Showing 267001 words to 270000 words out of 397328 words

Chapter 90 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69998

ta yanzu da na fito take zawarcina tana so a koma, da babu abinda ya haɗani da ita ƴaƴana kawai ya sa nake dubanta, amman yanzu ina ga gwara in je mu rufawa juna asiri a koma kar ƙarfina ya zo ya fara ƙarewa ban ci ƙaniya iya ci ba." AA dake cikin tunani mai tsananin gaske ya ɗago sanadiyar salatin da Muktar ke tafkawa yana istigfari ya ɗan zuba masa ido ya sake ɗaukewa ya kuma afka wani tunanin.

Ashe ashe zai yi aure dai, to wai dama ɗaurin auren kawai da lokaci ya yi yi ake yi? Shi abinda ya fi bashi mamaki auren wannan ƴar babu wanda ya rarrashe shi ko ya masa zancen, daga sama abin ya faɗo, amma ya ji ba zai taɓa musawa ba, ko dan ya san eh lalle bashi da gaskiya ne ko menene? Shi dai bai san dalili ba yana ji a ransa kamar ba zai iya musawa Aba ba, kuma kamar ba zai ƙi abin ba, kai inna lillahi, to wai yanzu shikenan sunanta matarsa yarinyar nan?

Dukan ƙafarsa da Muktar ya yi yana faɗin" Freind kana jin abinda Arif ke faɗi? wallahi sam bashi da kunya, aure ko? Ka jira lokaci zan yi aure nima verry soon in sha Allah yaro, kuma sai na zo na fika ganin mata iya gani yaro."

AA ya yi kiskirim yana kallonsa, can ya ɗan zabura ya ce" Astagfrullah! Kai wai zancen me ye kuke yi?"

Arif ya wani gyara zama ya ce" Zancen ƙaniya muke yi, wai shi d'an da auren ma ba'a masa ba yake ikirarin zai zo ya fi ni adadin ganin ƙaniya."

AA ya saka hannayensa biyu yana dafe kansa haɗi da haɗe ƙafafuwansa ya miƙe yana faɗin" Lokaci ya yi da zaku yi tafiyarku, ni zaku lalata da manyan maganganu? Ku tashi kawai ku yi tafiyarku."

Muktar da Arif suka kalli juna, Arif ya miƙe ya nufi ciki yana faɗin" To ka ji, ai yau sai na ga ƙwal uwar daka, sai na ɗauko Yussy na yi ɓarin wuta da ita kafin mu rabu."

Muktar kuwa ya taɓe baki ya yi kwanciyarsa ya shiga dokawa Abrar kira dan yana buƙatar ya ga wankanta na yau, yana son ya ga kwaliyar da aka cencenɗa a yau ta yiwu ya sume daga kwancen nan da yake.

Ganin sun maida shi shashasha sai kawai shi ya bar musu ɗakin ya yi waje yana ta tunaninsa dan so yake ya gama gane komai kafin su yi ido huɗu da yarinyar nan, a daidai motarsa ya tsaya ya ɗan haɗe fuska a ransa ya ayyana _' Ni na san biyayya zan yi, zan kuma rufa maki asiri in raba ki da ruɓaɓɓun samarinki, ina fatan zaki gane haka yarinya.'_


(Lokaci dai AA)


Har kusan ƙarfe biyar na yamma Hajia na fama da Bilal a ɓangaren ta, domin ƙarfe goma aka sallame su suka dawo gida ta masa shinfiɗa a ɓangaren ta, kawai kusan ƙarfe goma sha biyu ya ga sanarwar ɗaurin auren a Tiktok a shafin Uncle Sulaimane, kasantuwar yana da numbarsa kuma ya yi folowing ɗin sa ya sa da zarar ya ɗora abu yana gani da wuri ne, yana shiga ya ga taron ɗaurin auren da abinda ya rubuta a sama kamar haka "*Alhamdulilah, Allah ke da komai, Allah ya baki miji ƴata Yusrah, Allah ya sa Aswan Aliyu Anza ya zamo uba ga marainiya*." Ai tun daga lokacin ya birkice mata ya ringa rusa kuka da faɗin wallahi sai ta neme shi ta rasa ba tana ji tana gani ba ta masa sanadiyar da ya rasa Yusrah? Yayanan an aurawa Yusrah Yayan aunty Intisar, yanzu ya ya zai yi da ransa? Ya ya zai yi tunanin samunta? In dai bai samu Yusrah ba mutuwa zai yi ko ya gudu ya bar mata ƙasar, tun daga lokacin take fama da ranta, ta yi kiran Mubarak bata samu, ta yi kiran Imran bai ɗaga ba, Hauwa kuwa kwana kusan biyar yau bata da labarinta bata san me yake faruwa ba, hankalinta a matuƙar tashe yake, kenan Aswan Elhaji ya aurawa yarinyar nan? Lalle rayuwa, nan da nan ta fita hayyacinta ta yi zuru zaune daf da Bilal tana ta faman bashi baki da kwatanta masa bata ƙi Yusrah ba halayyanta ta guda, kamar da wasa suna nan zaune jikinsa yana neman rikicewa kira ya shigo wayarta da wata numba baƙuwa.

Ɗagawa ta yi tana yin sallama, daga ɗayan ɓangaren ko sallamar ba'a iya amsawa ba aka ce" Mama nice Hawa'u, ki sa Yaya Mubarak ya min Nita ta wannan numbar yanzu yanzu dan Allah mu ciro tiketen zuwa Kanya, gamunan mun sauka ba ki sisi a jikinmu daga mu har yaran muna cikin halin buƙatar taimako, yanzun ma wayar na amsa a wajen wani daga mu sai tufafin jikinmu dan Allah ya yi sauri."

Tsaye Hajia ta miƙe a razane dafe da ƙirjin ta tace "Hawa'u? Ke ce? Ban gane ba? Kuna ina ne?"

Cikin yanayin gaggawa Hawa'u ta sake cewa "Hajia dan Allah ki yi sauri ki faɗawa Yayan, wayar mutane ce na karɓa kuma babu isash..."

Ɗif! Wayar ta yanke wanda hakan ya sa Hajia bin wayar da kallo ba ta ɗauke hannun ta a ƙirji ba tace "Muhammadu rasulillahi sallalahu alaiji wa sallam! La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu mina zallumin! Me yake faruwa ne? Jama'a me yake faruwa dani ne?"

Sai kuma ta kalli Bilal da kamar bai ji salallamin da take yi ba hankali tashe ta miƙa masa wayar tace" Bilalu, inda kira min lambar Mubarak in yi magana da shi."

Miƙewa ya yi daga birgimar da yake yana yarfa hannaye kamar yaro ƙarami yace" Ni ba wata lamba da zan nemo miki, kawai ni Hajia ki sa a dawo min da matata wallahi."

Ya yi maganar yana ficewa ba tare da ya nemo mata lambar ba, da kallo ta bishi tana sake wani salallamin riƙe da haɓa, sai kawai ta fashe da kukan ita ma ta zauna kan katifar tana faɗin" Shikenan tawa ta ƙare, jama'a ƴaƴa duk sun juya min baya? Wacce nake sa ran samun sanyi daga gare ta ita ma gata na ban san me take nufi da basa amecira ba."

Cikin sa'a sai ga Yaya Mubarak ɗin ya shigo gidan kai tsaye kuma ya nufo ɓangaren dan ganin Bilal, nan ya tarda Hajia na wannan kuka, amma tana ganin shi ta share hawayen ta faɗa masa abinda ya faru da buƙatar ta Hawa'u, shi ma da mamakin jin wai basa can ya fita da gaggawa yana kiran lambar da ta kira, ya kuma dace aka ɗaga aka bashi Hawa'un, nan ta buƙaci ya tura mata kuɗin akan lambar ta da sunan ta tunda katin ta yana tare da ita sai ta ɗauka, bai tambaye ta komai ba dan ya ji kamar ba a nutse take ba, dan haka ya fara tura musu kuɗin sannan ya shige gari dan ba zai iya haɗa damuwar ta da ta Hajia lokaci ɗaya ba.


*Y. TURAKI*


A ɓangaren gidan su Yusrah biki aka wuni yi cikin kwanciyar hankali da ƙaimi fiye da yadda aka tsaro da farko, domin ƴan matan Anna na jin abin nasu ne mai suna nasu suka zagine suke shan bikinsu hankali kwance, suka bi Yusrah da addu'ar Allah ya sa ta yi haƙuri da wuri, domin ko da bata yi haƙuri ba su kam sun shirya rigima da ita sai ta yarda da oga babba, bata da miji sama da shi, shine duniyarta ya dace ta gane haka.

Tunda aka yi sallar magariba iyayenta suka shige da ita suka shiga shiryata dan miƙa ta gidan sirikanta sannan iyayen riƙon ta, kusan ƙarfe takwas duk wani shiri da ya kamata ace an yi an gama shi, Yusrah an saka mata ɗinkin kanance riga da zani basu da adon komai sannan ba'a yi mata ado ba, an rufata da irin zanin da aka yi mata ɗinkin an saka mata silifas ɗin ta blue sabo ƙal.

Iyayenta suka sakata a gaba suka yi mata nasiha mai ratsa jiki da zuciya, sosai suka yi mata nasiha da bata haƙurin zaman duniya da yin biyayya wa mijinta, sun tunatar da ita ta kula, babu maganar mijin da aka aura mata ba da shi suke soyayya ba, magana ake yi ta hukuncin da Allah zai iya ɗora mata idan ta shiga haƙƙinsa ta je da nufin yin zaman aure da yin biyayya, sosai suka yi mata faɗan da ko da iyayenta na raye abinda zasu yi mata kenan sannan aka fito da ita luluɓe su Manal da suka sha lafaya na rakiyar amarya sai wanke ta suke da turare da watsa fulawa mai ƙyalƙyali wacce dama ita suka tanadar dan kaita ɗakin ta.

A motar Arif aka sakata, aunty Furera da aunty Intisar suka sakata a tsakiya, sauran motocin suka kwasa, tasa ta shiga tsakiya sannan sauran suka rufa masu baya, a yan rakiyarta har da matan liman babba na anguwar da jama'ar anguwar sosai, haka suka kwasa suka nufi MENTION ALIYU ANZA dan sada Yusrah da ɗakin ta.

An yi jerin gwano sosai an yi abin cikin tsari, an tafi da ita a hankali tamkar an ɗauko ƙwari, masu ɗaukan vidio na yi masu ɗauka da wayarsu na yi har aka shige ƙaton gidan Aliyu Anza sannan aka sadata da Anna wacce ta ci kwalliya fuskarta sai walwal take na farin ciki, tana tare da matar uncle Hamat, da matar Humed, da Goggo Tidin da sauran aminan arziki sun shirya tarbar amarya sosai, duk da a cikin makusantan da ake yiwa kallon makusanta ne na daf da daf matar ɗanta kaɗai take walwala da murnar abin, sauran suna zaune ne dan ya zama dole.

A ƙasa aka zaunar da ita daf da ƙafar Anna, bayan gaishe gaishe da yi musu barka da zuwa Anna ta dafa kanta a tausashe ta ce " Allah ya miki albarka ƴata, Allah ya sa canjin nan shine alkairinki da mu baki ɗaya, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe duk wata fitina."

Jama'a ke ta amsawa da amen amen Anna kuwa haƙoranta cike da fara'a, kana kallonta zaka gane wannan rana babbar rana ce a wajenta wacce ta jima tana jira domin a bayyane farin cikinta yake, a tausashe ta ce" Intisar, ku kaita ta huta, sai a zo a tarbi baƙinmu sosai."

Goggo Tidin ta taɓe baki tana cire kai a ranta ta ayyana _' Aikin banza, sai kace wanda idan ya tashi aure zai ɗauko mana ƴar shugaban ƙasa, ashe a nan za'a tile, ba wani tsinto yarinyar nan aka yi, ama fito a faɗa mana gaskiyar lamarin tun yaushe suka san juna sannan yaron nan a sanar mana ta yiwu jikan Aliyun ne na gaske ba wai taimako ba, dan ba zan taɓa yarda cewar taimako ne ya kawo har haka ba tunda babu wanda kuka fi balle ku ce kun fi wani zuciyar musulunci!'_

Ɗakin da aka gyara mata aka sake mata furniture aunty da aunty Furera suka kaita, bayan sun ƙara shirya mata komai suka fito suka barta da ƴan matan Anna da su Maryam, suna fita ta yaye luluɓin nan ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya ta sauke masu harara ta ce" Wallahi kun cika surutu, yanzu a barni in huta kafin mu raba hali."

Maryam ta zaro ido ƙasa ƙasa ta ce" Ke amarya kike fa, kika yaye luluɓin tun kafin a bamu kuɗin buɗar fuska da siyan baki? Yau ga rashin mutunci."

Manal ta zaro ido tana kama baki, Abrar ta riga ta faɗin" Aunty Maryam, a wajen wa zamu amshi kuɗin siyan bakin? Ni kam ba da ni ba ku yafe min in kun amso a ban rabona."

Manal ta yi dariya tana faɗin" Ai inaga siyan bakin nan sai dai amaryar ta yo mana, mun bita bashi dan wallahi ni ɗin nan da yarintata ba zan ja abinda za'a min haƙoran ƙashi ba, dan nawan na asali zai sauke ƙasa."

Yusrah ta girgiza kai tana gyara kwancin ta dan idan suna magana irin haka basu sani bane haushi suke bata har ranta, wai wani amarya, ba amarya ba dai haihota aka yi, ita abinda ta sani shine ta je anguwarsu ta wuni ta dawo gidan Anna yanzu kuma zata yi barci, tana so garin Allah ya waye ta ƙara samun nutsuwa zuwa jibi ta yi tafiyarta wajen aikinta, shikenan ta manta komai sai fatan Allah ya kawo rabuwar abin nan da wuri ba tare da an ba kai wahala ba.

A hankali aka yi ta watsewa, ya yi sauran mutanen gidan kawai sai matar uncle Hamat dake zaune dan son ƙurewa ƙwal uwar daka, sai da kusan kowa ya watse sannan ta miƙe tana taunar cingan ɗin ta da yatsina sosai ta cewa Anna " Sister zan wuce, sai na je asibiti sannan in ƙarasa gida."

Anna ta yi murmushi ta miƙe tana ta yi mata godiya da fatan Allah ya ƙarawa uncle Hamat lafiya sannan ta ɗan taka mata daidai ƙofar ɗakin ta koma ciki, Tidin ta yi mata rakiya har kusan motarta suka tsaya suna fira kamar yadda suka saba kamar haka" Ki duba ki gani, yanzu ace Hamat na kwance ba lafiya amma matar Yaya ke hidima haka hankali kwance dan ba yaya bane ba lafiya babu abinda ya dameta ko?"

Tidin ta taɓe baki ta ce" Ke raba kanki da matar nan, ta wuce duk inda kike tunani, wannan ai kaɗan kika gani, babu abinda ba zata iya aikatawa ba, a duniya kanta kawai ta sani da kika ganta a nan, hidima ai kaɗan kika gani, ni da nake rayuwa da su ni nake ganin hidima, wuni suke suna sharafin gabansu, Akhi babba kaɗai ya damu da lafiyar ɗan uwansa, amma daga ita har ƴaƴanta babu wanda ya wani damu, su ai gani suke yi sun samu duniya sun yi hayewar da babu wanda ya kaisu a familly, kin ga kuwa dole su taka uban kowa, duba kiga hidimar nan da aka yi akan auren wannan banzar, zabin da aka yanka ko ni dake tsaye kan aikin su da ma'aikata ban san adadin su ba, gwara ma shanu na san jiya an yanka guda biyu, yau ma aka yanka biyu, ƙarshe ba burin ta ya cika ba tasa Yaya ya kashe kuɗi, naman kuma ta rabarwa talakawa da matsiyata."

Baki ta taɓe ita ma da takaici ta ce" A'a fa, su dai yi jira su gani ai dukiya kowa nada ita a jininsa, kwana kusa sai sun gaza gane wanene mijina wallahi, dan kuwa ni na san in taƙamar dukiyar ce a yanzu yana daf da kamo Akhi, wannan mention ɗin sai mun gina wanda ya ninka shi, lokaci dai, ni sai na ga dangin amaryar kamar rakaye, kamar ƙauyawa wallahi, ji fa wata shiga da suka yi mata, zamanin nan da ake shirya amarya ta sha kwalliya ta hau uban hlle shine suka saka mata silifas?"

"Ke ƴan ƙauyen ne ai, amma ina ga ba danginta bane, dan wallahi amaryar nan a luluɓe kika ganta kamar ƴar ƙauye, nan da kwana biyu in kika ganta kema sai kin rakata da ido, da wahala idan tana saka takalmi plate in ba a cikin gida ba, takalmanta duk masu ɗan tudu ne, ta iya saka kaya sosai kuma suna amsar jikinta ki ga kamar a jikin nata aka auna su dan a ga kyan su, ke dai ai ana wulaƙanci, ni fa ban san da auren nan a kan Aswan za'a ɗaura shi ba sai da na ji a gari." Tidin ta faɗa bayan ta ɗan ranƙwafa jikin motar.

Ido ta zaro tana kallonta ta ce" Kar ki rantse, wai Allah da gaske?"

Tidin ta amsata tana sake yatsine fuska, matar uncle Hamat ta shige motarta tana faɗin" Cabdijan, kin ga bari in je sai na biya na amshi odern abincinsa na tabbata yana can rai ɓace ban zo da wuri ba yau, ni kuwa da ta yi kirana ɗazu ta ce bata ganni ba a taron gidan nace dan na ga auren na baƙuwa ne, sai kawai take ce min ai auren fa ya koma kan Aswan idan na samu dama in an jima in zo mu amshi amarya shine fa ba shiri na garzayo dan in ganewa idona wani sabon salo, aure sai kace na munafurci ace auren mutum kamar Aswan da muke jiran ganin an fasa garin nan ranar auren dan auren ɗan gata ne auren da duk muke jira ne sai gashi an yi abin a rufe kamar tusar manya? Kin ga bari in je Allah ya kiyaye wannan lamarin gidan nan sai hamdala."

Tidin ta ɗan ja baya tana faɗin" Sai na shigo asibitin ki gaida min shi, ki faɗa masa dalilin da yasa ban zo ba yau, ai lamarin gidan mu sai mu ke dai zamu yi ta taka rawar daidai da kiɗan da uban kowa zai bamu!"

Baki ta taɓe bayan ta ja motarta a fili ta ce" Wai lamarin gidan su, ko ya zama gidan su a ina? Ai Aslama tana da ƙoƙari ma da take iya riƙe ƙatuwar mace irinki har da ƴar ki, ni ba ma zan taɓa yarda da haka ba wallahi sai dai ki kama haya in ba zaki je familly hause ɗin ku ki zauna ba ko ki kama ɗaki a hotel ki zauna."

Sai da ta biya restaurant ɗin da take ɗaukar abincinsa ta ɗauka ta wuce asibiti, da ta iso nurse ɗaya ta ɗauko kwalin abincin ta bita da shi suka nufi ɗakin da Uncle Hamat yake, da suka ƙarasa ɗakin sun same shi ya fito daga wanka ɗaure da tawul sai kace gidansa, domin jikinsa da sauki sosai likitocin dake kula da shi ne suka ce dole sai sun ga yadda jikin zai ƙara samun lafiya kafin a gama shirye shiryen fitarwa waje dan sun nuna dole fa sai an kai shi waje an ƙara cajin lafiyarsa an ɗora shi a maganin da ya dace kamar yadda binciken su ya basu.

Kallonta ya yi ya ɗauke kai, bai damu da ganin irin kwalliyar da ta ɗanɗasa ba da irin ƙamshin da take bazawa ba a irin wannan lokacin, bai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login