kai tana turo baki gaba har ta ƙaraso, ta bayan Anna ta zagaya tare da rumgumota ta bayan cike da ƙaunar juna tana lumshe idanu cikin harshen buzanci tace "Anna ina kwana?"
Cikin farin ciki da ƙaunar Nawal ɗin a duk cikin ƴaƴan ta itama ta haɗa kai da ita ta shafo kumcin ta tace "Barka da safiya Nawal."
Sakin mahaifiyar tasu tayi