Showing 306001 words to 309000 words out of 397328 words
Nabihat na zuwa gidan tunda gidan iyayenta ne, hakan ya sa ya yi shiru ya kuma zuba mata ido ita da Yayar ta a kan maganar saka ranar aure, shi dai abu ɗaya ne ya sani idan har suka kaishi maƙura zai yi fita ne ya ɗauro auren nan sai dai ta tare dan wallahi ba zasu masa taron biki ba, basu san kalar tasa rigimar ba sai sun yarda sun kai shi bango.
Anna na shagalinta ne da ƴaƴanta da ƙannen ta, takan je ganin jikin Hamat dan yana asibiti kuma cikin ikon Allah rashin lafiyarsa an kasa gane menene, dan a yanzu Aba a dole yake zuwa ya ɗan kula da lamarin asibitin da kansa, domin Hamat ɗin jiki ya ƙiya har an fara yi masa na hausa, dan Aba ya fara nema masa taimako na hausa domin jikin nasa gaba ɗaya kamar mai kamun iskokai ya rikice ba'a gane masa gaba ɗaya.
Su Yusrah kuwa babu inda suke zuwa, dan ko wajen aiki bata koma ba Anna ta nuna ta yi haƙuri sai ta tare a gidanta ta daidaita gidanta sannan zata ci gaba da zuwa, su Manal kuwa sukan je school, sai Safwan dake zuwa school a kai a kai, uncle Sulaiman kuwa ya fara karatunsa cike da kewar ƴan uwa da aminan arziki da ƴaƴansa, uwa uba da ta Manal wacce a yanzu a wuni sai su yi waya sau biyu suna zagaye zagayen juna da neman magana a zuwan dan su gaisa ne, masu kallon su na kallon su, masu musu dariya a ɓoye na yi masu yi a bayyane suna yi dan kalar tasu soyayar abin dariya ce.
*A* yau ne Anna ta sa suka shirya dan su je su gaisar da dangi, saboda yau ta cika sati biyu da auren, Anna ta ga ya dace su je su gaishe da dangi a santa sosai kafin a zo yi mata rakiya ɗakin ta dan kuwa Anna ta yi niyyar sai ta yi taro na musamman dan a rakata ɗakin ta nan da sati biyu kamar yadda ta tsara.
Tunda safe suka tafi su dukansu ban da Nabihat, sun sha shirrinsu tsaf tsaf da sucikin class, suka yi tafiyarsu Manal na tuƙa su idan ta gaji Abrar ta amsa dan twins sister ɗin Manal bata son tuƙi yau ko kaɗan, Yusrah kuwa har yanzu bata fara tuƙi ba, bata ma iya ba, har yanzu bata tsaya ta koya ba, kuma ko a hanya suna tafe ne ita ɗaya tana wani tunani a kan maganar aurenta, ta rasa inda zata ajiye mutumin nan, ya kan zo gidan safe, rana, yama, idan bai ganta ba yakan zauna har ta sauko, in ta sauko sai ya taƙaleta da wata rigimar sun yi kafin ya miƙe yana buɗewa yana faɗin duk mai raina miji ɗan wuta ne, sannan ya tafi, sam bata ganin yaren soyayya ko gigita kamar yadda Bilal yake nuna mata a da, bata san me zata yi tunani ba dai, amma ta san kamar Bilal ya fi damuwa da ita fiye da shi, kai ba ma haɗi, Bilal fa mayen soyayya ne wallahi, a dole ta ture tunanin dan yana neman ɗaga mata hankali suka yi tafiyarsu.
***A gida kuwa wajen yamma ya shigo gidan daga asibiti saboda a dole yake zuwa yana kula da asibitin nan yana taya Aba, domin Humed shi yana kula da harkar transport ɗin su ne, ba zai taɓa iya haɗa aikin nan da wani ba domin aiki ne mai ɗaukar hankali matuƙa, shi yasa shi yake zuwa can ɗin idan ya samu sarari ya taya Aba ayyukan, a hankali kuma yana ƙara shirya zuciyar Aba da idanuwansa da abinda zai gani ya kuma ji, domin Aban da kansa ne ya fara faɗin a asibitin nan ya tarda wasu abubuwa da suka bashi mamaki, sai dai ya rasa ta inda zai kamo, shi dai ya san abu ɗaya, zai kasance nan a duk lokacin da buƙatar hakan ta tashi, in sha Allah zai taya mahaifinsa fuskantar matsalar nan yana fatan Allah ya sa ya amsheta da sauƙi.
Ya samu Anna a falon, dan haka ya zauna bayan sun gaisa ya shiga amsa waya suna magana da malamin Safwan yana sanar masa yau zasu jima suna lesson saboda wani exam da zai yi monday, shi kuwa ya amsa shi ba damuwa amma kar ya jima a zaune idan ya ɗan jima ya tashi ya ɗan zagaya ya dawo dan saboda ƙafafuwansa da bayansa, yana kashe kiran ya ɗan dubi Anna da kyau ya sake bin falon da kallo, tsitt ɗin gidan yau ya yi yawa fa, ko ina yaran gidan da matar ɗan gidan suka nufa kuma? Ta yiwu suna ciki, ko da yake bari ya tambayi matar Aliyu kawai.
Da ya sake duban Anna sai ya ga kamar wacce ke harararsa, ya ɗan kawar da kai ya sake dubanta ya gane eh ko da ba harara bace wannan kallon na gargaɗi ne kam, gaskiya ba kallon zaman lafiya bane, sai dai ya cije sosai ya daure, cikin ɗar ɗar ɗin tambayar da zai fara jefo mata ta dube shi tana gyara zama haɗe da cije fuskar ta wuri ɗaya dan kar ma ya kawo ata wargi, gaisuwar sa ta amsa tana mamakin yanzu sabon salon da ya samu na wani zuwa musu gidan duk lokacin da ya so wanda a baya zuwan shi ƙa'ida gare shi, gyara zaman da ta ga ya yi a kujerar gefen ta yana ciro wayar sa daga aljihu yasa ta sake zuba masa idanu tace "Yau ba sabgogin ne ɗan Aliyu?"
Saida ya ɗan kalli fuskar Annan kafin yace "Da dama dai Anna."
Shiru duk sukayi ita da shi yana danna wayar sa, sai dai kuma idanuwan shi ba wuri ɗaya ba suke, da ya ga shirun ba za ta gyara shi ba ne ya dubi Annar yace "Anna ina Nawal?"
Kamar Anna ta san me yake so ta faɗa sai kuwa tace "Ta fita."
Da sauri ya ɗan kalli Annar da mamakin yadda yau ta amsa da ta fita kawai, bayan idan aka tambayi Nawal to har da Manal da Abrar aka tambaya, kai wani sa'ilin ma har da Y. Turaki, amma sai ya haɗe mamakin shi yace "Ita ɗaya kenan? Ina kuma ta je haka?"
Anna dai ta gane me yake so ya ji, sai kawai ta fito masa a mutum tace "Ziyara suka tafi tare da Yusrah, kasan tunda aka ɗaura auren ku bata fita ba har yau gashi kusan sati biyu, shine na ga ya dace tayi girki ta kai wa iyayen ku maza da mata, ka ga su ma sun shaida sun ci tuwon amarya."
Ƙyafta idanu ya fara yi tare da gyara zama yana aje wayar shi gefen kujerar kusa da guiwar hannun sa, da yanayi irin yana so ya fahimci daidai ɗin nan yace" Anna, kika ce ziyara? Gidan su kawunai da Goggunai ne ko? Kuma Anna ita kaɗai fisabilillah?"
Da wani mamakin sababi Anna ta kalle shi kamar za ta sake haɓa tace" Ban gane ita kaɗai ba? Da Abrar, da Manal da Nawal fa duk suna tare da ita, dreba ne ma dake wani uzurin ya sa suka tafi su kaɗai."
Sororo ya ci gaba da kallon Anna ya tallabe haɓa ya kasa cewa komai, Anna ma ɗauke kai ta yi ba ta sake cewa komai ba, sai zuwa can ya ɗan saci kallon ta a tausashe yace" Amma Anna ina ga bata buƙatar izinina wajen fita ko?"
Wata uwar harara Anna ta ƙwalo masa jin wai ita zai wa tambayar shaguɓe sai kawai tace" E, ai na faɗa maka ni na aike ta, jiya kuma da ya kamata a tambayi izinin naka naga ka saka ƴar mutane kuka ne, shiyasa na ce ta tafi zan sanar da kai."
Jinjina kai ya yi yana sake ɗaukar wayar shi yace" To, to ba damuwa, za ta zo ta same ni, Anna Y. Turaki ta raina min wayo, kuma wallahi yau zan yi maganin ta, ni ba sakarai bane ko shashasha."
Ƙwafa ya yi yana ɗora ƙafar shi akan ɗaya yana wata jijjiga da sake haɗe fuska tam, sai kuma ya sake kallon Anna yace" Amma Anna, a musulunce ba ni ya kamata ta tambaya ba idan za ta fita ba?"
Da shashantar da zancen Anna tace" Kai wa fa?"
Sakin baki ya yi da fari irin mamakin tambayar ta Anna, amma kuma da ya ga da gaske Anna take sai ya karkata kai yace" Ina ce Anna aka ce wai ni mijin ta ne ko?"
Ba tare sa ta ɗauki abun da gaske ba yanzu ma tace" Oh! Wai ne ma? Haka naji an faɗa nima."
Shiru ya yi yana kallon Annar amma ta ƙi kallon shi, a tausashe ya sake cewa" Amma Anna ai da ni ta tambaya ko? Ko iyaye ma suna bada izinin ne?"
Kallon shi ta yi a lokacin a zafafe tace" Aswan, ka fita idona in rufe, bana son ƙananan iskancin nan naka fa."
Da sauri yace" Na fita Anna, Allah baki haƙuri."
"Idan ya bani ka bi dare ka sace." Cewar Anna tana sake ɗauke kan ta.
Jinjina kai ya yi irin ba komai ɗin nan yana ayyana _'Ina ga da cikin ubanina ne ta auri ɗaya? Da haka za ta dinga fita ba da izinin su ba kuma ba yadda zasu yi da ita, nima dai da ake gani gagararren ne ai gashi na kasa mata komai, saboda sam iskokan ta ba sa shiri da ni.'_
A zahiri kuma sai ya murtuke fuska irin da gasken nan fa yace "Shikenan, bari ta zo na ji da izinin wa ta fita tunda ba tsoron ta nake ba, ni za ta mayar sakarai?"
Tangale haɓa Anna ta yi tana jimƙe wayar ta gam a hannu da ƙoƙarin laluben lambar Aba ta kira shi ta roƙe shi ya kira shi ya ce yana son ganin sa ma, idan ba haka ba to fa yau sai ta kai ga dukan kumatun shi dan ba za ta bari ya sake saka marainiyar nan kuka ba haka kawai.
Ta danna ok ta kara a kunne kenan ƴan matan suka dinga rangaɗa sallama da murnar su na tsarabar da suka samo da labaran da suka taho da su, sai Yusrah da suke ta tsokana a bayan su cikin sanyin jiki tana biye da su da kukan shagwaɓar bata so wallahi su daina, Nawal ce ta fara cik karo da shi, ai tuni ta ja birki ta shiga takowa a hankali tana sake yin sallama ƙasa ƙasa cikin nutsuwa, sai kuma ta yi saurin rusunawa tace "Barka da yamma Akhi?"
Banz ya mata haka har suka gama shigowa ya sauke duban shi kan Yusrah dake ƙarshe, wacce ita ma ko da ta ji suna gaishe shi gaban ta ya faɗi cikin ta ya ɗuri ruwa da tunanin yau kuma wace kalar wainar za su toya da *sojan ta*?
Kaf ɗin su ita ya shiga ƙarewa kallo yana nazartar shigar ta, wato riga da wando ma Y. Turaki ta saka ta fita da su ko irin na turkish ɗin nan sakakku da ɗan kwalin su ta wani yane kan ta da shi, ta haɗa wani mayen macthin da takalmin da ƙaramar jakar hannun ta da kuma agogo, ba kwalliya a fuskar ta amma sharri na ɗan liss sai take masa wani wal wal haka kamar wacce aka mannawa stone a fuska, sai yake ganin kamar ta masa kama da irin larabawan nan na Pakistan da su Jordan haka, hmmmm.
Taɓe baki ya yi ya kawar da kai yana ci gaba da sauraran su suna ta gaishe shi har da ita ɗin, sai kuma duk suka zagaye wajen da Anna ke zaune tana kallon shi, da kallo ya bita irin fa so yake ya feso zanxe a bakin shi, amma da suka haɗa idanu da Anna sai ya ga tana masa irin kallon nan na kai nake jira ɗin nan. A hankali ya cira idanuwan shi ya sake kallon fuskar Yusrah da ta ke ƙyaren fuskar shi tana fata kar ya mata ihu a kai, sai kawai ya dawo da duban shi kan wayar shi yana ayyana _'Anna kenan, fisabilillah marainiya ma irin wannan me zan ce mata ni kuwa?'_
Sai kawai ya dube su gaba ɗaya a ɗan kausashe yace "Kai, ku wuce ɗakin ku."
Kowace na turo baki suka juya da sauri har kamar za su tafi a guje suka nufi ɗakin nasu, Yusrah kuma saida ta sake kallon fuskar shi, haka kawai sai ya ji kamar murmushi ta masa kamar kuma kallon gargaɗi, dan haka ya zuba mata idanun shi a tausashe yace "Ki je ki huta sai ki sauko ki ci abinci."
Daga haka ya ɗauke kan shi daga duban ta, Yusrah da farin cikin bai ce mata komai ba ta juya da sauri ta bi bayan su Manal, inda ta bar Anna riƙe da haɓa tana mamakin me kenan? Tun yana danna waya da gaske har ya dinga jin idanuwan Anna na yawo a kan shi, a hankali ya ɗago ya kalli Annan sai kuwa sukayi ido huɗu, da tsantsar mamaki tace "Ka haƙura kenan?"
Wani marau marau ya ma idanu yace "Da me Anna?"
Taɓe bakin da Anna ta yi yasa ya ɗan yi murmushi yace "Oh, Anna bari nayi har ta ci abinci sai muyi magana."
Jinjina kai Anna ta yi irin oho ɗin nan, sai kawai ta duba wayar ta da Aba ya dawo mata da kira dan ta fara ƙara ya ga an katse, ya kuma san ba dai matsalar rashin kuɗi ba, saida ta ɗauka ta ma Aba bayanin ba komai kawai ta kira ne sannan ta aje wayar.
AA kuma kamar an tsikare shi ya sake kallon Anna ya gyara zama daf da ita ya ranƙwafo cikin raɗa yace "Anna, me zai hana ke ki mata maganar ta daina fita ba da izinina ba? Kinga Y. Turaki ba magana take ji ba, da na mata magana za ta fara tutturo min baki, ki faɗa mata da kan ki kawai Anna."
A ɗan hassale Anna ta dube shi tace "Me ya sa kai ba za ka faɗa mata da kan ka ba? Baki na fika?"
Girgiza kai ya yi yana faɗin "Allah ya baki haƙuri Anna." Sai kuma ya wani matse fuska yana gyaɗa kai shi kaɗai yace "Haba mana, sai na dinga abu kamar ina jin tsoron ta, wacece Y. Turaki?"
Galala Anna ta yi tana kallon shi sai kuma ta miƙe tana rarumar wayar ta tna cewa "Allah ya shirye ka."
Da kallo ya bi Annar kamar yana tsarguwa da hakan, sai kawai ya ji a ran shi _'Anna ki turo min ita na mata faɗan yanzu, dan Allah ki turo ta zan mata yanzu.'_ Amma kuma ya kasa faɗan haka a fili.
Ganin zaman ba zai anfaneshi ba sai kawai ya tashi ya yiwa Anna sallama ya nufi gidansa a ransa yana ayyana _' Zan mata magana ne, wace Y. Turaki? Ita ɗin banza ita ɗin wofi, yo na yi gwa da gwa da ƙarti na sha lafiya balle wata Y.turaki? Zamu haɗe ne zaki gane bana son rainin wayo, kar ki kuma fita ba da izinina ba, yanzu na yafe miki amma kika kuma sai na sassaɓa maki a gaban Annar taki a yi abinda za'a yi, yarinya kawai da take son sakani surutu!'_
*A* yanzu da Anna ta basu ranar tarewa wuni suke yi suna abinda zai fishe su, Nabihat kuwa ta fara ɗagawa mahaifiyarta hankali kan a saka nata auren ita ma kwana kusa dan bata so su tare su barta a nan ita kaɗai, wallahi a saka nata auren ta rigayi Yusrah tarewa.
Ai kuwa mahaifiyarta ta samu mahaifinta da maganar, a ranar ne ransa ɓace ya ce" Look Hajia, kina tunanin ke kike aurena ne ba ni nake aurenki ba ko kin fara tunanin kin fini iko da gidana? Ki kiyayeni fa, ki yi kiran yarinyar nan maza ta dawo gida bana son shashanci, ta yiwu tana can tana aikata wani abin da ba za'a min magana ba dan ana ganin girmana, kar ki cakula min lissafi da mutumina, tunda kin ce zata tare nan da sati biyu ai ba maganar ɗaura auren nan sai nan da wata biyu, ya zamo ta tare sun zauna sun fuskanci juna in yaso sai ita ma ta je su yi zamansu, ina fata kin fahimta?"
Da wannan ɓacin ran ya fita ya bar mata gidan, ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi, ta ringa kai kawo hankalinta tashe, dan kuwa a yanzu ita ma tana ganin a ɗaura ɗin Nabihat ta fara tarewa da shi zai fi alkairi fiye da ace Yusrah ce ta fara tarewa da shi, balle irin yadda aka zo aka faɗa mata gidan da zai saka matansa ita da kanta sai da abin ya gigitata, irin tsarin gidan abin ba'a cewa komai, bata san yaron ya kai matsayin nan ba sai da aka sanar mata kuma aka kawo mata vidion gidan, a nan ta ƙara ji a ranta ai ƴar ta bata da miji sama da shi, ta kuma yarda da maganar Yayar ta ko yana gwada su ne kafin a kawo kuɗin auren saboda wasu mazan haka suke wai basa gaggawar sakarwa mace kuɗi sai ta shiga gidansu, kai eh lalle zata san hanyar da zata bi a ɗaura auren nan su samu su yi waje da banzar can su gaji dukiyar gaba da baya.
(Kowa da bikin zuciyarsa.)
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku