Showing 255001 words to 258000 words out of 397328 words

Chapter 86 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70006

ya ƙi auren ta saboda haka? Kenan rayuwar ta za ta tabbata a hakane? Me ya sa? Me ya sa ya yi haka?"

Sai kuma ya yi tsaki cike da takaici yace" Har zan zauna ina tambayar shi wai ya faɗa min sai na nutsu zai sanar da ni, a ina zan nutsun? Ya ga alamar zan nutsu anan kusa? Yarinyar da babu uwa babu uba ace haka na faruwa da ita, ya yake so muyi dan Allah?"

Sosai hankalin Chef shi ma ya tashi, shi kam ba wai na dakatar da auren ba, sai dan fitowar vidion bayan kuma aikin su bai kammala ba, sunan wanda ya ɗora vidion ya duba duk da sunan bogi aka yi anfani da shi, amma sai ya numfasa yace" Elhaj, na san wa ye Aswan na kuma san me zai iya aikatawa, na san ba zai yi wannan abun haka kawai ba tare da wani dalili ba, ina ga ka sake zaunawa da shi sai ka fahimce shi."

"Wane dalili ne zai sa ya shafa mata kashin kaji? Idan ma ha'inta ta yake yana aikin sa ne a ɓoye, me ye na sakata a ciki daga hanya ta haɗa su? Me ya sa zai sakata a ciki?" Aba ya faɗa muryar sa sama sosai.

A tausashe Chef ya sake cewa "Bana jin haka kawai zai sakata a maganar, na tabbata dai akwai wani dalili mai ƙarfi Elhaj, amma ita yanzu mahaifiyar su Bilal ɗin ba za'a sake rarrashin ta bane? Fasa auren ai bai kamata ba."

Da takaicin halin Hajiar nan Aba yace "Ba zan kuma rarrashin ta ba, sannan wani ba zai je da yawuna ba, idan ɗan ta ne autan maza to ta je ta jiƙa shi tasha kayan ta, aikin banza kawai."

Shiru Chef ya yi yana kallon kayan da zai mayar, cikin wata sanyayyar murya mai nuna tsantsar alhini da jimami Aba yace" Zan sama mata wani mijin, wanda na tabbatar zai riƙe ta da gaskiya, yarinya abar tausayi, yanzu bata san hawa ko sauka ba kawai sai ta ji an fasa ɗaurin auren ta? Ni wannan ne tashin hankalina, shine ban san ta inda zan fara sanar da ita da dangin ta ba, zasu iya kallon mu a matsayin wasu mutane na daban, zasu iya ganin kamar ɓata musu lokaci mukayi, har ma suyi tunanin ko hakan da san ranmu ya faru."

Da sauri Chef ya girgiza masa kai yace" A'a Elhaj, duka ba zasuyi wannan tunanin ba, mutanen suna da fahimta sosai da kuma yarda da ƙaddara, kuma tunda kai tashin hankalin ka shine yadda zaka faɗa musu an fasa auren ne, to me zai hana ka *ɗaura auren da shi Aswan* ɗin? Kaga kenan sai ya zama gyara ga abinda ya lalata."

Ƙuri Aba ya masa da idanu yana kallo, ya ɗan jima haka kafin yace" Aswan kuma?"

Da tabbaci yace" Ƙwarai, Aswan, ba ya yi ikrarin mijin ta bane a ɗaukar? To a tabbatar da maganar tasa, sai kuma muga da me duniya za ta ci gaba da zargin su? Kowa dai yasan ba ƴan ta'adda bane su."

Wani irin sakayau ne Aba ya fara ji a ran shi wanda rabon da ya ji shi tun kafin zuwan shi asibiti da safe jiya, amma dan kar ya nuna farin cikin sa kai tsaye sai ya gyara zama yana cewa" To amma Aswan kuma? Nabihat ɗin fa? Ko ka manta da magana mai ƙarfi a tsakanin su ne?"

Girgiza kai Chef ya yi yana ƴar dariya yace" To shi ba namiji bane Elhaj? Huɗu ma zai iya haɗawa lokaci guda, bare kuma Nabihat da ko ranar ba'a saka ba har yanzu, na yarda da ɗana fa."

Ya yi maganar da ƴar zolaya, hakan ya sa Aba taɓe baki ya kawar da kai, Chef ne ya sake cewa" To ya, na kai mata kayan waɗannan daga nan na gayyace ta ɗaurin auren Yusrahn a jibi in sha Allah da ɗana?"

Kallon shi Aba ya yi, sai ya ji ya ƙara girmama amintakar su da Chef ɗin, murmushi ya masa tare da ɗaga kai a hankali alamar e, da sauri Chef ya miƙe har da sara ma Aba irin dai da tsokanar nan yace" Da umarnin ka Chef."

Sai kuwa ya suri akwatinan nan da ƙarfi ya cicciɓi ɗaurikan goron nan bayan ya saka kuɗin aljihu sannan ya fita yana faɗin" Sai na dawo, daga nan zan bugo sababbin katin ɗaurin aure."

Dariyar da Aba bai shirya ma zuwanta bane ta suɓuce masa, saida ya ga fitar shi ya girgiza kai yana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya furta" Jikan Anza, da gaske ka ɓata min rai, yanzu ya kake? Da fatan ba ka yi kuka da na mareka ba?"

Ko da Anna ta shigo kafin ma ta zauna Aba ya ce "Kira min Fureira dan Allah?"

Ɗan tsai ta yi tana kallon shi, so take ya kalle ta dan ya fahimci abinda fa take nufi, amma Aba kamar ya sani ya sunkuyar da kan sa yana neman lambar uncle Suleiman, yana danna ok ya ɗago ya kara wayar a kunne suka haɗa ido, da idanun ya mata alamar tafi mana, jinjina kai kawai ta yi ta juya tana ayyana _'Ka gama zagaye zagayen k same ni.'_

Uncle Sulaiman na ɗaga kiran Aba yace "Ba ka fita bane?"

Da ladabi ya amsa da "E Aba."

A taƙaice Aba yace "Ka sameni a falo yanzu?"

"To shikenan, gani nan zuwa." Ya faɗa yana ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin dan dama yana shirin fita ne, saida ya zo dag da ƙofar shiga ɓangaren ya ɗan rage saurin sa ya dafe ƙirji ya lumshe idanu yana faɗin "Allah ka ƙara min ƙarfin guiwa, Allah ka sa na daina jin wannan faɗuwar gaban idan na ga *ƙanwar boss* (Manal), abun tashin hankalin ma da suke rikitani wallahi."

Sai kuma ya zura kai ciki yana tura ƙofar madubin da sallama, bai yi sa'ar haɗuwa da kowa a corridorn ba sai daf da ƙofar shiga wajen Aba ya ga Anna da aunty Fureira a bayan ta, gaisawa sukayi sannan suka shiga gaba ɗaya da sallama, wuri suka samu duk suka zauna kan kujera Ana na kusa da shi suka yi shiru suna sauraren shi.

Anna ya kalla ƙasa ƙasa yace "Tidin ta fita ne?"

Amsa Anna ta bashi da "Ta fita tun ɗazu."

Shiru ya ɗan yi, kamata ya yi ace akwai ko da ɗaya ne daga cikin shaƙiƙan sa anan shima dan su shaida wannan lamari, sai dai babu kowa anan ɗin sai shi da ya haifi abun sa, dan haka ya gyara zama ya kalli ahalin Yusrah ya fara da "Kun ji nace ina neman ku ko? Wani abu ne ya faru tun jiya, amma ban sanar da kowa ba saboda nayi tunanin zan iya shawo kan matsalar, sai dai Allah bai bani damar hakan ba, jiya ƙanin mahaifin su Bilal ya zo nan ya same ni ina shirin fitar nan asibiti..."

Abinda duk ya faru ya kwashe ya sanar da su, tare da nuno musu vidion ya fara ba Anna ta gani sannan ya ce ta basu yana ci gaba da faɗin" Saida na zo gida na ƙara kallon vidion da kai na tabbatar da Aswan ne dai a ciki, a tattaunawata da shi daren jiya ya tabbatar min da e shine, na shiga tashin hankali marar misaltuwa, na yi ta tunanin me ye dalilin sa na aikata haka? Shin dama sun san juna ne kafin tafiyar su aikin Safwan? Sai dai bai bani wata tsayayyar amsa ba, raina ya ɓace da shi har na kore shi daga nan, yanzu kuma bayan tattaunawar mu da Chef sai yake sanar da ni yasan waye Aswan, tabbas akwai dalili mai ƙarfi da ya sa ya yi haka duba da shi ɗin soja ne, ban masa gardama ba dan nasan zai iya yin komai akan aikin sa, to amma fa hakan na nufin ya ci amanata kenan yana aiki a ɓoye bayan an ce an dakatar da shi na wata uku? Ko ma dai menene shi mai laifi ne a wajena, ba kuma zan waiwaye shi ba har sai ya bani ƙwaƙwaran hujjar da za ta sa na yafe masa, abinda ya sa na ce ku zo dan muyi shawara da ku ne akan wata shawara da aminina Chef ya bani game da batun auren su."

Numfasawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa" A ganin shi, da kuma nima abinda na ga ya fi ɗin kenan, me zai hana a ɗaura auren Yusrah a jibi jibin nan kamar yadda aka tsara, sai dai ba da Bilal da mahaifiyar sa ta ƙiya ba, da shi Aswan ɗin da ya yi sanadiyar rugujewar auren ta? Dan ni dai a ganina idan bashi ɗin ba, to ina tsoron wanda ba sa son farin ciki da ci gaban yarinyar nan su ci gaba da bibiyar ta ta yadda ko ta sake samun wani mijin nan gaba a sake lalata maganar auren nata, kai wata rana ma za'a iya kashe mata auren idan ma anyi nasarar ɗaura shi kenan, shiyasa na ga to gwara shi da ya fara buga wasan, to ya ƙarashe ta da kan shi, amma ku ya kuke gani?"

Dukkanin su babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba, musamman aunty Fureira dake hango fuskar Hajiar saida ta riƙe haɓa tace "Ni nasan dama za'a yi haka, wallahi har ga Allah matar nan bata kwanta min a rai ba, yanzu kenan kunyata mu ta so ta yi?"

Kallon ta Anna ta yi, ita kam ta rasa a wane ƙadami za ta ɗora wannan lamari, Aswan? Dama shine wanda ya yi sanadiyar shigar Yusrah PG, wanda suke ganin rashin kyautawar sa da zaluncin sa ƙarara? Akan haka kuma Hajia ta dakatar da auren? Ta ƙi kuma ta saurari kowa? Har tana faɗin ita dama auren ba son shi take ba? To Alhamdulillah tana da ƴaƴa maza, yau ko babu Aswan ai akwai Humed, wallahi da Izinin Allah ba za ta bari yarinyar nan ta zubar da ƙwalla akan wannan lamari ba, Hajia kuma ba za ta je inda take ba a yanzu, amma ta san akwai ranar da zasu iya haɗewa ko da a hanya ne, idan tunanin ta ai yarinyar bata da gata shiyasa ta yi haka, to ta sani za ta yi kawar da kai akan Intisar da take takawa, ko ba komai Intisar na zaune da mijin ta lafiya sannan tana farin cikin zaman ta da shi, sannan a cikin kowane zama karatu ne bawa yake koya, dan haka ba ta cire rai da wata rana idan ta kai Intisar ko Zahra'u bango ba su mata feshin wuta da bata taɓa tsammani ba, amma akan Yusrah, wallahi ba za ta taɓa bari a ci zarafin ta ba saboda marainiya ce, idan aka ci zalin ta Allah ba zai bar su ma suma.

Dan haka ta aje duk wani tunani gefe ta sadda kanta tana murmushi tace "Bari mu fara jin ta bakin iyayen Yusrahn."

Da sauri uncle Sulaiman ya ɗago ya kalli Anna da ladabi wanda shi fa a gare shi wallahi hakan ya masa, dan yadda take cewa dama ba son auren ɗan ta da Yusrah take ba, haka shima a wajen shi wallahi ba son auren Yusrah da Bilal yake ba, dan ba ta yadda za'ayi ya dinga zuwa gidan nan har sau uku tana tarban shi da yatsinar fuska har ta buɗi baki ta ce ita bata san wata Yusrah a, sannan ya ɗauke ta a mai ƙaunar yarinyar nan, dan haka shi dai gaba ta kai shi gobarar titi a jos, hakane ma ta sa da Anna tayi maganar nan yace "Anna, Yusrah ai bata da wasu iyaye da suka wuce ku a duniyar nan a yanzu, ba wai ita ba mu kanmu mun sallama haka, sannan a ganina wannan ba sai kun nemi shawarar mu ba, wallahi duk abinda kuka yanke ya mana daidai, ba zamu ƙi haɗa jini da zuri'ar ku ba saboda halaccin ku gare mu, boss kuma ai aboki yake a gareni, zan bashi ƴa sai dai idan shine ba ya so."

Da fara'a aunty Fureira ta jinjina kai tace" Wannan gaskiya ne, nima abinda zan ce kenan, wannan bai kai sai an nemi shawarar mu ba, da mu da Yusrah duk kun isa ku yanke hukunci a kan mu wallahi bamu da ja."

Da jin daɗin haka Aba ya gyara zama yace" To Alhamdulillah, na ji daɗin haka sosai, dan haka wannan magana ta zama sirri tsakanin mu, dan har yanzu bamu san wa ye ya fito da wannan matsalar vidion ba, bamu da tabbacin na gida ne ko na waje, dan haka dole zamuyi taka tsantsan, mu barshi a iya mu kawai a ci gaba da shagulgula kamar yadda aka tsara su, safiyar asabar ta jibi kuma za'a ɗaura musu aure da izinin Allah, duk wani wanda zai yi gayyatar sa ya yi kan sa tsaye da sunan Aliyu Muhammad Anza, ni kuma zan wa Aswan ɗin ta sa gayyatar da taimakon Arif da kuma Mukhtar, ina jin dai sune sababbin abokanan da a yanzu za'a iya nuna shi da su, amma akwai wani abu ɗaya..."

Ƙurawa Aba idanu sukayi suna jira su ji me zai ce, ɗorawa ya yi da" Ƴar uwar ka Hindatu, ba zan gaji da baka haƙuri akan lamarin ta ba, ka yi haƙuri Suleiman, amma dole za ka je ka sanar da ita wannan sabon canjin, dan dolen ta ne ta sani, ka sani ni ba zan goyi bayan ka wajen yanke zumunci da ita ba, kamar yadda zan iya hukunta Yusrah bayan auren ta idan ta yanke zumunci da Goggon ta, dan haka ka same ta ka sanar da ita, ko da ba za ka faɗa mata da wanda za'a ɗaura ba yanzu, amma dai ta san an fasa da Bilal ɗin."

Ba dan ran aunty Fureira da uncle Sulaiman ya so haka ba ya ce ba damuwa zai je yanzu idan ya fita, dama kuma zai je can gidan shi ne saboda akwai ƴan uwan su na ƙauye da zasu shigo da yamma, shine zai je ya yi wasu ƴan gyara gyara da shirin tarban su, dan haka aka tashi akan wannan magana ba sai kowa ya ji ba, gwara masu baƙin ciki da wanda suka wargaza auren nata da fari su ji kwatsam kawai.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
10/06/2024, 10:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*64*



Martanin magana sai ɗan ƙauye, wanda ya san abinda yake yi yakan aikata lamarinsa ne sai dai ya fito, abinda yake faruwa da Anna da Intisar kenan, tun a lokacin da aka gama tattaunawar nan ta sameta da maganar a waya a nutse ta fayyace mata komai sannan ta yi kiran sunanta da babbar murya ta ce" Ki kwantar da hankalinki Intisar, dukkan tsanani yana tare da sauƙi, idan wani ya ƙi ka da wuni wani zai so ka da kwana, kin ji hukuncin da Babanku Chef ya yanke, ya maida abin a kan Yayanku, dan haka ko da wasa kar ki ɗagawa mijinki hankali a kan lamarin nan, ni na san da mahaifinki ya so tada zaune tsaye da ba zai bar ki a gidan nan ba, gobe in sha Allah tunda sassafe ki zo ki mata rakiya gidan su, sannan ki kula dan bata sani ba, hatta mijinki bai sani ba, idan ya ce ina zaki je kawai ki sanar masa biki ba'a daina ba sai dai baki san mijin ba, idan ya na son sanin waye mijin ya samu mahaifin ku."

Mamaki mai girman gaske ya kama Aunty Intisar ta ce" Anna, kenan biyun za'a aurawa Akhi jibi?"

Anna ta ce" A'a, idan ma zai auri Nabihat sai daga baya, su da suka ce zasu sanar da ranar da suka yanke har yanzu basu sanar ba? Allah ya sa haka shi ya fi zama alkhairi." Daga nan suka yi sallama.

Intisar ta jima zaune da wayar nan a hannunta cike da matsanancin mamaki, chef ne da kansa ya faɗa? Ikon Allah ikon gaske, wani farin ciki ne ya lulluɓe zuciyarta gaba ɗaya zulumin da take ciki na yanayin da mijinta ke ciki ya kau, a yanzu kam gaskiya ba zata tsaya damuwar Bilal ta dameta ba, ƙwarai Bilal abin tausayi ne, sai dai shi ai mai gata ne, uwa gare shi mahaifiya wacce ke da ikon zaɓa masa fari ko baƙi, ita kuma ɗayar ko oho, uhum lalle Hajia, da ace zata san wanene Imran da kunya ta hana mata sakewa a gabansu su sirikanta balle a kai ga maganar mutanen waje, ko da yake da yawa mutane kan danne laifin su su hango na wani, su dai zasu kasance masu yi mata biyayya muddin rai, dan ko ba komai jini mai ƙarfi ya riga ya haɗa, haihuwa ai ba wasa bace.

Daga nan ta shigewarta ta tsala wanka ta dawo ta yi kwanciyarta hankali kwance, sai dai duk irin yadda ta so ganin shigowar Yaya Mubarak abin ya gagara har sai da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login