Showing 225001 words to 228000 words out of 397328 words

Chapter 76 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70019

ba, shin me kike nufi Hinda? Cin zalin marayu za ki yi kuma ƴaƴan ɗan uwan ki?"

Da ɗan harare harare ta kalle shi tace" Ita Khadijar ce ta gaya maka haka? Ba damuwa zan je har gidan na same ta."

"Ki same ta ki mata me? Dan ta faɗi gaskiya?" Sai kuma ya yi tsaki ya ɗora da "Iya Abu ta zo nan bata ji daɗin zama dake ba ta tafi, da ta sake dawowa saboda ɓatan yaron ya dame ta bata yarda ta nufoki ba, kinsan da saida ta kwana uku gidan Khadija, a sannan ne aka samu labarin su Yusrah hankalin ta ya kwanta? Sannan Fureira ta zo ita ma baku kwashe da daɗi ba, Hinda kar ki ɗauka ban san komai ba, ina can ne amma hankalina yana nan gaba ɗaya, ban gaggauta tahowa bane saboda ina so na gama karɓan kuɗina dan na zo da ƙarfin da zan iya shari'a dake idan har wani abu ya samu yaran nan."

A tsorace ta kalle shi ta dafe ƙirji tace" Shari'a kuma Suleiman, da ni ɗin? Akan su Yusrah?"

Cike da tabbaci yace" Ƙwarai kuwa, ke ɗin, na ji komai da ya faru wajen Aminu, bin diddigin komai na dinga yi saida na san komai da ya faru, Hinda ko kunya baki ji ba ace cikin mutane ki sallama ƴaƴan ɗan uwan ki har kina cewa ba zaki iya ɗaukar nauyin da kika san ba zaki iya ba, ni me ya hana ki yanka min ko nawa ne na abinda zasu ci duk wata na dinga biyan ki har sanda zan ɗauke su daga nan? Wallahi tallahi ban da ƙarfi Hinda kamar na wasu, amma kuma ina ji a zuciyata da marayun yaran nan su tagayyara gwara na dinga biyan ki milyan duk wata dan su ci mai kyau su sha mai kyau ko da hakan zai sa na yi bara a titi."

Miƙewa ya yi tsaye yana gyara rigar shi, hakan ya sa ta ɗaga kai sosai tana kallon shi saboda tubarkallah dogo ne sosai, da wata kakkausan murya yace mata" Ki ji da kyau, zan je har gidan da su Yusrah suke, zan ɗaukosu na dawo da su gabana, ni ba matsiyaci bane da zan kasa kulawa da mace ɗaya sai namiji ɗaya ba, kuma wallahi idan na samu yaran nan da wani ƙwarzane a tare da su, ko na samu suna rayuwar da bata min ba, Billahillazi Hinda ki shirya jiran kiran alƙawali nan kusa, dan ke zan ɗaure ba kowa ba, sannan ki gaggauta ajiye min duk wani abu da yake mallakin su ne, gobe zan dawo na karɓa."

Fittt! Ya juya ya fice a gidan ya bar ta baki sake da mamaki da kuma wani irin takaici da haushi na kowa da kowa, musamman ma na Khadija da Aminu da sune manyan munafukai kuma magulmata, sai kuma Yusrah da duk akan su ne ake ta wannan dambarwa. Safiya da komai ya faru kan idanuwan ta ne ta taɓe baki tace "Shi ma dai kawu Sulaiman wallahi bashi da mutumci, akan su Yusrahn zai wani ce zai ɗaure ki? Taɓɓ!"

Goggo Hinda kasa magana ta yi, saida ta gama cika da batsewa sannan ta miƙe tana aje robar albasar ta shige ɗaki, jim kaɗan ta fito da hijabin ta sanye ta kalli Safiya tace" Ki kula min da kayana, na tafi in dawo."

"Ina kuma Mama? An fara kiran sallah fa?" Ta faɗa tana turo baki, a zafafe tace "Gidan wannan munafukar Khadijar mana, zan je na ji ni zata haɗa da ɗan uwana, aikin banza kawai."

Duk da Safiya tana bayan mahaifiyar ta ne, amma kuma tunda tana girmama Yayar ta ko da ta ga Goggon ta fita ta ɗauki waya ta kira Khadija, tana sanar da ita abinda ya faru Khadija ta ce ai kuwa bari ta bar gidan ita ma, dan ta san wallahi kaf maƙota sai sun ji su yau, ita kuma ba za ta so haka ba a ce mahaifiyar ta ce, nan da nan ta kira mijin ta ta sanar da shi, ba gardama ya mata izinin ta tafi gidan su idan zai zo gida sai ya biyo su taho tare, tunda shima ya san komai dake faruwa kuma dama ba ta faduwa ne amma ya san sam sarakuwar tashi bata kyautawa.

Haka Goggo Hinda ta zo bata same ta ba, kuma dake fitar kai tsaye e ba wanda ya ce ga inda ta tafi, ai fa haka ta bar gidan tana zage zage da cewa za ta sake dawowa ne ko ba yanzu ba, ai ba za ta tabbata can ba, amma wallahi sai ta saɓa mata dan ta gane ba'a mata haka.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:21 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*57*




Da dare ma saida ya dawo gidan, kuma ba wanda ya yi mamakin ganin shi duk da ya shigo da wuri dan ko sallah isha'i ba'a yi ba, Anna dake tsaye tana kula da masu aiki suna gyara wurin cik abinci ya tambaya Intisar bayan sun gaisa, ba da tunanin komai ba tace mishi "Suna ɗakin Yusrah, kasan tana shirin tafiya ne."

Jinjina kai ya yi tare da nufa ɗakin kai tsaye, to nan ne Anna ta yi mamaki da bai ce a kira ta ba ya nufi ɗakin, dan ɗakin baccin ta kaɗai ya ke shiga kan sa tsaye.

Yana zuwa ya nemi izinin shiga, kuma dake basu san ko wa ye ba Intisar ta bada izni da a shigo, saida ya ɗan ja sakan biyar kafin ya shiga, da sauri Intisar dake zaune saman gado Yusrah ma a tsakiyar gadon ta wani rirriƙe hannayen ta sai faman kwantar mata da hankali take akan za ta koma gida ne, sannan ta yi haƙuri ta ci gaba da zama anan, a can ba mallai ta samu kulawar da suke mata fatan samu ba, ga kuma Bilal da ta san ba zai barta ta sake ba saboda tsakanin su, sannan Hajia ma ba lallai ta samu sakin fuska daga gare ta ba, sannan kafin su tafi zasuyi ƙoƙarin ƙara sati ɗaya a tafiyar su har su ji abinda manya zasu yanke game da lamarin ta da Bilal, idan bikin kusa ne sai su zauna har a yi, idan an saka nesa sai su tafi kawai.

Wannan hawayen ne Yusrah ke yi na wannan sabo da rabuwa da ake shirin yi, amma da ya ga tana kukan sai ya ɗan zubawa fuskar ta idanu na daƙiƙu, sai kuma ya ɗauke duban shi yana taɓe baki kawai. Intisar kuma tuni ta sauko daga kan gadon tana gyara ɗan kwalin ta sosai, Yusrah ma saukowa ta yi tana gyara zaman rigar ta.

Sai gani sukayi ya zauna bakin gadon riƙe da wayoyin shi, hakan ya tabbatarwa Intisar magana zai yi da ita muhimmiya, sai kawai ta dawo kusan ƙafafun shi ta zauna ƙasa tana sadda kanta da girmamawa, hakan da ta yi ne ya sa AA ɗaga kan shi ya kalli Yusrah da ta kalle ta da mamakin me ye na gurfanawa a gaban shi haka? Suna haɗa idanu ya mata duban kin gani ko? Maman ki ma rusunawa take a gabana, inda Yusrah kuma ta turo baki ta maka masa harara sannan ta juya za ta fice dan ta basu wuri su tattauna.

Saida ta kai ƙofa ta ji amon muryar shi yace "Dawo ko zauna Y. Turaki."

Ɗan satar kallon Yusrah Intisar ta yi sai kuma ta yi murmushi, Yusrah kuma da ladabi ta dawo ta zauna ɗin ko dan aunty Intisar dake wurin, har za ta zauna ƙasa kusa da maman ta in ji shi dan su zama ɗalibai a gaban shi sai ya ce" Ku koma ku zauna can."

Ya nuna musu lafiyayyar sofar dake ɗakin irin turkish ɗin nan, ba musu sukayi yadda ya ce sai dai duk kawunan su a ƙasa, Intisar ya kalla cikin dakakkiyar murya yace" Na san kina shirin komawa gidan ki ne saboda mijin ko anjima zai zo ya ɗauke ki, Intisar."

Yadda ya kira sunan ta ya sa ta amsa da" Na'am Akhi."

A kaifafe yace" Na lamunce ki koma ne saboda darajar surukar ki, niyyata shine nayi bincike har na gano zaman da kike yi a gidan nan da kuma wanda ƴaƴan ki sukayi a U.S, amma da ta zo da kan ta na kuma faɗa mata abinda bana so a zamantakewa ta yau da kullum musamman a zaman aure, babu abinda aka rage ki da shi na rayuwa a gidan mahaifin ki da zai sa ki je kiyi zaman haƙuri a gidan miji, zaman mata da miji ya fi daɗi idan ana girmama juna sannan ana ba wa juna dama, idan babu haka kuwa ban ga anfanin sa ba..."

Ajiyar zuciya ya ja ya sauke sannan ya ɗora da" Game da lamarin yaran nan na so na ɗaga hankalin kowa, amma tunda za ki koma ga mijin ki na bar zancen, sai dai fa ƙanwar mijin ki da mijin ta ba zan yafe musu ba, kuma ki sani sai na hana su zaman lafiya da ran su."

Ɗan gyara zaman shi ya yi ya ciro check ɗin da ya rubuto ya miƙa mata yace" Ki riƙe wannan saboda halin tafiya, Intisar ban yarda sisin kwabo ki karɓa a hannun wani ba, duk buƙatar da ta taso miki ki tuntuɓeni, sannan ki sani zan dinga bibiyar rayuwar ku, idan har na sake kama zaman ku da wani aibun, wallahi tallahi na rantse miki da Allah idan na dawo dake gidan nan ba Mubarak ba, ko mahaifiyar sa ta zo nan aure ke da shi ya ƙare idan autan maza ne shi, sannan ki sani idan har laifi daga gare shi yake, wallahi sai na gigita rayuwar sa da ta ahalin sa gaba ɗaya, *ki zama shaida*."

Ya ƙarashe yana kallon Yusrah da ta yi tsuru tana kallon shi da ayyanawa a ran ta _'Shi dai kawai haka yake, haka suke ta rayuwa da shi suna haƙuri, ina ka fito bala'i ina za ka masifa ne.'_

Da ya nunata har saida ta ɗan zabura ta dawo hayyacin ta sannan ta dafe ƙirji tace "Ni kuma? Shaida?"

Da kai kawai ya mata alamar e, hakan ya sa a ɗan gigice tace "Yaya Mubarak ɗin? Baban nawa?"

A ɗan kausashe yace "Ni ma kuma sai ya zama Baban nawa? Alhalin ƙanena ne."

Ɗan turo bakin ta tayi ta masa irin kallon nan na ka ji tsoron Allah wallahi, sai ya zabga mata harara ya ɗauke kai ya dubi Intisar yace "Kin fahimceni?"

Jinjina kai ta yi a tausashe tace "Na fahimta Akhi, kuma in sha Allah za'a kiyaye, na gode Allah ya saka da alkairi, amma ya ce ma na bari har gobe saboda yara da Anna ta ce za'a wa kitso da ƙunshi."

Bai amsa mata ba ya miƙe ya fice daga ɗakin bai sake kula Yusrah ba, ita kuma da kallo ta bishi da tarin mamakin wannan abun arziki na mutumin nan da abun tsiya, idan ya yi wani abun sai dai ka zuba mishi idanu kawai, shi dai kawai gashi nan ta rasa gane ma wa ye shi? Wane irin mutum ne shi? Ba'a gane gaban sa da bayan sa?

Da mamakin hakan ta girgiza kai a rashin sani maganar zuci ta fito fili ta furta " *Wai wa ye shi?*"

Intisar da ta duba check ɗin hannun ta ta ga milyoyin da ya rubuta mata, tana miƙewa tsaye ne da gyara kallabin ta tayi murmushi ba tare da ta dubi Yusrah ba tace "Akhi? Hmmmm! Aswan Aliyu Anza kenan, babban Yayanmu, Canal ɗin soja kuma ɗan kasuwa sannan magajin Aban mu, alkairin sa ya fi sharrin sa yawa, ba ya shjga sabgar ka sai ka shiga tashi ko ta ahalin sa, sannan Aban Safwan da bai taɓa aure ba."

Da sauri Yusrah ta kalle ta da wani sabon mamaki tace" Canal? Dama soja ne?"

Jinjina mata kai tayi tana fara'a tace" E, amma wata ɗaya da ya wuce aka dakatar da shi saboda wata ƙa'ida da ya kauce, Aba ma baya son aikin nasa na soja, shiyasa nake tamtamar ko zai bar shi ya ci gaba idan wa'adin ya ƙare."

Numfashi Yusrah ta sauke tana ayyana _'Dama soja ne? Haba shiyasa, shiyasa kullum a cikin masifa da bala'i yake, dole ne mana, idan abun ta motsa sai ya yi ta saukewa kan jama'a, gashi sojawan ma sun gaza da shi sun koro shi.'_

Kamar ta san me take tunani ta dubi Yusrah tana murmushi tace "Akhi kenan, Akhina da ban da kamar sa, tsananin sa, takurar sa, duk ba sa damuna, saboda idan ɗaya daga cikin mu ya shiga wani hali marar daɗi ko da rashin lafiya ne, ya kan fimu shiga damuwa sannan ya nuna mana tausayi da ƙauna da kulawa fiye da yadda Anna ma za ta mana, shiyasa babu wanda yake tsallake umarnin sa ko kuma yake jin haushin sa, dan duk tsaurin sa akan kyautata rayuwar mu ne."


*WASHE GARI*



Washe garin ranar tunda safe aunty Intisar ta tafi gidanta bisa rakiyar ƙannenta su dukansu ƴan matan, suka ɗan jima mata suka juya dan girmama maganar Anna da ta nuna masu suna rakata su taho, su Uka da Anna ƙarama ma sai washe gari za'a kai su, Anna ta nuna sai an kai su an masu kitso, hakan ya sa basu wani jima a gidan ba suka juya, dan da Yusrah ta nuna zata je ta gaisar da Hajia aunty Intisar ta nuna a'a ba sai ta je ba, ba dan komai ba sai tana gudun Hajia ta wulaƙanta mata ita a gaban su Nabihat, wacce har yanzu take yi wa Abrar da Yusrah wani gani gani, gani take yi sam basu kai wajen da zasu iya shiga mota ɗaya ba ma balle har sauran zancen ya biyo baya, tsakanin su da juna ido idan waje ya matse masu, in ba ma dan ruwan da ya daki babban zakara ba da Nabihat ta gane wacece Yusrah, duk da a yanzu bata da wata damuwar da zata gigitata sama da tunanin iyayenta, tana bin duniya a hankali, sam bata matsewa abubuwa waje, tana takawa a hankali cike da tsoron duniya, amma duk da haka bata taɓa tsayawa wajen da za'a wulaƙanta ta, bata yarda, bata so, shi yasa take kiyaye Nabihat tunda ta karanceta ta gane take taken ta sai ya zamo ita da ita ido ne.

Da suka tashi tafiya aunty Intisar ta masu kyautar turaruka, Yusrah kuwa ta sake ɗibowa a kayanta turarukan da bata yi anfani da su ba ta zuba a boot da kayanta na anfani, sauran kuwa aunty Intisar ta ce tunda ta dawo yanzu sai ta kai mata su har gida hankali kwance, sannan suna ɗan taɓa fira ne aunty Intisar na tsokanar su su duka da maganar amare amare, ita dai Yusrah kunya ke sakata soke kai kamar ta nutse, ita kuwa Nabihat harda cewa" Aunty Intisar idan aka yi, sai ki dawo ce min aunty ni kuma ina ce maki ƙanwata ko?"

Su dai su Manal sun yi dariyar maganarta, Abrar kuwa ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idanuwanta tana sake faɗawa Allah, ƙwarai Allah yana gani, ta buɗi ido da soyayyar bawan nan ne, soyaya irin mai ƙarfin gasken nan da ta yi zaman rubuta sunayensa a duk wani shafi na litafinta na makaranta, a hankali tsoro ya cakuɗe da soyayya na yanayinsa da kuma yanayin mu'amalarsa da mahaifiyarta, sannu a hankali ta gwamaci faɗawa Allah damuwarta fiye da kowa saboda irin tarin damuwar da tafiyarta da wannan bawan Allah ke ciki, ta sani zata so ta same shi a matsayin miji, amma idan har hakan ne alkairi a gare ta, babu abinda ya fi ɗaga mata hankali sai idan ta duba ta ga ita ɗaya mahaifiyarta ta mallaka a duniya, yau ko da su ashirin mahaifiyarta ta haifa idan ɗaya daga cikin surukanta suna irin ƴar tsamar da shi yake yi da mahaifiyarta ya ya zaman zai kasance kenan? An zauna ɗin? Ya ya gaba? Damuwa zata fi farin cikin yawa, wannan a ajiye take, abinda ba zata taɓa so ba kenan, shi yasa take tafe cike da addu'a da roƙon Allah zaɓinsa, kuma ta san yana sane da ita, Allah maji roƙon bayinsa ne, idan har hakan alkhairi ne ta tabbata tana zaune hankali kwance komai zai tabbata, in ba alkairi bane ba ta ɗaga hannu tana neman alkairi a wajen wanda ya ƙagi duniyar.

Da suka fito hannun Nanal sarƙafe da na Yusrah suna magana ƙasa ƙasa suna dariyar takalmin Abrar dake neman taɗeta ita ma tana dariyar ta ce" Wallahi zaku yi ku gama takalmin nan tunda na siye shi da tsada sai na hau shi, ko ni ko shi idan zan fita ai faɗa masa nake yi, to zan fita sai ka dage ka karya ni ko in karya ka."

Yusrah ta sake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login