Showing 180001 words to 183000 words out of 397328 words

Chapter 61 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70013

ta hirar su cikin nishaɗi da farin ciki har sanda yanzun kiran Yusrah ya shigo wayar ta suna falo zaune tare da Anna suna hira cikin raha.

Tana ɗaga da farin ciki musamman da fuskar Yusrah ta bayyana gare ta tarau ta fara da "Hi my Yusrah, ya tafiyar taki? Ya kuma majinyacin ki?"

Amsa mata ta fara yi da "Lafiya lau aunty Intisar, albishirin ki? Aunty Intisar an yi aiki lafiya in sha Allah, yanzu jiran farfaɗowar sa kawai muke a tabbatar da aiki ya yi kyau, aunty Intisar kin san wane yaro ne marar lafiyar nan?"

Da farin ciki Intisar tace "Kai ma sha Allah, na taya ki murna, a ƙalla kinga evacuation ɗin ki na farko ya yi kyau matuƙa duk da ba ke kikayi aikin ba, amma dai ina tayaki murna sosai, wa ye yaron fa?"

Da zumuɗi Yusrah tace "Aunty Intisar Safwan ne fa, Safwan ƙanina da muke nema."

Zazzaro idanu Intisar ta yi ta dafe ƙirji tace "Me? Safwan? Safwan dai naki? Ta ya ya Yusrah? Ya aka yi haka to? Wa ya ɗauke shi?"

Shin ƙarfin network ne ko kuma dan wayar na babba ne ya sa Intisar bata iya gano yanayin firgicin dake tare da Yusrah ba saida ta ji muryar ta tana faɗin "Aunty Intisar, ina mutumin da na baki labarin nan? Wannan ɗan balaja'un ɗan sholishon? To a hannun sa naga Safwan, aunty Intisar wallahi shi ya sace Safwan kuma yanzu haka muna tare da shi."

Zaro idanu Intisar ta yi ta miƙe tsaye tana faɗin" Da gaske Yusrah? Kuma kin tabbata Safwan ɗin ne? A New York ɗin? E ƙwarai na tuna mutumin nan na PG, yana ina? Kina kusa da shi? Yana ina yanzu? Bari na kira Akhi ya mana hanyar da zamu damƙe marar mutumci a can, za ki ga yadda za'a masa ɗaurin goro har ƙasar nan."

Da irin sigar gulmar nan Yusrah ta dinga karkata wayar tana son hasko AA da ke tsaye a bayan ta ɗan nesa da ita yana jan carbin shi, a zahiri dai a nutse yake, amma daga idanun shi da kuma bugun zuciyar shi za ka fahimci girman tashin hankalin da yake ciki, shi kam idan ba ce masa akayi ɗan sa ya farfaɗo ba bai ga ta nutsuwa ba, duk da yana ƙaren ita kan ta Yusrah shi ma saboda ganin tana magana kuma yana ɗan kama maganganun nata sama sama haka da yake da tabbacin wani take ba wa labarin haɗuwar ta da shi. Yanzun ma anyi katarin ya ɗan sake juyowa da takaicin ita ta ma samu damar yin waya ko ta yi gulmar sa? Bayan Safwan da take ikrarin ƙanin ta ne amma har take ganin kamar an gama yin nasara kenan? Lallai wannan bai yarda da hankalin ta ba, da nutsuwar ta, da imanin ta ma, dole ya sake nesan ta ta da ɗan sa gaskiya, dan wannan tsaf za ta iya bayar da yaron nan a bata wasu canji da basu taka kara sun karya ba...

A daidai lokacin Intisar ta hangi fuskar sa, to ai ko face mask ya saka tsaf za ta gane ɗan uwan ta rabin jikin ta, bare kuma daga nesa ko mai kama da shi ne ai za ta ce wannan suna kama da wane bare kuma shi ɗin ne, sumar tsaye ta yi bakin ta kaɗai ta iya motsawa tace "Yyyyusrah! Wannan shinnnnnnn."

Jin kalmar ta ƙi fitowa ya sa Yusrah saurin cewa "E aunty Intisar, shine dai, ki dube shi ko kunya ba ya ji aunty, ya ɗauke min ƙanena kuma ya min barazanar idan na sake cewa ƙanina ne wai zai haɗani da jami'ai na nan su ɗaureni, aunty Intisar ya zanyi yanzu?"

Kamar ta farka daga mafarki ta zabura ta juya inda Anna take har ta gyara zama tana ta kallon Intisar ɗin ganin kamar ba lafiya ba da sauri ta zauna kusa da ita tana nuna mata wayar tace" Anna, Anna duba, wannan ba Akhi bane? Anna akhi ne fa ko?"

Lokacin Yusrah ta ɗauke wayar daga kusa da shi, dan haka Intisar tace" Yusrah nuno mana fuskar shi?"

Da ɗan tsoron da ya fara shigar ta na jin kamar tana ambatar Akhi ko me? Ko kuma dai service ne ba kyau? Ta ɗan sake hasko inda yake, Anna kuma a nutse sosai ta dubi Intisar ɗin bayan ta ga AA dake tsaye da kuma kayan da Humed ya nuna mata hoton shi shi da Safwan bayan shigar su jirgi tace "E mana, ba na faɗa miki ba dama zai fitar da yaron sa dan ayi masa aiki ba, ai safiyar yau suka tafi? Ko dai Yusrah ce nurse ɗin da Dr. Siddik ya haɗa shi da ita?"

Yusrah ta yi tsuru tsuru da idanu tana kallon su kamar baƙi kuma bata gane me suke faɗa, sai kawai Intisar ta kalle ta a sanyaye sosai kamar mai nadamar furta abinda zai fito daga bakin ta tace" Yusrahhh, *ɗan uwana ne*, Yayana, uwa ɗaya...uba ɗaya."

Ƙitttt! Yusrah ta yanke kiran tare da faɗuwa ƙasan wani sissilɓan tiles ɗin asibitin dake ta masifar ƙyalli ta yi zaman ƴan bori tana furta"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Wai me yake faruwa dani ne? Me yake shirin faruwa dani ne? Wacce irin ƙaddara ce wannan? Hasbunallah wani'imal wakil! *Yayan aunty Intisar*?"

Sai kuma ta ɗan yi kamar za ta miƙe amma bata tashi tsayen ba tace" Ta ya ya to? Ta ya wannan marar imani ya zama ɗan uwa ga aunty Intisar? Ita kirki gare ta, fara'a gare ta, raha gare ta, sannan tausayi da jin ƙai sun mata yawa, amma ta ya wannan mai zuciyar fir'auna zai zama ɗan uwan ta? Hakan na nufin kenan ta san ƙanina na wajen shi? Ko dai ita ma bata sani ba? Wai ma ta ya Safwan ya zama ɗansa da har sum suke mara mishi baya? Anya wannan mutumin ba aljani bane."

"Mtsssssss!" Dogon tsakin da AA ya ja ya sa ta juyawa ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi, shi kam tunda ya ga ta shiga tafa hannaye kamar mai salati ko zikiri tana ta maganganu ya sa shi tasowa dan ya dakatar da haukan nan tun wuri kafin a farga ma tare suke tafiya ta zubar masa da kimar sa a idanun jama'a, amma yana zuwa ya ji wannan sambatun nata sai shima ya ɗan shiga shock da tunanin _"Intisar kuma? Ko dai wannan ita ce ƴar riƙon ta? Intisar ɗin da take ta faɗa dama ita take nufi? Ƙanwar sa? Nutsatsiyar gidan su? Take renon wannan abar? Ta ya ya?"_

Amma sam a zahiri ya ƙi nuna mata bare ya gaya mata haka ya juya ya koma inda yake tun farko ya ɗauri niyyar ko larurar za ta kaita ga yin tsirara ba zai nuna ya santa ba gaskiya, sai dai zai ƙoƙarta daga nan ya sa su shiga da ita ɗakin masu taɓin hankali kawai, shi wallahi yana ma mamakin yadd wai aka turo babbar majinyaciya jinyar ƙaramin majinyaci, a ganin shi larurar Safwan idan aka dace ai an samu maganin ta yanzun nan da izinin Allah, amma ita fa, ga shegen ƙi faɗi da ya sa ita kallon mai hankali take wa kan ta.

Turawan dake ta kai da kawo ta ga suna kallon ta kamar a baibai, duk da mafi yawa ba suna mata wani kallo na daban bane, saboda fatar ta bata bambamta da tasu ba sai shigar ta da abin da ba'a rasa ba, dan haka ta yunƙura ta tashi tana kama wayar ta da kyau sannan ta juya ta koma kusa da ɗakin da aka shigar da Safwan ta tsaya tana ƙarewa AA kallo a sace wanda shima hakan yake mata da tunanin kowane lokaci za ta iya kawo masa farmaki, shiyasa yake hankalce da ita dan kafin ta illata shi ya farga.

Yusrah ta shiga ƙarewa shigar shi da shi karan kan shi kallo, ita kam ba dan ta yi saɓo ba sai ta ce bayan jar fatar babu wani abu da ya nuna mutumin nan na Allah ne, kuma fa a haka wai ya haɗa jini da aunty Intisar, ko da yake dama a kowace zuri'a ana cire wanda aka bayar zakka a cikin ta, wannan dai ba tamtama shine zakkan gidan, aunty Intisar imani gare ta, tausayi gare ta, lokaci ɗaya Allah ya saka soyayyar junan su a zuƙatan su, ya sa suka shaƙu da juna, yanzu haka saboda kirkin aunty Intisar ya sa take walwala har ta samu aiki mai kyau...To amma wannan? Ban da saka ta baƙin ciki da ɓacin rai babu abinda yake yi, ita kam ko a yanzu da za'a bata bindiga wannan harbe shi za ta yi idan ya so Safwan na warkewa ta ɗauke shi su gudu.

Gyara tsayuwar ta da ta yi ta furta _"Hmmmm!"_ Ya sa shi ɗan juyowa, Yusrah kuma sai ta shiga girgiza kai tana sake tsare shi da idanu kamar dai tana so ta gano wani abu a jikin shi.

Kiran da Intisar ke ta doka mata tana kallo amma ta kasa ɗauka, to ta ce mata me? Oh Allah! Ya salam! Jama'a da wane idanu za ta kalli aunty Intisar? Ta kira Yayan ta da ɗan balaja'u, ta kira shi ɗan sholisho, duk da tasan ita ma tasan gaskiya ta faɗa, amma ai mutane ba gaskiyar suke so ba, ya za ta yi yanzu ta iya sake haɗa idanu da ita? Ba za ta iya ba gaskiya...

*Ganin* bata ɗagawa Intisar kuma ta san dalilin Yusrah na ƙin ɗauka ya sa Anna ɗaukar wayar ta tana faɗin "Bari na kira Aswan ɗin na ji ko suna tare ne? Ina fata dai lafiya?"

Anna ta yi tambayar tana kallon Intisar da ta gaggauta zama kusa da ita, amsa ta bata da "Lafiya lau Anna, kira Akhi mu ji?"

Kiran Anna da ya shigo ya sa shi ɗauka yana matsawa daga kusan ɗakin tiyatar da jiran tsammani, sallama ya yi Anna ta amsa suka gaisa ta tambaye shi sun sauka lafiya? Duk ya bata amsa sannan ta ɗora da "Ya jikin Safwan ɗin? An shiga tiyatar ne?"

A tausashe yana mai zuba hannun shi na dama a aljihun suit ɗin shi yana takawa yace "Alhamdulillah Anna, na so sai ya farka zan kira na muku albishir, amma an masa aiki, kuma sun tabbatar mana da anyi nasara, muna jiran farfaɗowar sa ne kawai."

Da murna Anna tace "Kai ma sha Allah, to Alhamdulillah, dama abinda nake faɗa maka kenan, in sha Allah zai samu lafiya."

A tausashe yana juyowa ya fuskanci Yusrah amma suna nesa da juna amma kuma idanun shi a fuskar ta ganin wani kallo da take ta masa kamar za ta tsorata shi haka ko tana so ta mishi magana sai mimi take da baki tana ta mamatsa hannaye alamar a ɗarare take ya furta "Hakane Anna, Alhamdulillah ala kulli hal."

Sai kuma Anna tace "Da zaran ya farka ina jiran kiran ka ka sanar dani labari mai daɗi."

"In sha Allah Anna." Ya faɗa yana juyawa saboda tsarguwa da kallon da Yusrah take masa, Anna ce ta sake cewa "Jikan Anza."

Yadda ta kiran sunan ya saka shi amsawa da girmamawa sosai har kamar zai rusuna, ɗorawa ta yi da "Nurse ɗin da Dr. Siddik ya haɗaka da ita, anya kuwa ba Yusrah bace? Ƴar riƙon Intisar?"

Tambayar ta Anna sai ta so saka shi dariya, a nutse sosai ya juyo yana sake kafeta da idanu, sai yake jin wataƙila fa ko haƙuri take so ta bashi akan kar ya faɗawa Intisar ciwon ta ya tashi a cikin jirgi? Da irin gayyar nan ya shiga takowa inda take yana faɗin "E Anna, ita ce ina ga fa, ko ba Y. Turaki ba? Tare muke Anna, gata nan ma tsaye tana ta lazimi."

Da tsarguwa da kuma jin harbawar zuciya Yusrah ta fara sadda kan ta tana sake ƙamƙame wayar ta, ƙwarai tana tsoron ko maganar ta suke yi, ba ta so ya faɗi wani abu mummuna akan ta, duk da dai ita bata ga abinda zai iya cewa ta yi ba marar kyau, komai da ta masa akan gaskiyar ta tayi shi, to amma ai mutumin gwani ne wajen iya sharri da ƙage, tsaf zai iya cewa an same ta da makamai ko ƙwaya yanzu haka ma gasu a gaban jami'ai, ko kuma ya sake katoɓarar da ya yi ta cewa matar sa ce ita duk su mata kallon wata iri, wannan shine tsoron ta game da lamarin mutumin da shi kan shi gaba ɗaya yake bata tsoro.

AA na sauraron Anna amma idanun shi akan Yusrah yana jin Anna na faɗin "Fine, jikan Anza, ka kula min da yarinyar nan amana, ina so yanzu ka ɗauka ba ma'aikaciyar ka bace tamkar *ƙanwar ka ce*, ka fahimce ni?"

Murmushi AA ya yi yace "Na ji Anna, amma da kin kira min Intisar ki tambaye ta ko da maganin da suke bata idan ciwon ta ya motsa haka? Ko kuma ruwan addu'a da suke bata tana sha, dan gaskiya tsoro take bani Anna."

Da sigar tashin hankali Anna ta kalli Intisar dake kallon ta tace" Ciwon ta kuma? Yusrahn? Me yake damun ta...? "

Sai kuma ta ɗan ɗaga wayar daga kunnen ta tana sake duban Intisar tace" Ke dama bata da lafiya ne? Akwai maganin da take sha?"

Da mamaki ita ma Intisar tace" Yusrahn, a'a Anna, gaskiya ba wani abun da ke damun ta? Ba fa binciken da ba'a mata ba a asibiti da na kaita, ƙwaƙwalwar ta ma lafiyanta ƙalau."

Sai kuma Anna ta mayar da wayar a kunne tace" To kaji ba abinda yake damun ta, me ka gani wai kai?"

Duk wannan bidiri da Anna ke yi yana sauraron su, sai yanzu da ta tambaye shi ya sake juyowa kaɗan ya saci kallon Yusrah da ya ji yawan haɗa idanun da suke yi ya fara kayar masa da gaba haka kawai ya taɓe baki yace" Shikenan Anna, ba zan rasa yadda zan yi ba."

Kafin Anna ta ce wani abu yace" Anna zan sake kira anjima."

Ya faɗa yana kashe wayar tare da sake dawowa inda take amma daga nesa yana sake nazarin abubuwan da suka faru, irin coinsidence ɗin nan da aka samu tsakanin shi da yarinyar nan, alaƙar da ta ƙullu tsakanin ta da ƙanwar sa, da kuma alaƙar da ke tsakanin shi da Safwan a yanzu.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
30/05/2024, 05:38 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*47*



Ga rashin tsoronsa da yake gani a duk lokacin da zai kalli yarinyar, gashi a yanzu haka shi duk kallon nan da take masa ya tsargu, ya tabbata da wani abu a ranta dan haka shi ma yanzu sai ya tsayar da dubansa a kan fuskarta ƙyam ya zamo duk yadda ta basar in ya ɗago ta kalle shi sai su yi ido huɗu, hakan ya sa ta murguɗa baki ita ma da haushi haushinsa a ranta ta cire kai can ƙasa ƙasa ta furta" Ko aiki da addini baya yi, a ka ce ai kallo kar ya wuce ɗaya."

Shi ma ya taɓe baki kawai yana sake girgiza kai a ransa yana ayyana _" Kenan dai Anna na nufin in dawo da ita kamar yadda na zo da ita? Ni da na so ana fito da ɗana in je aeroport in sama mata jirgin da zai mayar da ita? Ai kuwa an haɗani da aiki gaskiya."_

Sun ɗauki awanni biyun nan a zaune sannan aka fito da Safwan a gadon marar sa lafiya yana kwance a saman ruwan cikinsa, an yi masa kwanciyar da zai ji daɗin ta sosai, yana cikin barci mai nauyin gaske domin aikinsa ko babba ana ɗirka masa alluran barci ne har a ga ya kame, tsananinta kuwa kamewar ciwon kwana biyar in an yi nasara kenan, idan ba'a jiƙa wajen ba ba'a yawan jagular wajen ba'a motsa wajen, in ya kame ne ake juyar da mutum.

Ɗakin da aka kai shi su da kansu sun yarda cewa ɗakin ya haɗu, babu abinda babu na buƙatuwar marar lafiya, ɗakin da faɗin sa haka, sai da aka gama shirya shi tsaf sannan Docter ɗin ya shigo da takardar nan tasa ya zauna ya fuskanci Aswan da Yusrah da ya gama yarda mahaifiyar yaron ce da mahaifinsa kawai domin a fuskokinsu da yanayin su ya kasa bambamce wanda ya fi damuwa da ciwon yaron.

Kasantuwar ba musulmi bane magana yana yinta ne zuu abunsa dan haka ya ce" Ina taya mu murnar fitowarsa lafiya, a yanzu zai yi kwana biyar cikin halin comma artificiell, zamu ringa saka masa abincinsa ta tiyo ɗin nan da muka saka masa, a kai a kai zamu ringa bashi kalolin abun shan da zai ringa sha kafin mu juyar da shi, zai kasance a haka har kwana biyar, babu abinda zai same shi, idan ya farka zamu ringa ƙoƙarin miƙar da shi na wasu kwanaki biyar ɗin, sune kwanakin da zai sha wahala matuƙa domin miƙar da shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login