Showing 57001 words to 60000 words out of 397328 words

Chapter 20 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70095

bayan ta zumuncin dake tsakanin Aba da Chef, to me zai sa ta damu da Yaya AA har haka har ma tana tunanin ita za ta rakata wajen ta? Ita ɗin ce za ta rakata gidan shi? Gidan da ko Anna ya ce kar ta je idan tana son ganin shi kawai ta kira, ba wai dan wani abu ba sai dan kare martabar su, uwa uba su Nawal da bata tunanin ma yanzu haka suna iya tuna fasalin gidan, dan tun da ya siye shi suka je gabaɗaya suka gani suka masa addu'a, ba wacce ta sake komawa a cikin su sai dai ka bi ta ƙofar gidan.

To wai ma, akan me za ta mata wannan tambayar? Shin ba ta fahimci yadda AA yake a wurin ta bane? Ko ta ce bata san tana tsananin girmama lamarin shi da kambama shi ba? Idan fa abinda take ji a ranta ita ma kwatankwacin sa take ji? Sai ya kenan? Danƙari! Ta faɗa tana ɗan kawar da duban ta daga kan Nabihat ɗin a shashance tace "Ba zan je ba gaskiya, dan ya hanamu zuwa."

Nabihat kuma mamaki ne ya so kamata ganin yadda ƙiri-ƙiri Abrar ta canza mata fuska take yanke, sai ta ji fargaba ya kamata kar dai ko ciwon su ɗaya ne? Shiyasa ba ta so wannan tambayar ba, ba ta taɓa ganin wani abu mai kama da soyayya ba tsakanin su, sai dai ta san Abrar na jin kunyar sa har ma ta rusuna ta gaishe shi, ba ta hayaniya ko rawar kai a gaban shi, ba ta shishige masa ko da da magana ne musamman idan ba ta shafe ta ba, hasalima bayan ina kwana ko ina wuni idan ta faɗa masa, a taƙaice idan ya amsa ba ya sake ce mata uffan haka ita ma.

Da yanayin zulumi Nabihat ta juya ita ma ta nufi ban ɗaki tana ci gaba da tunanin in hakane kuwa ta yi wauta da ta yarda ta mq Abrar wannan tambayar... Sai dai ko ma menene, da ta zo gidan nan da niyyar ta gan shi ta zo, ya kenan za ta yi? Da wannan tunanin ta shiga ban ɗaki ta yo alwala ta fito t kabbara sallah kamar kowa. Amma dai tuni ta ji a ranta idan ma hakane ɗin ne a ran Abrar, to kuwa tabbas za ta fara yaƙi da ita ta yadda ba za ta fahimta ba, dama gidan nan ba baƙon ta bane, to za ta sake shiga ko ina har ta yi nasarar shiga ran kowa ba tare da an ankara ba, ta yadda daga ƙarshe iyayen su da kan su ne zasu saka ranar ɗaurin auren ta da Yaya AA, dan tanan ne kaɗai za ta ce take ganin naƙasu a zamantakewar Abrar ɗin da ahalin AA, tunda Anna ma aunty Abrar ke kiran ta, ita kuma tana kiran ta da Anna ne kamar yadda su Manal ke faɗa, bayan nan bata ga makusar da za ta ce za ta wa Abrar fintinkau ba, hasalima ta fita da wani abun, dogon gashi da farar fata, sannan nutsatssen kyau ma Abrar ta fita, saboda su ko a buzayen ma irin masu gadon kyau ɗin nan ne da hasken fata saɓanin wasu da zaka ga kamar ma ba bugajen ba, dan akwai baƙaƙe kuma munana ko a ciki suma, to wannan ahalin musamman na Anza duk kusan ɗaya suke, hatta Aba da tsufa ya fara kama shi za ka gane asalin kyawun shi, haka ma su kawu Hamat da Aunty Tidin da sauran su, uwa uba kuma su Manal da su Inti, haka ma Humed da AA.


*AA ANZA*


*22:06* suka haɗu da mutumin nan a inda mutane ke koyon abun hawa saboda rashin matsatsi, ko da AA ya zo ya same shi ba tsayawa komai ya cire farin gilashin dake idanun shi yace "Ina jin ka?"

Kallon shi mutumin yana numfasawa a nutse yace "Tabbas yallaɓai ni na ɗauko motar daga asibitin Saddi Ja, sannan na kaita gidan Alhaji *Muntari Buza*, manajan banki mai zaman kanta ta *SSK*."

Da tsananin mamaki AA ya dube shi jin ana nema sake rikoto masa wani abun yace "Na san Muntari Buza, amma kuma... SSK bank ba bankin uncle Suraj Sidi Kofa bace?"

Jinjina masa kai ya yi yace "Bankin sa ce, Alhaji Muntari kuma ai shine yake shirin zama siriki ga Alhaji Aliyu Anza, dan yana neman auren ƙanwar sa ne Hajia Tidin."

Abunda bai taɓa tsammani zai fito daga bakin sa bane ya fito, kalmar " *Goggona kuma*?" Da ya ambata ta sa mutumin kallon shi da mamaki, sai kuma ya razana sosai yana rarako idanu har da ɗan ja baya yace" Yyyyya...llaɓai, ko dai..."

Wani kallo AA ya mishi fuska a ɗaure yace" Aswan Aliyu Anza, ni ne, Goggona ce ita kuma."

Sai kuma ya kalli gaban shi yace" Me ye haɗin wannan kuɗin da Muntari Buza kuma?"

Da ke ya riga da ya razana a tsorace yace" Ka yi haƙuri yallaɓai, dan Allah kar ka ƙara tambayata komai bayan wannan, wallahi nima ban sani ba, ka min rai kar ka sake jefo min tambayar da za ta sakani bala'in da ba zan iya fita ba, sai dai..."

Kallon shi AA ya yi cike da mamakin duk me ye haka? Su wa yake tsoro? Aljanu ne ko mala'iku? Ƴan adam? Haba dai mana, shirun da ya yi ya sa yace" Sai dai me?"

Da sauri yace" Idan kana son sanin masaniyar da ta fi wannan, kana iya zuwa ka ga lauyan mahaifin ka, Issufou Hassan."

Wani banzan kallo ya mishi yace" Issufou Hassan kuma?"

Ɗaga masa kai kawai ya yi alamar e, wani shaƙiyin murmushi AA ya yi ya jinjina kai, shiru motar ta ɗauka tsawon wasu mintuna kafin ya kalli mutumin yace" Me ye sunan ka?"

Da sauri ya amsa da" Suleiman, amma an fi sanina da *Bahago*."

Ɗan taɓe baki AA ya yi yace" Shikenan, za ka iya tafiya."

Sai kuma ya ciro kuɗi ya miƙo mishi yace" Ka sha mai." Saboda ya ganshi a babur, kuɗin ya fara kalla kafin ya karɓa yana masa godiya har ya fita daga motar, ya rufo masa ƙofar kenan AA ya kalle shi yace" Kar kowa ya san mun haɗu da kai, bare a san abinda muka tattauna a kai, ka fahimta?"

Jinjina kai y yi yace" In sha Allah yallaɓai." Kwaraiya rufe bakin sa da faɗin wannan magana, ba dan haka ba da niyyar sa da ya matsa ya sanar da oga Hamat ɗan Yayan shi fa na masa bin diddigi a harkoki, amma haka ya hau moton shi, shima tayar da motar ya yi zuciyar sa, kwanyar shi, ruhin shi ma fal tunanin me ke shirin faruwa? Me ya jima yana faruwa a ƙasar shi da aikinsa na soja bai sa ya gano ba sai yanzu da yake matsayin jami'in bincike kuma na sirri.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*17*



Lokacin da Yusrah ke ta fafutukar yawon neman kuɗin da za'a wa Safwan aiki, lokacin kuma a asibiti wani abu ke faruwa, tun fitar ta Iya Abu na ta karɓan baƙi masu zuwa duba su, tun daga mijin aunty Khadi da saurayin da aka saka musu rana da aunty Hannah, har Yaya Kadiri ma ya zo ya duba su sannan ya tafi, duk ziyarar da ake ta kawo musu Iya Abu bata faɗa ma kowa cewa an ƙi zuwa a duba Safwan ba, ko kallon shi ba likitan da ya yi idan ba wannan nurse ɗin da ta kula da Yusrah ba har ta rakata ofishin Docter, ita ma ba wai ta zo wajen su bane, sanda t gamu da Iya Abu ne ta yo alwala a waje a taƙaice kawai tace mata "Iya ku yi ta haƙuri, idan Yusrah ta zo idan zai yiwu ku ce ta kai koken rashin lafiyar Safwan wajen mai asibitin gaba ɗaya."

Daga haka ta wuce ba ta ba Iya Abu damar faɗa mata wani abu ba, haka suka ci gaba da zama duk sauran ƴan ɗakin su suna samun kulawa amma ban da su, daga ƙarshe da yamma ta yi lis sai aka turo wata nurse ɗin da takardar abubuwan da aka musu da kuma adadin kuɗin da za su biya, duk ƴan kuɗin da Iya ta samu wanda ake bata da aka zo dubiya su ta miƙawa nurse ɗin, hakan ya sa ta kalle ta a sheƙe ta dubi kuɗin tace "Iya, nan kuɗin menene?"

Da rarrashi Iya Abu tace "Su kenan gareni ƴar nan, amma idan Yayar shi ta dawo nasan za ta samo kuɗin sai ta biya."

Taɓe baki nurse ɗin ta yi tace "Taɓɓ! Zan gayawa likita kawai, sai yadda ya ce za'ayi."

Juyawa ta yi ta bar Iya Abu sake da baki saboda a ganin ta kamar wannan nurse ɗin ta fi rashin kirki, Sakina kuma na asibitin, sai dai bata zuwa inda suke ne saboda kunya na kasa taimakon su da komai, ba ta da ikon sakawa ko hanawa, kuma Docter Hamat ya mata gargaɗi kan kar ta kuma yi masa maganar wata Yusrah da ƙanin ta, duk abinda ta ga yana mata yana sane kuma yana da hankali, dan haka ba ruwan ta.

Haka dare ya tsala ba Yusrah ba labarin ta, hankalin Iya Abu ya tashi sosai, amma rarrashin Safwan dake ta kuka yana faɗin ƙafar shi ya danne waccen tashin hankali, da ƙyar ta lallaɓa shi ta fita waje can gefe ta siyo maganin kashe raɗaɗi ta bashi ya sha, kafin awa ɗaya ko ya ji sauƙi ciwon har bacci ya ɗauke shi yana ajiyar zuciya.

*Yusrah* kuma na can cikin farin ciki ba tare da ta sha wahalar komai ba mutanen nan suka ɗauke ta wannan aiki, dake aiki ne da zaka yi da jikin ka kana karaɗe gari da ƙafafun ka, shiyasa babu wani ƙa'idoji da dokoki masu tsauri ko yawa. Sauƙin ɗaya shine gari babu rana saboda yawan ruwa da ake samu, dan haka fa ta fantsama ita da wata su ka famtsama a inda aka tura su, a wannan lokacin niyyar ta shine ba za ta koma asibiti ba har sai ta kammala kwana ukun nan ta haɗa kuɗin aikin ta da wanda ta samu da kuma wanda za ta samu nan gaba sannan ta koma, dan in ta je dole Iya Abu za ta tafi ta bar su daga ita sai Safwan, amma idan bata gan ta ba dole za ta haƙura ta zauna, Baffa kuma za ta bada ko saƙo ne wajen yadda za'a kula da shi.

Da wannan bayan magriba sun sauka daga aikin Yusrah ta wuce gidan su Maryam, nan suka sake jajanta mata har Maryam ɗin ke faɗa mata ai tun bayan azahar suna can gidan su har la'asar, nan ta sanar da ita abinda take yi da wanda take shirin yi, Maman Maryam ɗin ce ma tace mata "Amma Yusrah ta ya za ki bar su asibiti su kaɗai? Iya fa baƙuwa ce anan, Safwan kuma yana buƙatar ki sosai."

Da girmamawa ta kalle ta tace "Hakane Mama, amma ba wani abu bane, a asibitin nan nake aikina nima, ko Sakina da Ustaz nasan zasu basu kulawar da ta dace, sannan daga gida ma ana ta zuwa ganin su kuma ana kai musu abinci, amma na san Iya babu abinda zai hanata tafiya gida idan naje asibitin nan, kuma kinga dole muna buƙatar wani babba kusa damu musamman ma idan na kai kuɗin aikin Safwan."

Cike da gamsuwa ta jinjina mata kai tace" Gaskiya ne wannan, amma ni gani nayi har kwana uku baki je ba, hakan ai zai sa hankalin su ya tashi su ɗauka ko wani abun ya same ki kema, sannan ke kan ki za ki so sanin halin da suke ciki a kowane lokaci."

Jinjina kai tayi ita ma da gamsuwa tace" Gaskiya ne Mama, amma ai ga Maryam nan, za ta dinga zuwa ganin su a madadina, kuma nasan za ta iya taimaka musu da wani abun tunda ita ma likita ce."

Sai lokacin Maryam dake ta kallon su da sauraron su tace" Hakane, kuma kinga ya kamata ki je wajen Docter Saddi, babban likita shi nasan ba za'a rasa taimakon da zai iya yi miki ba."

Kallonta Yusrah ta yi, a zuciyar ta kawai take ayyanawa _" A yanzu kam na fi so na nemi halak ɗina don ganin an wa Safwan aiki."_ A zahiri kuma sai tace" Jibi zan je kafin na wuce wurin aiki, dan gobe zan koma gidan aunty Fauziyya ne daga nan na wuce aikin."

Da mamaki Maryam tace" Amma ai duk wuri ɗaya ne, za ki iya tafiya ɗaya."

Girgiza kai tayi tace" Duk da haka, bana so na ɓata lokaci goben."

Maryam dama mahaifin ta ya jima da rasuwa, sai Yayun ta maza da suke kula da gidan su, dan haka Yusrah ta yi kwanciyar ta ba tare da wata matsala ba, sai dai gaba ɗaya hankalin ta yana kan ƙanin ta dake wani hali ne na neman taimako musamman nata.


*WASHE GARI*


Tare da Maryam suka fita daga gida ita ta nufi asibitin da take koyon aiki, Yusrah kuma ta fara wucewa gidan aunty Fauziyya, saida ta je ƙofar gidan sai ta tuna da yanzu dan za'a taimaka mata sai ta musu wannan sammakon? Wataƙila ko bacci mai gidan bai tashi ba, duba da an ce sai dare zai shigo garin, kuma sun saba gani idan suka shigo gidan wajen ƙarfe goma na safe ta ce musu yana bacci ko yanzu ya farka... Sai kawai ta shiga tattakewa zuwa gurin aikin ta dan ta ɗauki kayan aikinta da wuri ta kama gaban ta. Ita da wata babbar mace da za ta iya haihuwar ta suka fita tare yau saboda kusan sune farkon zuwa, kuma dukkan su larurar su ce ta sa dole suka fito da wuri dan aikin ba wai dan ƙwazo bane da son aikin.

*Haka* yau ma ta wuni a gajiye, lallai wata larurar na dame wata, dan kuwa ciwon Safwan ne ya ɗauki hankalin Yusrah sam ba ta jin yawan tartsatsin da bayan ta ke yi mata har zuwa ƙirji, sai idan abun ya motsa mata ne sai ta dafe ƙugu tana cije baki da addu'a, da kuma ya lafa mata sai ta ci gaba daga inda ta tsaya, a haka har yamma ta yi suka dawo da kayan aikin su nan da kuma bayanan mutanen da suka samo. Yau sai ranar ta zamar mata ta musamman ma, dan kuwa ta san gobe i warhaka in sha Allah kuɗin suna aje kayan aikin su kuɗin su ne za'a damƙa musu, dan haka da farin ciki ta wuce gidan aunty Fauziyya da niyyar to yanzu za ta iya jiran mijin ta har ya shigo ma idan baya nan.

Sanda ta je gidan faɗa aunty Fauziyya ta dinga yi wai akan me a ta zo da safe ba yadda sukayi da ita? Da ƙyar ta buɗi baki tace "Wallahi aunty har na zo ƙofar gidan, ku tambayi mai gadi ma ku ji saida muka gaisa, sai kawai na ga lokacin wataƙila Baban yara yana bacci, shiyasa na koma na ce na dawo anjima."

Cikin faɗa kamar za ta cinyeta tace "Ina ruwan ki da baccin shi? Shi ma ba ya san yana baccin ba ya kuma ce ki zo da safe? Me ya sa zakiyi haka Yusrah? Ni fa kamar ƙanwa na ɗauke ki, Yusrah jiya da ya zo har tambayata ya yi wai yanzu ina zaku zauna to? Na ce nima ban sani ba, sai ya ce to idan kin zo na tambaye ki, idan zai yiwu kuma kina ra'ayi, ke da ƙanin naki ku dawo nan da zama..."

Da wani irin mamaki Yusrah ke kallon ta, sai dai ita bata damu da kallon da take mata ba ta ci gaba da cewa" Yusrah, ban taɓa faɗa miki bane saboda ban cika maganar da kowa ba, kuna ganin kamar daga wani garin nake aure ne ya kawoni nan, ba haka bane Yusrah, ni ma haifaffiyar nan ce, kuma iyayena duka yanzu haka suna nan da ƙannaina da komai, saboda bambamcin ra'ayi na wanda zan aura ya sa muka kwashe shekara goma sha biyu ba'a tare da su ba, dan kawai na kawo mijin da nake so alhalin kuma ba soja bane sannan bahaushe ne? Sai su ce ba zan aure shi ba dole sai dai wanda yake aiki irin na mahaifina? Na zaɓi mu gudu muyi aure, amma ƙanin mahaifina ya dakatar da ni daga aikata haka sannan ya aurar da ni, tun daga lokacin da ni da ƙanin nashi mahaifina ya aje mu gefe ba ya kulamu, sai dai Yusrah daga baya na fahimci wautata ta ƴar fari, kuma har yau ina barar yafiyar iyayena, sai dai daga ƙarshe sun umarci mai gadi da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login