Showing 219001 words to 222000 words out of 397328 words
da gabana ya faɗi, ya ya za'a yi in auri yarinyar tana kayar min da gaba amini? Ni ne mijin fa, gwara a bani wata shi ya fi alkairi ko? Kuma kar ka saki ka min e yane a kan maganar aure, kaima ai tuzurun ne."
Idan abu ya girme ka rasa bakin magana ka ke yi, gaba ɗaya Mukhtar sai ya yi sake yana ji yana gani har AA ya shige motarsa ya ja ya bar wajen sannan ya zabura ya raka bayan motar da kallo.
Tunani ya shiga yi anya kuwa ba AA zai kashe shi ba? Ya shiga uku, la'ilaha ilalahu, wai tsoron ta yake ji? Da wannan al'ajabin ya shige motarsa yana sake duba lambar Abrar da ya amsa a wajen Manal, tabbas hatta jiƙo Hajia ta masa a kan maganar aure, a da maganar bata gabansa ko kaɗan, amma a yanzu yana ji a ransa kamar ya shirya fa, yana ji a ransa kamar auren idan an bashi zai yi shi ma, yana ji a ransa ya samu abokiyar rayuwarsa ne in sha Allah.
*Alhamdulillah* jikin Safwan na sauƙi a kowace safiya ta Allah, yana samun kulawar da ta dace da shi da ɗan gata gaba da baya, tunda aka sake dawo da shi asibiti ahalin Aswan basu taɓa nuna gazawa wajen zuwa duba shi ba, ko da Anna ba ta zo yau to ƴan matan gidan za su zo, suma ko da wata a ciki bata taho ba to a ƙalla dai wasu sukan taho. Amma Goggo Tidin bata taɓa zuwa duba Safwan ɗin ba, kuma tana ba Yayan nata uzuri ne da tana fita aiki tun safe sai yamma lis take zuwa, wannan lokacin kuma ta gaji shiyasa ba ta tafi ba, amma dai za ta je, a ranta kuwa ta jima da ayyana _'Ba zan taɓa zuwa duba wani miskinin yaro da bamu da haɗi da shi ba.'_
Haka ma ita da Yusrah ba wata mu'amula, matsayin ta na babba dai Yusrah ta kan gaishe ta a kowace safiya saboda dukan su masu zuwa aiki ne, sannan ƙa'idar gidan ce ma idan aka tashi da asuba da wuya ka ga wani ya koma bacci, ƙiri ƙiri take ganin tsanar ta a fuskar Goggo Tidin ɗin da ƙyama, dan Gogg Tidin idan ta ga gilmawar Yusrah har idanu take zuba mata ta bita da kallo tana mamakin yadda yarinyar aka ce ba ƴar uban kowa ba, amma kuma ita da su basu da bambamci? To da gaske tuwo da miyar kuka ta ci ta girma? Da gaske da yanzu suna hira da Intisar sai ta dinga bata labarin wai abinci ma sai an nemo ake ci a gidan su? Amma kuma ita da ƙanin ta suke da hasken fata haka, uwa uba yanzu da suke ƙara samun hutu da kulawa sai suka sake canzawa idan ka gansu sai ka rantse ɗin ita ma ƴar Anna ce, Safwan kuma ɗa ne ga Aswan Aliyu Anza. Ita kawai bata yarda da su bane, shiyasa ma bata shiga sabgar su, kai ba su ba ko Nabihat dake zaune gidan fa gaisuwa ce take haɗa su, sai yanzu ne ma da Yayan nata ya ce an haɗa auren ta da AA sannan take ɗan sakar mata fuska da kuma kiran mahaifiyar ta suna gaisawa, ba wai dan ta samu kusanci da Aswan ba, sai dai ta samu kusanci da matar da zai aura sannan ta ɗora mahaifiyar yarinyar a hanyar cin kuɗin Aswan ɗin a lokacin bikin su idan ya tashi.
Allah ya sa Yusrah ba ta da matsala da haka, ita dama rayuwar ta wanda yake yi da ita da shi ne take yi, wanda ya nuna baya yi da ita tafi shi nesan ta kan ta da shi, hakan ya sa iya wannan ina kwana da ina wuni ne kawai ke haɗa ta da Goggo Tidin, kuma dake sun yi mugun sabo da su Manal da Abrar, ga kuma aunty Intisar a gidan da take ɗebe mata kewa, sai ya zamana bata takura ba a gidan, saboda ko a fuska Anna bata nuna mata wai ita ba ƴar gidan bace, haka Aba idan ya same su a falo ko suka je gaishe shi yadda yake kama sunan ƴaƴan sa da Nabihat da Abrar, haka ita ma yake kama sunan ta ya tambaye ta ta tashi lafiya? Sannan Humed ma yadda yake kiran Manal, Nawal da Abrar da sis haka yake kiran ta, matar sa ma sukan je ɓangaren ta musamman da dare su sha hirar su, saboda ita yanzu bata cika zuwa can ba tunda cikin ta ya turo riga.
Nabihat ce dai har yanzu, har yau da take cika kwana bakwai zuwa na takwas a gidan nan, har yanzu bakin su bai haɗu ba ko da kuwa da sunan *sannu* ne, kawai raini take gani a tattare da Nabihat, bata da aiki da kwalliya da baɗa turare ta yi ta rawar kai tana karya jiki, ga kallon raini da za ka ga tana ma duk wani da ba Anna da Aba da kuma su Manal ba a gida, kowa a ɗage take kallon shi cike da rainin wayo tana farfara idanu uwa jinjinar jaka, dan haka ita ma ko zaune take ko za su yi saɓanin hanya sai ta haɗe fuskar ta tayi kamar bata gan ta ba.
Sai kuma *oga* mai gayya mai aiki, abu ya zamar musu kamar sabo, indai za su haɗu to ko da mutane a wurin sun kasa yin faɗan baki sai sun yi na idanuwa, suna haɗa idani zai maka mata kallon lafiya? Sai ita ma ta bishi da kallon yo kai ma lafiya? Sai kuma ya mata alamar shi fa Baban ta ne, wani lokacin har ya kalli Intisar ya bata umarnin ke ɗebo min ruwa? Ke tashi ki bar nan, ke kawo min abinci na kai wa yarona da dai sauran su, dan kawai ya ɓatawa Yusrah rai, ita kuma sai sun haɗu musamman a asibiti za ta dinga masifa tana faɗin ta ya zai dinga wahalar da aunty Yusrah haka? Ba fa ita kaɗai bace, juna biyu gare ta, sai ya taɓe baki ya ce "Idan ma juna dubu biyu ne ni na aike ta tayi? Ko juna biyun hujja ce da zan ƙi aikar ƙanwata?"
Yusrah kuma kamar za ta yi kuka sai tace "Wallahi ka ji tsoron Allah ka daina saka min uwa aiki, ni ka aike ni na maka duk abinda kake so."
Cike da shaƙiyanci yake taɓe baki yace mata "Ke ai ƴata ce, ba zan yi ta aikin ki ba bayan Maman ki na zaune."
To fa wani lokacin da ya faɗi haka kamar za ta fashe da kuka sai ta bar masa wurin, sai ya bita da kallo kamar zai yi murmushi, sai kuma ya gaggauta haɗe fuska irin _'Kai yane kuma?'_ Sai ya ci gaba da sabgar shi.
Haka abun ya zame musu jiki har idan ya zo gidan bai gan ta ba ya kan jinkirta har sai ya ga gilmawar ta, idan asibiti ne ma ba ya tafiya bai gan ta ba ko da kuwa aiki ya mata yawa sai ya ƙirƙiro abinda zai ganta ya hassalata sannan ya tafi. Ga maganar aunty Intisar da kullum sai sun cazawa juna kai sannan wata safiyar take yi, ƙiri ƙiri ya hana har fitar aunty Intisar ko ina ba da izinin shi ba, Yaya Mubarak ma idan ya zo gidan to ƴaƴan shi zai gani ya gaishe da su Anna sannan ya tafi, amma dai Intisar a cikin takumkumin sa take har yanzu, sauƙin ta ɗaya shi ne suna waya, shiyasa ma har damuwar su ta rage musamman da Yaya Mubarak ya fahimci ita ma tana son nuna masa mahimmancin Yayan ta ne kamar yadda shi ma ya nuna mahimmancin ƙanwar sa gare shi, sai ya share yake lallaɓata suna wayar su sosai.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:19 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*56*
Idan yana waya da Yusrah, sukan kwashe awanni suna yin wayar tamkar zasu janyo juna ta wayar su cinye juna, shi yasa in ba sallolinsa ya yi ya gama ba baya tarka idan ba zai je zance wajenta ba, saboda ba kullum yake zuwa ba, ita ce ta nuna bata so kullum suna zance, ta fi so jefi jefi su ga juna, shi kuwa ya amince dan bashi da ja a abinta take so, amma fa tana shan damu da waya, ɗazu suka yi yace zai kirayeta bayan sallar isha'i, to kuma ya zo yiwa Hajia sallama ya ga kiran Yusrah ɗin, ashe baby Aslama ce ke kiran sa dan ta faɗa masa chocolat ɗin da take so idan zai zo.
Yana ajiye wayar ya dubi Hajia dake zaune tana kallon tv ɗin da ba amo ko kaɗan a ciki, ya tabbata tunda ya kama sunan baby Aslama ne ta ɗauke amon gaba ɗaya dan kuwa shi ya san irin son da take yiwa jikokinta kawai masifa ce ta fi ƙarfin ta ta ƴarta har take biye mata.
Murmushi ya yi ya ce " Sai ki maida amon ai Hajajju makatu Babar Md da kansa."
Hajia ta juyo tana sauke masa harara ta ɗauke kanta, har ta yi shiru sai ta kasa ta sake juyowa ranta ɓace ta ce" Yanzu ace yaran nan kwana huɗu a garin nan amma da idona ban gansu ba? Wannan wace irin masifa ce? Mahaifiyarsu ma daga fita shikenan ta tare da yaran ta a gidansu dan ba'a son gaskiya? Ba laifi duniya ce ai."
Bilal ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya dawo gefen Hajia ya zauna ya zuba mata ido, a tausashe sosai, da sigar da ya iya karkato da tattaurar zuciyar mahaifiyarsa ta zama lallausan, ta hanyar da ya iya tanƙwarar da ita ko da bata son saurarenshi ta saurare shi, a gidan daga Hauwa'u sai shi suke iya yi mata magana kansu tsaye ta saurara, ko Hawa'u bata kai shi iya tanƙwarar Hajia ba, kuma duk abun nan da ake yi dama jira yake yi ta kawo kanta da kanta ta yadda duk abinda zai faɗa zata ɗauka ne ba zata ga an zageta ko an zagar mata ƴa bace, a tausashen nan ya ce"Hajia, Dan Allah ina so mu yi magana ta fahimta, ina so abinda zan faɗa maki ki gane cewar duk duniya ba zan taɓa son wani sama da ƴar uwata ta jini ba, ba kuma zan kware mata baya dan in birge wani ba, amma kuma zamu faɗa mata gaskiya saboda gobe ƙiyama kar Allah ya kama mu da abin ko?"
Hajia ta yi shiru tana kallonsa, Bilal ya ci gaba da faɗin" Hajia, ki duba ki ga abinda yake faruwa, kin san Allah idan kika je kika ga su Anna ƙarama a yanzu da suka jima a hannu mai kyau sai hankalinki ya tashi,Hajia yaran nan sun fita a hayyacinsu har da faso fa a ƙafafuwansu, gaba ɗayan su kamar ba jikokin ki ba, kin san har da sallah yaran nan basa samun yi a hannun Ule?"
"Kai Bilalu ka ji tsoron Allah, sallah kuma? Sai kace kafura zata hana su sallah? Wa ye ya faɗa maka haka kai ɗin? Yanzu haka wannan yarinyar da kake neman aure ce ko? Bilalu ba komai mace ke faɗi a yarda ba fa kar ta fara haukataka tun yanzu?" Hajia ta katse da sauri ranta ɓace.
Bilal ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ciro wayarsa IPhone ya shiga Tiktok ya shiga compte ɗin mijin ƙanwar tasu dan ita ta yi block ɗin duk wani ɗan gidan da wanda ta san ɗan gidan ne, ya kamo vidiyoyinsu a nutse ya ringa shiga yana buɗe mata, wanda hakan ya sa Hajia zaro ido har zufa na neman karyo mata, na tashin hankalin irin suturun jikin ƴar ta da ƴaƴan ƴar ta, uwa uba duk a vidion da za'a yi katari Uka ta fito yaran na aiki ne cikin wani yanayi marar daɗin gani.
A hankali ya shiga comment section ya ringa karanta mata irin maganganun da ake yi a kan yaran, da irin amsar da mijin ke badawa cewar ƴan aikinsa ne dole zasu yi aiki yaransa kuwa babu abinda zasu yi tunda ba ƴan aiki bane
Da kula ya fuskanci Hajia ya ce" Ban nuna maki vidion nan dan in ɗaga maki hankali ba, sai dai gani nake yi garin wani abin kar a cimma wani na tashin hankali da dana sani ba'a sani ba, Hajia, kar ki lalatawa ɗan ki dake son ki yake maki biyayya sau da ƙafa rayuwa a kan wacce a yanzu idan rantsuwa na yi bata yi sallar asubahi ta yau ba ba zan yi kaffara ba, saboda a bayyane yarinyar nan gaba ɗaya ta zubar da al'adun ta, da addinin ta dan kawai ta je rayuwa a ƙasar waje, a yanzu ina iya tabbatar maki ta fi mai kora shafawa dan yanayin ta zai nuna maki ta yiwu a yanzu yarinyar nan wallahi ta fi turawan iya zuba rayuwar tantiranci, Hajia ki duba dai ki gani sai ta yi wata bata yi kiran ki ba, sai ke kike damuna in kira maki ita, Hajia in ba ta yi kira ta nuna maki yara basa ji basa yi mata biyayya suna son haɗa ta faɗa da mijinta, suna yi kansu da ƙafar su ba'a gani, ke kuwa hankalinki ya tashi ki rasa ina zaki saka ranki ki yi ta faɗa daga nan in ta ɗauke ƙafa sai kuma wani abin ta faɗa makin ya tashi zaki ga kiranta. akwai wani abu da take ƙara ki da shi ne bayan wannan?"
Ya ɗan sassauta a sanyaye ya ce" Na san duk daɗin zobe bai yi ya wuyan hannu ba, amma rayuwa bayan mutuwa akwai tashin da za'a yi gaban Allah wanda sai ya maka hisabi tsakaninka da ƴaƴan cikin ka in ka cutar da su a zaman rayuwa balle a kai ga matan ƴaƴanka, Hajia me aunty Intisar ta rage ki da shi? Rashin lafiyar ki ita ce, kula da tufafinki ita ce, kula da duk wani abu naki ita ce, kina da masu aikin fa haka take zuwa ta ƙalƙale ko ina ta gyara, nan jiya kike faɗan ɗakin ki an maki gyara bai yi ba, yaushe rabona da in ji irin haka? Tunda suka zo garin nan da zama suke zaune a gefen ki, kin san da ta san halin da ƴaƴanta suke ciki ta yi shiru ta kawar da kai? Kin san da idan ta sanar tun a lokacin wallahi Hajia Yayan nan nata tsaf zai iya tadawa kowa hankali ya ƙwato mata ƴancinta, amma ta yi shiru ta ƙi faɗa dan kar rayuka su ɓace? Hajia, ita ma fa uwa ce, uwa ma yarinya, kuma ƴaƴa mata ake magana a kan su fa Hajia, dan Allah ki yi haƙuri ki sassautawa yaya Mubarack kar ya shiga wani hali, ki yi haƙuri ki daina rikicin nan kin ji uwarmu?"
Hajia hankalinta ya yi mummunan tashi, ire iren vidion su Hauwa sun girgizata, jiki duk a bayane suna ta abubuwa kamar kafuran ƙarshen zamani? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, kuma a vidion ɗin babu inda zaka hangi ɗaya a cikin yaran nan ka gansu da suturar kirki, hankalinta ƙwarai ya yi mummunan tashi, ta rasa inda zata kama, tunanin da zata yi har sai da yaya Mubarak ya shigo ne Bilal ya ƙyale ya mike yana susar kai ya masu sallama.
Yaya Mubarak ya zauna yana kallon yanayin Hajia, hankalinsa ya so tashi, yace" Hajia, lafiya? Me yake faruwa kamar hawaye a idanuwanki?"
Hajia ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" Ba komai Mubarak, abincin ka zo nema?"
Mubarak ya girgiza kai ya ce" Na ƙoshi Hajia yau bana jin yinwa."
Hajia ta ɗan zuba masa ido tana ƙaukewa, tarin tausayinsa na neman kamata, tabbas idan zata yi rigima ta san irin wacce zata yi, shin me yaron nan ya rageta da shi a duniyar nan? Kafin wani cikin ƴaƴanta ya yi mata ɗaya shi ya mata goma, yau ko da ace ƙanwar sa bata da laifi a cikin lamarin nan sai ta masa uzuri, ƴaƴansa ake magana fa, amma ta yi sanadiyar da matar sa ta tafi gidan su an je biko sau uku Yayanta ya ƙi haƙura kuma ita ta ƙi maida hankali a bashi haƙuri ya bashi matarsa su tattara su yi tafiyarsu wajen aikin da ita da kanta ta san babban ci gaba ne a wajen yaron nata da matarsa da su kansu baki ɗaya? Gaya nan yaya Mubarak a yanzu abincin kirki ma baya iya zama ya ci, daga ya zo tsurut sai ya tashi, kana ganinsa zaka fahimci yana cikin wani hali amma ya gaza faɗa saboda ba zai iya ɗaga mata hankali ba?
A tausashe ta ce" Mubarak, idan Allah ya kai mu gobe wajen ƙarfe goma in baka zuwa