Showing 81001 words to 84000 words out of 397328 words
fara sakin su.
Mahaukacin sojan nan ya miƙe ido ya masa jajir yana numfashi da bakinsa, amma dan bala'i ya dubi wajen su Attahir ya ce" Kai, uban waye yace ku mike? Ku tashi maza ku koma tsugunin da nace."
Da sauri da rarrafe suka koma suka yi tsugunnin, a yanzu kam hatta Dauda kuka yake yi, Attahir ne kawai yana inda inda yace" Ancien a gafarcemu yanzu kuwa."
Sai kuma ƙasa ƙasa ya ce" Minista ka daina kuka mana ba girmanka bane ba fa."
Samir yana shasheƙa ya ce" Girman ya ci uban babansa, ka ga ka ƙyale ni kawai ba ya hana mu surutu ba?"
Shima ya yi gum da bakinsa, hakan ya sa mahaukacin sojan nan juyawa inda AA ya koma ya zauna kusa da ankwa ɗin sa yana ta lumshe ido da kayyaɗa lokaci, ya tabbata yanzu dare dai ya tsala duba da abubuwan da sukayi ta faruwa, ya yi zaton ya ɗan rintsa amma ga dukkan alamu yau ido biyu zai waye, kai ana iya shege a duniya wallahi , gaba ɗaya ya yi ja ya yi ruhu ruhu, rigar ma da ya mayar jikinsa duk ta yi wani iri.
Da tafiya irin ta rashin mutunci ya ƙaraso gabansa ya wara ƙafafu ya ce" Kai bani rigar ka in saka, kuma ka miƙe ka je ka bi layin su."
Idan har AA ya masa magana, tabbas ɗakin da suke ciki shi ma ya yi, hasalima sai ya ɗaga hannayensa gaba ɗaya ya ɗora a bayan kansa yana ɗan shafa kansa yana ƙarewa cel ɗin kallo da ido.
Da haushi haushi mahaukacin sojan nan ya ƙarewa damatsunan AA kallo, ya sake dubansa ya ce "...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*22*
Still AA bai bashi amsa ba, haka kuma bai nuna cewar ya san wata tsiya ne a wajen ba ma, rai ɓace ya kawo hannayensa ya shaƙi kwalar AA ya ce" Bari ka gani dan ubanka."
Hannayensa biyu ya saka da ƙarfi ya fincike hannunsa ya zuba masa idanuwansa a cikin nasa a mugun gadarance ya ce" Bari mana, tunani nake yi mai mahimmanci."
Da sauri Dauda ya juyo yana zaro ido ya ce" Kai, taɓɓ! Bawan Allah dan Allah zo ka ajiye guiwoyinka mu yi abinda ya ce, kar ya kashe ka mu zama sheda, dan Allah ka rufa mana asiri laifin da muka aikatama ya ishe mu a gida tabbas sai Yayanmu ya kusan yanka mu idan muka fito, to ina da mun zama shedun kisa a shiga yawo da mu kotu da gidan tsaro ga rashin kwanciyar hankali? Wannan fa da kake gani cewa ya yi soja ne shi, irin manyan sojawan nan ne da ake tsoro su ɗin da kansu tsaronsa suke ji, zo ka ji?" Ya wani ajiye ka ɗin da alamun rarrashi.
"Gaya masa dai! Wallahi bani da mutumci, zan maka magana ta ƙarshe ka bani rigar ka ka je ka duƙa a can tun kafin in wulaƙanta maka fata." Mahaukacin soja ya faɗa da ƙarfi yana ta neman a yi ba daɗi shi da AA.
AA ya miƙe tsam a nutse ya koma ɗayan wajen da ankwa ɗin nan a hannunsa ya ajiyeta gefensa, dan ba zai taɓa yin wasa da ita ba, ya san mahimmancinta, ya san irin hatsarin da ake iya samu idan ta shiga hannun da ba shi ba, ba ma kamar wannan sojan da aka tuɓe saboda yana aiki da kakinsa yana aikata ɓarna kala kala, har da ƙwace, kuma ba kowa ya tuɓe shi ba sai su, shi yasa kawai yake bashi mamaki da dariya, ya ya aka yi aka bari rashin jinsa yayi nisa haka? Ina maza suke jama'a wai ƙaramin ƙwari irin wannan ya ishe su da ihu da zage zage da lalata a cikin gari ba'a yi masa naƙasun da zai sanar da shi akwai hukuma a ƙasa ba? Mtsssss abin takaici, abin haushi.
Lamarin wanda bai iya komai ba sai fitina da neman bala'i baya taɓa ankarar da shi cewa ya daidaita yana iya janyowa kansa wata fitinar a kallo ɗaya idan ya yi, ya zamto ya fahimci eh lalle shi baya ji amma kuma wanda ya kalla zai gane babansa ne a fagen duniyar rashin ji har ya yiwa kansa faɗa ya sassabto ya dawo ƙasa ya rufawa kansa asiri a rabu lafiya, a'a, sai ya zamo tiririn da ya shigo da shi ya gama haifar masa da hayaƙin fitinar fahimtar cewa ya fi ƙarfin kowa tunda ya san duk bala'i nmba fa kashe shin zasu yi ba, su ɗin doka ne, hukuma ne, ba zasu yi kisa ba sai dai su jikata shi har su fitar da shi a hayyacin sa, amma ba batun duka gaskiya, shi yasa yake baza kolinsa dan ya ƙara tabbatarwa kansa cewar ya fa zama wani ƙwaro, ya gagari kowa, ya kuma tabbatarwa doka cewar shi fa uban doka ne, ga kuma tsagerun yaran cikin gari su zamo a ƙasan sa su ringa bada labarinsa ga duk wanda suka gani kamar yadda Dauda ya bada a yanzu.
Sai kawai ya nufo AA ya kuma nufar wuyansa da nufin yi masa shaƙar da zai kai shi ƙiyama, domin bashi da niyyar idan ya riƙi wannan ƙaramin ɗan daban zai bar shi, shi yasa ya zo da nufin yi masa riƙon na kirki, sai dai ya makaro bai san ko ya ya ka ke taƙama da rashin ji tabbas akoy wanda ya dameka ba, sai da AA ya miƙe ya haɗe hannayensa duka biyu ya ruƙo masa idanuwansa ya take ƙafafuwansa da nasa ƙafafuwan da ƙarfin bala'i ya murza sosai da sosai ya yi masa riƙon ƙarfin da ya saka mahaukacin soja kiciniyar ƙwatar kai ko dan kar mutumcinsa ya zube a gaban yaran nan da gabansa shi ɗin shi kansa ta hanyar neman cizon AA, sai dai ya ƙi bashi dama ya matse shi da hannu ɗaya, da ɗayan kuwa ya masa tankaɗeta mareta ta hanya gaura masa mari irin na ka je ka dawo ya kuma riƙe wuyansa a daidai kunnansa da ƙarfi ya ce" Na ce ka barni ina da abu mai muhimmanci a ƙwaƙwalwata amma sai ka kaini bango, mtssss! To kwanta ka huta dan tunanin nan dole sai na yi shi." Ya ƙarashe yana mai sakar masa duka a gefen kunnen sa wajen wuyansa, sai ga mahaukacin soja ya saki, gaba ɗaya jikinsa ya saki harda sakin wata uwar tusa ta wahala ya ɗauke lokaci ɗaya kamar mai yin fitar rai.
A hankali ya ja shi ya kai ya kwantar da shi sannan ya gyara masa kwanciyar ya juyo yana yatsine hancinsa dan warin da ɗakin ya ɗauka sai kuma idanuwansa suka sauka a kan su Samir da suka miƙe ido waje suna kallon su AA a haukace suka ruƙunƙume juna sunna ihu da faɗin a taimake su wallahi makashi aka sako ya kashe mahaukacin soja.
Kai ya girgiza yana bin fitsarin da Attahir ya saki a wando ya ce" Kai ku min shiru dan Allah, ba kwa gajiya ne? aza ku kwanta ku yi barci, gobema kwa taka dokar iyayenku ku yi rashin ji, ina mai tabbatar maku sai na je har gidajenku na zane ku, jibeka ƙaton banza ka yi mana fitsari a wando." Ya ƙarashe yana binsu da ido, suka nufi inda ya nuna masu da gudu suka kwanta ɗin sannan suka yi tsitttt suka rukunkume juna kowane jikinsa na ɓari suna ta addu'a a cikin zuƙatansu.
A nutse ya ɗan kwanta shi ma ya harɗe ƙafafuwansa da hannayensa ya afka tunanin idan har basu hauda shi sama ba a gobe ina kuma zai kama? duk rintsi ba zai so a kai shi kotu daga nan ba, dan tsaf Aba zai gane shi ko me ya yiwa jikinsa shikenan sai a lalata masa aiki, dan haka zai ga abinda zai sake aikatawa zuwa an jima, Allah dai ya sa su bar shi ya yi sallar asubahi dan an fara kiraye kiraye tuni.
Shirun da ya wanzu a ɗakin ya saka sojojin nan dawowa suka kuma sanar zasu buɗe duk wanda ya musu hatsaniya zasu kuma sakar masu barkonon tsohuwa, ya sa ya miƙe zaune yana kallon su har suka buɗe ɗakin suka shigo a shiryen su sai kuma suka yi turusss suna kallon wani baƙon lamarin kuma.
Samarin nan suka kalla da sauri ɗayan ya matsa kusan mahaukacin soja yana haska shi da kyau ya ce" Wannan lafiya?"
Tsitt ka ke ji sun kasa faɗin abinda ya faru, sai da ya ga dama ya ce" Barci ne yake yi."
Da sauri Samir ya kalle shi ya kalli sojan nan ganin kamar sun yarda kuma fita zasu yi ya saka kuka ya ce" Dan Allah ku cenza mana ɗaki, mu ma kashe mu zaya yi idan kuka bar mu da shi."
Da sauri suka ƙarasa wajen mahaukacin soja dan su gane ya kashe shin ne? Suna isa yana farkawa daga sumar da AA ya aika shi a firgice yana ihu tamkar za'a zare masa rai da kuma neman inda zai shiga da neman ƙwatar kai, da sauri suka rirriƙe shi, AA kuwa yana kallon sa ganin shi yake kallo a firgice yana ihun ya saka shi sake girgiza kai ƙasa ƙasa ya ce" Ban fa gama tunanin ba ka min shiru wallahi, ka yi barci mana wai da jarabar nan."
Ɗif mahaukacin soja ya yi ya kifa fuskarsa ya daina kwaramniyar, da matsanancin mamaki suka sake shi suna kallon su sororo gaba ɗayan su ba shiri suka fice, ɗayan na rufewa ɗayan ya je office ɗin Chef ya same shi da Lauya Muktar haɓakar, Yayan su Samir ne, tun jiya bayan an shiga da AA ya zo, kuma an bashi belin ɗin su domin abinda aka kama a motar su ba nasu bane na abokin su ne, amma yace dan Allah a bar su, su kwana su ɗanɗana zafi da sauron cel, ta yiwu gobe ba zasu ƙara ba, ƙarshe shi ma sai ya yi zamansa nan dan idan ya koma gida tabbas mahaifinsa da mahaifiyarsa zasu saka shi dawowa ya kai masu ƴaƴansu, dan ba zasu taɓa iya haƙuri a basu matsanancin horo ba.
Yana zuwa hankali tashe ya sanarwa Chef wannan baƙon fa ba ƙaramin mai hatsari bane ga abinda suka tarar ga irin tsoron da mahaukacin soja ke ciki, basu san me ya masa wanda ya fi irin wanda suka masa ba, kar aje zuwa ya yi ya tada wajen nan da boom dan sai maganar wai ko a barshi yayi tunani yake ko me? Nan hankalin Chef ya karra tashi, ya ƙara yarda cewar wannan mutumen da biyu ya shigo, nan take ya miƙe ya sake kira, aka tabbatar masa yanzu za'a zo a ɗauke shi a ƙara gaba da shi.
Yana kashewa ya ce idan ya fito daga sallah a kawo masa wacce aka kawo su tare zai ƙara bincikarta, dama an kawo ta tsakiyar dare ta masa bayanin komai da komai, ita wacece daga inda ta fito, hasalima ya sa a je anguwar tasu dan a tabbatar masa kuma an tabbatar da bayananta, amma duk da hakanan zai sake bincikarta dan ya gane cewar ba tare suke ba, domin tana iya faɗawa wata hanyar saboda yanayin rayuwa.
Wajen ƙarfe bakwai na safe zuwa da minti ashirin haka aka nufo office ɗin Chef da AA, a lokacin ne kuma aka gama sallamar su Samir bayan an ƙara rikitasu cewar zuwan gaba da wanda ya fi AA bala'i za'a haɗa su in sun isa su sake yin rashin jin, haka kuma Yusrah an yarda cewar bata da laifi ita ma an bata sallama ya zamo ta miƙe ta nufo ƙofar sojawan dake masa rakiya dan a kawo shi a miƙa shi wajen sojawan babbar prison da suka zo da ƙatuwar bak'ar motar su mai baƙin teinti
sun buɗe ya fara shigowa kenan a lokacin da Yusrah ta amshi kuɗinta ta totse tana sake duƙawa tana godiya, juyowar nan da ta yi suka yi ido huɗu, kumatu duk sun suntume mata saboda kuka da fargaba da mugun jin haushinsa, ya ɗan waro ido irin lah da kina nan ɗin nan, sai kuma murmushi ya ɗan sauka a leɓensa, hakan ya sake ƙular da ita ta yi kukan kura a haukace ta afka masa, lokaci ɗaya wajen ya kaure da hayaniya kafin sojawan nan su ɗauketa daga ruƙunƙumar da ta masa yana tsaye ƙiƙam ya zaro ido ta samu ta danna masa wani mahaukacin cizo a kuncinsa dan da aka cirata nan ɗin kawai haƙoranta suka kai sai ƙafafuwanta da ta samu ta nausa masa a ciki , da sauri ya haɗe ƙafafuwansa dan ra'ayne da ayne idanuwansa suka tabbatar masa idan ta samu makasa tsaf zata kar maza ta saka shi ihun bala'i da kuka da burgima a gaban kowa da kowa dan wallahi dukan da ta yiwa cikinsa da ƙafarta idan dukan nan ya sauka a Aswan ɗin sa babu mai hana shi kuka.
Da sauri suka direta ƙasa sojan ya ɗaga hannu zai kasheta da mari tsugul a gabansa tana haki da kuka chef ya dakatar da shi da sauri, ita kuma rai ɓace tana kuka tace" Sai Allah ya saka min sharin da ka min, kuma in sha Allah haɗuwa goma jinyatawa goma ni da kai dan bana tsoronka azzalumi."
Yayan su Dauda ya zarro ido yana kalon ikon Allah, a tsorace Dauda ya riƙo hannunsa ya ce" Yaya mu tafi tunda an gama da mu dan mu yi wanka mu je islamiyya kar ya kama mu."
Da mamaki ya kalli Dauda, Islamiyya? taɓdijan, lallai baba da babansa, to rabon ƴaƴan Abansu ƴan gata su kalli hanyar islamiyya ai har an manta, har an dangana ana bin su da addu'a, murmushi ya yi ya sake zubawa AA ido wanda ke shafa kuncinsa bayan an zaunar da shi saman kujera yana kallon Yusrah, wace Chef ya ƙara yi mata faɗa da nasiha sannan ya salameta.
Ga mamakin barista sai ya ji a tausashe AA ya ce" Wannan fa kar ku sakarwa bayin Allah ita, bata da lafiya fa, ashe abin har da cizo, ko me na mata da zafi? Allah dai ya sa haƙoran ba dafi dan zugi nake ji a kuncina sosai."
Barista ya yi yar dariyar da bai shirya ba still yana kallon AA da mamaki, balle irin yadda aka ringa faɗin bala'in mutumen, gaba ɗaya sai yake ganin kamar ba haka bane, bai san dalili ba, but gaba ɗaya gani yake yi AA ya shiga wata riga ce da ba tasa ba, ama zai bi didigi, haka kawai ya ji zai bi didigi dan kuwa dodon su Samir zai so ace amini yake a wajensa dan ya daidaita masa balagagun ƙannensa masu tashen balaga.
Ita dai YUSRAH tana haki ta fice tana ji a ranta bata gama hucewa ba, ta fita juwa na ɗibanta ta yunwa ga ƙaiƙayin dake damun jikinta, ga sallar da bata yi ba ta asubahi, kai uwa uba ga tunanin abinda ke gabanta, neman Safwan!
A cikin ofishin chef kuwa harhaɗa bayanan da ya rubuta ya yi da kansa ya yiwa AA rakiya har babban ofishin sojawa dan daga nan ya tabbata kai shi za'a yi a adana a babban prison har a samu bayanan waye shi ko ya yi ta zaman dindindin domin hatsari ne sakinsa a fili ba tare da an san waye shi ba balle a san makomarsa.
Tunda suka shigo ofishin nan AA ke kallon mutanen dake matsayin manyan wajen da kallo mai girma da bege a zuciyarsa, tabbas mutanen nan suna cikin manyan manyan mutanen da suka bayar da rayuwarsu dan ceton ta al'umma, basu da lokaci nasu, a kullum idan suka rabu da iyalansa kuwa tabbacin fitar suke da shi daga gidajen su, basu da na sake ganin wani nasu, domin lokuta da dama an kawo masu hari kuma an yi kashe kashe, sai dai a mayar da gawa gida wajen iyalan su.
Tambayoyin da ake yi masa a yanzu, tsaf yake bada amsa daidai yadda ya shiryawa kansa, har Chef na PG ya zuba masa ido ya shiga wani tunanin daban kamar haka _"Anya kuwa wannan ba ya san abinda yake yi ba kuwa? Fuskokin da ya nuna masu yawa ne da su, anya ba sune suke tafe basu san me suke ba kuwa?"_
AA kuwa a lokacin da aka buƙaci ya dangwala yatsarsa dan a tabbatar da shigarsa wajen ya dangwala haka kuma da aka zo ɗaukan gashin kansa da jininsa dan a yi binciken waye shi, domin ya ƙi ya bada gamsashiyar amsar da ta dace sai da ya ji anya zai bada kuwa? Dan gudun kar su fitar da sakamako da wurin da bai shirya ba, sai dai a dole ya bada ɗin saboda in bai bada ta laluma ba ma tsaf zasu kai shi duniyar suma ko su saka shi dogon barcin da