Showing 285001 words to 288000 words out of 397328 words

Chapter 96 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70087

Nabihat da yanayin shigarta, wani irin ɗaci da haushin hakan suke ji har ransu, a ganin su wannan ɗin ba ranarta bace da zata zaƙe har haka, a tunaninsu babu wani haɗin da zai sa ta saka sutura irin ta amaryar da za'a tarba yanzu yanzu a karramata.

Tidin kuwa tana kusa da Aba suna ƴar fira suma ƙasa ƙasa a kan rashin lafiyar Hamat da abinda ya shafe su iya su, sai Safwan dake gefe yana fama da tab ɗin sa domin Aba ya saka masa game mai ɗauke hankali sosai ya shiga buga abinsa hankali kwance.

Abrar kuwa tana ɗayan gefen kusa da tagwaye ita ma tana doka murmushi da waya a hannunta ga dukkan alamu da sahibinta take zantawa, sai Humed dake kokowa da yaronsa yana masa wasa, matarsa Wa'at kuwa tana riƙe da plate ƙarami tana fama da ƴan ciye ciyenta irin na masu ciki, zaman dai a tsare yake sai sanyi dake busawa da ƙamshi.

Tunda ya shigo kowa ya ba da hankalinsa kansa ban da Tidin da ta masa kallo ɗaya ta ɗauke kai, murmushin da ya kusan sumar da Nabihat ya saki a tausashe, lokaci ɗaya ƙirjinta ya nemi riƙewa da wani irin zafi na kishinsa, tsarin shigar hausar da ya yi a yau ta matuƙar karɓar shi, ta masa kyau sosai, ya yi shiga ne da farar shadda mai tsada wacce ta samu ɗinki madaidaici da hula wa ce ta hau zaren blue mai haske da aka yi aikin da shi da fari sosai.

A nutse ya cire takalminsa, farar safarsa ta bayyana a nutse ya miƙa hannunsa inda Safwan ya zo ya janyo shi jikinsa yana faɗin" Fine boy, waye ya shirya ka haka?"

Safwan ya yi murmushi ya ce" Dad papy ne ya shirya ni, ka ga jikina sai ƙamshin manya nake yi."

Ido ya ɗan zaro zai sake yin magana Aba ya ce" Ma sha Allah, ga amaryar nan tafe."

Wani irin yammm da jikinsa ya masa sai da ya ɗan lumshe ido, a nutse ya kai dubansa inda ƙannensa da Abrar da matar Humed suka miƙe suna ɗaukan vidio domin a tsakiya Anna da aunty Intisar suka sakata.

Idanuwansa ya sauke a hannayenta da suke cikin na Aunty Intisar da kuma Anna sannan ya ɗan ɗauke dubansa ya kai kan Safwan da yace" Dad kalli amarya, la'ilaha illalahu, to wa ye ya yi aure bana nan?"

Ido kawai ya zubawa yaron, kunayensa na jiye masa kalaman da suke tashi a kan saukowar tata da yi mata oyoyo da suke yi sai video suke yi na saukowar tata cike da farin cikin ganin tufafin jikinta ashe an canza? A da shadda ce aka so saka mata, amma a yanzu an maye gurbin shaddar da fari ƙal ɗin lesh lallausa mai kyan gaske, wanda ya ɗauki ɗinkin doguwar riga ta bi lafiyar jikinta ta yi mata ɗass, shigowar aunty Furera ya saka Nabihat da wani irin takaici ke neman kashewa ɗauke dubanta daga kan su ta maida kan Aunty Furera dake sallama tana gaishe da jama'ar falon ta shiga tafawa ita ma ta bi ayarin su Abrar.

"Jikan Anza?" Aba ya faɗa da ɗan ƙarfin da ya saka shi ɗagowa ya kalli Aba da sauri, Aba ya ce" Ka zama gentlemen mana, ka karɓeta a hannun Annar ku mana, me ye haka? Haka ka ga ina yi ne?"

Yawun bakinsa ya haɗiye da ƙyar sakamakon dariyar da suka ɗauka, ai kuwa Anna ta saki hannun Yusrah da aunty Intisar suka sauko Anna na faɗin" Ai kam, kai ma dai ka faɗa, yaro sai wani abu yake yi kamar ba ɗan AA babba ba."

Wata dariyar diramarsu aka yi, ban da Nabihat dake zaune ranta na ƙara cinkushewa da abinda ake yi gaba ɗaya da irin yadda ake yin, tsayuwar sa a can ta kwantar mata da hankali sai gashi sun katse kwanciyar hankalin suna yin abu kamar da gayya?

A inda suka barta a nan take tsaye jikinta a mace murus, ta kasa saukowar ta kasa taɓuka komai, ta rasa me ma ake nufi da a karɓeta, abu ɗaya ta sani ba za'a taɓa ɗaukanta ba gaskiya, sai dai karɓar tata ma bata gane me ake nufi ba.

A nutse ya nufi wajen bayan ya kai Safwan ya zaunar da shi saman kujera ya ce masa ya zauna kar ya saki ya ɗago sai ya ce ya ɗago, ai kam ya zauna ɗin ya ci gaba da game ɗin sa domin bai gane amaryar ba, bai matsa ba, mayafin kuwa da aka yafa mata mai shara shara zai hana ka gane wacece daga nesa idan ba daman ka san wacece ɗin ba.

A nutse ya ratsa tsakiyar tagwaye dake ɗaukan vidion, yau ba zasu ɗaga ƙafa ba sai sun ɗauki komai gaskiya, domin hararar da ya watsa musu ma su dai basu wani damu ba saima ci gaba da ɗauka da suka yi, amma fa sun daina ihun da waƙoƙin da suke yi, aunty Furera kanta ta juya cike da jin kunya ta koma ta laɓe, haka ma Anna ta zaunawarta kusa da Aba, Tidin kuwa daga nesa take tana amsa waya ko dubansu bata yi dan bata da wata damuwa ko buƙatar duban nasu.

A nutse ya ƙaraso daf da ƙarfen matatakalar ya ɗan taka na farko a nutse ya hau ya ɗan lumshe idanuwansa bayan ya sake bin ƙafafuwanta da kallo wa'inda suke cikin takalmi fari sol plate mai laushi sosai.

A nutse ya miƙa mata hannun nasa daf da nata yana kallon ta, ai Manal kasa riƙewa ta yi, ta yi wata shewa shewa da ta sa Yusrah ɗagowa da sauri bayan ta zubawa hannun nasa ido.

A fuskarsa ta sauke dubanta, inna lillahi, kai inna lillahi, ita Yusrah balagaggiyar budurwa ta zo a gaban iyayensu ta kama hannun ƙato? Allah ya kiyaye, idan ta aikata haka ta tafi zirrr kenan? Ina ita ina aikata wannan tashin hankalin? Ƙasa ƙasa ta ɗan harari gefe ta maƙale kafaɗarta bayan ta ƙi amsar hannun, hakan ya sa yaran zaro ido tare da shi baki ɗaya.

Ɗayan hannun nasa ya kai ya dafe kugu, sai kuma ya juyo ya dubi ƴan matan Anna ƙasa ƙasa ya ce" Ku juya kai za mu yi sirri."

Kaɗan ya hana Manal cewa babu inda zata juya, sai dai tunawa da ta yi waye sai ta juya ɗin bayan ta cika kunci, ƙasa ƙasa sosai ya ce" Ki ɗan rufawa kanki asiri ki kama hannun nan in kai ki can in zaunar, kin ji Y. Turaki?"

Yusrah ta ɗago ita ma ƙasa ƙasa ta ɗan saki harara ta ce" Ina ni ina kai da zan kama hannunka? Allah kiyaye, ace me na yi kenan a gaban mutane?"

Baki ya yatsina ya ɗan juyo ya kalli mutanen falon, kowa ya juyar da kansa ban da Aba jama'a, Aba ya masa ƙyam yana wani murmushi jama'a, shi wallahi bai san wanda ke bayan tunanin ɗan Anza ba, wani lokacin idan ya yi wani abun sam ba kyau.

Ƙasa ƙasa ɗin ya sake faɗin" Ke idan ban ɗauke ki ba ubana goma, ni zaki rainawa wayo Y. Turaki? kwarto kika ɗaukeni ko me? Dilla miƙo kafin in maki ɗaukan jarirai."

A zabure ta zuba masa ido ta shiga auna gaɓoɓinsa a ranta ya fi a irga, sai da ta gama yarda cewar idan ƙwanji za'a gwada bata da riba a kokowar sai ta sadda kai ta fito da hannun nata fili amma ta ƙi ajiye hannunta a hannun ƙato, gaskiya ba zata aikata haka da kanta ba.

Harare ya sakar mata kafin ya kamo hannun a hankali ya sauka ya jira ta sauko sannan ya ja ta a nutse ya kai ta daf da Anna ya zaunar da ita a shinfiɗar da aka yi mata gaban Anna da Aba.

Aba ya saki murmushi ya wani langwaɓar da kai ƙasa ƙasa ya cewa Anna " Ji soyaya dan Allah?"

Anna ta sadda kai ta yi kamar bata ji ba, dan ta kula idan ta biyewa Abansu sak zai sa ta shiga uku dan kunya a wajen nan, ko dan ya jima yana jiran ranar nan? Tunda aka ɗaura yake sakata a uku da zanceceku kala kala, idonta idonsa ya ce shi ya yarda lafiyar ɗan sa ƙalau, amma zata gani kwana kusa, tun daga lokacin take kiyaye fira mai tsayi a kan lamarin nan da shi.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:53 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*71*




A nutse ya koma ya zauna sannan ya dubi ɗan sa ya ga lamarinsa yake yi wallahi sai kawai ya ƙyale shi bai shiga sabgarsa ba.

Cikin nutsuwa, cike da wayewa su huɗun nan suka gabatar da kyautar da ta saka aunty Furera gigicewa ta yi tsuru tsuru tana kallon ikon Allah, Anna ke karɓar kyautar ta yi addu'a sosai ta yi nasiha ta nuna cewa daga yau ta zama yayarsu, ta zama ɗaya daga cikin wa'inda suka isa da su, tana da damar yi musu faɗa ko nasiha, idan suka kauce zasu haɗu da fushin Yayan su ne.

AA dake kallon ikon Allah shi da kansa kyautar nan ta bashi mamaki, eh lalle ya yarda tana shigowa rayuwar mutum kamar an jeho ta ne sannan ta gaje komai da komai, ya yarda sun amsheta, hakan kuma ya sanyaya zuciyarsa.

Tidin kallonsu take yi da mamakin irin dukiyar da suka bayar wa matar da aka ce auren haɗi ne, lalle ahalin Yayanta sun yi nisa sai fatan Allah ya sa idan sun haɗu da macuciyar ta barsu da ransu.

Nabihat dake zaune gaba ɗaya jikinta rawa yake yi, kwaliyar da aka yi mata duk irin kuɗin da aka kashe da sanyin falon nan gumi ke neman wanketa ta zubu kan farar shaddar da ta je ta siya ɗinkakkiya da uban tsadar tsiya a babban burin ta tozarta lokacin nan na Yusrah, amma abin ke neman juye mata? Da ƙyar ta iya lalubo nutsuwarrta a lokacin da ta fuskanci ana watsewa cikin dabara ne, dan iyayen suka fara tafiya, ƴan matan suka fita filin gida suna ta ihun vidion da suka samu, aunty Intisar da aunty Furera suka haye da dukiyar Yusrah, Humed ya ja matarsa suka fece ya zamo an bar su su huɗu ne, shi yana zaune ne yana kallon take taken kowa, Safwan na buga game, Yusrah kanta a ƙasa dan tunda aka fara abin kanta ke ƙasa ta rasa a irin halin da zuciyarta take ciki, sai Nabihat dake zaune, kyautar ma bata samu ta yi ba sai yanzu da idea ta faɗo mata ta miƙe tana rangaji ta nufi inda Yusrah ke zaune ta kashe murya ainun ta ce" hi, ga nawa kyautar, ina fatan zaki anfana."

Yanayin da ta yi furucin kaɗai ya isar wa da Yusrah saƙon wacece, a hankali zuciyarta ta shiga raya mata _'Dama tana nan? Dama tana gidan? Saƙo? Kyauta? Nabihat? Nabihat? Nabihat fa, ita ce wace aka kai kuɗin aurenta da AA?'_

A nutse ta ɗago kanta, inda su Aba suke ta fara kaiwa dubanta, ganin wayam basa nan a hankali ta ɗan ringa satar ƙafafu, nan ta gane daga su sai su fa, a nutse ta dafa ta miƙe daga zaman da aka sa ta yi ta sauke dubanta sosai a fuskar Nabihat, duban ido cikin ido suka yiwa juna na ƴan sakanni kafin ta kai dubanta inda yake zaune.

Ya yi zaman nan na hamshaƙai, cikakkun maza, ya wani ɗan kashe dubansa yana kallon su, kallon da haka kawai ta ji bai yi mata ba, bata san dalili ba amma kallon nan ya dace ace idan an halasta maka mace kawai zaka yi mata shi, amma shi gaya nan yana yiwa yarinyar nan, dan sak ta kama shi yana kallon yarinyar nan fa.

Kai ta ɗauke ta sakar mata murmushi ta saka hannu ta amshi envelope ɗin, bata buɗe ba ta nufi inda yake zaune ƙasa ƙasa ta ce" Ya dace ki wanke fuskarnan, dan kwalliyar ta caɓe fa..."


Nabihat da ta so ace shine ya fara yabawa kyautar nan ta ga ta nufe shi bayan ta yaɓa mata maganar da take iya kira da mummunan zagi ta ƙarasa inda suke zaune ta duƙa sosai a gaban Safwan tana yalwata fuskarta da murmushi bayan ta ajiye envelope ɗin a saman ƙafar AA, da sauri ya kalle ta ya kuma kalli cinyar sa da ta ajiye envelope ɗin, wato shi ga wanda ta raina ba, saboda an gaya mata shi ɗin drower ne ko gadon ɗora komai nata? Ita kam ba da niyyar komai ta ɗora ba sai dan haka kawai abun ke zuwa mata, ko ranar ma da ta ɗora pizzar ta anan bata ga wurin ajiyewa bane, ido ta zubawa Safwan zuciyarta cike da farin cikin ganin sa, da kuma mamakin duk abin nan da ake yi bai san ana yi ba ya tsunduma a duniyar waya, ta miƙa hannu zata janye wayar ya saka hannunsa ya riƙe nata hannun, wanda hakan ya sake haifar musu da faɗuwar gaba kamar dai ɗazu da kuma ranar can a U.S, bai san me ya sa ya ji har tsikar jikin sa ta tashi ba, amma sai ya basae ƙasa ƙasa sosai da gogaggen french ya ce" Tu veu forcement faire de ca une habitude jeune fille? Pourtant c'est une mauvaise habitude hein?" (Kina so ƙarfi da yaji ki mayar da ɗora min abu a nan sabo, bayan muguwar sabo ce ƴar budurwa?"

Ido ta zaro kaɗan ta kalli cinyar tashi, sai kawai ta ɗan ɗage masa gira alamar _'To daman fa?'_

Sai kuma ta ja hannunta dan ta janye, shi ma ya ja ya riƙe yana ɗan waro idanun shi da yi mata alamar ta ɗauke fa ko ya tattaka ta, kamar wata jaririya sai kuwa ta ɗan turo baki gaba sannan ta maƙale kafaɗa alamar um um ba za ta yi ɗin ba, da fari da mamaki ya sake zuba mata idanuwa, sai kuma ya ɗan karkata ya mata alamar _'Da gaske?'_

Kafin ta bashi amsa Safwan ya ɗago ya bi hannayen da kallo da mamaki ya kalli Yusrah sannan ya kalli Abansa, idonsa ya sadda da sauri, duk irin yadda ya ji wani irin farin cikin ganin Yayarsa, lokaci ɗaya ta janye hannun ta da sauri ɗago da fuskarsa ta ce" Safwan?"

Safwan ya saki dariya ya faɗa jikinta yana faɗin" Aunty Yussy, inna lillahi! Wai dama ke ce amaryar? Kai kai kai, aunty Yussy to wa ye angon?"

Daga ita har shi sai da suka ji kunya ta kama su, ta kasa amsa shi, sai ma ta miƙe ta ajiye mayafin ta shiga faɗin" Oya taso in ga tafiyarka? Taso in gani babban gidanmu?"

Inda oga kuma ya ɗauke kai gaba ɗaya daga gare su kunnuwan shi na jira ya ji amsar da za ta ba Safwan, amma idanun shi akan Nabihat da ta gama sarewa lamarin su take daf da fara ɗurawa Yusrah ashar, wallahi da gangan ya tsare Nabihat da idanu yana kallon ta, shi sai yanzu ne ma ya ke ƙarewa shigar ta kallo yana nazarin anya ƴar nan ta Chef kan ta ɗaya kuwa? To kaya ta saka irin wanda ya kamata ace amarya ta saka, duk da bai san komai akan suturar mata ba, amma wannan shirin da ta yi shi ya san bata yi shi a inda ya dace ba, baya ga haka ga wata uwar kwalliya da ta zuba a fuskar ta, abun ai ya yi yawa a ganin shi, to me ye nufin ta? Me ma ya sake dawo da ita gidan nan wai ta tare? Sai an ɗaura musu aure take nufi ko me?

_'Hmmmmmm!'_ Da Yusrah ta faɗa a ƙasan maƙoshi ne ya sa shi ɗan karkato duban shi gare ta, haɗa idanu sunayi ta tsare shi da wani kakkausan kallo kamar mai jin haushin sa ko mai aika masa da saƙon gargaɗi, da narkakkun idanun shi ya mata alamar _"Ya dai Y. Turaki?"_

Ƴar harara ta cilla masa tare da murguɗa baki ta dubi Safwan ta miƙe tsaye tace" Babban mu, taso mu je ciki ko? Mu bar Dadyn ka zai yi zance ne da fiance ɗin shi."

Zaro idanu ya yi ya kalli Safwan da shima ya juyo ya kalle shi, ya dai fahimci komai a maganar ta amma ban da kalmar fiance ɗin dan gaskiya karatun shi bai kai can ba, ganin Safwan ya ɗauke kai daga gare shi sai kawai sake duban ta a kausashe yace" Y. Turaki."

Miƙewa tayi tsaye sosai ta ɗauki mayafin ta tana kallon shi, da idanu ta masa signa da Nabihat dake bayan ta tsaye, sannan ta ɗan nunoshi da yatsa alamar _kai da ita_, sai kawai ta yi wata alamar da yatsun ta irin dai _Kun dace fa_, sai kuma ta saki wani murmushi tare da masa kallon sama da ƙasa sannan ta kai hannu ta ɗauko envelope ɗin dan kar Nabihat ta ga ko ta raina ne,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login