Showing 36001 words to 39000 words out of 397328 words
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*11*
Kamar kullum yadda suka saba fitowa daga gida suka fito kafin kowa ya ɗauki hanyar sa, sai dai yau duk tafiyar nan haka Yusrah ba tare da ta sanar da kowa ba ta kama ta a ƙafafun ta, ba ta ji wahala ba saboda lokacin da take zuwa makaranta ma a ƙafa take zuwa kuma da nisa, haka ta share doguwar tafiyar nan ta iso asibiti har ta ɗan gota lokaci da kaɗan.
Ta samu an sallami su Zahra'u suna shirin tafiya, daga nan bakin motocin su suka gaisa ta tambayi lafiyar baby, Bilal dake saka kaya a boot ne yake cewa "Ba ki tambayeni sunan da na saka mata ba?"
Kallon shi ta yi, amma narkakken kallon da ya bita da shi yasa ta sunkuyar da kai, kyakyawa da shi ga shi dogo da iya ɗaukar kwalliya, cike da kunya tace "Me ka saka mata?"
Ba tare da ya kawar da idanun shi ba yace " *Yusrah*."
Murmushi tayi a shashacan nan tana tunanin kawai ya faɗa ne dan ya birge ta ko dan ya tsokane ta, maman su ta kalla tace "To Mama Allah ya tsare, Allah ya raya baby akan sunna."
Har za ta juya Maman dake riƙe da babyn tace "Ameen Yusrah, ai kam kin samu takwara, uban ta ya nuna mana ikon shi akan ta, fatana dai ta yo halin ki."
Da mamaki tace "Mama, da gaske Yusrah aka saka mata?"
Jinjina mata kai tayi sai Zahra'u dake dariya tace "E, mun kasa tsayar da suna ne, shine ya kira Baban ta ya ce shi a bar shi zai saka, kuma ya bashi dama shine ya miki takwara."
Ƙayataccen murmushi ne ya kubce mata tana faɗin "Kai, amma naji daɗi sosai..."
Sai kuma ta kalle shi tace "Nagode Baban Yusrah, ba zan manta da wannan karamcin ba."
A sanyaye yana kallon ta yace "Kar ki damu, ni ma ba zan gaji da addu'a yadda na zama Baban Yusrah, na zama mijin Yusrah nan da ɗan lokaci kaɗan."
Kallon shi tayi, hakan yasa suka kalli juna sosai, sai kawai ta yi murmushi tace "Mama ku sauka lafiya, ni zan shiga ciki."
Ba ta sake jiran kowa ba a cikin su ta shige, sai dai tana shiga ta fara jin hayaniya haka sama sama, ɓangaren ɗakunan masu sauƙin kuɗi ta nufa na haihuwa inda take jin hayaniyar kamar ana faɗa, tana ƙarasawa ko ta samu wata tsohuwa sai masifa take inda wasu ke bata haƙuri, ga Sakina tsaye tare da Mama Rabi unguwar zomar su, sai da ta zo ta tsaya sannan ta fahimci akan me ake faɗan, tana neman a bata mahaifa ne za ta rufe su kuma su Sakina na faɗa mata basu san inda take ba, shine take cewa wannan ma ai ƙaryar banza ce ba zata saɓu ba, har tsohuwar na ikrarin da a ƙi bata wannan uwa wallahi gwara a haɗa da ƴar da aka haifa duk su ɓatar ya fi mata.
Gashi dai an sallame su tuni ma mai jegon ta tafi gida, ita ce kawai ta tsaya wannan masifa, cikin taushin murya Yusrah tace "Mama, Mama dan Allah ki yi haƙuri, bari mu ƙara dubawa mu gani, wataƙila dai wani kuskuren aka samu."
A masifance tsohuwar tace "Ba wani, ba wani kuskure ƴar nan, tun jiya fa aka yi haihuwar nan, suma iyayen yarinyar ba dan sun zama sakarkarun banza ba, ace a baku ƴa amma ba'a baku uwar shi ba, to me ya ci ta? Wallahi sai da mahaifar nan zan bar asibitin nan, kin ji na rantse."
*Docter* Hamat da babu wanda ya san shigowar shi, muryar shi kawai suka ji daga bayan su lokacin da zai shiga ofishin shi yace" Nurse Yusrah, ki biyoni yanzu."
Duk juyawa sukayi, sai Yusrah da gaban ta ya faɗi saboda ita tunanin ko ɗan lattin da ta yi ne ya sani zai mata masifa akai, haka dai ta bi bayan shi da girmamawa ta samu yana shirin zama yace" Me yake faruwa ne a can wurin? Hayaniyar me waccen tsohuwar take mana anan? Ba ku sanar da ita akwai manyan mutanen da basa buƙatar ko da kukan tsuntsaye bane?"
A ladabce Yusrah tace" ka yi haƙuri yallaɓai, tana faɗa ne akan sai an bata mahaifar jikar ta, shine muke lallaɓata."
Wani wawan tsaki ya ja ya jingina a kujerar shi yana kallon Yusrah yace" Shine me? Dan Allah ku kira masu gadi su fitar da ita, ko kuma ku kama aikin gaban ku idan ta gaji za ta tafi."
Da mamaki da kuma ɗar ɗar Yusrah tace" Amma yallaɓai, a ce mahaifa ta ɓata a asibiti, abun akwai tashin hankali, ina ga idan an s..."
Da hannu ya mata alama yace" Kinga dakata, ki je kiyi abinda nace kawai."
Da ladabi ta sake cewa" Amma yallaɓai ta ya mutane hankalinsu zai ɗauka ace mahaifa ta ɓata, zamu iya zama abun zargi fa."
Wani kallo ya shiga binta da shi, sai kawai ya nuna mata kujerar dake gaban shi yace" Zauna Yusrah."
Da ɗan mamaki ta kalle shi, dan likitocin da suka fita ma bata tunanin suna zama anan idan suka shigo, amma tunda umarni ne sai kawai ta ɗan ɗosana mazaunanta tana kallon shi, miƙewa ya yi ya zagayo inda take yana cewa" Yusrah, ke sabuwar ma'aikaciya ce anan, irin waɗannan abubuwan su bar damun ki, akwai matakin da na tanada domin ki wanda nake so mu kai tare da ke, wannan ne ya sa nasa aka kawo min ke nan, ki nutsu Yusrah, akwai arziƙi mai yawan gaske da yake jiran ki, shin baki ga Sakina ba?"
Duk a takure take sosai saboda tsaye yake bayan ta kuma daf da ita, cikin ɗar ɗar tace" Yallaɓai ba wai na ƙi bane, sai dai wasu abubuwa ne dake faruwa na kasa gane musu, sai naga kamar ba'a bin doka wajen yin wani abun."
Kamar a mafarki Yusrah ta ji ya ranƙwafo kan kujerar da take ya ɗora hannayen shi a kafaɗun ta haɓar shi saman wuyanta, zabura tayi tana son miƙewa amma ya ƙara mayar da ita zaune cikin raɗa mata a kunne yace" Doka fa kika ce Yusrah? Ke ce zakiyi maganar doka a asibitin nan? Bayan ke kan ki kinsan alfarma aka miki kika zo nan, shin anan ya kamata duk wani ɗalibi ya yi stage ɗin shi? Ina ƙawayen ki da kukayi karatu suke? Wasu suna can ƙauyen da ko wuta babu, wasu kula suna cikin gari amma a asibitocin da sai a wuni ba'a karɓi marar lafiya ko ɗaya ba, amma kinga k..."
Zaburar da tayi har da sakin siririyar ƙara ta furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Saboda sauko da hannayen shi ya fara yi daga kafaɗun ta zuwa wuyanta har yana neman kai hannun shi kusa da ƙirjin ta, a rikice ta miƙe har saida ta bige mishi haɓa da kafaɗar ta sannan ta juyo tana kallon shi tuni hawaye sun fara gangaro mata, cikin kaɗuwa take kallon shi tana ja baya tace "Yallaɓai, ka ji tsoron Allah, ya zaka nemi cin zarafina? Idan ƴar ka ce ni za ka min haka dan Allah? Gaskiya ni dai in haka aikin asibitin nan yake..."
Kukan da ya ƙwace mata yasa ta toshe baki, da sauri ta juya za ta bar ofishin tana faɗin "Na haƙura da aikin nan."
Tana fitowa kafin ta shanye tsayin couloir ɗin da ofishin nasa yake tana tafe da sauri ne tana murzar idanu ba ta ma san da mutum na tafe a wurin ba saida ta ji ta yi karo da abu...
*A* ɗan firgice ta janye hannunta daga murza idanuwanta da take yi ta sauke dubanta a kan fuskarsa, irin tsayuwar da ya yi daf da daf da ita, uwa uba hannunsa da ya riƙo tsintsiyar hannunta da shi ya sakata rai ɓace ta warce hannunta da ƙarfi, sai dai ta ji ta gaza warta ɗin irin riƙon gaske kenan ya mata dan kar ta faɗi.
Daga ƙasa zuwa sama ta sake kallon shi, bai yi kama da irin dai zauna gari banza ba haka, amma da ta sauke duban ta kan ƙwaryar molon shi da ya fara tsiro masa da gashi, yake kuma kallon ta ido cikin ido ba kunya ko rusunawa (🤔), sai take ganin shima ɗin dai wani basaraken tantirin ne wataƙila ma mai lasisi.
Wani ɓacin ran ya sake kunno ta da tashin hankalin ganin abinda ke neman samunta a yau ɗin nan, ta gama rabuwa da wancen tsohon banzan ga wani gardin banzan zai nuna mata lalata bayan bata san waye shi ba bata taɓa ganinsa ba, a hargitse ta nuna shi da ɗayan hannunta muryarta na rawa duk da kuwa har ga Allah bata ga wata makusar da za ta iya bata ƙarfin guiwar yi masa tsiwa ba, bugu da ƙari yana da wani kwarjini da haiba a tattare da shi da ɓacin ran da ke tare da ita ne kawai ya rinjayeta ta hanyar faɗa masa cikin faɗa da ɗaga murya har ma da nuna shi da yatsa ta ce" Kai, cika ni! Cika ni dallah malam kar na gurguntar da kai a wajen nan."
Da mamaki ya sake kallon ta, a nutse ya saketan yana kallon yanayinta ta ja wani mahaukacin tsaki kamar zata kifa ta raɓashi tana sakar masa harara ta fice, hakan ya sa ya ɗan langwaɓar da kai a ransa ya ayyana _" Ayya, na zata nurse ce, ashe mahaukaciya ce, ko ina ta samu rigar likitocin nan kuma? Allah ya sawaƙa, ta yiwu duka take."_
Ya yi gaba yana ayyana zancen zucinsa hankali kwance ya ƙarasa office ɗin uncle ɗinsa dan gabatar da abinda ya kawo shi.
Bai ƙwanƙwasa ƙofar ba, dan duk da baya yawan zuwa anan amma dai kai tsaye yake shiga ganin shi, ɗan buɗa ƙofar ya yi ya zuro kan shi da fara'a saboda sosai suke ganewa junan su shi da kawun nashi yace "Hello! Uncle ɗina yana nan?"
Lokacin yana zauna kan doguwar kujera yana shan lemu mai sanyi yana murmushi da tunanin ba zai taɓa bari Yusrah ta bar aikin nan ba haka kawai, ai ba haka kawai ɗin ya ɗaukota aiki anan ba, dan haka dole sai ta mishi abinda ya sa ya ɗaukota. Da aka turo ƙofar gyara zaman shi ya yi yana tunanin wani haukan ne kuma haka? Sai ya ga kan AA tare da jin maganar da shi kaɗai ke masa ita a faɗin duniya, da fara'a ya aje glass ɗin hannun shi ya taso yana washe baki yace "Hey my son, kai ne? Wannan wace irin bazata ce?"
Ƙarasa shiga AA ya yi suka rumgume juna cike da ƙaunar junan su, suna sakin junan su Docter Hamat ya shiga ƙarewa AA kallo yana tattaɓa jikin shi yana cewa "Son, ya naga kamar ka rame? Me yake faruwa ne? Aiki ko rashin isashen lokaci?"
Murmushi AA ya yi ya fara girgiza kai, kafin cikin nutsuwa yace "Ko ɗaya Unclena."
Ƴar harara ya watsa mishi cike da tuhuma yace "And, kasan bana son ganin haka kuma ko?"
Jinjina kai shima ya yi yana murmushi yace "I know, amma zan dawo yadda kake so."
Hannun shi Uncle ɗin ya kamo da niyyar su je su zauna, shi ma kuma zai so haka ɗin dan maganar da ta kawo shi, amma kuma ganin fuskar uncle ɗin nashi, da tuna wa ye shi a gare shi sai ya ji ai ba lallai ma yana da masaniya akan abinda ke faruwa a wannan katafaren asibitin ba, dan haka kawai zan binciki ma'aikatan da ya san sune ma da laifi.
Uncle ɗin dake faɗin "Muje in ji me ke labari, kwana nawa rabona da kai? Ka manta da uncle ɗin ka ne hala?"
Togewa ya yi ya ƙi matsawa yace "Uncle, ba zama zan yi ba, but i promise zan same ka gida mu sha hirar mu, yanzu ina sauri ne."
Wani tuhumammen kallo uncle ɗin ya bishi da shi, sai kuma ya yi murmushi kawai yace masa "Ok son, ba damuwa, amma fa ka cika alƙawarin ka, ka san nayi kewar ka."
Jinjina kai ya yi ya ɗan masa kusa da shi ya rumgume shi sannan ya juya yace "Sai anjima."
Da kallo ya bishi yana taune leɓen shi na ƙasa yana shaƙiyin murmushi, jiya ya zo asibitin nan bai neme shi ba, yanzu kuma ya dawo amma kai tsaye? Me yake faruwa? Me AA ya ke shirin aikatawa? Me yake kawo shi nan da har ya sa ya yi magana da Mani dreba? Wani murmushin ya kuma saki yace "Hmmmmm! Yaro kenan."
*A* nutse AA ya fita yana tafe yana dubawa ko zai ga ma'aikata, amma duk wanda ya ci karo da shi sai ya fahimci aiki yake, shi kuma yana so ya ji ta ya aka rasa mahaifar da har ya samu tsohuwar can tana wannan masifa da ƙyar ya rarrashe ta ya ce ta bar komai a hannun sa shi jami'i ne, ta tafi amma ta ce za ta dawo gobe ta ji yadda aka yi. Gashi gaba ɗaya ma ya kasa samun ganin Mani bare ya yi abinda shi ma ya kawo shi asibitin ma gaba ɗaya.
*Tunda* ta shiga wajen zaman su ba kowa saboda da safe dama kusan kowa na wani aikin, ita ce ma ya kamata ta zauna anan kujerar dan duba mata masu awo, kuma yanzu haka matan suna nan bakin ƙofa a laye suna jira a sube su, sai dai ina! Barin asibitin nan gare ta yau ya zama wajibi farilla, duk wani abu da ta san nata ne ta shiga haɗawa tana ta masifar "Wallahi ba zan sake zuwa asibitin nan ba, aikin banza aikin wofi, kawai mutane basu da gaskiya a rayuwar su, suna mantawa da za su tsaya gaban mahaliccin su, to gwara na je na samu Docter Saddi na roƙe shi Allah Annabi ya taimaka ko ƙauyen ƙayau ne ya kaini, wallahi zan zauna nayi aiki tunda dan ahalina nake yin shi, amma ba aiki da wannan tsohon najadun ba."
Rigar asibitin ma cireta tayi ta rataya a hannun ta tunda ta ta ce, da sauran abubuwan ta duk ta riƙe ga hannu sannan ta fito tana ƙara gyara zaman kayayyakin a hannun ta yadda za ta ji daɗin daɓawa a ƙafa har ta isa gida kamar yadda ta zo a ƙafa.
... Karo na biyu kenan da suka kusan sake gwara kawunan su, da ta Yusrah ce kam da sun yi ƴar gwaren saboda kanta ƙasa yake duba, shi ma da fari yana duba wayar sa ne kawai ya ji motsi ya yi gaggawar ɗaga kai, yana ganin ta ya ja birki yana yatsina fuska da kuma mamaki saboda bakin ta sai mimimi yake alamar magana take ita kaɗai fa kenan.
Ita kuma tsayuwar da ya yi gaban ta dan kar su kauru da juna yana kallonta ya sa da ta kalle shi ta ga na ɗazu ne ko ta ce na yanzu, sai ta sake kici-kicin da fuska ta ja tsaki ta juya ɓangaren damar ta da nufin ficewa.
Ganin tana shirin tafiya ta barshi ne a tsaye kamar wani sakarai, bayan kuma rainin hankali da wautar da take ta masa tun haɗuwar su, sai kawai ya bita da kakkausan kallo tare da murɗaɗɗiyar muryar sa ya furta "Ke dakata!"
Dakatawar Yusrah ta yi saboda kakkausan amon da ya mata magana da shi tare da juyowa, magana ta gaskiya gabanta ya faɗi har ta ji wani maɗaukakin tsoron shi ya shgeta, amma dai da ƙarfin halin ta ko alama ba ta bari ya gane hakan ba, sai ma kumburo baki da ta yi irin tana jiran shi ɗin nan da duk abinda yake ji.
Tako ɗaya ya yi da ya sa suka ƙara samun kusanci sannan ya dakata, ba tare da ya daina mata wannan kallon ba, a dai wannan muryar da kan neman sakata jin fitsari yace "Ba'a san kin fito bane daga inda kike jinya? Idan ɓangaren ku kike nema me zai hana ki yi tambaya? Ya zaki kunto ki shigo cikin mutane har ma da saka kayan da ba naki ba, sannan kina neman takani ki wuce, ba ki san nayi doguwar *TAFIYA* da waɗanda ma ciwon su ya dake naki ya shanye ba? Bare kuma ke da ko gama nuna bakiyi ba a harkar."
Shi ma wani irin basamuden tsaki ya ja da ya saka Yusrah rintse idanuwanta, ba ta san da fitowar su ba kawai sai da ta ji ɗumin su a saman kumatun ta. Cikin bebayen dake sharar asibiti ne ya zo wucewa ta bayan Yusrah, da wata irin izza AA ya ɗaga masa hannu alamar ya zo, dake ya san shi kuma da rusunawa ya ƙaraso yana masa alamar gaisuwa da hannu, ba tare da ya amsa gaisuwar ba kawai ya nuna mishi Yusrah da wutsiyar ido har yana taɓe baki kamar ya ga wata halitta sannan ya ɗan ɗaga murya yadda zai ji shi yace "Wannan, ka riƙe hannun ta har zuwa psychiatrie."
Kallon Yusrah beban ya yi sai kuma ya kalli AA da girmamawa yace "Yallaɓai ta ɓata hanya ne?"
Murmushi Yusrah tayi kafin AA ya bata amsa tace "Na godewa Allah da dama shirin barin asibitin nan nake yi da babu komai a cikin ta sai zalinci da take doka da rashin bin ƙa'ida, wataƙila kai ma acan psychiatrie ɗin kake aiki, ina fata ba kwa ƙarasa rikitawa al'ummar Annabi ƙwaƙwalen su, kuma ka sani wallahi Allah ba zai yafe haƙƙin bayin sa da ake cuta ba,