Showing 240001 words to 243000 words out of 397328 words

Chapter 81 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70097

sanyo mata da kuɗi dan ni ban yarda da ajiyar kuɗi a banki ba, kuma kin ga bana kunyar ace an kawo kuɗin auren ƴaƴana kaza, ko jaka goma ce Allah ya sanya mata albarka, abinda nake tunani ɗaya ne wanda zai iya zamowa damuwa a tsakanina da sarakuwarki idan ta takura yarinyar nan, Intisar tabbas zan ajiye ƙafa a gidanku saboda yarinyar nan, kuma idan har abinda na gani bai min ba ba zan iya kawar da kaina a cuci marainiya ba, ki yi kwanciyarki in tana so karma a kawo kuɗin mu zamu musu sha tara ta arziki, Allah ya bamu lafiya."

Daga nan suka yi sallama, Anna ta miƙe ta je ta samu aunty Furera dake nafila a ɗakin da aka sauketa, ƴarta na barci ta zauna ta yi jiranta har ta gama suka yi maganar, Aunty Furera ta ce" Aunty, kuɗin nan ya yi sosai fa, caɓdijan to ai idan tana tunanin saboda wannan ran wani zai ɓace gaskiya ta canza shawara, dama Hajiar nan na kula kamar tana da tsamin rai sosai, Allah dai ya sanyaya mata." Anna ta amsa da amen, suka ƙara tattaunawa sannan ta komawarta ta nufi ɓangaren Aba, shi maganar ma bata yi masa ba, dan ta sani ko da ta masa cewa zai yi me ye a ciki Allah ya saka masu albarka.


*WASHE GARI*

Washe garin ranar aka kawo lefen da kuɗin sadakin, hakanan ɗin kuwa aka kawo, a wajen mazan a babban falon Aba aka amshi sadakin, da Aba ya amsa ya saka albarka ya miƙawa uncle Sulaimane shi ma ya amsa ya saka albarka ya miƙawa AA.

Kuɗin AA ya duba a hannunsa ya dubi Yaya Mubarak wanda ya sadda kai, sai kuma ya dubi Aba ƙasa ƙasa sosai yace" Amma Aba kamar jaka hamsin?"

Aba ya masa shiru bayan ya masa kallon kar in ji ka ce komai, sannan aka yi addu'a aka watse bayan an sake tabbatar da ranar ɗaurin auren nan da sati biyu, kuɗin ya fitar ya jera a gabansa, e wallahi mai aku ce ƙwaya biyar sai uban goro a jibge gayacen wanda ya tabbata da ace cin goro suke kuma zai ajiyu wannan har su mutu ba zasu rasa na ci ba.

Kai ya ɗago ya dubi Aba dake tattaunawa da Uncle Sulaimane sai ya kawar da kai, dama bashi da lafiya tun shekaran jiya, gashi wannan abin zai ƙara masa ciwon kai, yanzu shine aka mayarwa da kura aniyarta aka kawo jaka hamsin kuɗin auren haka? Yanzu fisabililahi yarinyar nan ai ta fi ƙarfin kuɗin nan, in ba ƙaniya ba irin ta Mubarak da uwarsa shi zasu kawowa kuɗin auren yarinyar gidan su nan jaka hamsin? Lallai, ƙwarai abin ya masa ciwo ya ga an ma raina masa wayo, amma kuma wanda zai taya shi a watsa auren ya ƙi bada haɗin kai sai kawai ya haɗe kuɗin ya tusa a aljihunsa ya miƙe yana sake cin magani ya kalli Aba ya ce" Sai da safe."

Aba ya kalle shi ya sake duban yanayinsa ya ce" Ina kuɗin to?"

AA ya dubi Aba ya ce" Suna wajena, ai iyaye ke riƙe kuɗin kafin su ba ƴaƴansu ba kakaniba, ko bros Sul?"

Uncle Sulaimane ya yi dariya yana faɗin" Ƙwarai kuwa boss, ka adana kuɗi kawai in an ɗaura sai ka bata ka mata nasiha."

Bakin uncle Sulaimane da ya ce in an ɗaura ya ɗan kalla sai kuma ya yi gaba ya fito, yana saukowa falo ya tarda wani sabon rashin mutuncin, ya rasa yaushe ƴaƴan Anna suka zama ƴan buru'uba wallahi? In ba ƙaniya ba su rasa abinda zasu yi sai kunna kiɗa a falon nan suna ɗauke ɗauken vidio da hotunna ko? Har da Intisar dan wata ƙaniyar.

Wajen abin kiɗan ya je ya kashe sannan ya juyo fuska a haɗe ya ce" Ke Intisar me kike yi a nan har yanzu?"

Aunty Intisar ta miƙe da sauri tana faɗin "Akhi, Yaya Mubarak ne ya ce zai zo ya ɗauke ni idan an jima."

Kai ya ɗauke ya ce" Dallal wuce gidanki, kai ku kuwa ku wuce min ɗakunanku."

Kusan rige rige suke dan su tafi sama, Yusrah na kallon su da shi baki ɗaya kafin ta ɗauko hijabinta dake gefe ta juyo zata saka dan ta tafin ita ma kamar yadda ya bada umarni, ya ƙare mata kallo mai kama da harara ya ɗauke kai ya zo ya wuce ta kusanta ƙasa ƙasa ya ce" Kin ji kunya ke kam!"

Yusrah ta ɗago ta zubawa bayansa ido har ya ɓacewa ganinta kafin ta zauna ta rafka tagumi haka kawai ta shiga wani yanayi na daban da tunanin me kuma ta yi masa? Me kuma aka yi ne? Ya salam, kiran da Bilal ke ta yi ne dan yana so wai ya zo ya ga Aba ta ɗauka dan dole, domin tun jiya suke kwasa da shi kan maganar kayan da kuɗin, ta nuna masa ko ya ƙaro ba zata amsa ba abinda mahaifiyarsa ta yanke ya yi sun isa ta yi kayan aure da su sosai da sosai dan haka kar ya wani damu, a dole ta miƙe ta nufi ɗakin ta dan ta kwantar masa da hankali domin bata ga abin damuwa a nan ba, kuma yadda su Anna da aunty Furera suka nuna mata ta nuna masa ba wani abu kuma ba za'a amshi ƙari ba zata nuna masa, shi ma ya cika rigima a muryarsa har kamar yana kuka fa.

Shi ma kuma yana tafiya motarsa ya shige ya ɗauki hanyar gidansa dake wajen gari a tsohon daren nan in da su Mani dreba suke, sai dai ba zai ma waiwayi inda suke ba dan hutu yake buƙata, haka kawai yake ji rashin lafiyarsa ba zata barshi ya je gida ya samu damuwar su Meem ba, kuma ba zai je asibiti ba, yana so ya ɗan kaɗaice kansa ke ciwo sosai, kuma komai haushi yake bashi.

Yana zuwa ya ciro kuɗa&en nan ya ajiye su gaban madubi ya ƙare masu kallo kafin ya yi murmushi ya tuɓe ya nufi bayi.


*WANNAN KENAN*


A yanzu kam za ta iya cewa bata da matsalar komai, damuwar ta ɗaya dama Safwan ne, kuma Alhamdulillah Safwan na samun sauƙi ko wajen motsa masa jikin sa kullum ci gaba ake gani, wanda hakan ke tabbatar mata wataƙila ma ranar ɗaurin auren ta ya nemi takawa dan farin ciki, ita da Goggo ko a waya bata kiran ta su gaisa, ba wai dan tana hushi ko ta riƙeta ba, sai dai a ganin ga ba zata samu gaisuwa ma mai daɗi ba, musamman da ta ga kamar da gaske baƙin ciki take mata da za ta auri Bilal, sai lamarin na Goggo ya sake ɗaure mata kai matuƙa. Amma bayan Goggo kowa suna gaisawa ta waya, in ma kira kai tsaye in ma ta WhatsApp, dan yanzu haka su aunty Fureira a waya ta samu labarin irin dandazon d zasuyi su zo dan bikin ta, dan yadda aunty Fureira ta dinga lissafa mata da wa ne da wace sai da abun ya bata mamaki, kuma sun ce za su zo ne kwana uku kafin bikin zasu sauka gidan su da ya rushe wanda kawu Suleiman ya ɗauko gyaran gidan, amma da Aba ya ji ya kuma tabbatar gidan mahaifin su Yusrah ne, sai ya saka hannu a gyaran wanda yanzu haka ya yi nisa, kuma sun yi magana da kawu Suleiman ɗin kan idan aka gama hidimar a yi ƙoƙarin siyar da gidan sai a siya musu wani da kuɗin, amma dai su bar unguwar tunda ba ta da kyau.

Ita kan ta har Allah Allah take su zo, dan an gama magana idan suka zo zata koma can gidan ne na kwana ukun nan suma a basu dama su zauna da ƴar su inda akwai abinda zasu mata sai su yi, Safwan ne ma da ta faɗawa Aban shi tana so su koma tare sai ta ci gaba da kulawa da shi, ya kalleta sama da ƙasa sannan yace _"Babu inda zai je."_

Da takaici ya rufeta ta nuna kanta tace _" Ƙanena ne fa?"_

Sai ya tabbatar mata da _" E ƙanin ki ɗin, ni kuma ɗana ne na, naga wanda ya isa ya min iko da shi, duk mai son ganin shi ya samu Anna ta bashi katina ya tuntuɓeni, idan hakan ya kwanta min laba'asa."_

Saida ta yi ƙwallan takaici tace _" Ƙanin nawa? Ba fa kai ka haife shi ba, dan mutuwa ta rabamu da iyayenmu ba shi ya nuna za'a takamu ba."_

Taɓe baki ya yi yace _" Na sha gaya miki ke ma ƴata ce, Safwan kuma babu inda zai je, sannan ki sani zan canza masa suna dan ma ki cire rai da sake zama da Safwan."_

Rushewa ta yi da kuka tana faɗin _" Allah ya sawaƙe na zama ƴar ka *oga*, wallahi ni ba ka haifeni ba, Safwan kuma baka isa ka canza masa suna ba, ni a Safwan zan kirashi dan haka Babanmu ya saka masa, *mai ƙwacen ƙannai* kawai."_

A ranar ta sha kuka, AA kuma ya sha farin ciki, dan da ya tuna kuka da ta ɓarke da shi da ƙafafun da ta dinga bubbugawa ƙasa sai ya ji murmushi ya taho masa. To wannan matsalar ɗaya ce kawai ke damun ta, ba ma idan ta tuna da Nabihat zai zauna a matsayin uwa ko matar mai ikrarin Baban shi ne, wacce ko gaisuwa bata taɓa haɗa da ita ba, ita wallahi da Abrar ce zai aura da ta yi farin ciki sosai, ko ba komai tana ganin ƙaunar Safwan a tare da ita, amma Nabihat ta san Safwan zai sha wahala ne kawai.

Zo ka ga aunty Intisar uwar amarya, tana farin cikin yadda aka ɗaga tfiyar su saboda bikin nan, hidima ta zame mata biyu, ta yi a can gida dan Hajia ta ɗan saku yanzu tana sakar mata fuska sosai har ma ta damƙa wasu ragamar bikin a hannun ta, sannan kulawa da Yusrah take kamar ba gobe, idan ka ga gyaran da ta ɗauko masu zuwa har gida suyi suke mata zaka san abun ba ƙarami bane.

*BAYAN WASU KWANAKI*


Da mamaki Aba ya tsare fuskar shi da idanu kamar ba shine ya bashi izinin shigowa falon ba, bai daina kallon shi ba haka kuma bai ci gaba da saƙala agogon shi ba dan shirin fita yake yi har saida ya zo kusa da shi ya tsaya da ladabi da kuma rashin gaskiya yana ta sinne kai.

Aba da ya sake baki yana duban shi ya gyara tsayuwa ya ƙarasa ɗaura agogon yace "Jikan Anza, ina ce yanzu muka rabu da kai kan cewa za ka je gidan su yarinyar nan? Me kum ya dawo da kai? Ba ka tafi bane dama?"

A dake AA ya ɗago yana kallon Aban, sai kuma ya ga yadda ya haɗe fuska irin ba zai saurare shi ba, dan haka ya kyaɓe fuska shi kuma tare sa yanayi irin na shagwaɓa shagwaɓa yace" Aba, dan Allah to me zan ce mata? Ni wallahi na rasa me zan faɗa idan na je, Aba ka ga ban cika son barin yarona a asibiti ba da dare, da..."

Katse shi Aba ya yi yana nuno shi da yatsa yace" Kai dakata jikan Anza, kasan Allah ne ɗaya? To sai ka je, Safwan kuma kwana nawa suka rage masa dama a sallamo shi daga asibiti? To ka yi wasa yanzu zan sa a dawo da shi gida, kaga sai ya dinga raka ka wajen zancen ko?"

Zaro idanu ya yi har da ɗan dafe ƙirji yace" Aba! Ɗan nawa? Zance fa?"

Da tabbaci Aba yace" Ƙwarai kuwa, kai ko siyan baki ba sai ya raka ka ba, wani abu ne a ciki?"

Juyawa ya yi yana gunguni ƙasa ƙasa yana cewa" Fisabilillah Aba sai ka yi ta zuwa mana da rigima, ina yarona ina wannan lamari, ni kaina uban sa sai an koya min bare kuma shi, ni kawai ku ma san yadda zaku yi da ƴar mutane idan ta zo gidan."

Cikin sa'a kuwa yau sai Aba yaji saɓanin sauran lokuta da yake masa irin haka ba ya jin me ya ce sai dai ya ce ba komai, dan haka Ab da ya murmusa yace" Na zo da rigimar jikan Anza, kuma jikan Aliyu dole ya samu *ƙane* nan da wata tara in sha Allah."

Gaba ɗaya AA ya juyo yana kallon Aba, irin kallon nan da babu sakin fuska a ciki, kallon da har saida Aban ya ɗan zaro masa idanu yace" Ko dukana za ka yi?"

Da sauri kuma ya juya yana faɗin" Ni ɗin me?"

Har zai fita daga falon Aba dake ɗan biye da qhi yace" Idan ba za ka iya zuwa kai kaɗai ba, ka kira Baban su Yusrah ya raka ka mana, naga dai duk taron ku ne ai."

La'ilaha illalah! Subhanallah! Subhanallah! Yau me ya yi wa Aba wai? Daga rigima akan sai ya je zance ya ce ba zai je ba shi kuma ya dage sai ya je, to ba gashi ba zai je, me ye na sukar sa da Aba ke yi kai jama'a? Nufin shi fa taron su ne gwagware ko? Bayan wannan ma sai ya ja baban ƴar nan su je zance fisabilillah! A aboki ya ɗauke shi ita kuma ƴa, to idan fa ya zo gaya mata sun je zance ta masa dariya? Haba mana Aba, madadin ya dinga yin abun da hankalin zai ɗauka, sai kawai ya dinga yin abu dai da za'a waiwayo a kalle shi.

Ficewa sukayi tare da Aba har Aba ya yi gaba ya bar shi dan ya gama sallama da Anna da ta wuce madafa mayar da kayan shayin sa, shi kuma tsayen da ya yi su Nawal dake ta faman kwaɓa sabon haɗin gyaran jikin su yake kallo yana tunanin _'To ko dai su yake ɗauka su tafi zancen? Su zasu ɗauki hankalin yarinyar ai suyi ta hira, kaga kenan ya cika umarnin Aba sannan ya dawo da kimar sa gida.'_

Sai kuma ya girgiza kai shi kaɗai a tsayen saboda jin ai gwara ma ya tafi da Baban ƴar can ya fi sauƙi madadin ƙannan sa, abun kunyar ya yi yawa wallahi. Sai kuma ya tsayar da kallon shi kan Yusrah dake duba hotunan da Maryam ta sa ake turo mata na ɗinkuna da har yanzu suke ta yi ba ji ba gani, wani tunani ne ya zo masa a rai nan ma _'Shin ko sarauniyar soyayya da zance ba ya ƙare musu yake tambaya abinda zai faɗawa waccen ƴar?'_

Nan ma da sauri ya girgiza kai da tunanin me za ta faɗa masa da ya wuce yadda zai ƙasƙantar da kan shi a gaban Nabihat tunda ita ma mace ce, yadda ya ga yaron nan na mata kullum bakin shi a buɗe haka za ta umarce shi ya yi... Me ye abun yi? Mukhtar ba soyayyar nan yake yi ba shima duk da dai yaga suna ɗan waya da Abrar, Suleiman ma dai tuzurun ne kamar sa shi ma sun tara shekarun a kai ba shiga sabgar mata.

Cike da alfaharin haka ya wani gyara tsayuwa yana murmushi shi kaɗai irin ya fa cika ɗin nan gaskiya, wannan ai shine mazantaka. Arif kuma idan ya tuntuɓe shi iskanci ne zai ta soka mishi har su rabu baram baram, takaicin rasa madafar kamawa ya sa shi jan dogon tsakin da ya saka Yusrah da su Nawal ɗagowa, sai kuma ya kama hanyar fita yana jin gaskiya ba zai iya zuwa shi kaɗai ba fa, ba zai je wajen yarinyar nan shi kaɗai ba gaskiya...

Karo ya ci da Anna ita da Manal ta fito daga ɓangaren ma'aikata ta ƙofar falon, da mamaki ita ma tace "A'a, kai ba ka tafi bane ko me? Me ya dawo da kai? Mantuwa ka yi ne?"

Girgiza kai ya yi yana dai ta rarraba idanu bai ce komai ba yana kuma satar kallon Manal, taɓe baki Anna ta yi ta raɓa shi ta wuce tana faɗin "Idan ba zaka je ba ka tafiyar ka sabgar gaban ka mana, zuwa zance ya zama kamar an tura ka bakin iyakar Somaliya."

Saida Anna ta wuce sannan ya bita da kallo yana kuma hararen Manal da ya ga tana neman fashewa da dariya, sai kawai ya juya ya tafi a sukwane yana faɗi ƙasa ƙasa" Kwarankwatsa dubu gwara a kaini bakin bodar da in je wajen yarinyar nan, tsarar su Nawal ce fa, haba mana dan Allah."

Sai kuma ya ɗan cije leɓen shi da takaicin rantsuwar da ya yi yana shiga motar sa, niyyar sa ita ce sai fa ya samo mai raka shi zancen nan zai tafi, idan zai kai sha biyun dare kuwa sai dai ya kai amma sai ya samo, kuma sai ya je ko ƙarfe nawa ne tunda Aba da Anna suka ce ya je, idan ma bacci suke zai sa a tashe su a fito da yarinyar ya yi yadda su Aba suke so, ba shikenan ba dai.

Tafe suke cikin motar suka nufi gidan Chef ba tare da Arif ya gane cewa zance zasu je a irin wannan lokacin da ƙarfe ɗaya ta kusa na dare, mai gadi ne ya buɗe masu bayan AA ya sauka ya tashe shi daga barci, sojawan dake ciki suna gadin ɓoye kuwa yana shiga suka gaisa ya ƙarasa ya ajiye motar sannan ya ɗauki wayarsa ya yi ɗan jim yana tunanin to ya ya za'a yi ya sanar da zuwansa ne? Bashi da lambar yarinyar a wayarsa ai, ɗaya daga cikin sojojin nan ne ya zo zai wuce dan ya sanarwa da Chef cewa AA ne, sai AA ɗin ya dakatar da shi bayan ya yi murmushi ya ce" Ba fa Baba zaka taso ba, yarinyar wajensa zaka ce na zo."

Ɗan tsai ya yi yana kallon AA da tarin mamaki, dan kuwa lokaci ɗaya ransa ya ayyana masa kar dai zance ya zo a wannan lokacin? Sai dai kasantuwarsa gaba da shi, da kuma zamowarsa siriki a wajen chef a dole ya sara masa ya nufi falon Hajia ya danna lambobin ƙofa dake jikin wayar talho ya kara a kunnansa dan sanar da Hajiar zuwansa.

Yana juyowa suka yi ido


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login