Showing 270001 words to 273000 words out of 397328 words

Chapter 91 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69990

damu da tunanin sanin daga ina take ba a irin wannan shigar, dama jiranta yake yi ta kawo masa abincin ta tafi ko ya samu ya ga Sakina su ɗan yi daren nan tare kafin gobe da safe ya je gidan Yayansa ya samu Yusrah su zauna su fahimci juna, domin maganar fasa aurenta ya gama duniya ai, har nan aka zo aka sanar masa sannan ya ga vidion shi ma , tunda ya ga haka hankalinsa ya kwanta ya ƙara kwantar da hankalinsa yau ya wuni yana barcin hutu da kwanciyar hankali da samun salamar zuciya, dan kuwa duk wani abu dake damunsa ya kau sai target ɗin sa na gaba shine ya samu ya karkato da hankalinta kansa ya rarrasheta su fuskanci juna su rungumi juna su yafi juna su rayu da juna.

"Mon amour ya ya jikin? Bb wannan ai ka warke, mu yi tafiyarmu gida kawai ko?" Ta faɗa cike da kissa tana kashe murya sosai.

Kallonta ya yi sheƙeƙe kafin ya ɗauke kansa, gaba ɗaya a yanzu bata yi masa kyau, kuma ko me zata yi sai ya ji haushinta yake ji maimakun ta birge shi, wai su tafi, su je gidan uban wa ita da ƴar ta su hana shi sukuni? Kai shi fa da ya tare a nan harda takurar matar nan da ƴar ta, sam basu da hankali, basu san su bashi lokaci nasa ba, ko da yaushe cikin takura masa, ga yarinyar nan sam bata da tarbiyya, rashin hankalinta ya yi yawa, bata jin magana ko kaɗan, ihu baya tsorata ta, ka yi mata faɗa ma a banza wallahi, shi yasa daga ita har uwarta suka fita a ransa gaba ɗaya, gaba ɗaya ji yake yi baya son ganin su sai dan sun zame masa balaki suke manne da shi.

Murya a haɗe ya ce" Ban warke ba babu inda zan je, ki yi ki koma gida ai kin ga dare ya yi ko?"

Ta bishi da kallo dan a nan ya yadda tawul ɗin ya ɗauki gajeran wandonsa ya saka ya zo ya zauna bakin gadon yana janyo wayarsa tamkar ba mutum bace ita bai wani bata daraja ko kaɗan ba, kai ta ɗauke tana faɗin" Dan na yi dare ne ranka ke ɓace? Daga gidan Akhi nake fa, ba ka san yau aka ɗaurawa ɗanka aure ba kai ma hala? Zuwa muka yi muka amshi amaryar, shi yasa ka ga na jima."

Ɗagowa ya yi ya zuba mata ido, a zuciyarsa ya ringa ayyana _'Anya ta san me take faɗa kuwa? Ɗana? Aure?'_

A bayyane ya ce" Wa ye Akhi?"

Da mamaki ta kalle shi, duk duniya waye yake cewa Akhi sama da Aliyu Anza? Da mamakin nan tace" Wai honey lafiyarka ƙalau kuwa? Wa ye Akhi kuwa bayan Aba? Aliyu?"

Ransa ya fara tafasa da raininta, rai ɓace ya ce" Idan kika bani amsa sak ai ya fi da ki nemi raina min hankali ki ce wani wa ye Akhi bayanshi, aure? Wani ɗana? Humed ya ƙara aure?"

Ɗan zuba masa ido ta yi tana jin can ƙasan zuciyarta na son tayar mata da hankali, a yanzu tsakaninta da shi motsi ma idan ta yi abin ya yi tashin hankali ya rufeta da faɗa ne, ya zama bata isa ta yi ƙwaƙwaran motsi a kusa da shi ba, ko me ta yi laifi ne, abu kaɗan ke zama babba, kome ƙanƙantar laifinta kuwa baya yi mata uzuri sai kace ba mijinta ba da ya riƙe mata kan maciji take wasa da jikin.

A sanyaye ta ce" A'a ba Humed ba, Aswan."

Sake kallonta ya yi da mamaki ya ce" Kina nufin, Aswan ɗina ne ya yi aure yau bani da labari? Kina da hankali kuwa?"

Irin yadda ya yi maganar a kausashe ya sakata taɓe baki tana tunanin shima abin ne zai ɓata masa rai ace Aswan ya yi aure bai ji ba duk irin yadda yake ikirarin shine uban Aswan ba Aliyu anza ba, dan haka ta ce" Wallahi shi dai, ai in faɗa maka Tidin ma bata da labari sai da aka ɗaura ta ji a gari, wai yarinyar da wani ne zai aureta ya fasa shine kawai shi Akhi ya aurawa Aswan ita."

Ƙafafuwansa ya sauko ƙasa, mamaki na neman tsayar da bugun zuciyarsa, What? Dama Aswan yana da maɗaurin aure sama da shi a duniyar nan? Ba Aswan ba kaf ƴaƴan Yayansa ai shine alkalin su, shine tashi ɗaya zai ji wannan maganar? Kai ko dai bata gane da kyau bane abinda ake nufi? Dan haka ya matso kusa da ita sosai yana kallonta ya ce" Kin kuwa san me bakin ki ke faɗa? Aure? Wani irin aure? Da wa? Kai tsaye haka? A kan me ni ban sani ba?"

Hannaye ta watsa ta ce" Na san a kan me ya ƙi faɗa maka, ko yana tunanin zaka yi masa baƙin cikin abin ne? Ni dai na san an ɗaura masa aure dan yanzu yanzu aka kawo amaryar sannan na fito, ko Yusrah ko me sunan amaryar..."

Fuskarta da bakinta ya ƙurawa ido tunda ta ambaci sunan Yusrah har ya samu hankalinsa ya ɗan dawo kaɗan ya dubeta bayan ya riƙo fuskarta da ɗan ƙarfi ya ce" Ke, nutsu, ki daina min magana kina kame kame, wacece aka aurawa son? wace Yusrah ce?"

Ta ɗan zuba masa ido, irin yadda ya riƙo ta ya sa ta tuna kwanaki wani suna da ya ringa kira exactly irin sunnan nan ne, dan haka ta saka hannunta ta ɗan riƙe nasa dan ƙara matse mata kumatu yake yi, ta ce" Yusrah aka ce sunanta, da a gidan nasu take ma, ance wani Bilal ne ya so aurenta sai ya fasssssssssss."

Fassss ɗin ta ta ta ɗauke ne sakamakon fatsa mata mari da ya yi tankaɗeta mareta, lokaci guda ya hankaɗata baya yana miƙewa jikinsa ya kwashi rawa yana faɗin "...




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
11/06/2024, 22:19 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍??🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*67*



Ƙarya kike dan ubanki, Aswan ba zai taɓa aurar Yusrahta ba, domin Yusrah tawa ce, Yusrah haramun ɗin sa ce, Yusrah haramun ɗin duk wani namiji ce, ke ba namiji kaɗai ba hatta mata ƴan luwaɗi Yusrah ta fi ƙarfin su, wallahi ko ƙanin ta uwa ɗaya uba ɗaya kishinsa nake a kan Yusrahta balle Aswan, ki dawo hayyacinki ki faɗa min abinda kika ji kafin in halaka ki dan ubanki!"
Ya ƙarashe yana nufarta gadan gadan.

A haukace ta shiga rarafawa tana ihun a taimaketa haɗi da kuka, faɗi take yi" Aban joli me yake damunka ko ka haukace? Me ka ke faɗa? Na shiga uku zai kashe ni."

A guje nurse biyu suka shigo da vigil guda dan vigil kwana suke yi suna zagaye a asibitin, nurse kuwa su suka fara jiyo muryarta sama sama suka nufo ɗakin, kama shi suka yi da ƙyar suka ƙwace ta a hannunsa suna afkin
salallami da kiran sunansa ko ya dawo hayyacinsa, amma kamar abin ƙwaƙwalwa ya taɓa masa ihu yake yana faɗin" Yau sai na kasheta, ita ba ita ke kawo min gulmar mutane ba? Har ta fara kawo min ƙarya ko? Dan ubanki abinda kike faɗa haramun ne, ba za'a taɓa aikata shi ba, Yusrah tawa ce ni kaɗai babu namijin da zai mallaketa sai ni, duk ubanda ya ce kuwa zai mallaki Yusrah wallahi sai na ga bayansa ko ubana Anza ne ya dawo duniya balle Aswan."

Ganin abin ba na wasa bane ya sa suka ɗirka masa allurar barci har biyu suna riƙe da shi yana ta fizge fizge kafin abin ya ci ƙarfin sa barci ya kwashe shi, tana kallo a maƙure a gefe suka saka belt ɗin nan na abin gado da ake ɗaurawa marar lafiyan dake iya jima kansa rauni ko ya jima wani suka ɗaɗɗaure hannayensa da ƙafafuwansa sannan sauran suka tafi aka barta da docter da Sakina wacce ke riƙe da kayan da aka masa aiki da su hankalinta tashe tana kallonsa da tunanin lalle lamarin Yusrah ya fara bata tsoro sosai wallahi, anya kuwa lafiya ? Anya wannan abin ba ya wuce tunanin mutane ba?

Docter ta kalli maman joli a tausashe ta ce" Madame, ki yi haƙuri ki daina kuka sannan ki kwantar da hankalinki, ya kamata ki tafi gida ki huta, sannan idan da hali a sa a ringa yiwa docter roƙon Allah, kin san lamarin rayuwar nan yadda ya zama, a yi ta yi masa sadaka ko menene in sha Allah zai yi sauƙi, mu ma a nan yanzu kuma zamu karkata ɓangaren psychologique mu yi dukkan abinda ya dace, in sha Allah ko menene za'a gani sannan za'a shiga yi masa maganinsa, amma yanzu ya kamata ki yi nesa kaɗan dan kin ga ya fara neman lafiyarki."

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta matso kaɗan tana kallonsa da wani irin kallo mai tafe da tarin ƙiyaya da jin haushinsa na furucin bakinsa, kai ta ɗauke ta yiwa likita godiya ta juya ta fita bayan ta ɗauki jakarta, Sakina ta rakata da kallo kamar ta kirawota ta faɗa mata babu fa maganar roƙon Allah da tunanin an shiga gabansa, shi fa ya kai kansa ya baro ta faɗa mata abinda yake faruwa sai dai ta san idan ta faɗi haka abin na iya zama matsala, dan haka ta kame bakinta ta ci gaba da aikinta duk da irin yadda jikinta ya yi sanyi.

Ita kuwa tana zuwa cikin motarta bayan ta tayar ta fashe da wani irin kuka mai zafin gaske ta daki sitiyarin motarta da ƙarfi ranta na tafarfasa da abinda ya faru, a bayyane take faɗin" Yusrah? Wacece Yusrah? Saboda ita har ka mareni yau? Saboda ita ka ke faɗin sai ka kashe ko waye? Saboda ita ka ke cikin wannan halin? Ni na san ba wani maganar aljanu ko asiri, a hayyacinka ka ke son zuciyarka ne ke hana ka ganin kowa da kima ko tausasa abu a gabanka, Hamat wallahi wallahi baka isa ba, idan kuwa ka nace ni ɗin nan sai na zamo maka mugun mafarkin ka, dan wallahi sai na tsiyataka tasss sannan in miƙa ka hukuma da dukkan shedar da nake da ita, ɗan naka kaɗai ya isheka bala'i a garin nan balle ubansa har zuwa hukuma, idan ka yarda a kan maganar nan ka ɗaga min hankali wallahi sai ka dawo ɗan sholishon bakin hanya da bashi da wata daraja ko a wajen ƴan iska irin sa, Hamat ni da kai dan shege ka fasa!" Daga nan ta ja motarta ta yi tafiyarta.


*AA ANZA*


AA kuwa bayan an gama kai amarya an watse yana asibiti wajen Safwan da docter Siddik ya ƙi saki yau ya ce sai gobe saboda sai gwajin da aka masa sun fito gaba ɗaya ya yarda cewar eh yana iya zuwa gida sannan zai sake shi yasa uban ya zo dan yau tunda safe bai ganshi ba sai yanzun da ya zo wajensa, har ya fara barci ya tashe shi yana bashi abinci a bakinsa har ya gama ya masa bruch ya maida shi ya lulluɓa masa bargo sannan ya zauna a hankali ya zuba masa ido da wayarsa a kunnansa yana sauraron iya shegen da Arif ke masa.

Ƙasa ƙasa sosai ya ce" Freind ka faɗa min gaskiya, an kaita gidan Anna?"

Arif ya kalli Muktar yace ce" Abokina anya mutumin nan ba son abinsa yake yi ba dama muke nan muna son mu rarrashe shi?"

Muktar ya yi dariya ya ce" Nima irin yadda ya amshi abin nan ba gardama ya bani mamaki abokina."

AA ya yi ɗan yi tsaki ya kashe kiran ya ajiye wayar gefe a hankali ya ɗan dage girarsa sannan ya saki, sai kuma ya cije leɓensa na ƙasa sannan ya saki yana sakin ɗan murmushi haɗi da girgiza kansa, ya sake zubawa Safwan ido sannan ya ɗauke ƙasa ƙasa ya furta" Da aka faɗa maki wai an aura maki ni, me ki ka ce *jelata*?"

(☹️☹️☹️☹️☹️ ita dake cen tana kukan da aurenka gwara ta sha wiwi?😏😏🦧)

Sai kuma ya sake yin murmushi yana ture abin a ransa ya gyara zamansa da kyau ya shiga tofawa Safwan adu'ar tsari, har ya gama sannan ya miƙe ya danna abinda ke shaidawa ana buƙatar likita a ɗakin, jim kaɗan nurse ɗin sa ta zo, ya bar mata shi ya tafi gida da niyyar gobe da sassafe in sha Allah zai zo ya ɗauki abinsa kamar yadda suka yi da Docter Siddik.

Yana ƙarasawa gida wayarsa na ɗaukan ringin, ganin sunan Aba sai da zuciyarsa ta amsa, a hankali ya ɗaga wayar ya yi sallama kansa a sadde, Aba ya sauke ajiyar zuciya shi ma a tausashe sosai ya furta" How are you?"

Aswan ya lumshe idanuwansa yana jin ƙaunar mahaifinsa na ratsa dukkan gaɓɓan jikinsa, a sanyaye sosai ya ce" I miss you Abana."

Aba ya yi ɗan murmushi a hankali ya ce" Jikan Anza baka jin magana."

Da sauri ya ce" Na tuba Abana, ka yafe min"

Aba ya yi ɗan tsai sannan ya ce" Na yafe maka, sai dai zan daina fushi idan ka zo gobe da safe na haɗaka da matarka na maku nasiha, sannan ka buɗi baki ka sanar min abinda yake faruwa, Aswan ni na haife ka, sai dai in faɗawa wani ya waye kai, ka kula ka sani na san kana aikata wani abu mai mahimmanci da ya hana ka amsar ayyukan da na baka, kuma ka san na san baka ajiye kaki ba, ina binka a hankali ne dan a yanzu ka kai mizanin zaɓar hanyar ka, sai dai idan ina raye nine gaba da kai Aswan, ko me ka ke yi ka yi ƙoƙari ka ajiye gefe ka sanar min komai, idan baka yi haka ba a gobe ba zan daina fushi ba da gaske nake, ba zan daina fushi ba ka ji?"

Jikin Aswa ya mutu murus hankalinsa gaba ɗaya ya tashi, har Aba ya katse kiransa bayan ya ƙara tabbatar masa wallahi da gaske yake ya kasa taɓuka komai sai ido da ya zubawa waje ɗaya, ya salam.

Me zai faɗawa Aba a yanzu? Ta ina zai fara?
Idan ya faɗa masa abin ba zai taɓa lafiyarsa ba?
Idan ya sanar masa ba zai taɓa zuciyarsa ba?
Idan a yau ya sanar masa abinda ƙaninsa ke aikatawa ya ya zai ɗauki abin? "Ya Allah, na shiga uku, ya ya zan yi? Aba dan Allah ka rufa min asiri ka bari in na gama komai ka ji..." Ya faɗa a saman leɓensa zuciyarsa na sake bugawa da tarin tsoron goben, dan bai san ko zai iya zuwa gidan ba ma balle har ya fuskanci Aba, abu ɗaya ya sani in dai suka haɗu da Aba to kuwa sai ya sanar masa koma menene.


*GOGGO HINDA*

A gidan Goggo Hinda abu kamar mai kamun iska haka ta ringa yi musu tijara kala kala, sai ta koro da bala'i sai kawai ta fashe da kuka ta ɗora hannayenta saman kanta tamkar wacce aka faɗa mata rasuwar iyayenta da sabunta, abin ya ɗagawa Safiya hankali ta zuba mata ido, malm kuwa ya balbaleta da faɗan shi fa baya son fitina ta faɗi damuwarta ta ƙi faɗi ta saka su a gaba da kuka goɗai-goɗai da ita, to wallahi ahir ɗin ta ta bashi lafiya dare ya yi ya sa sai shigowa ake ana tambayar lafiya?

Ama abun mamaki zuciyarta ta ƙi bata damar kwantar da hankalin nata, gaba ɗaya duniyarta a hautsine take, kuka take yi ba ji ba gani, ƙirjinta zafi yake yi mata sosai, a zaune take har sai da ta fara wani irin amai jikinta ya kwashi zafi sosai suka kwasheta suka nufi asibitin gwamnati da ita dan abin kamar mai dafara sai bige bige take da kuka tana riƙe ƙirji, sosai abin ke nuƙurƙusarta har dai Safiya ta ga abin na nema ya zama tashin hankali na gasken gaske ta sanarwa babansu abinda yake faruwa.

A tsaye sai da ya zauna dan firgita da jin wai abinda ya haɗawa Hinda ciwon nan kenan, tsoro ya kama shi mai tsananin gaske, a tsugunen da yake ya rasa ina zai kama, me zai ce, ba shiri ya miƙe ya ƙara kallon Safiya tsoro na sake kama shi na lamarin uwarta da ita ɗin da kanta, muryarsa har rana rawa ya ce" Yanzu kina nufin kukan nan da ta kwana yi, da riƙe ƙirji dan ƴar ƙaninta ta samu miji na rufin asiri ba'a wulaƙantata ba, Allah ya ɗaga darajar ta ne?"

Tsuru tsuru ta yi ta kasa bashi amsa, ita fa ta faɗa masa ne dan ya je ya yi rubutu ko na dangana ne a ba Babarta, domin shi ɗin ai malami ne babba, duk wani hatimi na kasuwa da na tsari shi ke rubuwata Babarta, mahaifiyarta ta sha faɗin in ba dan sirrin dake hannayensa na addu'o'i da tuni ta rabu da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login