Showing 336001 words to 339000 words out of 397328 words
haka" Yau ma ba zaka buɗe idanuwanka mu yi magana bane Hamat? Yau ma zaka yi kamar kana barcin ne bayan na san idanuwanka biyu? Hakan na nufin baka gaji da kwanciyar ba kenan bare ka yi shirin tarban sauran rigimgimun da ka siyowa kan ka."
Dakatawa ya yi yana ɗan ƙifta idanuwansa ya saurara saboda muryar nan dai ta Aswan ce, kalaman kuma da suke fitowa suka saka shi dole ya dakata dan idan ya shiga tabbas ya tabbata maganar da ake faɗa za'a tsayar da ita ne.
Aswan ya yi murmushi a zaune a gaban uncle Hamat dake marmar da ido kamar zai koma ya sume kamar wanda ke fuzga dai haka, a hankali ya ce" Gaba ɗaya ban samu barci ba, na gaza samun barci saboda na rasa gane dalilinka na abubuwan nan Hamat, kenan kai rayuwarka ka ɓata ta da son lalle lalle sai ka shafawa masoyinka kashin kaji? Ka manta Allah ke da komai? Ina ce hatsarin da aka yi na anguwar su Yusrah shi da kansa ya ce a kula da duk wani marar lafiya kyauta? Ashe kai ka dubi Yusrah ka nuna mata idan bata baka haɗin kai kuka yi lalata ba, ba zaka yiwa Safwan aiki ba?"
Da sauri Aba ya sake zuba idanuwansa a jikin ƙofar a lokacin da ya ji muryar uncle Hamat cikin jigatuwa yana dubansa ya ce" Yusrah? Son Yusrah? Son ka kuwa san da Yusrah ba da lalata zan rayu da ita ba? Dan Allah ka yi haƙuri, na ji duka kaf abinda kake tuhumata da shi hakane, na sani ina fitar da uwar haihuwar mata ina siyarwa a ƙasashen waje, na yarda ina amsar kuɗi ina siyar da abubuwa sosai a asibitin nan, na sani ina yin tiyatar ƙarya ina kama kuɗaɗe, na sani bana haƙuri a kan duk wani wanda ya ƙi biyan kuɗin aiki ko kuɗin ɗaki ko na magani, duka abinda aka faɗa gaskiya ne, kuma da ka tambayeni har zina nake yi a nan ma'aikatar nace maka a'a yau na yarda gaskiya aka faɗa maka, babu abinda aka faɗa maka ƙarya a ciki, kuma da kace na saka Humed a ciki ƙwarai hakane, amma bai san komai ba ɓoye masa muka yi muka zurma shi, kana maganar ina son saka ɗan uwana a wani hali haka ɗin ma hakane, amma tsakanina da ɗan uwana ne, ka yi haƙuri ko menene ka bada dama a barni in fita in samu Yusrah, son wallahi na fika son ta, na tabbata ba ka sonta, kuma na san baka taɓa ta ba har yanzu, ka sako min ita in aureta, sai in je in duƙa in ba Akhi haƙuri, dan Allah ka yi haƙuri ka barni in fita daga ɗakin nan, na gaji da kwanciya a waje ɗaya da barci da farkawa kullum, ina so in je in sameta, haukacewa zan yi in ban fita ba, rabona da sigari tunda ka saka dokar a barni a nan, ka tausaya min mana nine fa."
Idanuwan Aswan lokaci ɗaya suka kaɗa suka yi jajir, yana kallonsa ya ce" Matar tawa kake so? Ashe har yanzu baka gane na fika iya iskanci ba? Bari ka gani."
Miƙewa ya yi ya ɗora ƙafarsa ɗaya a saman gadon, lokaci ɗaya uncle Hamat ya dage ya ringa ihun a taimakeshi ya ja baya da ƙarfi ya doka ƙeyarsa da jikin garun ɗakin yana ihu yana faɗin " Ni fa babanka ne, a kan mace zaka kasheni?"
AA ya miƙa hannu zai masa shaƙar ɗiban albarka Aba ya turo ɗakin ya shigo yana lumshe idanuwansa haɗi da sauke ajiyar zuciya ya tsaya yana kallon Aswan wanda ya ɗago da sauri ya juyo, yana ganin Aba yayi wata irin dirowa daga gadon yana zaro ido ya ce" A....a.....Aba? kai ne? Aba? yaushe ka zo? Tun yaushe ka zo? Yaushe ka buɗe ƙofar nan? Me da me ka ji?"
Kallonsa kawai Aba ke yi kafin ya sauke idanuwansa a kan uncle Hamat da ya ɗora hannayensa biyu a saman kansa shi ma ya zaro idanuwansa a mugun tsorace yana kallon Aba, wallahi duk faɗi ne yake yi cewar zai je ya faɗawa Aba abubuwan nan da bakinsa, shi ɗin banza? In yana da ƙarfin faɗa masa ai ba zai yi a ɓoye ba, so ya yi ya yiwa AA wayo ta yadda idan ya fitar da shi ya masa sharrin da uban zai tsane shi ya tsine masa ya bi duniya shi kuwa salim alim ya samu Yusrarsa su yi aurensu hankali kwance.
Shi ma a rikice ya ce" Akhi, yaushe ka zo? Akhi tun yaushe ka zo? Akhi ka ga jikina ko? Akhi jikina sai ƙara rikicewa yake yi."
Aba ya sake sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Allah ya baka lafiyar abinda yake damunka Hamat, jikan Anza mu je."
Gaba ɗaya jikin Aswan sai ya sake neman yi masa nauyi, fuskar Aba yake kallo ƙirjinsa na dokawa, Allah ne shaida babu abinda ke ɗaga masa hankali da gaggawa irin damuwar iyayensa, a hankali ya janyo ƙofar ɗakin yana tafe yana sake matsewa Aba waje har suka sauko, Aba bai nufi motar sa ba dan ya sani ba zai taɓa iya tuƙi ba, sai ya je ya shiga motar AA wanda hakan ya sa AA ƙara yarda cewar gaskiya ne Aba ya gama jin komai.
Yana shiga motar shi ma ya kunna motar ya kashe ya kai sau uku, har sai da Aba ya ɗago yana dubansa da idanuwansa suka yi ja shi ma a tausashe ya ce" Ko dai in tuƙa mu ne jikan Anza? Lokacin magariba ya gabato fa ina so in samu sallah a masallacin anguwarmu."
Tayar da motar ya yi jikinsa na sake mutuwa sosai ya harba motar bakin titi ya shiga tuƙawa hankalinsa duk ba a jikinsa ba, a daf da masallacin ya tsaya ya sauka ya cikawa Aba ruwa a buta shi ma ya cika ya buɗe gefen da Aba yake zaune ya miƙa hannu da nufin sauko shi, ya zarce hannun ya taɓa goshinsa har da gefen wuyansa hakan ya sa Aba zuba masa ido kafin ya sakar masa lallausan murmushi ya sauko ɗin ya kama butar ya duƙa ya yi alwala shi ma ya yi yana kallonsa, yana gamawa ya miƙe ya nufi ciki shi ma ya bi bayansa da sauri ya je suka shiga sahu dan tuni an fara sallah.
Da aka gama sallah duk aka watse ban da liman da ladan da Aba da Aswan, Aswan ya ƙi ya motsa nan da nan, haka kuma hankalinsa gaba ɗaya a kan Aba dake ta jan carbi idanuwansa a lumshe, har lokacin sallar isha'i ya yi aka gabatar aka yi addu'a a nan ma Aba bai miƙe ba sai da kowa ya watse sannan ya miƙe a nutse ya sake kallon Aswan da ya taso da sauri ya zo daf da shi.
Murmushi ya sake yi masa ganin irin yadda cikin dabara yake matse masa waje dan kar ya faɗi a ƙasa, a nutse suka fice suka nufi motar suka shige ya ja suka ƙarasa har cikin gida. Da suka je ana ta gyaran gidan, dan haka suka wuce direct ɓangaren Aba basu nemi kowa ba, suna shiga bayan ya buɗe ƙofar Aba ya shiga ya sake bin bayansa ya ƙarasa da sauri inda yake zama ya sha shayi a ɗakin sa ya kakkaɓe wajen, Aba ya ƙarasa kuwa a nutse ya zauna daidai shigowar Anna da butar shayi a hannunta ta ce" Dama da na ji shiru na tabbata kaine ka fitar min da mijina, sai ka zo ka bashi waje ya huta dare ya yi kai ma ka je gidanka, dreba ba na can yana jiran shigowar ka ko ƴaƴana sa dawo kar a barta a wannan tanƙamemen gidan ita kaɗai tana jin t..."
Shiru ta yi da maganarta ganin yanayinsu, a nutse ta ƙaraso ta ajiye shayin ta zuba ta ziga sosai tana kallo Aswan ya ɗaukowa Aban ruwa a frij ya kawo ya ɓalle masa ya bashi ya sha bayan ta ziga shayin ta miƙo tana kallon su a tausashe ta ce" Me yake faruwa jikin nasa ne? AA babba me yake faruwa ne?"
Aba ya amshi shayinsa ya sha a nutse sannan ya kalli Aswan dake kallonsa a tausashe ya ce" Ba zan ce maka ba'a gigice nake ba, ba zan ce maka ban ji kamar ban ji da kyau ba a lokacin da na ji gaba ɗaya tattaunawar ku, sai dai tunda na buɗi ido na gan ka a tsaye gaba ɗaya hankalina ke kanka, tausayinka ya gama rinjayata, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un."
Sai ga hawaye a gefen idanuwan Aba, wanda ya rikita Anna da Aswan, dan Anna har ta fashe da kuka wiwi abinta tana hailala bayan bata san abinda yake faruwa ba ma, da ƙyar Aba ya sassauta yana dubansa ya ce" Ka san wani abu? Tun muna yara mahaifinmu ke min nasiha a kan halayar ɗan uwana, Ina sane na sakar masa abubuwa da yawa na dukiyata, ina sane nake rayuwa da shi da nufin ban san ciwon kaina ba, ina sane na sakar masa duk wani abu dan kawai burina shine in ga canji a halayyarsa na hassada, ganin ƙyashi, baƙin ciki, dake damunsa sosai da sosai, sai dai kashh, ina nan na yi kwance shi ashe burinsa ya ga bayana ta hanyar cimmaku? Kai kuwa bawan Allah sai ya zamo kaine ke shan bugun da ya dace ace ni ke shan abina tunda ƙanina ne, kana ta kokowa cikin *WATA TAFIYAR* mai nisan gaske dan ka ga ka kare kowane a cikinmu? Ya Hayyu ya Qayyum, Allah ka hana mana mantawa da ranar ƙiyama dan daɗin duniya, wai Aslama ace Hamat ke son Aswan ya saki mace shi ya aura?"
Anna ta zarro ido ta kai hannunta wajen bakinta a birkice ta ce" Warjetttt, tuf tuf tuf binaki luftar nah Ya Abih?" (a ina ka ji wannan maganar Aba?)
Aba ya yi murmushi ya dubeta, ya sake kallon Aswan dake riƙe da hannunsa yana faɗin" Aba dan Allah ka rufa min asiri kar ka saka haka a ranka ya saka maka rashin lafiya."
Aba ya kai hannunsa a hankali ya shafi gefen fuskarsa a tausashe ya ce" Ka san me? Alhamdulillah, ni da kaina ban san zan iya tafiya ba, sai gashi na kawo kaina har ɗakin nan, kuma a yanzu bana jin komai na rashin lafiya sai ɗacin zuciya da dana sani mai tarin yawa da tarin tausayin ka, tell me, hukuma na cikin maganar ko? Shine aikin da ka je yi kwanaki ko?"
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Aba, eh shine, kuma maganar aikin ne, in sha Allah zan kawo maka komai gobe, kuma hukuma na ciki dama ni nake ta jinkirtawa saboda kai, ina tsoron abinda zai faru."
"Kai faɗa min menene ni wai ka ji?" Anna ta katse shi tana dubansa.
Aba ya ce" Ni zan faɗa maki, shi yanzu gida zai je tana jiransa ne ai, kana ji son? Ka je ka huta, goben kar ka fito da wuri ka ji? Zuwa yamma ma haɗu in sha Allah sai ka kawo min in gani, lokaci yayi da zaka fitar da shi daga hannunka ka miƙa shi hukuma, duk abinda yake faruwa sai a daidaita idan zai daidaitu, maganata kuwa kar ka damu in sha Allah yau ma zamu kwana muna sallah da mamanku babu abinda zai sameni sai abinda Allah ya hukunta, ba zan taɓa ɗaga hankalina har lafiyata ta taɓu in yiwa ƴaƴana asara ba, in sha Allah duk abinda ya min ni na yafe masa kuma Allah ya shirye shi, maza je ka amarya fa gareka jikan Anza, kuma har ga Allah nawa jikan nake jira wanda zan ƙwace daga gare ka, ka ji?"
Murmushi ya yi da ƙyar yana sadda kansa, Anna kuwa ta ɗauke kai tana girgiza kai, har ya miƙe ya tafi bayan ya yiwa Anna alamun wayarta a gefenta dan yau bai san ko zai iya rintsawa ba saboda kwana zai yi yana kira dan ya ji yanayin jikin Aba, ƙwarai ya yi mamakin irin yadda Aba ya jure abin nan, tabbas Allah ya amshi adu'o'insa bashi da abin faɗa sai godiya ga Allah, a yanzu kuwa zai miƙa bincikensa wa hukuma in yaso duk abinda ya biyo baya daidai ne da mai laifi.
*AA MENSION*
Goggo Tidin ba ta zo gidan ba, amma daga can gida ta shaidawa Aba nan za ta zo, saboda duk abun su suna girmama shi dan shima yana ɗaukaka lamarin su, amma sai tayi tafiyar ta gidan uncle Hamat suka sha hirar su ita da matar sa. Rashin zuwan ta kuma babu abinda ya hana, hasalima wanda ya san matsayin ta ya kuma ga bai gan ta ba yake tambayar ina take? Amma Alhamdulillah komai ya tafi yadda aka tsara shi kuma sai san barka.
Tun daga gidan Anna da aka yi ta karɓan baƙi suna shaida lallai bikin babban ɗan su suke yi, dan kuwa abinda aka yi ranar ɗaurin auren sai ya zama kamar nafila ce aka yi yau aka tabbatar da farilla, dan nama da mutane suka ci ma Anna bata haɗa su da na manyan dababbobi ba sai na zabi zalla, kuma abun farin cikin aka ba kowa damar yin yadda yake so, tunda kowa a babban takeaway aka saka mishi abun ci da shan shi aka bashi iya shi kaɗai, saɓanin yadda aka saba anan aka ga kuma ana yi, hakan ya janyo dayawa yin guzuri da shi, dan in ma bakayi dan kai ka fi ƙarfin abun ba, to za ka yi ne dan ya maka yawa, saboda ko ma'aikatan dake ta kai kawo ba wanda ya damu da wanda ake ragewa ana ajiyewa a ƙasa.
Hajiar Mukhtar da Hajiar Arif sun yi kara sosai, dan Hajiar Mukhtar ma tare da su Rihab ta zo, nan ne ta gasgata lallai da AA ke mata irin wannan manyan kyautuka ashe gada ya yi daga gida, kuma abun aka tara shiyasa yake yi kamar bai san ciwon su ba. Har bayan magriba suna nan kafin aka yi sallah aka tattara zuwa gidan amarya, kuma mutane dayawa ne suka dunguma a motocin da aka tanada bila adadi saboda ganin ƙwam.
A can ma tarba suka samu da wani sabon abincin da naman da suka kasa shaida ko na me ye saboda markaɗa shi aka yi sai irin su kayan ɗanye da ƙwai, a taƙaice nan ma ci aka yi aka sha, aka fito da amarya da aka rufe mata fuska manya suka saka mata albarka kafin kowa ya fara watsewa gudun kar dare ya yi.
Da haka sannu sannu kowa ya fara tafiyar sa, da dare ya yi dare kuma har aunty Fauzy ma Jamil ya zo ya ɗauketa, daga nan su Manal ma dreba ya ɗauke su da Anna ta turo suma suka tafi, hakan ya sa gidan ya sake yi wa Yusrah girma saboda sai ita ɗaya aka bari bayan an bar ta da wasu sababbin huɗubobin.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
30/06/2024, 23:13 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*85*
Da fara'a ta shigo ɗakin baccin nashi da sallama a bakin ta saboda tasan da ta gama tsaro duk abubuwan da take da buƙata daga gare shi, kuma ko rabin su ya bada bata da matsala da hakan saboda ita kaɗan ta ma za ta iya ɗaukar nauyin bikin Nabihat saboda ta ci buri da alwashi akan auren nata. Sallamar ta ya amsa yana ɗan tsare fuskar ta da kallo saboda ganin wannan murmushin, har ta ƙaraso ta ɗan zauna kan kujerar dake kusa da gadon shi tana faɗin "Barka da dare Papan Nabihat?"
Ba tare da ya daina kallonta ba ya amsa da "Barka maman Nabihat, kun wuni lafiya?"
Amsawa ta yi da lafiya ƙalau tana jinjina lamarin nashi, wato idan bai son takura sai ya ƙi kwana kusa da ita, da kaga ya nemi kwana shi kaɗai to kuwa ka yi nesa da shi, idan ba haka ba ka kuskura ka hassala shi za'a kwashe babu daɗi, ko ma dai menene, takardar hannun ta ta miƙo mishi tana faɗin "Yawwa, Papan Nabihat ga abubuwan da ka ce na lissafa maka wanda muke da buƙata ni da Nabihat, komai yana nan ciki, fatan za'a dube mu kuma a gyara mana, sai fatan Allah ya sa alkairi ya kaimu lokacin kuma."
A ranshi ya ayyana _'Ko da nace, ni kam nasan da walakin goro a miya, amma ba damuwa muje a haka.'_ A zahiri kuma karɓar takardar ya yi yana sakin murmushi yace" Ma sha Allah, bari na duba na gani to, da fatan dai ba za'a karya min tattalin arzikina ba?"
Dubawa ya yi ya ga list na abubuwan daga ƙarshe kuma ta yi total na kuɗin, kallonta ya