Showing 27001 words to 30000 words out of 397328 words

Chapter 10 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70003

wata."

Ɗan saurarawa ya yi da maganar, a nutse ya sake bin mahaifinsa da kallo, lokaci ɗaya kuma mahaifiyarsa ta zuba masa ido itama, a zuciyarta tana tunanin tabbas akwai abinda yake faruwa wanda ya sa ya kasa barin maganar nan, domin ya yi maganar nan a shashance, ya yi a gaggauce, yanzu kuma ya zaunar da su? To kuwa ƙwarai zata dube shi ta saurare shi, Humed kam a ransa ayyannawa yake yi an zo wajen, inda gwagwonsu ta yi wani tsittttt cike da mamakin me kuma yake nufi shi uban iya yin nan?

Da kula sosai Dad ya ce" Ina jinka AA."

A nutse ya ɗora da faɗin" Ba zan so ace a cikin ɗan ƙanƙanin lokacin da zamu yi a cikin hurumin gwamnati mu kwashi baban kason da zamu je ƙiyama ya fi ƙarfin kanmu, a zamantakewa ta yau da gobema ana wayar gari da rikicin da idan aka je gaban Ubangiji da shi sai ceton fiyayyan halitta Sallallahu alaihi Wa sallam, ina ga haƙƙin talakawa? Na duba na kuma dubawa ban ga aikin da ɗayanmu ke yi ake bashi albashi har haka ba, ya zamo dan kawai muna cikin layin manya sai mu kwashi abinda ya fi ƙarfinmu?"

"Son, amma ai haka tsarin yake, ba nine na yanke a ringa yin hakan ba fa, and ba iya famillyna bane kawai ake fitarwa." Mahaifinsa ya faɗa da kula sosai yana kallonsa.

A tausashensa ya ce" Aba, idan har za'a saka kowane bawa a kabarinsa shi ɗaya tak, sannan in har bawa ya yi imani zai tsaya gaban Ubangijinsa ya yi masa bayanin dukkan abinda ya samu da yadda aka yi ya samu, me ya yi da shi? To kuwa za'a ringa sara ana duban bakin gatari, Please Dad ka dakatar da wannan abun wa ahalinmu."

Da mamaki sosai Goggonsu ta dubi Yayanta, ta sake kallon AA, gaba ɗaya ta ji ba zata iya yin shiru ba, domin wannan ai hurumi ne ya shiga da ba nasa ba, wani irin a dakatar da albashin da duk ƙaryarta shi ne? Albashin nan duk wata facakarta da shi take yi, ina! Inama zai yiwu ya fito mata da wannan abin, ta buɗi baki ta ce" Akhee, wace magana ce wannan yake yi kuma kana wani binsa ta laluma bayan ba wani haramun da muke ci a nan? In ba abinka ba Aswan ai ba wani haramun muke ci ba, kuma in kai kana da hanyoyin samun kuɗinka ai baka san wani ba, kai kana iya daina amsa amma mu ka bar mana abinmu, dan gaskiya ni dai ina so kuma ba zaka hanna a bani ba tunda ba komai zan zira maka ido ko hannu in yi jira ka min ba."

Tunda take yin maganar shi dai uffan bai ce ba, amma kuma yana kallonta, har sai da mahaifinsa ya yi mata alamun ta yi shiru hakanan sannan ta yi shirun tana ɗan girgiza ƙafarta alamun bata gama faɗin abinda ke ranta ba.

Kai Anna ta soke ƙasa, ita kaɗai ta afka tunani... Ya salam, yanzu idan wannan abun ya zame masu masifa gobe ƙiyama fa? 'Eh lalle da sun yi aikin banza a kan ɗan abun nan na ɗan lokaci su kai kansu wuta.'

Shine abinda take ta ayyanawa a zuciyarta har muryar AA ta saka ta ɗaga da sauri domin kuwa tar da tar ya dubi Goggonsa ya ce "Lalle kuwa, da tun a duniya zan bibiyeki kafin ki je inda mai cdn zai tsayar da ke a kan hakan! Kuma aikin da kike yi fa da ake biya duk wata?"

Sai kuma ya risinar da dubansa dan ya tabbata gaba ɗaya an zaro ido ana kallonsa ne, a tausashe ya ɗan rage buɗewar hannayensa ya ce" Ina fata za'a duba maganar Dad, na barku lafiya."

Daga nan ya miƙe ya juya a nutse ya ficewarsa a ɗakin ya barsu baki buɗe, ba ma kamar Dad da hankalinsa ya so tashi ya shiga tunanin to ko dai yaron nan bai bar aikin sojan nan na fitina ba? Ta ya yasan hakan? Bayan shi dai iya mahaifiyar su ne kaɗai tasan daga ina kuɗin ke shigowa sahihanin zance, sai kuma ƙannensa da suma yana tura musu saboda kar su ce an ware su.

Daga nan asibiti ya nufa, a ƙofar asibitin ya aje motar sa ya ƙaraso wurin mai gadi, duk da ba zuwa yake ba idan babu dalili mai ƙarfi, amma dai ya san ko wanene Aswan, dan haka ya tarbe shi da girmamawa suka gaisa, gyara tsayuwar shi ya yi daga nan yana kallon mai gadin yace "Malami, kai ne a bakin aiki kwana huɗu da suka wuce?"

Jinjina kai ya yi yace "E yallaɓai, ni ne kasancewar kwana bibbiyu ne muke yi ni da abokin aikina."

Gyaɗa kai AA ya yi irin yawwa ɗin nan sannan yace "A ranar da dare, za ka iya tuna motar ujila nawa ce ta fita daga asibitin nan ko kuma ta shigo?"

Shiru ya ɗan yi yana nazari kafin daga bisani yace "E to yallaɓai, gaskiya da dare dai ambulance biyu ta fita, ɗaya ana sallah isha'i ta fito ta dawo da majinyaci da suka yi haɗari, sai ɗayar kuma cikin dare sosai, dan ina gyangyaɗi ma ta yi oda na buɗe musu ƙofa suka fita."

Jinjina kai AA ya yi yace "Ok, kuma wa ye yake tuƙa motar da ta fita tsakiyar dare?"

Ba tare da wani ɗar ba ya bashi amsa da " *Mani* ne yallaɓai."

Jiinjina kai ya sake yi tare da bashi hannu suka gaisa yace "Nagode sosai, zan tafi, sai anjima."

Da gayya ya nuna masa zai tafi, sai kuma ya ɗan dakata yace "Ko Manin ya na ciki ne?"

Da sauri ya amsa mishi da "E yallaɓai, dukansu ma zaka same su acan sashin su dake kusa da sashen tsananta kula."

Sai kawai ya shiga ciki gadan gadan, hakan ya sa ba kowa ya san Aswan Aliyu Anza ya shigo asibitin ba, kai tsaye kuma can ɓangaren da zai samu Mani ya nufa kan shi tsaye.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍??🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*9*




Cikin wata ƙatuwar rumfa ya samu drebobin har da dreban Dr. Hamat, sallama ya musu duk suka gaisa, kafin ya tambaye su "Dan Allah Mani fa?"

Manin da kan shi ne ya amsa yana mai ƙarewa AA kallo, murɗaɗɗen jikin shi dake ɓoye cikin manyan kaya, shigar shi da fatar shi duk sun nuna ba ƙaramin mutum bane, kuma shi dai bai da wani laifi da yake aikatawa ko ya aikata da zai ji tsoron bayyana kan shi, dan haka ma ya miƙe ɗin suka keɓe kamar yadda AA ɗin ya buƙata.

Ba ya son jan magana, dan haka kawai ya je ga gundarin magana ta hanyar faɗin "Malam Mani, kwana huɗu da suka wuce an tabbatar min kai ka ja motar ujila da aka fita da ita da dare daga asibitin nan, shine nake so naji me ye a cikin motar? Kuma ina ka kai abun cikin ta?"

Duk da bai san komai ba, amma yadda ya tambaye shi ɗin sai gaban shi ya shiga faɗuwa, a daddafe yace" Yallaɓai ban san komai ba, ban san me ye a cikin motar ba nima."

Ɗan duƙar da kai AA ya yi, a sakanni kuma ya ɗago fuskar shi a kausashe ya kalli Mani da yanayin da babu wasa ko fara'a a ciki yace" Kar ka min ƙarya Mani, hakan zai hassalani gaskiya, ka faɗa min me ka ɗauka kuma ina ka kai abinda ka ɗauka? Masaniya gareni mai ƙarfi shiyasa har na zo nan."

Cike da tabbaci Mani yace" Wallahi yallaɓai ban san ko menene a ciki ba, abinda zan iya cewa kawai bayan ma an kusa gama loda kwalayen ne aka tadoni dan har na fara bacci, ina zuwa makullin motar aka ban aka faɗa min asibitin da zan kaita, iya abinda na sani kenan."

Wani kallo ya masa kamar harare yace" Su wa suka ɗora kayan a wannan lokacin?"

Da inda inda yace" E to, biyun dai ba ma ma'aikata bane a asibitin nan, sai kuma dreban oga (kawu Hamat)."

Da mamaki AA ya dube shi yace" Ba ma'aikata bane? Su waye kenan?"

A hankali Mani yace" Gaskiya ba ma'aikata bane, sai dai lokaci lokaci sukan zo nan wajen oga, musamman ma ranar juma, kusan duk juma'a ma tare da su muke zaman nan, jefi-jefi yakan kira ɗaya daga cikin su ya aika."

Hannu AA yasa yana murza goshin shi tare da jinjina kai a ranshi yana ayyana" Dreban oga? Sani kenan?"

A ɗan dubarance ya karkata dan ya kalli Sanin, amma ikon Allah sai ya kama shi yana kallon su irin kallon ƙurilla na son gano ko jin me ake tattaunawa, bai yarda ya ƙarasa juyawar ba kawai ya basar yana wani irin shegen murmushin gefen laɓɓa.

Cikin tsareshi da idanun da da yasan yadda yake ji da yake masa kallon nan yace" Me ye a cikin kwalayen?"

Girgiza kai ya yi da rashin tabbaci yace" Gaskiya yallaɓai ban sani ba, amma dai bana raba ɗayan biyu cewa kwalayen magunguna ne."

Taɓe baki AA ya yi yana kawar da dubansa gare shi yace" Dama kuma ka saba ɗaukar magunguna zuwa wasu asibitocin?"

Jinjina kai ya yi yace" E akan yi hakan, tunda idan aka yi odar kayan aiki ko magunguna muna zuwa mu ɗauko, wani lokacin kuma Pharmacie asibitin nan takan siyarwa da wasu asibitocin kaya, saboda ko shakka babu asibitin nan ita ce ta farko wajen ajiye kayan aiki da magani."

Wani shaƙiyin kallo AA ya mishi yana ɗaga gira sama yace" Wace asibiti ka kai motar?"

Ba tare da shakku ba yace" Asibitin koyarwa ta Alhaji Saddi Ja."

Cikin jinjina kai AA ya ɗan shiga juyawa yana ambatar" Saddi Ja?" Abokin mahaifin shi ne, to me kenan hakan yake nufi? Mota cike da kuɗi, an kaita asibitin abokin mahaifin shi? Ya salam! Ƙwarai wani lokacin ya kan ji kamar ya dakatar da abinda ya fara, saboda idan ya ji wani sai ya dinga jin abu kamar tsoron inda binciken nan zai kai shi, sai kuma ya ƙwarara kan shi tare da ba wa kanshi ƙarfin guiwar ci gaba.

Kallonshi ya yi yace "To amma da ka kai motar ba gaban ka aka sauke kayan ba? Sannan ka juyo da motar?"

Da tsanaki Mani yace "Abun ma da ya ɗan ban mamaki kenan, dan oga cewa ya yi na kai motar na baro acan da safe za'a ɗauko, abinda bai taɓa faruwa ba kuma sai a ranar."

Shiru AA ya yi yana nazarin abinda Mani ya faɗa masa, kafin daga bisani ya mishi sallama tare da godiya ya fice a asibitin ba tare da kawun shi ya san ya zo ba, Sani kuma zai dawo kan shi, amma yadda ya ga yana kallon su yasan ya fahimci wani abun ne, dan haka ba yanzu zai ritsa shi ba, sai lokacin da yake bille-billen neman tsere masa, sai ya take wutsiyar sa ya hana guduwa, duk wanda suka ganshi ba su san wanene shi ba idan ba dreban kawu Hamat ba, hakan ma ya sa AA na fita ya miƙe da sauri daga shayin da suke zugawa zasu sha yace yana zuwa.

Bai zame ko ina ba sai ofoshin Dr. Hamat, kai tsaye ya shiga duk da babu mai yi masa wannan shigar ƙawarar, amma ko da ya ga Sani ne yasan akwai abinda ya zo mishi da shi, hakan yasa ranshi bai ɓace ba sai ma gyara zama da ya yi yace "Sani, me ya faru ka shigo min haka?"

Ba tare da ya zauna ba dan bai da wannan hurumin yace "Oga, akwai matsala fa."

Da sauri ya ɗora hannayen shi kan makeken table ɗin shi cikin harshen Sanin wato zabarmanci yace "Wace irin matsala kuma?"

Shi ma a harshen nashi da ya fi iyawa yace "Oga, Chairman na gani fa a asibitin nan, kula yana magana da Mani dreba."

Da ɗumbin mamaki kawu Hamat yace "Akan me suka tattauna?"

Girgiza kai ya yi yace "Ban sani ba yallaɓai, sai dai hirar su ta ɗauki a ƙalla minti ɗaya ko biyu, ina tsoro fa oga."

Da jin haushi kawu Hamat yace "Tsoron me? Kawai daga ganin su suna tattaunawa sai ka ce kana jin tsoro?"

Da wata irin gurguwar hausa Sani yace "Oga, kasan chairman rigimammen soja ne, ina tsoron shi fa gaskiya, ba ya da kirki ko kaɗan idan aka shiga harkan shi."

Da wani malalacin kallo kawu Hamat ɗin yace "Ka shiga harkan tashi ne kai?"

Girgiza kai ya yi alamar a'a, dan haka kawu Hamat ya gyara zamanshi cikin lumtsumemiyar kujerar shi yace "Je ka kawai, ka rage tsoron nan kar kasa ma ya zarge ka."

Jinjina kai ya yi yace "Shikenan oga." Jiki a sanyaye ya fita a ofishin sam bai ji nutsuwa ta saukar masa ba, saida ya tabbatar ya rufe masa ofishin sannan ya ƙara ɗagowa daga kujerar da mugun sauri yana rarako idanu yace "Aswan a asibitin nan? Kuma tare da Mani dreba?"

Babu zufa a goshin shi, amma saida ya kai hannu saman goshin ya shafa sannan ya ɗauki wayar tangaraho da niyyar kira ya ce a turo masa Mani yanzu yanzu...

*Amma* shigowar Yusrah ta dakatar da shi daga hakan wacce ta ƙwanƙwasa tare da yin sallama, a ƙage da jin an takura masa yace "Wa ye? Shigo?"

A nutse ta murɗa abin buɗewar ta shiga kanta tsaye, a tausashe ta furta" Barka da warhaka Docter."

Wayar da ya taɓa ba ajiyewa ya yi ba dan kuwa ya zama wajibi ya ga Mani direba, hakan ya sa da ɗan yanayin gaggawa ya amsa ta da yawwa.

Da kula ta ce" Dama wata mai naƙuda ce aka kawo, cikin ikon Allah har ta haihu shine nace bari in shigo in sanar maka."

Sai da ya ɗan yi tsam dan ya gane me take nufi, sannan ya ƙanƙance idanuwansa kamar dai bai gane ɗin ba yace" Me kike nufi?"

Yusrah ta ce " Eh da ta zo ne muka amshi haihuwar har ta haihu shine na shigo in sanar maka dan a yi dukkan abinda ya yi saura."

Da mugun ɓacin rai ya ce" Kika amshi haihuwar dai! Ke kina da hankali kuwa? Ko me kike taƙama da shi? A kan wani dalili zaki amshi haihuwa a asibitina kai tsaye ba tare da an sanar min ba? Wannan wani irin hauka ne? Ke a wa? Wacece ke? Daga ke har kwalin da kika mallaka na zama likitar banza ne a wajena, saboda wani dalili zaki take min doka?"

A ɗan tsorace da yanayinsa ta ja baya kaɗan dan kamar zai shaƙota haka yake masifantarta, murya a sanyaye sosai dan kare kanta ta ce" Ka yi haƙuri Docter ba take dokar ka na yi ba, da aka kawota tuni kai ya bado shi yasa kawai na shige da ita ɗakin haihuwar."

"ki min shiru, ki min shiru nace, ko da ace ɗan na yawo a ƙasa aka zo asibitin nan kar ki kuma min haka, kin fahimta?"
ya katseta rai ɓace, kai ta sadda jiki a sanyaye ta ce" Ka yi haƙuri in sha Allah ba za'a kuma ba."

Rai ɓace ya koreta, ta juya ta fita a sanyaye
tana tafiya daidai da nufowar wata kyakyawar matashiya da za ta girmi Yusrah a ƙalla da shekaru huɗu ko biyar ma, fara tas da ita cikin lafaya mai kyau da tsada, tare take da Bilal dukkansu bakunan su a washe saboda farin cikin haihuwar Zahra'u.

Tunda suka tunkarota Bilal ke kallonta yana ma matashiyar raɗa da cewa " *Aunty Intisar*, kinga likitar nan? Dan Allah bata dace dani ba? Dan Allah ki mata magana ki ji nutsuwa, wallahi yarinyar ta haɗu."

Kallon shi tayi da murmushi tace "Uhumm?"

Gyaɗa kai ya yi yace "Allah da gaske nake, ki yi wani abu auntyna."

Ƙarasowar su da sukayi ya sa Intisar kallon Yusrah dake jiki sanyaye kamar za ta yi kuka ita tun kallo ɗaya da ta musu ba ta sake ba tace "Sannu sister?"

Da sauri Yusrah ta kalle ta, da ƙyar ta ƙaƙaro murmushi tace "Yawwa, sannun ku?"

Bilal dake ta kallonta da fara'a ya amsa da "Yawwa likita, ya aikin?"

Kafin ta ce wani abu Intisar tace "Sister Docter yana ciki ne?"

Jinjina kai tayi tace "E yana ciki."

Murmushi Intisar tayi da ya sake bayyana kyawunta tace "Nagode."

Kallon Bilal tayi ta masa alama da suje, tuni Yusrah ta raɓasu ta wuce sai Bilal da ya bita da kallo sannan ya kalli Intisar yace "Aunty ya haka kuma? Sai ki barta ta tafi baki faɗa mata ba?"

Ɗan hararan shi tayi tace "Kuma haka ake yi aka gaya maka? Kai tsaye sai na ce mata kana son ta? Ka kwantar da hankalin ka, a asibitin nan muka ganta, zan samo maka bayanan ta har na gidan su ma."

Tana ƙwanƙwasa ofishin saida ya ja dogon tsaki saboda ya aika kira ne kenan an ɗaga aka sake katse sa, aje wayar ya yi yace" Shigo?"

Ganin Intisar da Bilal a bayan ta yasa shi dole ya ƙirƙiro murmushi a fuskar shi yana gyara zaman shi da faɗin" Lalala! My lovely


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login