Showing 300001 words to 303000 words out of 397328 words

Chapter 101 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70088

ƴar kuma? Na tafi ni kaɗai mana, sai kuje tare da ita."

Da wani yanayi kamar na shagwaɓa kamar na rarrashi Anna tace" Please jikan Anza."

Murmushi yanayin na Anna ya bashi, sai kawai ya jinjina kai alamar to, hakan ya sa Anna tallabo ƙeyar shi da hannun hagun ta ta kai bakinta saman goshin shi ta sumbata sannan ta shafa kumcin shi ta juya tana sakar masa murmushi, gaba ɗaya sai ya nemi haushin haɗa shi tafiya da Nabihat ya rasa, da karkasashi ya zagaya mazaunin shi ya buɗe ya shiga yana jiran Nabihat ɗin ta ƙaraso.

Nabihat kuma tunda ta ga abinda Anna ta yi ta kawar da kai ta taɓe bakin ta tana ayyana _'Ki yi ki gama, wallahi na same shi a hannuna ganin sa ma wuya zai miki bare wannan shafe shafen, aikin banza kawai, su a wani jariri suke ɗaukar sa hala?'_


Ba ƙaramin farin ciki ne ya baibaye ta ba da Anna ta ce mata ta tafi zasu tafi tare, da wannan rawar kan ta je ta buɗa motar ta shiga ta zauna tana ta yage baki, da ɗaya bai kalli inda take ba ya ja motar sukayi gaba, shi dama idan a gaban Y. Turaki ne da ta cewai sun dace ya ke ɗan kulata, ba dan komai ba sai dan yana so ya gane me take nufi da shi da idan ta ganshi bakin ta baya rufuwa, sannan ta dinga masa kallon wuce ƙa'ida tare da masa wasu irin kwarkwasa kala kala, shin a kwarto take ɗaukar sa ko me? Ta ɗauka ɗan iska ne shi? Kuma idan ma yana yi kenan sai ya yi da ita? A haka?

Sun yi nisa a tafiya kamar ba da wata halitta aka haɗa shi a motar ba, Nabihat kuma tun bata damuwa tana dai satar kallon yadda yake murza sitiyarin motar cike da wata irin ƙwarewa da izza da hutu da ya ratsa shi, saboda irin tuƙin nan yake yi da kana ganin shi kake sallamawa cewa wanda ya jiƙu a cikin kuɗi ne a motar ba wanda ya musu taka-haye ba, yana ya kwanta kan kujerar sosai ya karkace abun ya birge ta ainun, amma da suka jima a haka sai ta gaji da shirun da yadda ya basar da ita kamar bai san da halitta a wurin ba.

Ƙara gyara zaman ta tayi ta dube shi cikin kissa da maƙale murya tace "Yaya AA."

Yadda ta kira shi da yanayin muryar da ta yi magana ya sa ya yi saurin kallon ta yana yatsina fuska, sai kuma ya ɗauke kai kawai ya mayar kan titi, a ganin ta ita kuma ya amsa mata kenan, sai kawai ta ɗora da "Wai kai Yaya ba ka damuwa da yadda har yanzu ba'a tsayar da ranar auren mu bane?"

Saida ya fara wara idanun shi akan titi sannan ya ɗan juyo ya kalle ta, ba ya damuwa? Dan ba'a saka ranar auren su ba? Hmmmm! Irin wannan ne hausawa ke cewa magana ɓannar baki, sai kawai ya sake mata shiru yana tuƙin shi a cikin maƙoshi ya iya ce mata" Um um."

Da jin haushin amsar da ya bata tace" Kenan baka damu da ni ba Yaya AA? A ganina ai aurenmu ne zai zama gagarumi a gare ka, tunda naga waccen na *haɗi ne*."

Yanzu kam sosai ya kalle ta ba dan ya so kula ta ba yace" Me ye zai dameni to? Wataƙila iyayen ki basu shirya rabuwa dake da wuri bane."

Galala ta kalle shi, sai kawai kalli titi ita ma kamar yadda ya yi yana sake cije fuska sosai, ba wanda ya sake cewa komai har suka isa ƙofar gidan su aunty Intisar lokacin ana shirye shiryen fara kiran sallah magriba. *Hakan* kuma daidai da fitowar su Nawal suna ta hira da dariya sun nufi motocin su dake ajiye.

Kamar yadda duk wanda ya fito daga gidan sai ya kalli motar, haka ita ma ta yi sai dai kawai abinda ake rayawa ne a rai ya bambamta, dan Intisar da su Manal duk basu yi tsammanin ganin shi nan ba, suna kuma tambayar kawunan su shima rakasu aeroport din ya zo ya yi? Haka Yaya Mubarak ma yake wannan tunanin yana kuma sake gasgatawa lallai Aswan akan ƴan uwan sa zai iya komai, dan gaskiya gidan nan idan kaga ya zo to Intisar ce ta haihu.

Aunty Intisar da Yaya Mubarak ne suka nufi motar sanda Nabihat ke fitowa ganin shima zai fita ɗin, lokacin ne ma kowa ya gama tabbatar da wa suke tare, ba wanda bai yi mamakin haka ba gaskiya, amma kuma ba wanda ya nuna bare ya ce zai tambayi garin ya ya haka ta faru? Gaisawa sukayi da su ya shiga musu fatan sauka lafiya da nasarori akan abinda zai kai su, Anna ƙarama na jikin shi riƙe da hannun shi ta kalle shi tace "Dady2, ina bro? Zamu tafi bamu gan shi ba?"

Murmushi ya mata yana shafa kan ta yace "No baby, son yana can Granny za ta kai muku shi aeroport, happy?"

Faɗaɗa murmushin ta tayi tace "Yeah, thank you."

Yaya Mubarak ya kalla, a sanin sa dai yana da mahaifiya, amma tana nufin ba za ta raka ɗan nata filin jirgi ba kenan ko me? Sannan mahaukaciyar ƙanwar sa ma ya sani sarai suna garin nan dalilin safarowar da ya sa aka musu, ita ma ba za ta raka su ba? Sannan ina wannan guy tsohon yaron Y. Turaki? Sannan ma ai akwai wannan ɗan duniyar shima? Hmmmm! Lamarin gidan su kam sai du'a'i, dan haka shi dai ya sake bashi hannu sukayi sallama.

*Duk* bidirin nan da ake ƴan matan na tsaye na jiran su, haka Yusrah da ta gama zaucewa da tunani kala-kala akan zuwan shi shi da Nabihat ta zuba mishi idanu, kuka take so ta yi ko za ta ji sanyi a ran ta, so take ya kalle ta yadda za ta ƙwala masa harara ta murguɗa masa baki, musamman da Nabihat ta tunkaro su tana yaƙe baki bayan ta masa bye bye ɗin da ko gani bai yi ba ma shi dan ita ba ƙaramin daɗi ta ji ba da aka samu wannan katarin a tsakanin su, shiyasa take ta wani yaƙune yaƙune a dole so take ta nunawa kowa tare suke kuma cikin farin ciki suke. Da ƙyar ta kawar da idanun ta daga kan mutanen wurin tana haɗe wani irin maƙwallato da ya tokare mata wuya, sannan ta ja numfashi tare da haɗiyi hawayen da ta ji sun cika mata idanuwa taf, ko da ta ga Nawal ta shiga mazaunin ta na matuƙiya da sauri ita ma ta gyara tsayuwar ta sannan ta buɗe motar za ta shiga...

Daidai nan ne bayan ya yi sallama da Yaya Mubarak ya kalli inda take da nufin yi mata tsattsauran kallo mai cike da gargaɗin ai dai ni kika raina ko? Kika shiga Nawal ke tuƙa ki ko? Sannan kika fito ba da izinina ba? Amma sarautar Allah yana kallon fuskar ta ta a lokacin da za ta shiga motar ta mako masa wata bazawarar harara, sai kawai ya ji gaban shi ya girɗe ya faɗi shakku ya ɗarsu a zuciyar sa na tunanin to hararan me ta masa? Me ya mata yanzu da suka haɗu nan? Bayan kuma shine aka ma laifi fa, shi wallahi sai ya ji kamar yana so ya bita ya ji kallon me ta masa haka? Idan laifin shi ne sai ya bata haƙuri ai ko? Me ye duniya da abinda ke cikin ta? Kallon sam bai masa ba kuma ya ji hakan ya tsaya masa a rai saboda har da kamar gargaɗi ta aiko masa fa.

A gaban idanun shi ta hakimce gaban motar ta kuma ƙi ɗaga kan ta har suka ɗauki hanya motar su aunty Intisar na biyo ta su a baya, Abrar da Manal suna baya suna ta zabga hirar su, Nabihat ma na bayan su, sai dai fa ta lura da abu ɗaya tare da Yusrah dake gaba shine bata walwala, hasalima titi take kallo bayan tayi tagumi, duk da bata da shaida kan ganin su ne ya ɓata mata rai, amma sai ta zaro wayar ta a jaka tana yin kamar saƙo ake aiko mata ita ma tana mayarwa, kamar daga sama suka ji muryar ta ta bushe da dariya tana kallon wayar ta tace "Kai Yaya AA, abun har da jan rai ma, to bari ka gani..."

Ta yi maganar tana ƙara gyara zaman ta ta ɗan sauke gyalen ta ƙasan kafaɗun ta ta wani karkace za ta ɗauki kan ta hoto, ganin Manal dake tsakiya ta ƙura mata idanu ya sa ta kalle ta sosai, sai kuma ta sake yin murmushi tace" Sorry fa, magana nake a waya, ni da future husband ɗina."

Taɓe baki Manal ta yi inda Abrar ta furta _" Hmmm!"_

Nawal kuma ta madubin gabanta ta ɗan saci kallon ta taci gaba da tuƙin ta, Yusrah kuma da gaske abun sukar ta yake a rai, hakan ya sa duk ƙoƙarin ta na hana kanta kuka saida hawaye suka gangaro mata musamman a ijiyar ta ta dama da ta ɗan kwantar da kan ta, da sauri ta sa hijabin ta ta share ba tare da kowa ya kula da hakan ba sai Abrar, hakan ya sa Abrar ta ji bari su sauka ta gaggauta sanar da ita wacece Nabihat dan ta sha maganin zama da ita, idan ba haka ba za ta dinga ɓata mata rai a banza a wofi har ma ta haɗata da mijin ta da ko tarewa ba su yi ba har yanzu.

A aeroport suka tarar da Aba ya je tare da babban escort ɗin shi Sk, haka ma Anna zuwan su kenan, sai Imran shi ma da ya ɗauko Zahra'u daga gidan su suka taho nan, Bilal ne dai da ba lafiya bai taho ba, kuma ya so ya taho duk da Hajia ta hana, amma Yaya Mubarak ya ce ya bi umarnin ta, ita kuma daga can gida sukayi sallama, amma ita da Hawa'u sun ci alwashin ba zasu zo ba dama saboda abinda ya faru, ba wanda ya damu da rashin su a wurin, dan gaskiya ko shi Yaya Mubarak ɗin tunda dai sun rabu lafiya ai shikenan.

Ana ta burin haɗuwar ne ayi bankwana, amma sai gashi ko da sukayi sallah magriba suka tabbatar da yanzu fa tafiya ce gadan gadan sai kuma aka shiga koke-koke, ba ma kamar Yusrah da ita dama kamar tana jiran a fara kukan ne ta yi shi a bisa gaskiyar ta, dan kukan ta ya fi na kowa a wurin ka rantse da Allah tafiya ce da aka bata tabbacin babu dawowa, saida aka kira su Intisar sannan su Manal suka shiga ɓamɓare ta daga jikin aunty Intisar ɗin, da ƙyar suka raba su sannan aka shiga yi musu bye bye har suka ɓace ma ganin su. Aba ne ya fara juyawa yana share ƴar ƙwala da tissue Anna ta rufa masa baya, sannan su Manal duk suka kama hanya su ma haka ma Imran dake ƙyare kallon ƴan matan uku har ya rasa inda zai tsayar da duban shi, Nabihat ce kawai da bata da irin tsarin da yake son mace da shi ma bata wani dame shi ba, amma ganin tana da rawar kai bai kuma san wacece ita ba a cikin su ya ji da zai samu dama zai iya yin maleji hakanan.

Da wannan kowa ya tafi cike da fara jin kewar mutanen nan, dole ce kawai ta sa za'a rabu, Yusrah kam kuka har suka isa gida ba ta daina ba, wanda hakan ba ƙaramin haushi ya ba wa Nabihat ba, ta yi tsaki ya fi a irga ita ma har suka isa gidan.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*75*




Tunda suka dawo suna tare a falo har Wa'at ma, saida lokacin cin abinci ya yi wasu suka nufi dinning, Anna na tare da su ta umarci Abrar ta kira Yusrah dake ɗaki, jim kaɗan suka fito tare, Anna na kallon fuskarta da tausayawa ganin yadda idanun ta suka kumbura sukayi jajir, kujera ta ja ta zauna, saida ta yi zaune Anna tace "Yusrah, har yanzu ba ki daina kukan ba? To ni ko dai visa zan nema miki sai na tura ki can ke ma?"

Cikin shagwaɓa Manal ta turo baki tace "Haba dai Anna, ai sai dai ki sake yi wa Akhi magana ya barmu mu ma mu tafiyar mu karatun mu idan lokacin ya yi, kinga sai mu barku daga ke sai Aba kawai."

Kallon ta Anna ta yi tace "Uhum? Kuma za ki so hakan? Idan hakane to ba zan masa maganar ba sai dai mu yi ta zama da ku anan."

Kukan shagwaɓa ta sake fashewa da shi, sai Yusrah da ta ɗan murmusa tana kallon Manal ɗin, saɓanin Nabihat da ta yatsina fuska tare da taɓe baki, Wa'at ma da ba abincin take ci ba sai kayan kayan marmari da take ta sha, hira suke sha kan bikin ƴar ƙanwar Anna da za'a yi wata ɗaya mai zuwa, kamar daga sama suka ji sallamar sa suna shigowa falon shi da uncle Sulaiman.

A dole su Manal suka koma yin ƙusƙus suna sauraron gaisuwar su da Anna, suma duk da girmamawa suka gaishe shi tare da uncle Sulaiman da suka laƙaba masa uncle Sul, amsawa ya yi da jin daɗin yadda mutanen gidan ba sa nuna masa wani bambamci ko shi bare ne a cikin su, har sukayi nasarar haɗa idanu shi da Manal, da sauri ta janye nata idanun cike da kunya tana ƙara sadda kan ta, haka shi ma sai ya sunkuyar da kai yana shafa sumar kan shi.

Hakan da ya yi ne ya sa Anna lura da shi ta ɗauka wani abun yake so, da kulawa sosai ta tambaye shi "Uncle ɗin yara, ko kana buƙatar wani abun ne?"

Kallon Annan ya yi, sai kawai ya gagara cewa a'a sai ya ce "E Annarmu, ruwan fridge ɗina ya ƙare dama, sune zan ɗauka."

Murmushi ta yi tace "Haba uncle ɗin yara, kai da kan ka kuma? Ke Manal..."

Anna ta faɗa ba da wata manufa ko fahimtar wani abu ba, a tausashe Manal ta amsa da "Na'am Anna."

Kai tsaye ta umarce ta da "Je ki ɗaukowa uncle ɗin ku ruwa."

Jinjina kai ta yi ta miƙe tana amsawa da "To Anna." Sannan ta nufi madafa, ba tare da sanin shi ba ya ɗan bi bayan ta da kallo na sakanni sai kuma ya kalli da ya damƙi hannun shi sosai ya raɗa masa "Dubi hararan da ƴar ka ta min dan Allah? Baku gaya mata ko ni wa ye ba wai?"

Ƴar da ya ambata ya sa uncle Sulaiman kallon inda Yusrah take, e da gaske fuskar ta a cike take fam fam irin an hassala ta ɗin nan, amma kuma harare? Bai tunanin za ta aikata haka ga babba bare kuma AA da ya tabbata ya wuce hakan a wurin mutane dayawa, tsareta dai ya yi da idanu yana jira ya ga ko za ta sake aikata abinda boss ɗin ya ce.

*Abu* biyu ya kawo shi gidan a wannan lokacin, na farko ya faɗawa Anna da Aba baya son rainin da Y. Turaki ke neman ɗora masa sabo fil a takarda, idan ta gan shi yanzu sai ta dinga hararen shi? Gaskiya ba ya so ko kaɗan dan hakan damun shi yake tsawon wunin sa da daren sa, ya zo ne dan ya sanar da su idan auren ne bata so ita ma kamar dai shi, to a raba auren mana kowa ya huta, ta faɗa idan hakane sai iyayen su yi haƙuri ya sallame ta, tunda dama shi yanzu ne yake da nutsuwar sa da suke nesa, da zaran an haɗe su gida ɗaya bai san me yarinyar nan za ta dinga zuwa masa da shi ba na larurar ta, dan haka kawai su sawaƙewa juna tun wuri wallahi, dan shi da zaran ya kammala aikin nan ma U.K zai koma da zama yana kulawa da kamfanin Aba hankalin shi kwance ya manta da wata Y. Turaki, yarinya sai neman fitina? Ba ta iya girmama babba ba ko da wasa ne.

Sai dai da ya shigo, ya kuma ƙurawa fuskar ta idanu take sai ya fahimci kuka take yi ko ta sha irin na mamakin nan, tunda ƙuru-ƙuru ake gane hakan, me ye dalili to? Me aka mata? Me ya faru? Bai ga alamar damuwa ko hatsaniya ta faru a gidan ba, me kenan ya sakata kuka? Yana wannan tunanin Yusrah ta ɗago kumburarrin idanun ta ta kalle shi, da ta yi sa'a yana kallon ta kuwa sai ta watso masa hararan nan da iya gaskiyar ta daga zuciyar ta ta fito. Yanzu kuma da uncle Sulaiman ke jiran ta sake hararan mijin ta ya tsawatar mata, sai kawai ta kalli Anna da tausasawa sosai muryar ta na rarrabewa saboda shasheƙar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login