Showing 171001 words to 174000 words out of 397328 words
fa. Uhum, ya ɗan yi murmushi ya gyaɗa kai ya sakar masu labulen suma sun yi tsuru tsuru sannan ya juya ya tafi Hajia sai addu'ar a sauka lafiya take yi masa , yaya Muktar kuwa ya fara yin fargaba dan tsoro ya ji kar aje yayi wani abin ma ƴaƴan Hajia tana kusa.
Sai da suka fito kafin su isa inda su Samir suke yaya Muktar ya ce" Ka gansu ko? In faɗa maka haka suke rayuwa, a haka ɗin nan a haka ne, basu iya ɗauke komai ko gyara komai, ban ɗakin dake ɗakin su ba zaka iya shiga ba, ƙazanta ta masu yawa, Hajia ta haƙura da magana da faɗa ta zuba masu ido, ni na zata ai zaka saka su gyara ɗakin nan nasu ne."
AA ya yi ƴar dariya ya ɗan daki gefen hannunsa ya ce" Kai kuwa ba yau ba mana, yau fa na fara zuwa ko? Sai na saba da Hajia ta yadda idan bata ganni ba zata kirayeni in zo ta ganni, ka ga a haka in na taɓa lafiyar ƴaƴanta tsanata zata yi ta ga wannan ai jaraba ce daga zuwa gaisheta? amma in har na zama ɗan gida babu yadda ta iya da ni, sai ma na mata shawarar ya dace mu gyara ƙannenmu in ta yarda sai in samu in ɗauke su mu je anguwa mu dawo in sha Allah."
Yana fitowa su Samir suka sake duƙawa suna masa an fito? A sauka lafiya, ya dakata yana kallonsu ya ce" Ku daina min irin haka mana babu daɗi, ku tashi kun ji?"
Samir ya langwaɓar da kai a ransa yace _" Allah sarki, in ka ganshi haka sai kace wani lallausan mutum ne, sai ka ga waye shi zaka san maciji ne mai baƙin dafin da idan ya riƙa sai ya kashe."_
Ka ga fa su uku wai harda haɗa su da Allah, su dai sun tashin amma sun yi tsuru tsuru har sai da ya hau mashin ɗin sa ya tayar suka yi sallama da Yaya Muktar ya tafi sannan suka ringa sauke ajiyar zuciya, Dauda ya fashe da kuka yana faɗin" Mun shiga uku, yanzu yaya Muktar dama wannan zai zo ka ƙi sanar mana mu bar anguwar? Yanzu wajen wa ya zo wai? Dama ka san shi? Mu ai rabon da taka dokokin ka har ka manta ko? Dan Allah ka yafe mana kurakuren mu na baya in sha Allah ba zamu kuma ba ka ji yaya?"
Yaya Muktar ya yi dariya har ya godewa Allah yana kallon samarin ƙanen nasa, akwai fa wata rana da Samir ya ɗaga masa ƙirji yace da shi ya fa daina haye masa fa, ɗan zaki ya girma, yau ga shegen ɗan zaki ya yi bayi daga ganin mutum, uhum lallai dole zumuncinsa zai miƙe da AA, zai so ya ga yaya zai yi da] an matan can fitsararu da basa jin maganar uban kowa a gidan nan, gashi Hajia ta hana a masu faɗa sai tace a daina takura masu marayu ne, duk sun ɗauko shegen hali sun yaɓawa kansu wai su marayu, zai so ya ga a gidansu ana gyare gyare irin na gidan kowa wanda ba mai aiki ce zata yi ba, aiyukan gidan nan komai sai mai aiki ta yi gashi ita kaɗai ce ba zata taɓa iya gyara ɗakin yaren nan ba, tana gyara na Hajia a kai a kai amma fa bata gyara na ƴaƴan Hajia gaskiya.
*WASHE GARI*
Wunin washe gari sam bai yi tsayi ba, ta kowani fanni wunin sun cinye shi da gaggawa ne, Intisar da ta so su je gida Yusrah ta yiwa su Anna sallama gagara ya yi a dole ta ce washe gari idan sun kai Yusrah ɗin ita sai ta sauka gidansu ta wuni, domin Hajia ta ɗaga mata hankali sosai, saboda tafiyar nan ta Yusrah sai da ta sameta har ɗakin ta ta wanke ta sumul ta ce tana raga mata fa, ta fa kiyaye ta, ita kuma kanta a ƙasa bata iya cewa komai ba sai haƙurin da ta yi ta ba Hajiyar har ta gama faɗanta ta fita ta tafi ɓangaren ta bayan ta watsa ɗan zancen da Bilal ya kafa a falo shi da Yusrah ta ce ya tashi su je, ya kuwa bita suka tafi saboda gudun kar ta wulaƙanta Yusrah ɗin a gabanta ba zai so Yusrah ta fara jin haushinsa ba ko ta yi tunanin ba zata aure shi ba saboda ɗan rikicin nan da ake samu da Hajia wanda ya tabbata zata daina, zata haƙura ta daina ne, duk tunani take yi kuɗa&ensu ne ake ta ci shine damuwarta, suna tafiya suma suka shigewar su suka haɗa kayan Yusrah ɗin a akwati mai taya yar sumulmula mai kyan gaske, sai kayan aikinta na asibiti da yaya Mubarak ya mata siyayyar su.
*AA* kuwa harkar jirgin ya je suka idasa yi, ba irin ƙaton jirgin nan bane, kuma zai ɗauki kaya sosai da motoci huɗu da za'a kai can saboda gyara irin manyan motocin nan da masu kuɗi ke siyowa da zarar sun ɗan taɓu sai an mayar da su ko kuwa su zama hoto saboda in ba kamfanin da ya ƙera su ba ba zaka taɓa samun gyaran su yadda ya kamata ba,
yana can dai aka gama jera kayan ana ta kaiwa cikin jirgin, sannan ya sake duba wajen zamansu shi da yaron sa, da kuma inda ita likitar zata zauna sannan ya yi gida ya taɓo mai masa aski wanda ke zuwa har gida ya masa service home, ya zo ya yiwa yaronsa aski mai kyan gaske sannan ya fita ya je ya ga su Anna ya dawo suka yi kwanciyarsu da nufin tashi da wuri dan su shirya su tafi.
*LOKACIN TAFIYA*
Da sassafe sosai suka kawota asibiti, sannan basu jima ba a asibitin suka yi sallama bayan aunty Intisar ta sake faɗa mata idan suka sauka kawai ta kunna datarta ta saka mata layinta na can, da kuɗi isasshen da zai isheta hawa ta yi abinda take so, ta nuna mata ta whatsup zasu ringa magana da komai da komai dai, ta ƙara yi mata nasiha sannan suka shige mota ita da docter su kuwa su uku suna ɗaga mata hannu har suka ɓacewa ganinsu.
Sosai ta ji tamkar zata yi kukan tafiyar nan, sabo turken wawa, haka kuma ta yarda Aunty Intisar yar uwa ce a wajenta, yaya Mubarack yaya ne a wajenta, Bilal kuwa masoyin ta ne na haƙiƙa, ƙwarai zuciyarta ta ji ba daɗi, sai dai a hankali ta ringa buɗe idanuwanta tana bin aeroport ɗin da kallo har suka ajiye motarsu a wajen ajiye motoci suka fito, Docter ya ciro akwatinta ya janyo ƙarfen da ake ja ya shiga ja ɗayan hannunsa riƙe da blue ɗin gidan takardu mai ɗauke da file ɗin Safwan, ya yi mata bismillah suka je wajen auna kayan ya ɗora akwatin ta tafi zuuuuuu, sannan suka zagaya bayan an duba jakar hannunta da kuma blue ɗin abin, sai su ɗin da kansu aka tabbatar basa ɗauke da wani miyagun abu suka wuce suka shige direct accenseur ya kai su sama, suka sake shiga wani baban fili suka je wajen masu enregistrer ya bada takardarta da komai, ana dubawa a computer aka basu damar shigewa dan an san da zuwansu, ya rakata suka shige har inda jirgin yake a ƙafafuwansu sannan suka ɗan dakata yana sake faɗa mata kar ta saka tsoron komai a tafiyar nan, kuma duk abinda ta ga bata gane ba ga wayarta a kowani lokaci ta yi kiransa ko ta yi kiran Yayanta ko auntynta ta whatsup ta sanar in sha Allah za'a warware mata ko menene, kuma idan sun je lafiya ga takardar da zata ba likitocin, sannan a kayan da aka saka can inda yaron zai zauna akoy allurarsa ta sauke zafin jiki, da ta ɗauke raɗaɗin ciwon bayan, ana yin su duk awa uku, zasu yi awa shida ne a hanya, kenan zata masa sau biyu kafin su sauka, kuma shikenan sai idan a can asibitin an bata wani aikin na kula da yaron, wanda baya tunanin za'a bata ɗin, sai idan sun ɗauko hanyar juyowa ne kulawar da zata masa a hanya kafin su sauka har zuwa asibiti da za'a ci gaba da kulawa da shi.
Komai ta fahimta, ta kuma gane abinda ake nufi, tana fatan kuma ta yi komai yadda aka kwatanta mata, sai da comandan jirgin ya ƙaraso da hostes huɗu ya je ya buɗe sannan suka je docter ya rakata wajen zamanta, waje mai kyau ba kuma zata takura ba, har sai da ta ga to shikenan sauran kujerun haka zasu tafi? Ita dai ta zauna ta saka wayarta a flyth tun a lokacin ta kuma ga duk irin yadda ake zaman da komai da komai sannan Docter ya mata sallama ya juya.
Miƙewa ta yi tana ɗan kalle kallenta, shi look so cute ma sha Allah, tana sanye da tufafi ne wando sakake sosai da rigarsa wacce take buɗaɗɗiya sosai ta kai har wajen guiwoyinta, kalar su somon ne sai farar rigar ciki, sannan ta ɗora farar rigarta ta aiki da kuma baby hijab ɗin ta fari ƙal mai kyan gaske, bayan kwalli bata saka komai ba a fuskarta, amma nutsatsen sanyayen kyanta zai saka ka yi tunanin tana kashewa fatarta kuɗi da lokaci wajen kula da ita.
Tana tsayen nan hostes daya ta zo sanye da ɗamammen skzt ɗin ta ta ce da ita ta ƙara haƙuri kaɗan gasunan sun shigo aeroport ɗin in sha Allah nan da ƴan mintuna za su tashi, sannan ta tambayeta ko akwai abinda take da buƙata? Ta nuna ba komai ta yi mata godiya ta tafi.
Tana nan ɗin dai tana ɗan hangen kai kawon ɗaiɗaikun ma'aikatan gidan jirgin, sai dai kalar tufafin jikinsu kawai take iya hange bata iya hangar kamanin fuskokinsu, tana tsaye jikin yar tagar jirgin ta hango tahotowarsu, bata tsaya ƙurewa kowa kallo ba ta koma ta zauna ta gyara zamanta sosai ta ɗaura belt ta shiga jero addu'o'i da fatan Allah ya taimaketa ya sa kar ta tsorata, addu'a dai kala kala wacce ta ɗaukar mata lokaci bata sani ba har suka gama komai comandan ya shiga jan jirgi sannan ta buɗe idanuwanta tana jin tafiyarsa ta gane tafiya yake yi kenan kafin ya tashi? Ita dai bata ankara ba an yi tafiyar mai ɗan yawa kaɗan sai ji ta yi ƴaƴa. hanjinta gaba ɗaya sun yi ƙasa tamkar za'a kwashe su ko zasu bi ta ƙasa su fito.
Ido ta rintse gam tsoro na kama zuciyarta, har jirgi ya daidaita ya miƙe da tafiya yana ƙara haurawa sama daidai da gudunsa da nisan inda zai je sannan cikinta ya daidaita, amma kuma duk irin sanyin wajen, goshinta ya gama haɗa zufa, sai ajiyar zuciya take saukewa a kai a kai har hostes ta ƙaraso wajenta ɗauke da faranti mai kyau ɗauke da wata kwalbar jus sai kace ta giya, da wata jaka ruwan fara ƙal ta kampanin jirgin wacce ake saka kayan buƙata su abin rufe ido, su bruch, su clean, su safa, su byro, kai abubuwa kala kala dai ake sakawa a cikin yar jakar mai kyau mai ƙwari, sai kuma wani box mai kyau shima ɗauke da kayan ciye ciye ta ajiye mata tana murmushi ta ce" Madame Barka da tashi, ina fatan baki da wata damuwa? kina jin dadin tafiyar?"
A ranta ta ayyana _" Kayya, ina ni ina jin daɗi gani a tsilin matsolo Allah ka sauke yan ƙafafuwana ƙasa lafiya ya Allah."_
A bayyane kuwa sai ta gyaɗa kai tana haɗiyar yawu da ƙyar, hostes kasantuwar aikinta ne, idan ta ga wanda bai saba da shiga jirgi ba ko bai shigo ba daga waje zata iya gane shi, saboda shigar farko bata ɓoyuwa, sosai ake shedaka, ya sa ta buɗe wannan yar jakar ta cirowa Yusrah safar nan fara ƙal irin gidan da safar ke ciki ta bata, ta kuma ciro abin sakawa a kunne shima farin ne ta bata, ta ciro mata abin ido da zata iya rufe idanuwanta ta bata, sannan a tausashe ta nuna mata kayan abincin da jus ɗin ta kuma ce" Idan akwai wani abin da kike son ci, ki yi kira zan zo in kawo maki ko menene, sannan idan ba kya jin daɗin tafiyar ki sanar min in cenza maki waje, ko da wani wajenki ke ciwo ki danna nan zan zo, idan kewa na damunki shima ki yi magana duka muna da yadda zamu taimaka maki ki ji daɗin tafiyar tare da kamfanin mu."
Yusrah kam godiya kawai ta iya yi mata har ta ɓacewa ganinta, sai dai ta ji daɗin safar nan da kuma abin idon nan, nan da nan ta saka ta saka earpeace ɗin ta ta saka karatu a kunnenta ta lumshe idanuwanta, a hankali a hankali nutsuwa ta fara ratsa ta har ta ringa jin hankalinta na kwantawa na tsayawa waje ɗaya.
*A* ɓangare su Aswan kuwa bayan an shinfiɗa Safwan yadda zai ji daɗi saman babbar kujerar vip clsss ya buɗe masa laptop ɗin sa ya saka masa papy pig aka kawo masa yan kayan ciye ciye ya gyara masa a kusa da shi da ƙyar ya samu ya yi shiru da tambayoyin wai jirgi ne suke ciki? To ya tashi? Wun yi sama kuma? Har hostes ɗin dake kula da su sai da ta yi mamakin tambayoyin yaron a ranta ta ayyana _"Ta yiwu haka yake duk idan zasu yi tafiya da babanshi."_ Domin ba zata taɓa tunanin cewa yau ne Safwan ya fara ganin jirgin a kusa ba ma balle maganar shiga wai, sun kuwa sha costume ɗin su color ɗin iri ɗaya marque ɗin kawai ta bambamta, ruwan ash color mai duhu ya karɓe su sosai.
Cire rigarsa ta sama ya yi ya bar ta cikin kaɗai fara ƙal sannan ya zauna a tashi kujerar ya maƙala carbin nan na yatsa fari ƙal ya ci gaba da jan ya salam domin tunda aka saka ranar tafiyar nan ya amshi addu'ar wajen ustaz ya ce masa ya lazumceta ya yi ta roƙon Allah ya sa a yi aikin nan lafiya kuma yaronsa ya samu lafiya, shine fa idan dai bakinsa baya wata maganar daban to yana jan carbin nan ne, dan Allah kaɗai ya san me yake ji idan ya tuna aikin nan ana iya yi bai yi ba fa, ana iya saka yaronsa da ransa a fitar masa baya numfashi, wannan tunani shi ya fi tayar masa da hankali, shi yasa ko yanzu Aba sai da yayi ta masa nasihar ban da ɗaga hankali, a je a yi lafiya a gama lafiya in sha Allah a yi ta addu'a in dai an riƙe addu'a babu abinda zai faru sai alkairi.
Suna tafe yana taɓa jikin Safwan da barci ya ɗauke shi ne, a hankali a hankali har zuwa ukun nan ta yi, jikinsa ya fara ɗaukan zafi sannan ya fara alamun yana son farkawa saboda raɗaɗin ciwon bayan ta yiwu ya fara motsawa, ya dubi agogon hannunsa ya fi a irga, da tunanin lafiyar likitar nan lau kuwa? Ba ta ga time ba ko bata san aikinta ba?
Ganin jikin na ƙara ɗaukan zafi ya saka shi miƙewa a nutse ya nufi inda take a ransa yana ayyana _"Ba fa zai yiwu ba, idan baki san aikin ki ba ina iya juyawa da ke dan shirme a zo da ke ko sau ɗaya ba zaki je ki ga yaya jikin patient ɗin ki yake ba?"_
Yana faɗa a zuci ne yana ƙarasowa inda take har ya zo kanta ya tsaya daga bayan ta amma bata sani ba idanuwanta a rufe, hijabinta ya ɗan ja baya kaɗan, abun rufe idon ya rufe mata, barci take yi birlhaƙƙi ta ɗan duƙunƙune jikinta, wacce ke faɗin ta tabbata ba zata taɓa iya rintsa ido ba a tafiyar nan, sai gata har tana barcin da bata san inda kanta yake ba? Da ɗan takaici ya bubbuga gefen kujerar da kanta yake yana kallonta.
Firgigit ta yi ta motsa ta saka hannu tana cire abin idon, idanuwan suka buɗe tarrr a kansa da abin barcin nan sun mata luhu luhu sai shau shau da suke yi kalar zasu rufe rufffff sai kuma ta masu wani luuu ta buɗe su.
Ido ya sake tsura mata da mamakin ganin fuskar nan a gabansa, a hankali ya kai hannunsa wajen hancinsa ya ɗan murza ya sake zuba mata ido sai kawai ya juya ya je ya ɗauko file ɗin da Docter ya bashi cikin jakar computer Safwan ta likitar da aka ce zata kula da Safwan ya buɗe ya shiga karanta sunanta da komai da komai.
Mamaki ne? Ko menene ya daskarar da shi a tsayen nan ya ɗan dafe goshi cike da tunanin ta ya ya ? Ya ya aka yi hanyarsu ke haɗuwa? Babu irin neman da bai yi mata ba dan su tattauna da tsoron kar aje an yi mata ilar ita ma? Babu irin tunanin da bai yi ba na rashin haɗuwa da ita har ya tattara ya mayar gefe ya ajiye sai gata a yanzu a nan tare da shi kuma?
Shigowar Yusrah da sallama ƙasa ƙasa ta ja ta tsaya tana son sake kallon fuskar mutumen tunanin ta san fuskar nan ya hanata kallon mutumen, dan a iya hangen ta a duniyar mutane dai bata ga ta inda zasu iya haɗuwa da juna ba sai dai a duniyar mafarki, wcace bata tunanin ta taɓa yinsa da shi.
A nutse sosai ta ce" Sorry sir, barci ne ya ɗaukeni, ina box ɗin alluransa Please?"
Fitar amon muryarta a yau ya bambamta sosai da ranakun da suka haɗu, a yau wata irin nutsuwa ke tare da muryarta da sanyi wacce ta saka shi sake juyowa ya zuba mata ido kafin ya cire dubansa ya nuna mata ya ɗan ja baya yana kallo ta ƙarasa ta buɗe kayan aikin ta haɗa alluran biyu sannan ta dube shi a nutsen nan dai yanzun