Showing 93001 words to 96000 words out of 397328 words

Chapter 32 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70115

wannan da daɗaɗɗen albishir na tabbata da sai ya min kyauta, iyeah, kai da na ji daɗi tabbas da kin yi babban kamu yarinya dan kuwa yaron mai gida ne da ya gyashe mai gida, ke gani nan zuwa ki sanar min idan kin gudu ni ai gani nan haurowa."

Da wannan fara'ar ta haura ta tar da ita ɗakin, ta samu ta faɗa wanka a dole ta sauko tana jiranta dan kuwa yau sai sun zanta ta ji me yake faruwa, domin ita a daidai in har haka ta kasance wallahi.



*WAIWAYE*



*Tunda* Yusrah ta yi waya da aunty Fureira hankalin mutanen can ya tashi fiye da kima jin wannan abu da ya faru, a washe garin ranar da aunty Fureira ta so ta taho amma aka ce ta haƙura tunda akwai waɗanda ke son zuwa kowa ya kimtsa sai a tafi gaba ɗaya, hakan ya sa har aka kwashe kwana ukun nan na zaman makoki kafin a washe gari suka shirya tafiya, aunty Fureira tana ta gaggawa shiryawa saboda zasu taho ne su dayawa a motar da suka ɗauki shata, kawai ƴar dake tafiya ta ƙone da kokon da ta gama damawa yara zata bar musu su sha kafin su wuce makaranta. Wannan tashin hankali na ƙonewar yarinyar ya hana tafiyar da aunty Fureira sai sauran kaɗai suka taho.

Da suka sauka har ƙofar gidan su Yusrah maƙwabta ne suka dinga kula da su da ɗawainiya da su da kuma haɗa su da yaro aka kaisu asibitin da su Safwan suke, amma rashin sa'a sun tafi ne lokacin da masu dubiya ba sa zuwa dan ƙarfe 02:00 ta wuce, haka aka ce sai dai su dawo da yamma su gan shi, haka rai a jagule suka lallaɓa suka tafi gidan wani ɗan uwan su da yake nan garin shi ma, anan ne ma suka baje hirar Goggo ana ganin ya yi wuri a ce ba'a same ta gidan ba duka kwana uku da rasuwar, hakan ne ma ya sa suka yi ta magana akan rashin kirkin ta da masifar ta.

Da yamma duk suka shirya zasu koma asibiti daga nan su wuce gidan su Yusrah su kwana biyu kafin su tafi a ƙalla suma su karɓi gaisuwar ƴar uwar su, amma sai Aminu da suka sauka gidan shi ya hana su tafiya ya ce su kwana anan tunda dai akwai ɗaki, maza biyu da suka taho kuma ai ko soro sun kwana, amma bai kamata su je can su kwana ba bayan ga nan ɗin, haka kuma ya roƙi alfarmar su jira shi har zuwa washe gari ya sa matar sa tayi girki sai su je duka gaba ɗaya tunda shi ma bai san abinda ya faru ba dan bai jima da komawa nan yana sana'ar dafa indomie da ƙwai a bakin babbar tasha ba. Aka ce wai ba'a ƙin ta mutane, basu gagara yi masa wannan alfarmar ba, *sai dai* jinkirin da sukayi zuwa washe gari ya sa suka je basu samu Safwan ba, sun jima basu bar asibitin ba suna ta tunanin wannan wane irin abu ne to? Yanzu ya zasuyi? A duk cikin su ba wanda ya san gidan Goggo Hindatu, gashi suna ta kiran aunty Fureira ba sa samu, kuma ita ƙaramar waya gare ta bare ko ta WhatsApp a same ta, haka suka koma gidan Aminu suna ta jimamin lamarin da tunanin gobe ma za su koma, idan basu same shi ba kawai zasu koma su sanar da sauran dangi abinda ke faruwa.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*25*



Tabbas Elhaj Anza shine babba tushen wannan ahali kuma wanda ya yi fafutuka ya tara musu abun duniya, sannan a kwana a tashi bayan ba ran shi Elhaj Aliyu ya gaje shi har ma ubangiji y sa ya fi mahaifin nasu nasibi, dan arzikin da ya mallaka ya fi wanda mahaifin shi ya mallaka sau ninkin ba ninki, sai dai duk da wannan kawu Hamat na ɗauke da wani irin jin kai da izza da ya fi na Yayan nashi. Dan yanzu haka da suke zaune suna fuskntar juna akan wasu lafiyayyun kujeru dake cikin ofishin na Aba, sanye yake da wata ɗanyar farar shadda da ya zuba mata ɗinki irin dai na matasa kamar yadda ya saba, kuma kamar kullum babu hula a kan shi sai agogo da takalmi da suka dace da ɗinkin shaddar masu bala'in tsadar gaske.

Ƙafar sa ɗaya take akan ɗaya yana ɗan jinjinata, hannun shi dake tangale saman guiwar sa kuma yana riƙe da gwangwani lemu mai sanyi yana sha, cike da shan ƙamshi da jin yanzu shi ma yana daf da zama wanin da sai ya fi Yayan sa shahara da yin suna ya ɗan murmusa yana kallon Aba da shima yake kallon shi yace "Taron ya gudana da kyau, saura na gaba da za'ayi tsakanin ƙasashe."

Murmushi Aba ya sake yi yana jujjuya alƙalamin hannun shi, wasu lokuta sai ya ji kamar ƙanin nasa Hamat zai bashi mamaki, sai kuma ya gaggauta kawar da wannan mamakin ta hanyar tuna su fa *jinin Anza* ne, tsabar miskilanci da iya hura hanci mahaifiyar su ke yawan faɗa cewa haƙuri ta yi da shi sosai, amma kuma duk da haka wani lokaci ya kan ɗan ji kamar irin girman da ƙanin sa Hamat yake bashi ya ja baya, a da baya iya haɗa idanu da shi, ba ya masa magana murya ba ta ɓari na girmamawa, amma... Yanzu sai ya ga yana kallon shi ido cikin ido, da wani ji da kai haka da kamar dai irin kai ma kai ɗin nan ne.

Iska ya feso daga bakin shi yana kawar da tunanin ta hanyar maye gurbin sa da ayyana _"Wataƙila yau da gobe ne, ko ɗan da ka haifa idan kuna fahimtar junan ku, wata rana zaku zama abokai ne dama."_

Da wannan tunanin Aba yace" Da kyau, fatan nasara a na gaban ma, amma sai dai na ga dreban ka Sani jiya, sai yake ce min ba tare kuka tafi ba, kuma a sanina ba kwa kowace irin tafiya ba tare sa shi ba."

A taƙaice kawu Hamat yana sauke gwangwanin lemu daga bakin shi yace" Ummm!"

Bai sake cewa komai ba, jingina Aba ya yi a jikin kujera cike da ɗaure fuska dan amsar da ya bashi bata masa ba yace" Me ya kawo hakan to? Ina fata dai ba koran sa ka yi ba? Dan kasan ai na jima da haɗaka da shi."

Wani irin ɓoyayyen kallo mai ma'anoni kawu Hamat ya ma Aba, cike da takaici da son danne abinda ke ran shi ya girgiza kai tare da cewa" Um um! Na tafi tare da Mani dreba ne, dreban ambulance na asibiti."

Da kallon tuhuma Aba yace" Komai yana tafiya daidai a asibiti?"

Amsawa ya yi da" Komai lafiya lau."

Shiru Aba ya yi yana juyawa a hankali kan kujerar sa yana jira ya ji me ye dalilin ziyarar kawu Hamat ɗin wanda ya san dalili ne mai ƙarfi tunda haka kawai ba ya zuwa ko gidan sa bare office, sun fi haɗuwa a gidan shaƙatawa na Aba ɗin idan za su tattauna wata maganar. Shiru Aba ya tabbatarwa da kawu Hamat ya gama masa tambayoyin kenan, shi kuma zai iya fara nasa, dan haka a tsanake ya sauke ƙafar sa ɗaya tare da zura hannu ya aje lemun hannun shi kan table ɗin glass dake tsakiyar su da taushin murya sosai da ya fi na ɗazu yace "Akhi, my son na zo nema, yana ina dan Allah?"

Da ɗan murmushi a fuska Aba ba tare da mamakin komai ba face ganin yadda su dukan su Aswan ɗin ke wahalar da zuƙatan su dan begen shi, shine babba a ƴaƴan Anza guda uku, saida suka shekara uku kafin Allah ya azurta su da samun Aswan, har sun fara ba wa kan su wahala wajen neman maganin haihuwa, sai ubangiji ya dube su ya basu shi a farko, tsakanin sa da Humed kuma shekara biyar ce zuwa ta shida, hakan ya sa sukayi ɗawainiya da Aswan, suka rene shi da gata mai tsananin gaske da kulawa ta ban mamaki, sannan har ka rasa wa ya fi son Aswan ɗin, Anna ce? Ko Aba da ba ya da alkunya ko kara game da lamarin ahalinsa? Ko kuma shi kawu Hamat da ya fi nuna ya fi son Aswan akan ƴaƴan sa ƙwaya biyu rak da ya haifa a duniya?

Duk da Aba ya san wa yake nufi, amma sai ya sake maimaitawa da cewa "Aswan wai?"

Sai kuma ya yi murmushin da ya saka kawu Hamat ɗin sake marairaicewa a fuska, ƙwarai yana jin Aswan har zuciyar sa, kuma Allah ne ya dasa masa soyayyar sa tun haihuwar sa, yana jin Aswan fiye da yadda yake jin kan sa, yana jin zai iya fansar rayuwar sa akan Aswan, yana jin ina ma Aswan ɗin nan nasa da a shekarun baya idan ya ɗauke shi a hannayen sa yake wangale masa bakin sa da babu haƙora har yana jin babu wanda ya kai ɗan sa iya dariya a duniya zai ci gaba da zama masa a hakanan? Har kuma yanzu da ya zama magidanci bai ƙi a ce Aswan na daf da shi ba, ta yadda kowace rana za su haɗu sau adadi marar iyaka, ya ji jikin ƙaramin yaron sa da a baya suke tare masa duk wani haɗari yanzu shine ya ƙarfafa haka, har yanzu yana son kallon fuskar Aswan ɗin sa, yana son shi da ƙaunar shi. *Amma* bai san me ke shirin faruwa da su ba duka, abinda yake faruwa a yanzu idan ya ci gaba a haka, to fa za'a kai ƙadamin da kowa zai ficewa kowa a rai ne, dan shi kan shi yana da tabbacin son da Aswan ɗin ke masa.

Kamar zai yi kuka yace "E Akhi, kwanaki kaɗan ya same ni a office asibiti, ko zama fa bai yi ba ya ce min zai je ya dawo, Akhi ya ce zai zo gida amma har yanzu shiru, na kira wayar my son har kamar zan yi hauka, amma Akhi lambobin sa basa shiga duka..."

Langaɓar da kai ya yi yace" Please Akhi ka cire shi a aikin sojan nan, sam bai dace sa shi ba, bai dace yana hanamu ganawa da ɗanmu ba."

Dariya Aba ya so ya yi ganin yadda ƙanin nasa ke fin sa neman zaƙewa, bayan kuma kafin zuwan nan nasa ya same shi ya gama waya da masu tsaron gidan sa ne har ma da wanda ya kan tuƙa shi ranar da ya so hakan fa amma, sam babu wanda ya ce ya ji daga gare shi bare ma a samu wata makamar. Duk da kuwa masu tsaron su ai sun so su ce dattijon nan ya kwantar da hankalin shi Aswan ya bar bashi wahala, duba da shirin da ya fita da shi tun ranar daga gida, su kam indai sun canka daidai to oga iskanci zai fara kwanan nan gaskiya.

Ɓoye ta shi damuwar ya yi da jin daɗin yadda ƙanin nasa ya damu da ɗan sa yace "Hamat, me ya sa za ka damu har haka? Na faɗa maka sai Aswan ya bar aikin soja in dai ina raye saboda bai dace da shi ba, kuma yanzu haka ma hukunci yake karɓa daga hukumar ta su na tsawon watanni ba tare da ya saka kaki ba, zan san duk yadda zan yi na hana shi komawa hukumar nan, wannan alƙawarina ne, ka ji?"

Wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana tsare Aba da idanu yace" Hankalina ya tashi sosai da wani abokina ɗaya ne daga cikin jami'an da suke gadin babban prison ya ce min ya ga Aswan ne ko me kama da shi? Na ɗauka aikin ne ya kaishi har shiga gurin da ko numfashi bai kamata mu bari ya yi a cikin gurin nan ba."

Ɗan zaro idanu Aba ya yi yace" Aswan ɗin? Babban prison fa? Shi ko me zai kai shi can? Bayan ko ziyara ba'a zuwa musamman ma idan ba'a tabbatar da laifin mutum ba."

Ta ƙasan idanu ya dube shi yace" Nima haka na faɗa masa ai, kawai nasan kama ce, kamar ma ba zatayi daidai da ta my handsome guy ba."

Murmushi sosai Aba ya yi yana girgiza kai yace" Kai ko, na ga yadda za ka yi idan na masa aure nan da watanni kaɗan, shin za ka dinga zuwa gidan surukar ka ne dan ganin taƙadarin yaron ka kullum? Ko kuma a gidan ka ma zai zauna?"

Ƴar dariya ya yi cike sa shaƙiyanci yace" Matar sa ba za ta hanani ganin ɗan da idan ban gan shi ba juwa take kamani."

Dariya duk suka saka gaba ɗaya suka ci gaba da ɗan taɓa hira, kafin daga bisani kawu Hamat ɗin ya miƙe da niyyar tafiya, sallama sukayi ya juya sai dai kafin ya fita Aba da ya tuno da wani abu yace"Hamat, ya maganar majinyatan nan kuwa da iftila'i ya faɗa? Shin ana kulawa da su ɗin kamar yadda na ce ayi?"

Zuba masa idanu kawu Hamat ya yi da fari, sai kawai ya yi murmushi mai kama da kuka saboda jin zafin maganar wai *yadda na ce ayi*, yadda ya ce a yi ko? Kuma sai su yi ɗin bayan su ne da wahala? Hmmmm! Gyaɗa kai ya yi yace" E Akhi, ana yi kamar yadda ka buƙata."

Ɗan gyaɗa kai ya yi shi ma yace" Da kyau, amma ka dinga bin ba'asin komai, sannan kana saka idanu a asibitin nan da kyau, dan yanzu haka akwai wani ƙaramin yaro da muka samu shi ya rasa wannan kulawar."

Jinjina kai ya yi cike da takaici ya amsa da" In sha Allah za'a dinga kula."

Daga haka ya sake ce masa sai anjima ya fice yana jan tsaki da ayyanawa a ran shi _" Komai dai ya ce da kyau, da kyau, to ba kyau, za ka gane nan gaba kaɗan."_

Haka ya shiga mota Sani ya ja shi yana mitar har akan waɗannan matsiyatan majinyatan ne zai wani ce masa ya saka ido? Bayan ya gina asibitin ya damƙa ragamar kula da ita a hannun shi, babban ma dalilin da ya sa kenan ya fara jin haushin Yayan nasa, akan me dan ya karanci likitanci zai wani gina asibiti sai ya ce ya kula da ita? Ina ma laifin ya mallaka masa ita halak malak har abada? Amma ya haɗa shi da faman yi wa mutane wahala, kamar wani ƙasƙantacce haka zai dinga kai da kawo yana duba ƙazanta kala kala da raunika iri iri, daga ƙarshe nawa ake biyan shi? Bayan ma karatun shi sai da ya fita ƙasar waje ya yi shi, a dai ɓangaren tiyata ko yanzu akan yi masa waya daga wata ƙasar dan ya je ya yi tiyata, kuma dake jajayen sun fi baƙaƙen sanin darajar su, haka za ka ga ana masa magiya shi ko yana basarwa, sai adadin kuɗin ya masa sannan zai saka lokacin da zai shiga jirgi ya sauka ƙasar dan yin aikin da bai wuce awa ɗaya ko ƙasa da haka ba.

*Yana* fita Aba ya kira Chef da dama yake da niyyar kira, zuwan Hamat ɗin ne ya dakatar da shi daga aikata hakan, bayan sun gaisa Aba yake ce masa "Chef, ko kasan inda yarona yake kuwa? Ina fata dai ba wata dabarar kuka min ba kai da shi kuna ha'intata? Dan yanzu ake sanar da ni an ga mai kama da shi ko ma shi a babban prison."

Ba ƙaramar dokawa ƙirjin Chef ya yi ba saboda bala'in tsoro, dan in dai Aba ya san da maganar aikin sirrin nan ba fa lallai su wanye lafiya ba, hasalima zai iya sake daƙile Aswan ɗin, bayan kuma yaron ya yi doguwar tafiya kafin ya kai inda yake yanzu. Cike da basarwa Chef yace "Aswan ɗin? A prison kuma? Sannan ma babba?"

Amsa Aba ya bashi da "E, haka aka faɗa min nima."

Murmushin dole ya sakar masa mai sauti yace "Elhaj, ai ko AA na sanye da kaki zuwa wajen nan haka kawai ba nasa bane, bare kuma yanzu da ya ajiye hular sa na wani lokaci, ina ga dai kamar ce, amma kai wa ya sanar da kai?"

Cike da rashin damuwa Aba yace "Hamat ne yake sanar da ni, ni kaina hankalina ya so tashi, to amma kuma na ga me zai kai shi can? Ganin wani? Dan Aswan dai nasan ba zai aikata laifin da za'a kaishi can ba ban ma sani ba."

Tsamm! Chef ya yi yana ambatar sunan kawu Hamat a zuciyar sa, sai kawai yace ma Aba" Ka kwantar da hankalin ka wallahi, to amma ka jila ba ka ganshi bane da kake tambayata inda yake?"

Da irin son ya shashantar da lamarin kar ya fara damun sa yace" Kamar kwana uku dai kenan, ba wanda ya ce ma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login