Showing 99001 words to 102000 words out of 397328 words
ta yi shiru har ya zamo yana ƙorafin ta ƙi bashi dama, bayan baƙo yake a duniyar ta a yanzu da take a gigice wacce dama yake bayani kai? Ai bata da wata dama da ta wuce ta gaishe shin nan da take yi, tana matuƙar danne damuwarta na lalle sai sun je asibiti dan Hajia ta nuna cewar sai ta warke sumul zasu tafi, duk da ta nunawa Hajiar cewar jikinta da sauƙi fa, dan bata ga ciwon da zai jijjigata fiye da na zuciyarta ba, amma Hajia ta nuna sai ta warke, a dole ta yi biyayya ta yi shiru, Allah ya taimaketa yau tace zasu tafi wajen Goggonsu, shine sanadiyar shirinta a yanzu ƙarfe huɗu na yamma zuciyarta cike da tunanin abinda zai je ya dawo a tafiyar tasu wajen Goaggo.
"Yusrah, baki gama ba? Hajia ta sauko tace mu fito, taho mu je." *Fatila* autar Hajia ta leƙo tana faɗa hakan ya sa Yusrah ɗaukan mayafin abayar da aka siyo mata ta yara saman gashin kanta da ta samu ta dunƙule shi waje ɗaya ta ɗaure shi sannan ta juya ta fito ƙafarta sanye da takalmi plate ta sauke tana atishawar turaren da ta ɗan fesa dan kuwa an jima ba'a sadu da turare ba.
Hajia ta gama shanye shayin da mai aikinta ta dafa mata tana kallonta da kula ta ce" Yawwa zamu je anguwa mu dawo, ki dafa jelof ɗin shinkafa ki wanke salade dan ni shi zan ci, dan Allah kar ki cika gishiri a girkin nan fa."
Mai aikin ta amsata har tana ɗan duƙawa tana masu a dawo lafiya idanuwanta ƙyar a kan Yusrah da mamakin haka kawai baƙuwa ta zo ta fita fada a gida? Lallai yau zata faɗawa Hajia Tasneem cewa budurwar nan fa a nan take zaune kuma kullum sai Elhaji ya zo sun kaɗaice shi da ita.
Fatila ce ke tuƙa su har suka ƙaraso daf da gidan Goggo, ajiyar zuciya Yusrah ta sauke ta sauko ɗin ita ma jikinta duk ya yi sanyi ta yi masu jagora suka nufi cikin gidan.
Tana yin sallama ta fara yin tuntuɓe da kwanon masar da aka shaƙe za'a kai wajen mai anguwa da ya bado kuɗinsa a kan zai yiwa almajirai sadaka, wacce zata kai ɗin ce ta ajiye ta dakata tana amsa waya a nan kan hanya, shine Yusrah ta ci tuntuɓe da shi ta fancakalar da abinda ke ciki sannan ta yi suuuu ta zube cikin tarin uban kwanonin sana'ar da aka danƙame ake shirye shiryen fara wankewa.
Ido da baki Safiya taa saki tana kallon Yusrah da ta zaro ido kamar an jijiga ɓera a kwano kanta na juyawa ta ɗago a zaburen ita ma tana kallon Goggo da ta fito da sauri tana ɗage labulen ta zuba ido a abinda ya faru nan take ta ji zuciyarta ta yi mata ɗaci hakan ya sa ta fito gaba ɗaya lokacin da Hajia ta idasa yin sallama ta shigo ita da Fatila, Ya zamo Goggo na amsa sallamarta ta juyo inda Yusrah ta miƙe tana kakkaɓe jikinta da ɗauko ɗan kwalinta tana ƙoƙarin kaɓewa Goggo ta ce" Baƙi ne? Bismillah bari in gama da wannan marar mutuncin..."
Kallon Yusrah ta yi tace" Ke Yusrah, gaskiya rashin mutuncin ki ya isheni haka, ke shikenan duk in kika zo gidan nan sai kin haɗani da wani ciwon bakin? Ina dalili ne ni wai sunturin da kike min a cikin gida, wannan masar ta jaka biyu ce sai ki irga ki bata ta maidawa mai anguwa kuma ki faɗa min abinda ke tafe da ke yanzun ma dan mu samu matsaya guda dan gaskiya abin ya isheni haka."
Yusrah na kallonta, haka ma Hajia na kallonta da mamakin wacece wannan kuma? Sai dai Yusrah ta ƙara danƙara mata wani mamakin a lokacin da take son tabbatar mata ita ce wacce suka zo wajenta a hankali ta ce" Goggo dama zuwa na yi in amshi lambar aunty Fureira dan in kiranta in ji Safwan ɗin ko yana can, tsautsayi ne ya sa na faɗowa kayan abincin can wallahi ban yi da gangan ba."
"Dan Allah ki barni in huta da maganar Fureira da ta masakin yaron da kika ce anfaninsa ya gama ƙarewa, kai ku bani wayar nan ta ɗauki lambar nan in huta da wannan bidi'a ta yarinyar nan, tsautsayi kuma ban san shi ba."
Daga haka ta juya rai ɓace ta amshi wayar ta jefowa Yusrah sannan ta nufi ɗakin kishiyarta ta bankaɗa labule tana faɗin" Wai ke me kike yi a ɗakin ne da ba zaki fito ki tarbi baƙi ba gashi ni wannan abar ta riƙe ni? Ina sabuwar tabarmar bani in tarbi baƙin tunda ke kin zama isasshiya."
Da sauri ta ɗauko tabarmar ta fito ta shinfiɗa tana yiwa su Hajia sannu wacce ta daskare ta bi wannan da kallo ta bi waccen, ba ma kamar Yusrah dake loda lambar Innar tata kanta a ƙasa har ta gama ta ƙarasa ta ɗan duƙa ta miƙawa Goggonta wayar ta miƙe jikinta a mace murus sai dai idanuwanta sun yi wata irin bushewar da ba ɗis ɗin hawaye a cikin su, ta juyo kenan ta ji Goggo na faɗin" Ki fa bada kuɗin kafin ki wuce..."
Sai kuma ta ci gaba da cewa" Hajia bismillah mana ku ƙaraso ku zauna bismillah sannunku da zuwa lalle marhabin."
Hajia zainab ta haɗiyi yawun da ya tsaya mata a wuya da ƙyar, sannan ta dubi auta Fatila dake riƙe da jakarta ta amsa ta buɗe ta ciro kuɗi ƴan jaka jaka da bata san adadin su ba ta juyo inda Goggo ke tsaye ta ƙarasa ta kama hannun gwagwo ta saka mata kuɗin nan dake ƙamshi da maƙar maƙar ɗin sabintaka, bata iya ce mata komai ba ta juyo ta ce da yaran" Ku mu je, ke Yusrah wuce mu je."
Yusrah ta juya da sauri ta fara fita, haka ma Auta da idanuwanta suka gama cika da ƙwalla tana kallon Goggwo ta fice Hajia na bayan su suka shiga motar Yusrah da auta ne dama a gaba Hajia kuwa a baya a hakimce, Auta ta tada motar ta ja suka tafi.
Goggo kuwa na tsaye da kuɗi a hannu baki sake tana kallon hanyar da suka bi, har Safiya ta dawo ta ce" Mama wallahi sun tafi tare take da su a wata irin mota ƙatuwa mai shegen kyau, taɓdijan! Dubi jikin Yusrah ki gani Mama, dubi tufafin jikinta ko ina ta san mutanen nan?"
Goaggo ta yatsina baki ta irga kuɗi masu yawan gaske ta haɗe kansu ta totse a mara ta ce" Ke, maida hankali maza a tada mai a saka masa masar nan a kwashe a kai masa, wannan kuwa karta wani birge ki, domin da gani kuma an zama ƴan matan matan Alhazzai sai fatan shiriya dan ban ga abinda zai haɗata da wannan Hajiyar ba har ta yi kyauta irin wannan saboda ita, wai nan haushi ta ji dan an yiwa yarinya faɗa, sai ki yi ai mu gani, duk duniya dai yarinya bata da kamata, ta je ta dawo ne marar mutunci shikenan sai in ƙyale a min asara ban yi magana ba? Aikin banza aikin wofi kawai! Wannan dukiyar karma ta birge ki dan ni kuɗi in ba ta jiɓin goshi za'a neme shi ba duk aikin banza ne."
Daga nan ta ci gaba da kaye kayenta, sai dai wani abu ya danne ƙirjinta na irin lafiyar fatar da ta gani ita ma tare da Yusrah da alamun nutsuwa wanda duka kwana bai fi uku zuwa wuni na huɗu ba da rabuwar su, uwa uba matar nan da ko a bata ce mata ba ta matuƙar bata haushi, aikin banza Yusrah ai ƴar ɗan uwanta ce ba ta uban wani ba, babu ubanda ya san ciwonta sama da ita, yarinyar ce ke da kayan haushi, ana nuna mata hanya tana wani kaucewa dan rashin mutumci da raini, yaushe ma zata zo ta karɓi kuɗin gadonsu wai zata yiwa yaron da tace ƙashin baya ya lalace magani, kuma dan iskanci ta ringa dawowa amsar lamba bata dawo da kuɗin ba bata yi bayanin inda ta kai kuɗin ba, ai sai ta bari a ajiye mata saboda in miji ya fito a yi mata abinda ya samu da kuɗin, amma ta wani haɗe kuɗi ta karɓe, sai taje ta yi iri da su ai.
Tuki auta ke yi tana saka ɗan tissue tana share idanuwanta, sai Yusrah dake ta faman kiran lambar aunty Fureira amma kiran yana dawowa, Hajia kuma daga baya na cewa "Ki bari ko anjima sai ki jaraba sake kira, kinsan matsalar network?"
Yusrah dai bata haƙura ba har suka isa gida, sai dai suna ƙarasowar suka tardo Tasneem zaune da yaranta a falo, yaran sun yi kaca kaca da wajen, ita kuma tana zaune tana dannar waya da taunar cingam.
Tunda suka shigo cikin auta ya juya, amma ta dake ta kama hannun Yusrah ta ce" Mu je ciki sister."
Yusrah ta gyaɗa kanta tana sauke ajiyar zuciya haɗi da ɗaga kiran ƙawarta Maryam dake shigowa sabuwar wayarta wacce Elhaji Jafar ya bata tun washe garin da ta kwana a gidan su cike da kati.
A nutse ta yi sallama daidai lokacin da kunnen ta ya jiyo mata muryar Hajia na faɗin" Su Tasneem ne? Kun jima ba?"
Tasneem da ta bi Yusrah da kallon mamaki har ta ɓacewa ganinta ta fitar da zazzafan huci ta maido dubanta kan Hajia, tana karewa Hajiar kallo ƙirjinta na yi mata zafi, in ba dan abu ɗaya da mijinta ya tabbatar mata a haukanta idan ta saki ta zagi mahaifiyarsa ko ta taɓa lafiyar jikin mahaifiyarsa a bakin aurenta ba yau da babu abinda zai hana ta ɗurawa wannan matar zagi, kai! Kta zata ɗauki karuwar nan ta ajiye a gidan salon mijinta ya ringa zagayowa ana cin amanarta? Lallai.
Ciki ciki ta gaisar da Hajiar sannan ta yi shiru ta ci gaba da kaɗa ƙafa dan wallahi zata zauna daga nan har gobe ta ga in munafukin zai sanyo ƙafarsa gidan nan, idan kuwa ya sanyo lallai yau za'a mutu a gidan nan dan wallahi a shirye take uban kowa ya jigata a kan mijinta!
😳
*Maryam* ke bayanin zuwanta gidan a gobe dan kawowa Yusrah ziyara, ita kuma tana amsata a sanyaye cewar Allah ya nuna masu har auta ta yi mata kwatance da kyau sannan ta bata wayar suka ci gaba da zantawa kamar yadda suka saba.
A tausashe Maryam ta ce" Yusrah, gaba ɗaya kin canza, kamar ba Yusrahta ba, mai kazar kazar da rigima, duk kin zama wata iri hatta yanayin maganar ki ya zama wani iri, tamkar wacce ta sha duka, Please besty ki yi haƙuri ki dawo yadda kike."
Yusrah dake zaune saman kujera, wayar take jira Maryam ta ajiye ta shiga wanka ta wanke man jan da ta kwaso sannan ta ɗauro alwalla ta samu kanta da fitar da murmushi a hankali ta buɗe idanuwanta ta zubawa madubin dake nesa da ita kaɗan, nan da kwana uku zuwa hudu ta yi balaki da wani mahaukaci, amma tunda ta fito kuma sai ta koma irin na da, ƙwarai ta sha duka, duka mai zafin da bata tunanin in har zata iya komawa yadda ake so ta dawo, ta ya ya zata iya komawa irin na da? Ta ya ya zata iya samun murmushinta? Ta yiwu idan ta ga Safwan duniyarta ta ginu, ta yiwu idan yana gefenta ta samu ƙwarin guiwar rayuwa cikin duniyar nan mai abin mamaki.
A hankali ta ce" Maryam, in sha Allah zan dawo yadda kike so, bari in yi sallah zan yi kiran ki." Daga nan suka yi sallama, amma saida ta sake kiran lambar aunty Fureira da ta ji shiru sannan ta tuɓe ta shige wanka.
*A* falo kuwa Hajia ta kasa ta tsare, ta yi sallarta a nan ta ci gaba da jan carbinta tana bin yaran d'anta da kallo, tamkar su tsolewa juna ido, sani irin mugun wasa da zage zage abin tamkar rainon maguzawa, a saman kujera suke a tsaitsaye suna tafka kokowa tamkar zasu karya juna, sallah kuwa da aka kira da Hajia tace su tashi su yi sallah babu wanda ya kalleta balle ya je ya yi, hasalima iface ifacensu suka ci gaba da yi da kokoyinsu, to mahaifiyarsu ma bata tashi ta yi ba yaushe zasu tashi su yi? tana zaune tana kallon ikon Allah Jafar ya kama ƙofar falon ya sako ƙafafuwansa da sallama.
Wani irin turus da ya yi sai da tausayinsa ya kama Hajia, ya yi wani galau yana kallon Tasneem da ta taɓe baki ta tafa hannu ta saki wata dariya ta basawa ta shiga kaɗa ƙafa tana kallonsa.
A hankali ya kalli ƙofar da ya buɗe ya shigo, ya sake juyowa ya kalli Hajia da ta zuba masa ido a zaunen da take bata motsa ba, me yake tunani? Me da me yake saƙawa a ransa? Allah masani, amma a irin tsayuwar da yayi zaka karanci tarin nadamar shigowarsa gidan a yau, ga hannunsa riƙe da leda baƙa shaƙe da siyayya harda su awarwaro ya siyawa Yusrah da sabin atamfofi.
"Sai ka ƙaraso ai munafukin Allah, Allah ya toni asirinka Jafar ka ƙaraso in ga meye a ledar?" Ta faɗa da ƙarfi a gaban mahaifiyarsa da ƴaƴanta, bata jin kunya balle nauyi, bata tsoron tarbiyyar ƴaƴanta babu abinda ya shafeta a yi mata tofin Allah tsine, ta zo a shirye dan su raba hali babu idon ubanda zai hana ta ci masa mutunci a yau!
Hajia ta kawar da idanuwan ta daga dubansu, ta lumshe idanuwanta zafi da raɗaɗin wulaƙancin yarinyar na hauhawar mata da hawan jini.
Rai ɓace Tasneem ta karɓe ledojin hannunsa ta shiga zazzagewa, ta ɗago a gaban idanuwan mahaifiyarsa ta shaƙi kwalar rigarsa zata fara aikata halin rashin mutumcin Hajia ta miƙe ta ƙaraso ta kama hannunta rai ɓace ta fizge riƙon da Tasneem ta yi masa tana kallonta ce" idan idanuwanki sun rufe, ya zamo bakya jin kunyar idanuwan mahaifiya, ya zamo neman da kika yi kika samu ke kaɗa maki abubuwa kala kala ai kya ji tausayin kanki da tuna makoma, Tasneem ke ce ki zagi miji, kin yi kokowa da miji, kin wulaƙanta miji, Allah ya shirye ki, amma yau bana buƙatar rashin kunyar ki, ki sani idan ina rufa asiri dan kawai ban cika son wani ya shiga hurumin abinda ya shafi ƴaƴana bane, amma in har kika ce ke kin shirya nima yau a shirye nake, yarinya da kike magana kanta ni na sauketa, a gidana take, gidan da yake mallakina, baki isa ki kawo min tsarin ki ba, ki je kawai idan kuka haɗe a gida kwa yi dukkan abinda ya raya maku daidai, ki fitar min a gidana."
Da matsanancin mamaki Tasneem ke kallon Hajia Zainab, dan tunda suke idan faɗa suke da Jafar Hajia takan haɗa su ta tura su ciki tace su yi a sirri, bata taɓa nuna mata irin haka ba, kai bata idasa kasheta da mamaki ba sai da ta idasa fitar da ita daga falon rai ɓace ta ce" Ki kula, ina da limite ɗin da ba'a katsewa, idan aka katse nima na kan aikata aikin da bashi da daɗi, ki kula ba'a wulaƙantani a banza a sha a wofi, in ina maki kara kuwa ba yana nufin nima kin gama da ni ba, yarinyar nan idan kika yi gigin taɓa ta, Tasneem a nan zaki gane ina da limite." Daga nan Hajia ta rufo falon ta zo ta wuce Jafar dake tsaye tamkar gawa ta ƙarasa wajen yaransa dake ta durufkiya fuska a haɗe ta ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*27*
Fuska a haɗe Hajia ta ce" Kai, baku ji an yi sallar magariba da Isha tun ɗazu ba?"
Jin yanayin muryar Hajia ya saka yaran tsagaita kokoyin da suke yi, amma ta tsakiya fir bata wani daina ba saima ƙara tsakalar kokowar take yi tana ihu.
Hajia ta ƙarasa ta kama hannunta ta dirota ƙasa ta zarro mata ido sosai ta ce" Ki nutsu, a kan sallah zan saka bulala in zane ki, maza ku je ki ɗaura alwallah ku yi sallah kafin raina ya ƙiya min."
Da sauri suka nufi inda ta nuna masun, kowace na satar kallon mahaifinsu dake tsaye kai a ƙasa suka shige dan ɗaura alwallar domin tunda suke da kakarsu basu taɓa ganin fuskarta a haka a gabansu ba sai yau, gashi basu ga maman tasu ba ma balle su je wajen ta, ko ita ta tsakiyar dake faman faɗin ba zata yi sallar ba, wajen mamanta zata je sai da yayarta tace su yi sallar kar Hajia ta dake su sai su bi mahaifin