Showing 222001 words to 225000 words out of 397328 words

Chapter 75 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70028

ko ina ina so ka kaini gidan su Intisar in bada haƙuri ni ko a yi mu dawo gida ka ji?"

Wani irin farin ciki nan take ya wanzu a fuskarsa, har inda inda yake yi wajen faɗin" To Hajia, in sha Allah, bana yin komai Hajia, na gode Allah ya ƙara lafiya ya ƙara nisan kwana."

Daga wannan ya tafi zuciyarsa cike da farin ciki, Hajiar kanta sai ta ji kamar wani abu ya faɗa mata a ƙirjinta da ya riƙe mata ƙirji, ta kwanta da fatan Allah ya tashe su lafiya ta je ta ga iyayen yarinyar su sulhunta juna.

Yaya Mubarak kuwa yana zuwa ya yi kiran aunty Intisar, sun shirya da juna tuni, kawai ta nuna ba zata taɓa take dokar Yayanta bane, sai idan ya amince zata koma, Anna da Aba kuwa tunda ta buɗe baki ta sanar masu asalin irin rayuwar da take yi da Hajia da kuma irin abinda yaran nan suka gani sai suma suka ƙyale AA ya yi yadda ya ga dama, sun dai san ba zasu bari ya raba auren ba, amma kuma zasu bashi dama ya ƙwatowa ƙanwar sa ƴanci, idan ta koma gidanta kar wannan ƴar hatsaniyar ta jaza mata wani bala'in da sarakuwarta, kai su basu san cewa a yanzu haka su Hauwa'un suna can daf da shiga halin shiga uku domin a ɗan tsakin nan ya gama gyara hanyar da zai bi a tarkato su a watso su gida daga su har ƴaƴansu su zo kusa da shi ta yadda zai fuskance su kuma su dawo da zama Nijar ɗin ya ga ta tsiya.

Ai kuwa ta yi farin ciki sosai, ta yi farin ciki, bata san cewa tana son mijinta da so mai tsanani har tana iya jure koma me ye ba sai da suka ɗauki lokacin nan magana ita da shi sai dai a waya a ɓoye kamar yaran goye ba sai yanzu da haka ta faru, a daren har wani barcin farin ciki ta yi rungume da ƴaƴanta, ta tabbata gobe wajen ƙarfe goma Akhi ya zo gidan nan daga asibiti, idan kuwa ya zo zasu haɗu da Hajiar, tana fatan ko menene Allah ya sanyaya shi, ta yi kwanciyar ta bayan ta sanarwa Anna cewa Aban su Anna ƙarama yace gobe zasu zo da Hajia.

Anna ɗin kanta ta yi farin cikin haka, dan ita ke karantar ƴar ta, sarai ta san tana son komawa gidanta ama ta yi mata banza in har ba magana aka yi da sarakuwarta ba ita ma ba zata bada yarinya ba, son kai ɗin ai kowa ya iya shi.


*Washe Gari*

Wajen ƙarfe goma sha ɗaya na rana bayan zuwan su gidan sai da suka ɗan yi jiran Aswan, domin tun goma saura ɗin suka ƙaraso, shi kuwa ƙa'ida ne yana ba goma baya yanzu dan sai ya je ya ga ɗan sa sun sha fira sosai sannan yake zuwa gidan ya gaisar da Anna, in Aba na nan shima ya gaisar da shi sannan ya tafi.

In ba dan girman Hajia ba, yau da abubuwan da zai faɗa mata sai hankalinta ya tashi, amma ganin shekarun matar ya sa ya taushi kansa aka yi magana a tsanake, balle da ta nuna ita bata san ainihin abinda yake faruwa ba, yarinya ke kiranta ta ɗorata a kan abubuwa ita kuma ba sani ta yi ba sai ta hau, sai jiya da Bilal ya kawo mata komai a bayyane sannan ta gani, shine ta kasa barci tace yau sai ta zo ta bada haƙuri dan Allah a yi haƙuri komai ya wuce yarinya ta koma ɗakin ta da ƴaƴanta su yi zaman su.

A nan ne Aba ya saka baki ya fara nuna komai ya wuce, tunda har an fahimci haka shikenan zata iya komawa ɗakin ta Allah ya kiyaye gaba. A dole shi ma ya nuna shikenan its ok, komai ya wuce, amma ya ja warning sosai a kan irin rayuwar nan ya nuna ba zai iya lamunta da haka ba.

Ita dai Hajia da ita, da uncle ɗin su Yaya Mubarak da Yaya Mubarak ɗin sun nuna sun yarda an gode Allah ya saka da alkairi, Hajia na murmushi ta ce" Ni da na zo da magana biyu, maganar yaran nan da suke son junansu, ita ma nace idan na zo in sha Allah zan tambaya in har an bamu dama mu je mu fito, in ma kafin uban yarinyar ya tafi zai ɗaura auren ai shikenan sai a ɗaura ita ma ta tarewarta a gidanta in sha Allah."

Anna ta faɗaɗa da farin ciki da faɗin" Ma sha Allah, ma sha Allah kai Alhamdulillah, ai kam yara sun fahimci juna tuni, na tabbata jira suke a basu dama, ma sha Allah ai Bilal da Yusrah suna son juna, Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Aswan dake zaune bai iya furta A ba, kallon su dai ya yi ya taɓe baki, ya so guduwa tun ɗazu fa amma Aba ya nuna masa ai ba wannan maganar, ya tabbata maganar su zasu yi a yanzu wacce bai san yaya zasu kwashe ba, ya jima yana ta kauce masa dan kar su yi maganar, amma yanzu zuwan su Hajia dole ya ritsa shi ya kuma san sai sun yi ɗin, shi dai abu ɗaya ya sani yarinyar nan sam bata yi masa ba, ba zai iya aurenta ba, dan ma tun ranar da ya masa voice sun yi magana ta whatsup cikin dare shi da Aban, sun ɗan ganewa juna, amma Aba ya nuna zasu zauna ne, shi kuwa ya tabbata cewa zai yi ya tanƙwasa shi kan maganar, bayan sam yarinyar bata yi masa ba.

Yana dai zaune suka yanke ranar da zasu zo neman auren gyaɗigyaɗin, wato mandiya hamshaƙiyar can sannan suka tafi, shi kuwa ransa ya kai ƙoluluwar ɓaci da wasu tunanika da suka gama cike masa kai.

Aba ya fuskance shi bayan watsewar kowa ya ce "Aswan, ɗazu kuma muna magana ta waya nace a waje dai ya fi, ina sauraron ka?"

Aswan ya sauke ajiyar zuciya yana korar duk wani abu da ya nemi dagula masa lissafi da tunanin da bai dace ba ya mayar da tunaninsa a gurbin lafiya lau ne ya dace, dukkan abinda ya gani daidai ne, duk wanda ya fitar da miji kuwa a masa aure shine ya dace, a hankali ya dubi Aba a tausashe ya ce" Aba, kace ai ba komai bane, ba kamannin ta bane shikenan tunda ta maka bani da ja."

Aba ya sake sauke ajiyar zuciya, ya fuskance shi sosai ya ce" Bata da wata makusa jikan Anza, ka kwantar da hankalin ka ni da kaina ba zan samo maka macen da bata dace ba ka gane? Maganar auren ku ba fashi in sha Allah."

Aswa ya gyaɗa kansa bai ce komai ba, Aba kuwa ya sake jin hankalinsa ya kwanta tunda har ya amince a karo na biyu, cann suna zaune ya ɗan dubi Aba ya ce" To wai me yasa take matse murya uwa an shaƙe akuya ne Aba? Kuma me yasa in ta gani take hararena?"

Aba ya kalle shi da tarin mamaki, a ɗan sukwane ya ce" Harare kuma?"

"Eh Aba, harare ne sak." Aswan ya faɗa tsakaninsa da Allah da gaske yake, Aba ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce" A'a, ina ga baka iya ware harare da fari bane Jikan Anza."

Aswan ya ce" To shi fari ɗin a kan me take yi? Ni gashin idon nata ya fi komai tsoratani, jiya da gudu na fita, kuma sai da na kashe fitila na ga kamar ta harareni fitilar ɗakina a kunne ta kwana jiya, ni matan nan duk kamar a zare suke Aba."

Aba ya ɗauke kai ya ce" Zan ga gashin idon, ta yiwu shi ma sakawa ta yi, kar ka damu duk abinda bai yi maka ba za'a daidaita a gyara in sha Allah, zamu je maganar jibi a kai komai da komai, mahaifinta ya ce Mamanta tace ba sai an yi siyayyar kayan akwati ba a kai kuɗi kawai su yi, gashi nan da wasu kwanaki za'a dawo kan maganar auren Yusrah, in sha Allah dai zan yi auren ƴaƴa biyu bana."

Aswan ya mayar da kansa jikin kujerar yana taɓe baki bai ce komai ba, sai da ya tashi tafiya a tausashe ya ce" Aba, a duka tafiyar nan abu biyu nake roƙo a min, kuɗin kayan da suka buƙata a kai ina so a kai rabin milyan, kuɗin sadaki kuwa ina so a kai dubu hamsin, wannan shine kaɗai abinda nake roƙo kuma nake fatan a yi, bana so kowa ya saka sisi Aba, bana so kowa ya yi mata wata kyauta har sai an gama auren idan na bada dama dan Allah Aba."

Aba ya dube shi da tarin tambayoyi a zuciyarsa, ya kasa amsa shi har sai da ya masa sallama ya tafi ya bar shi cikin tunani, rabin milyan a wannan zamanin me da me zata siya ne ita amaryar? Me yake faruwa ne? Ba zai taɓa gigin tunanin ko bashi da kuɗi bane, dan ya san yana da su a yanzu, shin idan aka kai ƴan kuɗaɗen nan auren budurwa yarinya mai tsada kamar ƴar Chef ba tozarci bane ba kuwa? Ya Salam, dole ya yi kiran Anna dake kicin saboda yana gida bata sakarwa kowa aikin mijinta.

Anna da ta zo suka zauna ya sanar mata damuwarsa a nutse, Anna ta yi shiru na ɗan lokaci, aurensa guda? Auren da suke tunanin idan suka tashi siyayya sai ƙafafuwansu sun fara ciwo dan wahala da kai kawo saboda aure ne da ake jira aka ciwa buri sosai shine ya ce a kai sadaki haka? Sai dai ba zata taɓa hanawa ba saboda bata da hujja dan haka a tausashe ta ce" Abansu, sadakin dubu hamsin ba haramun bane, ko ba komai albarkar auren muke nema, maganar kuɗin kayan akwati kuwa ina ga a bashi dama mu ga me yake nufi, idan aka ɗaura aure sai a maido shi hankalinsa, dole zai ba yarinya wadatattun kuɗi ta yi tufafi tunda Allah ya hore masa, amma yanzu a je a haka ɗin kuma a bashi damar da ya roƙa."

Aba ya sauke ajiyar zuciya ya yarda da maganar matarsa, ya miƙe yana faɗin" Annar yara bari in je in huta kaɗan, kafin a yi kiran sallah." Sai kuma ya hangi Nabihat ta glass ɗin ƙofar shi, da kallo ya bita da gashin idanuwan nata, wa'inda bai taɓa kallonta haka ba sai dan irin yadda Aswan ke jadadda cewa yana bashi tsoro sai ya ga kai eh fa, abin zaƙo zaƙo ya yi yawa sosai, ai kam da kula ya dubi Annar su ya ce" Kuma, yarinyar can ki saka ta cire abin nan na idanuwanta, wai tsoro suke bashi, hum ita ma ya yi yawa abin nan ina dalili har ta janyowa kanta iskokai wannan."

Anna ta yi dariya ita dai ta nufi kicin ɗin a ranta ta ayyana _'Wannan lamari dai Allah kai na kaiwa kukana, idan har ita ɗin ce alkairinsa ka tabbatar sannan ka shirye shi.'_



*WAIWAYE*


Sati ɗaya da tafiyar Yusrah U.S kawu Suleiman ya diro garin, ba inda ya fara sauka shi ma dai kamar aunty Fureira sai gidan Goggo Hinda, rashin ɗaukar wayar sa da bata yi ya sa bata san zai zo ba, dan haka hankalin ta kwance tana ta sabgogin ta, dake shigowar yamma lis ya yi ita da su Safiya kowa da aikin da yake yi, kan mai dafa wake da shinkafa da ake yi na dare, kan mai suyar zabi da kaji da suma ake fitar wa waje, sai ƙanin Safiya dake ɗaurin kunu ita kuma Goggon tana yankar albassa kishiyar ta kuma na suyar fara baiwar Allah, aiki ne da ya zamar mata dole, sisi bata samu a aljihun Goggo, amma wannan aiki ya zamar mata dole kuma sai ta yi shi ta yi na gida ko da kuwa za ta mutu.

Sallamar sa kaɗai ta kayar mata da gaba da duƙe kai tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Ba ta iya ɗaga kai ba, ta sani ne sai ranta ya ɓace dan tashin hankali fiye da wanda ta gani ranar da mahaukaciyar Fureiran nan ta zo mata gida, dan haka duk jikin ta ya yi sanyi ta rasa makamar dafawa, ba ta san ya zasu ƙare ba, hasalima da Suleiman zai ji abinda ta ma su Yusrah wallahi ta san zai iya sa wa a ɗaure ta ya tuhumeta da ɓatan su, ƙaramin ƙanin su ne da gaba ɗaya shekarun sa basu wuce 34 zuwa 35 ba, amma haka Allah ya halicce shi ya fi Abdul-Hameed zafi nesa ba kusa ba, kai Baban su Yusrah ma ai ba ruwan shi, shi kaga ran shi ya ɓace to wajen tarbiyar yaran sa ne idan sukayi ba daidai ba, to zai iya zane mutum kuwa.

Da ƙyar ta ɗaga kai ita ma ta shiga sahun masu yi mishi sannu da zuwa amma fa ba da wannan kauɗin ko ɗaga murya ba, har Safiya ta kawo mishi kujera ya zauna ta kawo ruwa ta aje ya mata godiya, an ɗauki wasu mintuna kafin ya kalle ta suka sake gaisawa, daga bisani ya ɗora da "Aunty Hinda ya ake ciki game da maganar su Yusrah? An ji labarin su kuwa?"

Saida ta ɗan saci kallon shi irin bata da gaskiya sannan ta kalli inda kishiyar ta take, aka yi sa'a tana kallon ta ne ita ma sai kawai ta mata alama da idanu ta tashi daga nan, da sauri ta tashi ɗin sannan ta umarci Safiya ta ci gaba da juya mata farar ta kar ta ƙone, saida ta ga ba kowa sai ƴaƴan ta sannan ta dube shi murya ƙasa ƙasa tace "Suleiman, ya baka sanar dani za ka zo ba? Sai na ganka haka kwatsam?"

Wani kallon ban fa son iyayi ya mata yace "Ya ban sanar dake zan zo ba? Ta ina zan sanar da ke ɗin bayan kin sakani a baƙin jadawali bana iya samun ki, ni dan Allah faɗa min ina yaran nan suke in tashi."

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tace "Duka suna nan, an gan su, Yusrah ita na gan ta sosai ma, Safwan dai ne ban ganshi ba har yanzu."

Ɗan waigawa ya yi cikin gidan yace "Ina Yusrahn take? Kira min ita?"

Da sauri tace "A'a ai ba'a nan suke ba, Yusrah ai ta ƙi mu, tana can gidan masu kuɗi ta zauna abun ta tana sheƙe ayar ta."

Wani matsiyacin kallo ya mata yace "Ban gane gidan masu kuɗi ba? Su waye su? A ina ta san su? Danginmu ne ko dangin Maman su?"

Amsa ta bashi da "Ba ko ɗaya, nima sanda aka neme ta ɗin nan aka rasa, bayan wasu kwanaki kawai sai gata da wata Hajia mai kuɗi, wai ko ɗan matar ne ya banketa, amma tsabar rashin mutumci da suka zo ba dawo min da ita sukayi ba, wai suk zo amsar lambar Fureira ne, nima sai na ƙyaleta ta bi su suka koma, to in taƙaice maka rannan ma sai ga Aminu wannan ɗan uwan nasu dake bakin tasha, wai ana nema na washe gari, haka naje in gaya maka wani tanƙamemen gida, na samu Yusrah ta gyagyije abun ta ba ta da matsalar komai, wai a ƙarshe an kirani ne dan in yarda Yusrah ta zama ƴar gidan nan saboda su dai suna ƙaunar ta, sannan suka mana alƙawarin samo Safwan duk inda ya shiga."

Tunda ta fara magana irin kallon ci gaba ɗin nan ne yake mata ina sauraron ki, saida ta dasa ayar nan yace" To, ni gaba ɗaya ban fahimce ki ba, to da aka yi haka ke sai kika ce musu ya ya kenan?"

Murmushi ta yi da tausasawa da kuma ladabi kamar ita ce ƙanwar shi kuma Yayan tace" Suleiman ya zan ce musu ni kuwa? Manyan mutane ne, haƙura nayi na bar musu duk da ina son zaman su tare da ni, musamman da naga ita ma Yusrah tafi son zama a gidan tunda ya fi abun more rayuwa, sannan kuma su zasu iya tsayin daka wajen nemo mana Safwan ɗinmu, amma kaga mu tunda ba kuɗi gare mu ba ko wajen jami'ai muka je hanya hanya ne zasuyi ta mana."

Dogon tsaki ya ja yace" Yanzu aunty Hinda yaran Yaya Abdul-Hameed ɗin kika bari a hannun mutanen da baki san su ba? Kika tafi kika bar ƴa mace a tare da mutanen da bata da haɗin komai da su? Kuma har kike zaune gidan ki cikin farin ciki kin saka naki ƴaƴan a gaba?"

Girgiza mishi kai tayi tace" Wallahi ba haka bane Suleiman, da nace nima ba zan bar Yusrah anan ba ita ta kalleni ta ce na barta a nan, ya zan yi to? Shiyasa na bar ta."

Ɗaga mata hannu ya yi yace" Dakata dan Allah Hinda, kinga shiyasa kika ga ni da ke ba ma jituwa wallahi, son zuciyar ki yawa ne da shi, ni dama bani da burin barin yaran nan a hannun ki, tunanina shine su zauna hannun ki na kwanaki kaɗan kafin in zo, niyyata da na zo zan yi ƙoƙarin kammala aikina sannan nayi aure dan su Yusrah su zauna tare da iyalina, amma a ƙarshe wai a ce an nemi yaran nan an rasa saboda sakacin ki da wauta."

A sanyaye ta dafe ƙirji tace" Sakacina kuma Suleiman? Me nayi na sakaci? Kai baka san Yusrah ce ta tafi ta..."

Da sauri ya katse ta da cewa" Kinga, duka fa nasan me yake faruwa, na ji duk abinda ya faru wajen Khadija, ta faɗa min gaskiyar komai, tunda aka kwantar da su asibiti sau ɗaya baki taka kika je ba, sannan filin mu da aka siyar ni kin faɗa min kuɗi, amma yadda aka ce kin ba Yusrah a matsayin kason su ba haka kika bani ba, sannan zaman makoki da aka yi an tarawa yaran nan kuɗin sadaka da tallafi da gwamnati ta bayar ga duk wanda abun ya shafa, nasu an e kin taushe baki basu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login