Showing 165001 words to 168000 words out of 397328 words

Chapter 56 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70081

*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
27/05/2024, 10:25 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*43*




Tunda docter ya bata takardun Safwan ya yi mata bayanin ciwon yaron da tafiyar da aka ɗora kanta ta yi shiru kanta a ƙasa tana duba takardun ta kasa ɗagowa ta tofa ko da a ne har sai da docter ya ambaci sunan ta sau biyu sannan ta ɗago idanuwanta sun ɗan cenja kalla tana fitar da ɓoyayyen huci tana kallon shi, Docter Siddik ya ce" Sister Are you ok? Ko ba zaki samu damar yin tafiyar ba? Ina nufin ba kya son tafiyar. "

Yusrah ta yi gaggawar girgiza kai tana sake duba sunan, wato SAFWAN ASWAN ALIYU, Safwan ɗin kaɗai da ciwon bayan suka yi kama da nata Safwan ɗin, amma wannan sunnan mahaifinsa daban, haka na kakansa, sannan wannan har za'a fita da shi waje ɗan masu kuɗi ne ga dukkan alamu, kai ya Allah, ya Allah, Safwan kana ina?

A sanyaye ta yi ɗan murmushi ta ce" A'a Docter, sunan ne irin na ƙanina, in dai Yaya Mubarak ya yarda aunty ta yarda zan je ko ina ne ko dan sunan nan."

Docter ya yi murmushi ya ce" Ma sha Allah, ai in dai Mubarak ne mun yi magana, yace zai shigo ma, ina jiran shigowar tasa ne yanzu haka."

Yusrah ta gyaɗa kai, ta miƙe da takardun a hannayenta dan dole sai ta je ta ƙara dubawa a tsanake, gashi ance tafiyar nan da kwana biyu? Lallai dole zata je ta sake nutsuwa ta ga dukkan abinda ya dace ta duba na taimakon da ake iya ba mai irin ciwon a cikin tafiyar nan gaba ɗaya, a hankali ta juyo ta ce" Docter, yaron a wani ɗaki yake in je in ga yanayin jikin nasa?"

Docter dake hankalce da sanyin jikin da ya sameta ya yi murmushi ya ce" Sister yaron yana wajen babansa a gidan, ba ma lallai ki ganshi ba wataƙila sai a jirgi ko idan ba lafiya, zaku yi tafiyar ne a ɗaya daga cikin jiragen da kamfanin kakan yaron ke haya dan jigilar mutane da kuma kayan sana'a, kar ki damu yaron fa da sauƙi sosai, ya samu kula sosai hakan ya sa ciwonsa yayi gaggawar warkewa, yanzu haka za'a tafi da likita a kusa ne saboda Allah kaɗai ya san gaibu, kuma in dai da wanda ya san aikinsa a kusa ana kyautata zaton samun sauƙin wani abin, duk da ba'a isa a hana abinda Allah ya hukunta ba."

Yusrah ya gyaɗa kai a hankali ta furta" Allah ya bashi lafiya."

Ta juya ta fito takardun nan ƙamƙam a hannayenta, sai ta kula da irin kallon da ma'aikatan suka bita da shi, wa'inda ke harkar cika takardar ganin likita, kallo dai wani iri, shi ba na harare ba, shi ba na tsana ba, kuma shi ba na bege ba, ita dai ta yi gaba ta bar su bayan ta masu sannu da aiki ɗaya a na yin magana ƙasa ƙasa kamar haka" Kin gani, ita zata yi rakiyar, kai amma wannan ta shigo da ƙafar dama, daga fara aikinta ta samu babbar haja haka? Ai in nice ita ina damƙar kuɗaɗen nan sai in yi gini."

Ɗayar ta ɗan tura kafaɗar ta ta ce" Ke gini ya dama, wannan da kun ganta kun san ai gidaje dai ta mallaki hamsin a kaɗan, maimakun a ba talaka ya samu ya ɗan lasa shi ma, a'a, kullum sai dai su ringa ƙarawa junansu ƙarfi masu ƙarfin nan, Allah ya bamu muma hanyar da zamu samu."

Ire iren zancen da suka dasa kenan, a lokacin da ita kuma ta samu wata inuwa mai kyau ta zauna ta buɗe littafin rashin lafiyar yaron ta ringa bi da irin treatment ɗin da aka yi masa da komai da komai, a hankali hawaye ya ɓalle daga gurbin idanuwanta, har ya zamo ta rungume takardun a ƙirjinta ta lumshe idanuwanta a ranta ta ayyana _"Ba ka da uwa, ba ka da uba, ga ƙananun shekaru Safwan, ina kake ɗan ƙanina? Ni ce mamanka, ni ce babanka, ni ce duk wani gatanka a nan gidan duniya, Ya Allah ka sada fuskata da ta Safwan, ya Rabb ka sa babban gidanmu yana lafiya."

"What hppn sweetheart?" Murya ta furta a hankali, Da sauri ta buɗe idanuwanta, sai kuma ta ɗan so miƙewa dan ya duƙa daf da ita sosai ne, shi ɗin ya ja baya , yanayin fuskarsa da yanayin tashin hankalin ganin hawayen nan na zirya a kumatunta.

"Yaya Bilal? Yaushe ka zo? Ya ya aka yi ka san ina nan?" Yusrah ta faɗa tana share hawayenta da sauri harda ƙaƙaro murmushi ta nemi miƙewar ita ma.

Wajen ya sake nuna mata ya ce" Zauna, Please zauna."

Yusrah ta koma ta zauna tana kallonsa, zama ya yi shi ma ya ajiye ledar dake da shedar restaurant NUSNAN sannan ya dubeta da kyau ya ce" Na je wajen Yaya Siddik ne ya sa aka nuna min inda kike, because ina ta kiran numbar ki ba kya ɗagawa."

Yusrah ta lalubo wayar a aljihun rigarta na aiki ta duba, ai kam miss call har tara, ta dube shi fuskarta a sake sosai ta ce" Sorry Yaya, ka san idan muka fara aiki a silent nake saka wayar sai in na sauka nake cirewa daga silent, shi yasa ban gani ba, ina fatan lafiya? Ina su aunty?"

Murmushi ya yi ya ce" Lafiya ƙalau, staff na je na karɓo maki na kawo dan na tabbata baki ci komai ba ko? Tell me kukan me kike yi?"

Yusrah ta amshi ledar da ya miƙo mata ta buɗe tana ɗan balancing ɗin ƙafafuwanta dake cikin takalmi fari ƙal sau ciki ta buɗe ledar tana dubawa, ta ɗan zaro ido da yanayin sabon dake shiga tsakaninsu mai tsuma zuciya ta yi murmushi ta ce " Wow! Thank you my yaya, yau zan yi karin kilewa."

A dole ya yi ƴar dariya, dan ya kula bata son tambayar da yake ta yi mata kan abinda ya saka ta kuka, shi yasa take ta kawar masa da maganar, a dole ya bar maganar amma ya ƙudurta a ransa in sha Allah shi zai ɗauke mata kewa, zai zamo mata abokin fira, idan tana da damuwa zai zamo bata da wajen zubewa sai shi, dan haka ya bar maganar ya ɗauki files ɗin nan ya riƙe yana faɗin" Oya eat, bari in riƙe wannan ɗin."

File ɗin ta bi da kallo, sai ta yi murmushi tana riƙe abincin a hannayenta dan ba zata taɓa iya ci a gabansa haka a waje ba, ta yiwu dai da a cikin gida ne sai ta ci, amma a waje haka da wahala, a tausashe ta sanar masa tafiyar da aka sanar mata yanzun.

Da mamaki ya ce" Ma sha Allah, ma sha Allah, Allah ya sa a je lafiya a zo lafiya, lallai Yaya Siddik na son mu da alkairi sai na je na yi godiya tawa ta musamman ta mai gida."

Kunya ta kamata ta furucinsa har sai da ta sadda kai tana murmushi, shi kuwa hakan ya saka shi jin sanyi a ransa ya zauna tare da ita yana ta ƙara janta da fira, ita kuma a hankali a hankali ta ringa sabawa da shi tana ji a ranta eh tana iya yin sabo mai ƙarfin da ya wuce kasantuwarsa ɗan uwan Yaya Mubarak kuma ƙanin mijin aunty Intisar kawai, lallai tana iya dubansa idan har ya dubeta da zuciya ɗaya, domin zuciya ai tana son mai kyautata mata.

Ganin ba fa zai barta ta zauna a nan ita kaɗai ba, ba kuma zai zauna ba tare da yana sakata kunya ba sai kawai ta miƙe tana miƙa masa ledar abincin ta ce" Ya Bilal, ka je mota bari in je wajen docter in ce masa mun tafi gida sai in zo mu tafi."

Bilal ya amsa yana gyaɗa kai ya nufi motar hankali kwance, ita kuma ta juya ta je wajen docter ɗin, da ta shiga yana waya da mahaifin yaron da zata yiwa rakiya dan haka ta zauna tana jira, sai dai ga dukkan alamu wayar tana da ɗan ɗaukan lokaci domin a zaunen nan da take tana ji komai da komai ne Docter ke ƙara sanarwa mutumen a kan tafiyar, da sunanta, da aikinta, da shekarunta, harda su tambayar tsaftarta kamar wacce za'a kai wajen wajen zaɓen sarauniyar kyau, ita dai tana zaune mutumen ya gama zayyane sharuɗansa docter na amsa shi da biyayya, ya tabbatar masa an gama saka kuɗin da komai, ya kuma tabbatar masa kuɗin wacce zata yi rakiyar ne ba'a rigai aka bata ba , sai ta dawo zata saka hannu ta ɗauka, amma hatta hotel ɗin da zasu zauna da ɗakunan dake maƙotaka ita da shi, da abincin da zasu ringa ci kama daga kari, rana, da dare komai an gama sakawa a New york, ita dai tana saurare har ya gama ya ajiye wayar yana sauke ajiyar zuciya da murmushi ya ce" Sorry sister na barki ke kaɗai ko? Kin san manyan nan ba sa son a masu wasa da lamura, balle yana matuƙar son ɗan nan nasa, ni har mamakin soyayyar nake yi."

Yusrah ta yi murmushi ta ce" Allah ya bashi lafiya, docter dama zan je gida ne nace ko akwai wani aiki?"

Docter ya girgiza kai ya ce" A'a kina iya zuwa ki huta, sannan gobe ki ɗauki wunin ki ki huta, jibi dai in sha Allah da sassafe za'a kawo ki nan ni zan kai ki aeroport, ga takardar nan taki ta tabbatuwar takardar aikin ki da kuma zamowarki ma'aikaciyar mu a nan."
Yusrah ta saka hannu biyu ta karɓa tana ƙara yin godiya aka nemi izinin shigowa, ita ta je ta buɗe, ta ja baya tana rage tsayinta ta gaisar da yaya Mubarak.

Yana murmushi da sigar tsokana ya ce" Likita bokan turai, ƙanwata manyan likitoci how fa?"

Ta yi murmushin ita ma ta sake duƙawa ta karɓi jakar hannunsa tana furta" Alhamdulilah yaya." Sannan ta ajiye daf da kujerar da zai zauna bayan ta ja masa sannan ta sake yiwa docter sallama.

Da kula ya ce" Na ga Bilal waje, na faɗa masa daga nan a kai ƙanwata gida, ke ma zan faɗa maki a kula daga nan a yi gida."

Yusrah ta sake duƙawa da sigar girmamawa ta tabbatar masa in sha Allah zasu yi gidan daga nan sannan ta fice ta bar su suna zantawa shi da Docter.

Da ta ƙaraso motar ta shiga ta zauna tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Sorry Yayana na tsayar da kai ko?"

Bilal ya ce" Ba wani damuwa, ai zan iya kwana a nan ina jiran ki, yanzu Yayanki ya gama kashe min warning kanki, nace an gode Allah ya biya shi, sai kace shi ba zuwa ya yi zance yayi ta dakon jira sai da aka ga dama aka bashi auren oga madame ba."

Yusrah dai murmushi kawai ta yi, domin Bilal akwai barkwanci sosai, ya ja suka yi gidan kuwa, suna zuwa gidan bayan mai gadi ya buɗe sun shige Yusrah ta fito tana ta doka murmushin firar da Bilal ke yi, shi kuwa ya fito ɗauke da kayan har da jakarta domin murmushin da take yi kenan ya haɗe harda jakarta wai shi zai ɗauka ta yi ta yi ya bata ya nuna ba fa zai bata ba, aikinsa ne, shi zai ringa ɗauka a dole ta bar masa ta fito tana murmushi kawai.

Juyowar da zata yi ta ga Hajia na tahowa da wata maƙociyarta ita ma tsohuwa ce domin ƙawancen nasu har da shekarunsu da suka kusan zuwa ɗaya, dan haka ta ƙarasa da girmamawa sosai ta rage tsayinta kamar yadda ta saba ta gaishe da su, abokiyar hajiyar ce ta amsa tana ƙare mata kallo, hajiyar kuwa ta taɓe baki cike da takaici tana hangen Bilal ta ce" Jakar ki ne a hannun Bilal?"

Da sauri Yusrah ta juya ita ma ta kalli hannun nasa tamkar wacce ke son ganewa, yanayinta ya nuna bata ji daɗin haka ba, domin nan take ta je ta kama kayan muryarta a ɗan hanzarce da kuma girmamawa ta ce" Yaya kawo dan Allah kar ran Hajia ya ɓace."

Shi ɗin ma sai ya sakar mata dole dan ba zai so ace sun shiga takun saƙa da Hajia ba, hajiarsu kuwa idan da abinda ta tsana shine ta ga miji na ba matarsa kulawa, ƙarasowa ta yi ta ɗan ƙara duƙawar ta ce" Ki yi haƙuri Hajiya."

Hajia ta yi mata banza, ƙarshe ma ta kalli maƙociyarta ta ce" Mu je." Haka suka yi gaba maƙociyar na tafa hannu , abinda ya ƙara sanyayar mata da jiki kenan har sai da Bilal ya ƙaraso ya yi mata murmushi ya ce" Mu je ko?"Jiki ba ƙarfi suka yi ɓangaren yaya Mubarak.

Suna shiga shine ya fara yiwa aunty Intisar albishir, ai kam murna har da ƴar rawa ta yi ta murna, har bata iya duba takardun ba, ita dai faɗi take yi" Ma sha Allah ƙanwarta ta fara aiki da ƙafar dama, Allah ya ƙaro dubban nasarori, in sha Allah lafiya lau zaki je ki dawo, kwana goma kuma ai abu ne mai sauƙi a wajen Allah, in ban dama aiki zai kai ki ai da gida zaki sauka wajen Yayanki da sister, amma duk da haka ko ya ya ne sai sun kai maki ziyara duk inda kike, Allah ya nuna mana jibi my Yusrah."

Yusrah ban da aukin murmushi bata yin komai, sai yanayin da Hajiya ta yi mata da suka shigo duk ta manta ta saki, ta kama farin cikin da Intisar ke yi, daga bisani ta shige ciki da takardun ba tare da Intisar ta duba sunan marar lafiyan ba, ta shige wanka dan so take yi ta sake nazartar komai.

Da dare ya yi kusan ƙarfe takwas Yaya Mubarak ya yi kiranta, ya ƙara sanar mata mahimmanci tafiyar nan, ya tabbatar mata ƙwarai babbar nasara ce, tafiya dama abuɗin ilimi ce, a tafiya akwai ci gaba sosai, balle wannan *Wata TAFIYA* ce mai nisa da mahimmanci sosai, ga ci gaba, ga ƙarin ilimi, gashi za'a gano abubuwan da ba'a taɓa gani ba, ga kuma ladan tafiyar mai tsokar gaske, domin da docter ya gwada masa kuɗin aikin sai da ya jinjina ya kuma ƙara riƙe zumuncinsa da docter da mahimmanci fiye da da, domin da wani ne shi zai yi tafiyar nan babu ruwansa da wata maganar wai asibiti, zai bar asibitin a hannun wanda ya ga ya dace ya je ya kwaso kuɗaɗensa balle tafiyar da ba wani jimawa za'a yi ba da izinin Allah, gaskiya ya yi mata murna ya yi mata fatan alkairi sannan ya mata nasiha sosai mai ratsa jiki, ya nuna mata duk rintsi aiki ta je yi ta yi ta dawo lafiya, ta kula da mutuncin kanta, ta kama mutuncin kanta, kar ta saki wani abu ya ruɗeta ko me ye shi sannan yace ta je ta huta da safe za je a yi mata gyare gyare irin na mata da sauran su dai.

Ita ma ta yi godiya ta yi addu'a sosai sannan ta tafi ɗakin ta ta kwanta zuciyarta cike da kewar iyayenta, sosai kewa ta bijiro mata da tunanin yanzu da suna raye wannan ci gaba ya samu ko ya ya Aba zai nuna farin ciki? Mama kuwa fa ya ya ita ma zata nuna nata? Dalilin karatu gata har zata keta hazo, tana roƙon Allah ya sadata da Safwan, in sha Allah zata yi aikinta da zuciya ɗaya, kuɗin nan kuwa idan ta samu Safwan ita ma da su zata fitar da shi, idan ya samu ƙafa ya samu lafiya sai ta ga wa Goggo zata cewa musaki.


*AA ANZA*


A ɓangaren AA kuwa bayan sallar isha'i mota su Anna suka cika biyu suka nufi gidansa dan yi wa Safwan ban kwana da addu'ar Allah ya sa ya samu lafiya, domin mota ɗaya ƙin ɗaukansu ta yi har da Aba da Humed da ɗan sa da matarsa, sai ya zamo sun tafi da mota biyu.

Nabihat wani irin farin ciki take ji a ranta na yau zata je gidan sa, tunda take ƙafarta bata taɓa taka gidansa ba, ko ƙannen nasa ba zuwa suke yi ba, haka ma Abrar, ko Anna ba zata iya gane sau nawa ta je gidansa ba, sai idan bashi da lafiyar da ya kasa zuwa inda take.

Mai yawan zuwa gidansa ya shige inda ya ga dama Aba ne, shima yana yin haka dan ya ringa saka ido sosai a lamarin saurayin da ya gina gida ya ware kansa ba'a ɗaura masa aure da mace ba, saboda tsaro yakan yi masa surprise kuma ya shige har da bayin ɗakin ko ɗakin sa da nufin yin wani abin shi kuwa dube dubansa yake yi dan saboda in har yaronsa na wani aikin tabbas wata rana zai kama wata sheda, mata babu abinda ya gagare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login