Showing 258001 words to 261000 words out of 397328 words
barci ya kwasheta, haka kuma da asubahi ya kuma ficewa ita dai bayan ta yi sallah ta yi tsaye aka kimtsa mata gidanta sosai sannan ta ɗanɗasa wanka ta yi hawa na mamaki ta zauna tana jiransa.
A lokacin da ya shigo sai da yanayin sa ya bata tausayi, rigar nan ta yadi tun jiya take jikinsa bawan Allah, kenan da ita ya kwana kuma da ita ya fita? Ƙwarai tana tausayawa wannan bawan Allahn kuma tana masa addu'ar Allah ya dube shi ya sanyaya masa abinda yake damunsa ko menene, tana kuma fatan ya cire damuwa kar ta kama masa zuciya, da fara'a sosai ta tarbe shi ta kawo masa kayan abincinsa na safe, shi kuwa a ɗarare yake kamar wanda yake gudun su yi wata magana.
Ganin ya ƙi ci ya sa ta buɗe masa tana kallonsa da kula sosai ta ce" Bab, ka ci mana, gida fa nake son zuwa su Anna na jirana."
Gabansa ya sake faɗuwa, dan tsoron sa ɗaya kar aje ita ma idan ta je su riƙe abinsu su ƙi bashi matarsa, gaba ɗaya da wannan firgicin ya kwana, balle idan ya tuna Akhi gabansa har faɗuwa yake yi, duk da irin halin da Bilal ke ciki shi ma yana yi yana tuna nasa damuwar ne, balle da Bilal ya sanar da Hajia wallahi idan ta yarda aka hana masa Yusrah zai bar mata ƙasar, kuma ta ce zata bashi wacce ta fi Yusrah wallahi ko ƴar waye sai ya fara kirta mata rashin mutunci sannan ya bar masu ƙasar, da ƙyar suka rarrashi Hajiar dake kuka wai ta shiga uku ƴan duniya sun ƙwace mata yaro an sa yau Bilal ke faɗa mata magana, shi dai bai baro can ba sai kusan ƙarfe biyu na dare, a yanzu burinsa ɗaya tak ne, ya samu ya bar ƙasar nan da matarsa, baya tunanin in zai dawo da zama, ya gwada zaman ya ga ba alkhairi sai tashin hankali, zai je nesa inda kafin a tarda shi an sha wahala, idan ka je baka isa ka jima ba zaka juyo, dukkan abin kyautata zai ninkawa mahaifiyarsa, abinda yake dole shine dolenta zai zo ya ganta a duk lokacin da ta buƙata ko shi ya buƙata, amma a yanzu yana ganin ƙwarai za'a haifar masa da d'an da ba ido.
Jiki a sanyaye yana kallonta ya ce" Wajen Anna kuma? Bab, ki bari mana sai jibi?"
Ido ta ɗan zaro tana kallonsa ta ce" Bab, gobe ne fa ɗaurin auren, yau zamu kaita can anguwarsu a can zata zauna da danginta sai an ɗaura sannan a kaita fa."
Hannayensa biyu ya saka ya dafe kansa, ƙirjinsa na bugawa, a sanyaye sosai ya ce" Intisar, dan Allah akwai wata magana mai mahimmanci da nake son sanar maki, ina fatan ba zaki ƙullaceni ko ki ji haushina ba, ki sani babu irin ƙoƙarin da ban yi ba dan in daidaita matsalar nan, wallahi har kuka na yi amma abin ya gagara, Intisar ban san ya ya zan yi ba, ina jin kunyar su Anna ina tausayawa Yusrah, sai dai abin ya fi ƙarfina, ban san inda zan kama ba ban san ya ya zan yi ba, Intisar ki yarda da ni ina son ki ina matuƙar son ki kar ki bari wannan abin ya raba mu, ki ba babban Yaya haƙuri ta waya kar ki yarda ya ganki dan nasan raba mu zai yi, Bab ki gane ba laifina bane ki..."
Idanuwanta a cikin nasa suke, tausayinsa da ƙaunarsa na fuzgarta, a hankali ta kama hannayensa a tausashe sosai ta ce" Calm dawn bab, ka kwantar da hankalin ka, kana ji, babu mai auren matar wani fa, duk tsiya macen da Allah ya yi taka ce kaine zaka auri abinka, wannan abin duk ya sa ka fita a hayyacinka? Ka dubi tufafin jikinka, jiya fa ban ji shigowar ka ba, bab ban san fitarka ba, please ko ɗan hug ban samu ba fa..." Ta ƙarashe tana ɗan kanne idanuwanta da alamun tsokana da kuma yanayi na son sai ya saki jikinsa.
Da] ar gaggawar maganar da ta same shi ya ce" Kina nufin, kin san Hajia ta hana aurensu da Bilal?"
Intisar ta gyaɗa kanta a hankali ta ce" Eh na sani, kuma jiya Anna ta ce tunda an gama maganar an dawo da dukiyar auren Aba ya mata miji."
Yanzun ma sake zuba mata ido ya yi da sauri yana kallonta cike da jin wani tashin hankali da kuma wata salama na taso masa a tare, a hankali ya ce" Aba ya mata wani mijin?"
Intisar dake zuba masa abinci ta gyaɗa kanta, Yaya Mubarack ya ce" Amma wanene?"
Aunty Intisar ta girgiza kanta tana miƙo masa ta ce" Ban sani ba bab, please ka ci ka yi wanka ka huta, bari in je in dawo ko?"
Yaya Mubarack da kansa ya karɓa yana sakar mata murmushi a hankali ya ce" Please, ki dawo ina jiran ki, idan kuwa Akhi ya ce kar ki dawo ki gyara mana ɗakin sai ni in koma can ɗin."
Dariya suka yi gaba ɗaya ta juya ta ficewarta da jakarta, shi kuwa ya koma ya zauna jikinsa a mace cike da tausayin Yusrah da Bilal, ya sani suna son junansu, yana fatan su yi haƙuri su karɓi ƙaddararsu, idan Bilal ya ji eh da gaske maganar aurensa fa ta koma kan wani ya ya zai ji? Ya Allah.
A nutse ta ƙarasa ɓangaren Hajia, ta same su Zahra'u sai aiki take yi saboda tunda sassafe Hajiar ta yi kiranta dan ta ce ba zata nemi Intisar ba ta tabbata ba ma za ta zo ba, su dukansu sun yi mamakin yanayin Intisar, sai fara'a take yi fuskarta a sake sosai ta sake gaishe da su sannan ta masu sallama.
Har zata fita Hajia dake ta shashan magani ta ce" Ke kuwa ina zuwa cikin shiri haka? Ko baki san an daina auren bane?"
Intisar ta juyo tana kallon Hajia, tabbas da ba dan an koya mata cewa babba fa babba ne, ko me ya yi kuma a girmama shi ya fi a wulaƙanta shi a gidansu ba, yau da Hajia ta ji maganar da bata san cewa ta iyata ba, wallahi da yau sai ta faɗawa Hajia maganar da sai ta suma ɗan tashin hankali, ba fa iya iskanci bane bata yi ba, ta zaɓi ta yi zaman kwanciyar hankali ko dan lafiyarta ne.
A tausashe bayan ta saki murmushi ta ce" Gida zan je Hajia, na sani, amma da Bilal ne aka fasa, in sha Allah gobe za'a ɗaura auren Yusrah."
Daga haka ta ficewarta ta tafi inda motarta take ta shige ta yi tafiyarta dan yau ba ma zata nemi mai tuƙata ba, Hajia kuwa ta jima baki saki tana kallon hanyar kafin ta gyaɗa kai tana ɗan wuwurga ido ta ce" Wai zuciya aka yi aka bata wani? To can dai ga su gada ko waye aka bata ba zai kai darajar Bilaluna ba."
Ita dai Zahra'u kamar ta taka rawa dan farin ciki domin Yusrah abar tausayi ce abar a duba ce, ko me aka faɗawa Hajia ya dace zuwa yanzu ta fara duban jikokinta mata in tunaninta maza ta haifa, kuma maza ma ai suna saka ka a uku, Allah dai shi kyauta!
Intisar ta samu kowa a shirye, ita kawai suke jira dan sun so tafiyar sassafe, dan haka tana zuwa suka kwasa suka tafi bayan Anna ta sake jaddada kar ta ga kalle kallen wayar nan, maza su nutsu su kula da kansu, dama yau za'a sakata a lalle suna zuwa danginta zasu sakata sannan a shiga yi musu ƙunshi, tuni suka cika motoci da kayan fitar bikinsu suka bar sauran a nan, gaba ɗayansu zasu tafi ban da Nabihat dake bin su da kallon mamaki da tunanin sun kuwa ga saƙonta? Iyayen su Bilal sun kuwa ga saƙonta? Sai dai bata da halin tambayar kowa, kuma ta ce ba zata bi su ba sai gobe ta je, wai bata jin daɗin jikinta, tana kallo suka shige motocin suka tafi, ita kuma ta juya ta yi ciki cike da tunanin abinda ya dace ta yi dan ta gano wai sun ga saƙon? Idan sun gani bayan sun ganin zasu bar ɗansu ya auri yarinyar da ta je gidan yari, ake tunanin ta taɓa auren wani ɗan tasha ne? Wai me yake faruwa ne? Damuwar nan ta kanainaye zuciyarta ta rasa sukuni, har ma ta kulle kanta a ɗaki ta shiga duniyar Tiktok dan ta samu mafita.
Cike da rakiyar ƴan uwanta, da iyayenta suka ƙarasa tsohuwar anguwarsu, wace tunda suka tunkaro iyaye da ƴan mata da samari suka fito dan tarbarta domin su zaman arziki suka yi da mahaifiyarta da mahaifinta, kuma tunda abin nan ya faru ba ranar banza da ba za'a saka mamatan a addu'a ba da baban a masallaci, haka kuma tunda uncle Sulaimane ya zo aka fara ginin nan ya zamo suma suna mararin jiran ranar da zasu aurar da Yusrah.
An zauna an ɗan taɓa kuka na tuna mamatan aka yi musu addu'o'i sannan aka shiga gabatar da tarin gudunmawar da ƴan anguwa suka tara, da wacce ƴan ƙauyen su suka zo da ita, ma sha Allah tari guda har da tarin abincin gara abin dai ba'a cewa komai, sai da aka gama gabatar da kayayyakin nan sannan aka zaunar da ita a tsakiya suka shafa mata lalle ana ta guɗa ana ɗauka a vidio da sauransu, da ita, da aunty Furera da su tagwaye da Abrar da aunty Intisar kuwa sun sha kuka na sakata a lalle, daga nan suka wuce ɗakin da aka ce nan ne nata, gaba ɗaya sanfarin ginin gidan tamkar ba gidan da ya rayu da ƴan ɗakuna sun duƙo ba, an yi gini na bulo da bulo, an yi tsari mai kyau da zamani, shi yasa a yanzu da suke ɗakin ta su biyar sun baje a babban bed ɗin ɗakin suna shan fira har mai ƙunshi ta zo ta gama haɗa kayan ƙunshinta wanda ta yiwu yau sai ta kwana a gidan saboda ita ce zata yi musu baki dayansu, idan ta yiwa amarya zata hau na sauran ƴan uwan amarya, aunty Intisar ta yi musu sallama ta koma saboda kiran da Anna ke ta afka mata na shirye shiryen wajensu, wanda a yanzu gidan amsar baƙi ne suke yi na gayyar mai gayya, Tidin kuwa Hajia Nabihat ana ɗaki ana shan barci.
Da yamma liƙis Maryam ta ƙaraso ita ma da shirin kwana, haka kuma Fatila bayan sallar isha'i Yaya Jafar ya kawota ita ma da shirin kwanan, ya zamo ƴan matan sun haɗu sai shan fira suke yi na ƴan mata idan an taru, suna fatan ganin gobe lafiya, gidan ya kacame sai girke girke ake yi, domin hatta Hajia mahaifiyar yaya Jafar a nan take ta ce suna inda Yusrah take.
*Bilal* kuwa yana gida cikin wani irin hali na rashin lafiya, domin tunda yamma ta yi jikinsa ya rikice ga kuka yana yiwa Hajia tamkar yaro ƙarami, tun Hajia na faɗa tana faɗin a kan mace zai sakata gaba da kuka? Har hankalinta ya fara mummunar tashi a lokacin da Imran ke faɗa mata ai yanzu an daina yayin hana mutun auren zaɓinsa, barinsa ake yi in ya auro in ba'a so sai a raba su a hankali, gaba ɗaya dai ya tsorata ta da lamarin Bilal har ya zamo ta rasa tsaye ta rasa zaune, gashi yau kwana huɗu kenan rabonta da Hauwa, bata da labarinta, ta yi kiran ta yi whatsup ɗin shiru, ba ita ba mijin nata, wannan lamari ma na damunta ga damuwar maganar auren, yau dai da ace ta sameta da sai ta ƙara mata ƙwarin guiwa, sai dai kashhh bata da labarinta gashi damuwa na neman rikita mata lissafi.
Yaya Mubarak ne ya kai shi asibiti a lokacin da yake ta kukan a kai shi wajen Yusrah, Hajia na gefensa bayan an jona masa ƙarin ruwa gaba ɗaya zuciyarta a wasi wasi, ta yanke wannan ta yanke wancen, ƙarshe dai ta gama ayyana _'In sha Allah gobe zata je wajen Aba kawai a ɗaura auren, idan yaso a hankali zata yakice masa son yarinyar a rai, gaba ɗaya sai ta tashin masa tsaye ta karya abinda yarinyar ta masa dan ta kula yarinyar bata shige shi da wasa ba, idan yaso ba zata taɓa bari su tare ba balle wani abu ya haɗa su, dan ita a yanzu bata yarda da lafiyar yarinyar ba ma, ba zata bari ta kashe mata Auta ba.'_ Ɗayan abin da ya tsaye mata a rai shine maganar da Intisar da ta ce wai akwai aure sai dai ba da Bilal ba, ta yiwu kawai dan a nuna mata akwai maganar aure ne bayan babu, ko da yake koma meye zata ji goben in sha Allah, yanzu ta ɗan ta take idan ya nutsu ta yi yaƙi da Yusrah.
Yaya Mubarak kam tausayin ƙanin sa ya gama mamaye zuciyarsa, balle ɗazu da ya maida Bab gida dan a can zata kwana ta kawo masa katin ɗaurin auren da ya duba ya ga sunnan sai da jikinsa ya kwashi rawa, kuma ta nuna masa ita ma a lokacin ta gani, ta bashi ne bisa umarnin Anna, da ƙyar ya iya maido kansa gida cike da tunani, kuma yana zuwa ya tarar da halin da Bilal ke ciki dole ya ajiye komai suka rungume shi, a yanzu kam ya san ko shi idan zai yiwa Yusrah magana sai ya girmamata balle Bilal, ya kuma sadaukar dan ya san hanyar jirgi daban da ta mota.
...*BABBAR RANA*...
A cikin mota yake yana hangen ƙofar gidan da ta shaƙe da jama'a, tarin al'ummar ta bashi mamaki sosai, irin yadda Aba ke cikin babbar riga yana saukar baƙi ya fi bashi mamaki, ya rasa ya ya aka yi suka shawo kan angon da aka ce ya fasa auren, shi dai a jiya har ƙarfe ukun dare ta yi Chef ya sanar masa a yau ƙarfe bakwai ta masa a gidan Aba kuma ya saka tufafin da ya tanada na ɗaurin auren dan akwai maganar ɗaurin aure.
Arif yake kallo da ya nufo motar da yake, dan haka ya ɗan zuba masa ido da mamakin shi kuwa fa? Me ya kawo shi ɗaurin auren taɓaɓɓiya? A lokacin Arif ya buɗe motar ya shiga kansa tsaye yana lumshe ido da faɗin" Kan ubancan, ashe sanyi ka ke sha babba, fito mana za'a ɗaura fa."
Haka kawai ya ji gabansa ya buga har wani abu na son cure masa a cikin cikinsa, amma kuma ya rasa ko menene, ɗayan gefen da aka buɗe ya saka shi waigawa, da mamaki ya kalli Muktar ya ce" You? Guys me kuke yi a nan ne ? Wa ya gayyace ku?"
Muktar ya shiga shi ma yana faɗin" Aba ya gayyace mu, ku fito mu ƙarasa fa."
AA ya ɗan yi tsuru kafin ya ce" In ba abin sheɗan ba, sai tsoro ya kamani kar aje Aba ya yiwa ƴar mutane kishiya, na kula sosai ya damu da lamarin wancan haka-haka ɗin."
Muktar ya zaro ido yana kallonsa, Arif ya ce" Kana nufin Anna ce wai ƴar mutanen?"
AA ya gyaɗa kai yana rafka tagumi, shi kam bai san ya ya zai yi da ransa ba, yau kwana biyu basu yi magana da Aba ba, kuma gasu nan a gaban ɗaurin auren nan, malun malun ɗin Aba da ta chef sun tsorata shi ainun, Allah ya Allah ka sa ba ɗaya bane zai auri yarinyar can ta rikita masa tsufa, gaba ɗaya duk wanda ya yarda ya aureta a cikinsu kwana kusa zata saka shi zantuttukan shiruftaka, to wa Y.turaki ke tsoro a duniyar nan? Tsaf zata sa a rufe shi saboda zata iya taɓa masa lafiyar iyaye, in ba ƙaniya irin ta Y.TURAKI ba ta tsallaka ta auri uban mutum? La'ilaha illalah!
Rasa abin faɗa ya saka su fita suka bashi damar fitowa bayan sun tsaya suna kallon juna kafin su cira kai cike da takaicin AA dake neman kashe su.
*A* cikin gida kuwa a irin wannan lokacin da ake karamar ɗaura aure Goggo Hinda na zaune da Safiya suna kallon abin mamaki har da Khadija da ta saje cikin masu aiki tana ta kai kawo, suna dai zaune da jiran jin wai wace waina ce wannan ake son toyawa ta rashin mutunci? Waye wai za'a aurawa Yusrah? Bayan Goggo tana da tabbacin ba wannan zancen? Wa ye ne? Ta yiwu Sulaimane dan wata jaraba ya sama mata wani mijin, ko da yake ta tabbata ba zai taɓa kamo Bilal a dukiya ba, Bilal kuwa tana nan tana shirya ƴar ta dan kuwa sai ta shiryata tsaf zata turata dan ta je ta haukata shi ya kamu da sonta kamar zai mutu ya zamo an aura masa ita ta yi wuff da shi, a nan Hajia zata gane shayi ruwa ne dan kuwa idan taƙamarta saummako ita a hanya ta kwana, sai ganin Bilal ya gagareta da idanuwanta wallahi.
Uncle Sulaimane ne ya sake fita da sauri bayan ya je ya ga aunty Furera kan ta je kusa da Yusrah ta jata ɗaki ta sanar mata gafa da wanda za'a ɗaura mata aure dan baya so ko da wasa a samu wani abin faɗin, takatsantsan yake yi da kowa a zaman nan, idan taƙamar wanda ya yaɗa maganar nan shi ɗan duniya ne yau zai ga duniyanci dan tsaf ya gama ɗaukan akwatunan da aka jibgo da dukiya uwa uba zai ɗauki ɗaurin auren zai kai Tiktok ɗin, yana nan yana bincikar wanda ya yaɗa wancen vidion, zasu kafta wasan yadda ya dace, Yusrah ma ƴar gata ce wallahi babu wanda zai ci mata zarafi ya ƙyale shi.
Amon mai faɗa ta amsa kuwa ne ya fara sanarwar a saurara za'a gabatar da ɗaurin aure hakan ya sa da sauri Goggo ta yi shiru tana sauraro haɗi da turo baki gaba ba tare da ta gane ta yi haka ɗin ba, cikin lokaci ƙanƙani kunnayenta suke jiyo mata sanarwar za'a ɗaura aure, dan haka ta yi kiskirim tana sauraro bata motsin kirki dan burinta ta ji wai me yake