Showing 210001 words to 213000 words out of 397328 words

Chapter 71 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70005

daga zuciya ya fito ba, sannan yace mata "Ba komai Yusrah, kina lafiya? Auntyn ki tana ciki, sai anjima ko."

Da mamaki ta zuba mishi idanu tace "Amma Yaya Mubarak ba tare zaku tafi da aunty ba?"

A sanyaye ya girgiza mata kai alamar a'a sannan yace "A'a, Yayan ta bai bari ba, amma dai zan sake dawowa."

Daga haka ya yi gaba suka bar ta, ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan ta jinjina kai ta fita zuwa sabgar gaban ta, tana fitowa ta hango shi shi da Safwan yana masa magana ya yi tsugunno irin na maza, tana tafe tana ayyana _" Mutum har mutum a fuska, amma ka hana kowa zaman lafiya a gida, kuma babu wanda zai taka masa birki?"_

Da wannan ta ƙarasa ga Safwan ba ta ko kalli inda yake ba saboda haushin dalilin shi ne fa Yaya Mubarak yake zubar da ƙwalla, amma dai tace da shi" Ina kwana?"_ Sannan ta sunkuya ta ajewa Safwan cake ɗin da cokali dan zai iya ci da kan shi, sannan ta ɗgo ta kalli Anna ƙarama tace" Annarmu, bani wayata ina so zan kira aunty, idan na gama sai kije ki karɓa?"

Da sauri Anna ƙarama ta miƙo mata wayar, tana karɓa ta juya za ta koma inda ta fito dan bata tunanin zai tafi yanzu, har ta juya muryar shi ta dakatar da ita yana faɗin" Y. Turaki."

Cak ta tsaya ta lumshe idanu da tunanin wannan bahagon sunan da yake mata wani wai Y. Turaki, a hankali ta juyo ta kalle shi amma bata amsa ba, dan haka ya miƙe tsaye ya fuskance ta sosai yana zuba hannayen shi aljihu yace" Ki shirya shi, zamu kai shi asibiti yanzu."

A taƙaice kuma a tausashe ta furta" Ok." Sannan ta dawo ta ɗauki robar cake ɗin ta buɗe ta fara bashi dan su fi yin sauri.

A nutse AA kuma ya shiga takawa yana kiran lambar Chef dan jiya sun ɗauko magana mai mahimmancin kawun nan nasa ya shigo masa kwatsam, dan haka yana kin Chef ya ɗauka sai ya shiga takawa yana nufa bayan gidan ta wajen ɓangaren Humed.

Yusrah na ta hanzari ta gama ba Safwan cake ɗin nan ta ji aa buɗe gate ɗin gidan sannan mota na danno kan ta ciki da sake yin odar da ta sakata ɗan zabura ta waiga, niyyar shi ne ta wa motar da mai ita kallo ɗaya sannan ta ɗauke kai, amma da ta ga motar sai ta ɗan tsaida kallon ta da tunanin ina ta taɓa ganin irin ta ma haka tak tak? Yaya Imran ɗan uwan Bilal na da irin ta, amma kala ba ɗaya ba, sannan irin ita ce ake tuƙa twins nan ma dai kalar ba ɗaya bace... Dr. Hamat! Sunan da ya faɗo ran ta kenan, Dr. Hamat kuma? Anan? Ta faɗa da ɗan ƙarfi sanda ya fito daga motar ta ga zahiri, wata irin harbawa ƙirjin ta ya yi da mugun ƙarfi da ta tuna tana fa gidan Alhaji Aliyu Anza ne, Yaya ga Dr. Hamat Anza, sannan kawu ga su aunty Intisar.

Muryar Safwan ce ta saka ta juyawa gare shi da sauri sa'ilin da yace "Aunty, wannan shine likitan ku ko? Na can asibitinnnn?"

Yadda ya mata maganar da irin yana so dole ta tuna ya sa yin murmushi ta jinjina kai alamar e, sai kuma ta sake juyawa saboda jin tsayawar mutum a bayan ta. Idanuwa suka haɗa ita da uncle Hamat ɗin da bakin shi har kunne sai wani murmushin iskanci yake mata, da fari sumar tsaye ya yi da ya gan ta nan gidan, wacce yake ta bulayin nema? Sai gata anan kuma, me take yi? Ita ce nurse ɗin yaron da AA ya faɗa ko? Ya aka yi ma ta zo gidan nan? Duk tambayoyin da suke danƙare a zuciyar sa sai ya tattara su ya watsar ba wai dan zai haƙura da neman amsar su ba, sai dai a shirye yake ko da Yusrah za ta tona masa asiri indai za ta dube shi sannan ta yi zama da shi na aure, to wallahi tsaf zai kakkaɓe ko a kwalar rigar shi, dan so yake mata da yake jin ba ya ma ko ƴar cikin sa shi, so yake mata da zai iya saka shi barin duk wani abu idan ta ce bata so, so yake mata da idan ta ƙi shi zai iya haukacewa ya zama mai kiran sunan ta, yana mata son da idan ta ce sai ya saki maman Joli, to ko tunani ba zai tsaya yi ba zai aikata tsaf kuma ba zai yi nadamar haka ba, shiyasa ya tunkaro ta da maɗaukakin farin ciki na ganin ta a idaniyar shi.

Tsayen da ya mata ƙiƙam yana kallo da mamaki yace "Yusrah? Ke ce kuma anan?"

Shine ba ta ji daɗin sa ba har ta miƙe tana riƙe da robar cake ɗin nan ta dube shi tana yatsina fuska saboda yaran dake nan tace "Ina kwana Dr., e ni ce."

Faɗaɗa murmushi ya sake yi saboda ganin ta amsa shi da kulawa yau, dan haka ya na duban ta yace "To ya kike? Ya mai jikin? Wannan shine Safwan ɗin?"

Ya tambaya yana kallon Safwan da yake kallon shi yana ayyana _"Su dai dangin Dady kowa fari ne kuma mai kyau."_

Da taɓe baki tana wani gaggala masa kallon rashin mutumci tace" Ina nan yadda ka sanni, jiki kuma Alhamdulillah, ya san ran ka to?"

Dariya ya yi yace" Na ji daɗin jin haka..." Sai kuma ya kalli Safwan da ya yi saurin ɗauke idanun shi daga kan shi ya shafa kan shi yace" Boy, ya jikin? Da sauƙi ko?"

Jinjina kai Safwan ya fara yi sannan ya amsa da" Da sauƙi, ina kwana?"

Da fara'a ya amsa shi, sai Anna ƙarama da tunda ta gan shi ta ɗan laɓe jikin Yusrah tana game ɗin ta, ba wai dan tana tsoron shi ko wani abu ba, wasar kaka da jika yake mata yana kiran ta mummuna, shiyasa ba ta ma ƙaunar sabga da shi ko kaɗan. Ai kuwa kamar an ce ya dube ta ɗin ya ɗan leƙa bayan Yusrah yana faɗin "Wai wa nake gani ne haka? Mummuna? Ke ce anan?"

Ƙara lafewa ta yi saida Yusrah ta ɗan sunkuya tace mata "Ya dai Annar mu? Tsoron shi kike?"

A tausashe ta girgiza kai tace "A'a, bana so yana ce min mummuna, ko mai satar sunan manya."

Ɗan murmushi ta mata sannan tace "To ki gaishe shi mana, Papin ki ne fa."

A hankali ta leƙo ta masa ina kwana ta sake laɓewa, amsawa ya yi yana murmushi ya dubi Yusrah yace "Yaushe yaran suka dawo?"

Da wata harara harara tace "Da su muka zo."

Maƙale kafaɗa ya yi irin oho ɗin nan! Sannan ya gyara tsayuwar sa yana ɗan matsawa daf da ita, tana masa daɗin kallo wallahi yarinyar, gashi ɗan canjin nan da ta samu, da turai da ta tafi ba abinda take sai hutu da cin abinci, ma sha Allah ita kan ta tasan ta sake sauyawa ba kaɗan ba, dan ƙiri ƙiri wuyan ta ya shafe gaba ɗaya, sannan ta ji wani wuri na jikin ta da a baya ba haka yake ba amma yanzu take jin shi sosai har idan tana tafiya sai ta ji kamar ana kallon ta, wannan wuri kuwa shine mazaunai.

Matsowar da ya yi sosai kusan ta yana mata raɗa da cewa "To ya ake ciki yanzu? Ina maganar mu ta kwana? Kin san da ina ta neman ki a duk inda nasan zan gan ki? Jiya ma wajen Siddik naje amma ya min rashin kunya, sai dai dake akan ki ne ban ji komai ba."

Ɗan satar kallon Safwan ta yi ta ga shi da Anna ƙarama suna duba wayar ta, sai kawai ta yi ƙasa ƙasa ita ma da raɗar tace" Neman me ka ke me? Ba za ka bari hankalina ya kwanta ba sannan na waiwaye ka? Me ye haka wai?"

Da murmushi a fuska yace" Yusrahhhh, na faɗa miki ina son ki, kuma wallahi da gaske nake au..."

Da jin zafin maganar shi ta matsa daf da shi ita ma har kamar numfashin su zai gauraya sannan ta nuno shi da yatsar ta cikin raɗa sosai tace" Kar ka sake min magana irin wannan, ni Allah ya tsareni da soyayya da irin ka ma bare ta kaimu ga aure, Dr., zan ɗaga maka ƙafa ne kawai saboda kai kawu ne ga wacce ta min halacci a rayuwa, zan barin lamarin da duk ya faru a asibiti ga Allah ya mana sakayya tsakanin mu da kai, amma ƙoƙarin zo min da wata sabuwar bidi'a yanzu, bana jin zamu kwashe lafiya da kai duk da kuwa sona na ganin na saka halacci da halacci, dan Allah ka shafa min lafiya nayi rayuwata."

Tana juyawa a hassale da niyyar tura kujerar Safwan ta sauke idanun ta akan *AA* da ya ɗan ɗauki sakanni yana kallon wannan lamari, uncle Hamat kuma? Da dai mahaukaciyar nan? Me suke tattaunawa haka da har yaga kamar wani raini raini a tsakanin su? Mutumin da yake girmamawa shi da kan shi sannan yake tausasa masa murya? Ko da yake ba abun mamaki bane, to shi ma dake firgita ƙarti ta masa hauka bare kawun shi da take ganin idan abun ya motsa tsaf za ta danne shi ta narki banza. Hmmmmm! Ikon Allah, ka ji fa wani kusanci da suke ta ƙara samarwa a tsakanin su, me ye na wani yaƙe mata baki da uncle yake yi? Wai shi dan Allah me ye na wani ma *kulata* ne in banda jaraba shima? Abinda ya kawo shi gidan kenan? To yaje ya yi sabgar da ta kawo shi mana? Idan kuma babu ya tafiyar sa, mtsssssss!

A hassale shi ma ya shiga takowa kuma ƙwarai duk wanda ya kalli fuskar shi zai fahimci ran shi ya ɓace matuƙa wanda shi kan shi yasan abinda ya faru tsakanin shi da su Mubarak bai kai girman da zai hassala shi haka ba, yana zuwa a zafafen nan ya soka wayar shi aljihu tare da saka hannun shi na dama ya dafa kafaɗar Yusrah ya ture ta gefe sannan ya riƙe hannayen kujerar da mai turawa ke riƙewa da niyyar tura ɗan sa, shi kam ba ya son iskanci fa.

Turar da ya mata har saida ta kai wa uncle Hamat karo a ƙirji, shi kuma dama Allah bamu kuɗi mu kashe ne sai kuwa ya yi raf da lausasan damatsunan ta dake cikin doguwar riga... Karon da ta kai masa ya sa ta furta "Aouchhhh!"

Wannan furucin da ya fito daga bakin ta ya sa shi juyawa a zafafe dan ya ce ta rufe masa baki ko ya mare ta, amma dan jarabar sheɗan sai ya fara nuna masa hannayen uncle da ke riƙe da wuri mai...wuri mai daraja a jikin ta, sai kawai ya ɗaga idanun shi ya kalli fuskar uncle ɗin, ido cikin ido suka kalli juna.

Kallon da ya saka uncle jin cikin sa gaba ɗaya ya murɗa, dan wallahi kayar masa da gaba ya yi har ya manta ma a gaban su wa yake yi ya saki Yusrah da gaggawa yana sake washe baki yace "Son, barka da safiya."

Ba tare da ya sassauta masa kallon nan ba da yake yi masa na kamar ya kama shi yana wa mace ci wawu lega ya ɗauke kai, a ƙasan ƙasan maƙoshi ya furta "Barka."

Sannan ya tura kujerar Safwan ya nufi hanyar falo da shi dan ya sa cikin twins wata ta shirya shi su bar gidan ma, hakan ya sa Yusrah bin bayan shi da sauri, ita ba ma maganar Safwan bace matsalar ta, Yaya Mubarak da ta gani a halin ƙaƙa naka yi? Mutumin da ya taimake ta idan bata taimake shi ba me ye anfanin ta to?

Saurin da yake wajen tafiya ya sa saida ta ɗan tafi a guje kaɗan tana kiran "Ɗan dakata malam, ina magana?"

Cak! Ya dakata, ba wai dan ta ce ya dakata ba, sai ya ji kamar ya tsargu da me uncle ɗin sa ke kallo yanzu? Idan fa ya ƙurawa bayan ƴar mutane idanu? Sannan wane haukan banza ne za ta dinga masa gudu a baya gaban ƙarti?

A hankali ta ƙarasa kusa da shi ta tsaya tace "Dan Allah zamu iya yin magana?"

Wani tuhumammen kallo da haushi ya bita da shi, wallahi fa ta ɓata masa rai? Me ye na wani hira suna matsewa juna haka? Ƙin amsa mata ya yi sai idanu da ya zuba mata yana kausasa mata kallo, dan haka ta ɗan langaɓar da kai a sanyaye tace" Dan Allah fa nace? Minti biyu?"

Ƙara tsura mata idanu ya yi sannan ya ɗaga idanun sama ya kalli uncle da ya shiga motar shi ya nufi ɓangaren ƙofar falon Aba ta waje, sai kawai ya saki kujerar ta Safwan ya koma gefe sannan ya daddafe ƙugu da hannu biyu ya kafe da idanu ita ma tana matsowa dan jin me za ta faɗa masa?

Tana zuwa kusa da shi ta tsaya a tausashe kamar mai masa nasiha ta shiga faɗin "Magana ce dama akan Yaya Mubarak, dan Allah ka bar shi ya ɗauki matar sa idan ya zo anjima? Ka ga abinda ya faru babu masaniyar shi a ciki, laifin wani kuma ai ba ya shafar wani ko a lahira bare anan gidan duniya, dan Allah ka yi haƙuri ka bar su su tafi."

Da yanayin zafi zafi faɗa faɗa yace" Ke a wa da za ki min wannan maganar? Me kika sani game da aure? Me kika sani game da zamantakewar su ta gida? Wa ma ya ce ki zo ki saka min baki?"

Da mamakin nan baki buɗe tace" Tooo! Daga magana ta ruwan sanyi, wai ke me ya sa ba'a magana ta sulhu da kai? Yaya Mubarak kamar uba fa yake gareni."

A ɗan tsawace yace" And so what? Na ce sai aka yi me? Ni kuma ƙane yake a gareni, sai me?"

Da yanayin zafi ita ma dan ya fara kaita bango tace" Wa ɗin? Yaya Mubarak? Wallahi *ubana* ba ƙanin ka bane, dan haka ban ga dalilin da zai sa mutum da matar sa ka saka shi kama layi a gaban ka kamar ya zo wani shan man dan kawai kana taƙamar ita ƙanwar ka ce."

Maganar ta dariya ta bashi ko ya ce birgewa, to ko na ciki da ya baro duk suna son yi masa maganar nan fa, amma kowa ya kasa ana so har a ga yanayin sa ya daidaita... Murmushi ya saki da ya saka Yusrah al'ajabi da tunanin _" Dama yana murmushi haka?"_

Sannan ya gyara tsayuwar sa yace" Y. Turaki, ki cire min bakin ki a maganar nan dan ba abinda kika sani, ki je can ki ƙarata da ƙananan samarin ki da kuma tsofaffi, an ji kunya dai wallahi."

Da mamaki tace" Wa ɗin? Ni? Allah ya sawaƙe, waccen tsohon najadun..."

Saida ya yi wani kiskirim baki buɗe sannan da wani irin siga ta raɗa kamar ƙaramin yaro ya nuna kan shi da yatsa a ƙirjin shi yace" Y. Turaki, *ubana ne* fa? Dan na ce *maman ki* ba za ta koma gidan baban ki bane kike zagar min uba haka?"

Wani ƙif ƙif ta yi da Idanuwa kamar wacce ta shiga nadamar abinda ta aikata, sai kawai ta turo baki da shagwaɓa shagwaɓa tace" Ni dai ban ce komai ba, amma dan Allah ka bar ta ta tafi, ka ji?"

Laha'ilaha illalahu! Ashe Y. Turaki ma ta iya iskancin nan irin na ƴaƴan zamani? Kai duk ma a dakata, wannan yarinyar profesoshi zai ɗauko su yi zama a kan ta su bayyana masa wace iri ce ita, dan shi wallahi ko faɗa masa aka yi ta iya irin wannan kissar ba zai yarda ba, ka duba ƙiri ƙiri ƙato da shi ta saka shi jin kunya, ta sa ya kasa kallon ta sai wani done kai ya yi yana sosa goshi kamar ya zo gaban surukan shi.

Da ƙyar ya ɗaga kai ya kalle ta yana murje ido dan ya kori kunyar da ta bashi, ina dalili shi an namiji kuma shine mai jin kunya haka? Da yanayin ya fi son ayi ta bala'i yace "Ke dakata! Kashedi zan miki na ƙarshe, kar ki sake tsayawa kina hira a gaban yarona, idan zakiyi matsalar ki ce, amma dai ba'a gaban shi, kin fahimta?"

Yana faɗa ya juya da sauri ya shiga tura Safwan, bin shi ta sake yi wanda hakan ya sa shi yin murmushi kamar irin dai yana jin daɗin ta yi ta biyar shi haka hankalin sa na kwanciya sosai, saida ya ɗaga Safwan cak ya haye matakalar da shi sannan ya hau shi ma, da sauri ita ma ta haye tana faɗin "Maganar Yaya Mubarak, za su iya tafiya."

Juyowa ya yi a tsawace yace "Wai ke ba za ki rabu dani bane, bana son damuwa fa? Wannan matsala ce ta cikin gida, ƙanwata ce ita shi ma kuma haka, dukan su zan iya ladabtar da su idan sukayi ba daidai ba, ko baki san daga Mubarak din har Intisar zan iya saka belt na zane su ba?"

Girgiza kai ta yi da izza tace" Ba zai yiwu ba wallahi, *iyayen nawa*?"

Nunota ya yi yace" Iyayen naki mana, da ke, da su, kaf sai in zane ku kuma a gaban wanda kuke ganin shi ya ɗaure muku ƙugu, saboda har ke ma *ƴata ce*."

Da mamaki tace"...




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:09 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login