Showing 126001 words to 129000 words out of 397328 words

Chapter 43 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70020

barcin ba ta dai cire hijabinta yana ajiye saman jikinta ta yi barci hakan yasa ribom ɗin kanta ya kunce barci mai nauyi cikin ikon Allah ya kwasheta.

Ajiyar zuciya Intisar ta sauke a hankali ta je ta zauna gefen ƙafar Yusrah cike da tausayawa ta yi mata addu'ar bacci kamar ta samu yarinya ƙarama sannan ta tashi ta rufo mata ɗakin bayan ta kashe mata fitila ta nufi ɗakin mijin ta tana jin jikin ta da sauki sosai, ba kamar drip ɗin da ta sha na ɗazu ba dan ciwo, amma yanzu Alhamdulillah.



*AUNTY FUREIRA*


Goggo ba ta san ba za'a daina zuwa gidan ta neman Yusrah da Safwan ba sai yau da rana tsaka da aunty Fureira ta sallamo gidan, ƙwarai ta kai maƙura da wannan zuwa mata gida da ake neman su bayan ita ma bata san ina suke ba, kuma yanzu za ta fara bala'i da kowa dan ta gaji fa. Abinda bata sani ba ita kan ta aunty Fureira da ta zo da shirin kar ta kwana ta zo, ta zo ne ayi kowace amma sai ta fito da yaran nan, ba zai yiwu tana Yayar uban su ba sannan ta ce ba ta san ina suke ba, kenan barin su ta yi suna gantali a titi? Ƴar ta na can tana jinyar ƙuna amma haka ta barota dan su Yusrah ma kamar ita ta haife su take ji, sannan ta yi faɗa kamar bakin ta zai tsinke da danginsu suka koma mata da labarin wai basu ga su Yusrah ba, shiyasa ta baro yarinyar ita ta zo da kan ta sannan ta neme su kusfa-kusfa.

Tun daga yadda suke gaisawa bayan kishiyar Goggon ta bata kujerar zama za ka gane kowa a tsaye yake yana jiran tak ne, saida aunty Fureira ta dafe ƙugun ta daga zaune tana ma Goggon dake ƙullin kunu a leda wani kallon sama da ƙasa tace "Hinda akan maganar yaran nan ne na zo, ina so na san inda suke?"

Ita ma Goggon a wani fizge ta kalle ta sannan ta yatsina baki ta ci gaba da abinda take tace "Ban san ina suke ba Hurera, Yusrah ba jaririya bace da za ta kasance goye a bayana, dan haka ita tasan inda ta nufa tare da ƙanin nata."

Aunty Fureira na wata irin jijjiga daga zaune tace "To amma garin ya ya aka rasa inda suke? Matsayin ki na babba ba ke ya kamata a ce kin basu masauki ba?"

Sheƙeƙe Goggon ta kalle ta tace "Ba'a gaya miki daga asibiti bane ta gudu, hatta Iya dake tare da su tana jinyar Safwan ɗin neman ta tayi ta rasa."

Girgiza kai aunty Fureira tayi tace "Koma dai menene ɓatan su Yusrah da sa hannun ki, wallahi yau idan suka shiga mugun hannu ko rayuwar su ta salwanta duk ke ce sila, ba zan kasa faɗa miki gaskiya ba Hinda dan ke kin san bana ɓoyeta idan dai har gaskiyar ce, dama a waya Yusrah ta faɗa min irin abubuwan da kike mata tunda aka yi rasuwar nan, ban kuma yi mamaki ba dan nasan kin aikata fiye da haka, kuma wallahi ki sani mutuwar nan tana kan kowa, jiya Yaya Abdul-Hamid ne da aunty Habiba, gobe kuma ke ce Hindatu kuma kina da ƴaƴan nan kema."

Aje ɗaurin kunun ta yi daga zaune cike da masifa tace" Hurera me kike nufi? Ya zaki sameni har cikin gidana ina tsaka da yin abinda ya fi sha min kai, ki nemi ki gaya min magana? Yusrah ce miki tayi na zage ta? Ko na dake ta? Ko ta ce za ta zo nan ta zauna na hana ta? Haka kawai za ki nemi ki taka ni, dama tunda kika shigo na san da abinda kike nemana da shi, to ki ji da kyau nima ina daidai da zamanon ki wallahi."

Sai kuma ta miƙe tana jan kujerar ta zuwa cikin rumfa dake can ɓangaren ɗakin mijin su tana ci gaba da faɗin" Daga yau kar uban da ya sake zuwa min gida neman wata Yusrah, ina ce da ta zo shekaran jiya lambar ki kaɗai ta amsa ta juya ko gaisheni ba ta yi ba a gidan nan, bugu da ƙari Yusrah bata cikin wata damuwa saboda ta canzawa kanta rayuwar da take ganin ta fi dacewa da ita, haka kawai kowa ya kwaso baƙar ƙafar shi dai gidan Hinda gidan Hinda kamar ni na haife su."

Da takaici aunty Fureira ta miƙe ita ma tana faɗin" Kya faɗi haka yanzu tunda ɗan uwan ki ba ya raye, tabbas ba ke kika haife su ba, amma ki sani wallahi tallahi akwai ranar da za ta zo da zaki alaƙanta kan ki da su saboda kina so a ce ke ce dolen su, a wannan ranar kuma idan kin isa Hinda Allah ya tsine min..."

Ta ƙarashe da hargagin da ya saka kishiyar Goggo fitowa tana kallon su jiki a sanyaye, ba ta saka baki ba goggon ta koma kan ta, cikin ɗaga murya Goggon tace" Baƙin fata kike min? To ki sani ni ban ma ga ranar da za ta zo ɗin ba da har zan danganta kaina da su ba, idan kuma wannan ranar ta zo ki ɗauki matsayin nawa Hurera na bar miki har abada."

"Subhanallah! Hindatu, Fureira me yake faruwa ne haka? Lafiyar ku ƙalau?" Mijin Goggo da tun a ƙofar gida yake jin muryoyin su ya faɗa yana duban kowace, aunty Fureira ce ta nuna masa Goggo a wulaƙance tace "Ni da Hinda ne, furuci take ta yi marasa daɗi akan ƴaƴan ɗan uwan da take yaƙe masa baki da yana da rai, amma tunda ya kwanta damar shi yaran sa suka zama kamar almajiri, abun takaici Hinda ta fi ɗaukar wannan banzan kunun..."

Ta faɗi kunun tana mai saka ƙafa ta yi cilli da bokitin dake ɗauke da kunun fiye da rabin sa duk ya zube a ƙasa sannan ta ƙarasa maganar ta" Ta fi ɗaukar sa da daraja sama da su, ace kwana uku cikin na huɗu sukayi a asibiti amma har aka rasa inda suke ba ta taka ta je ba saboda tsiya ta gama baibaye ta."

Da wani irin tashin hankali Goggo da ta ga ɓarnar da aunty Fureira ta mata ta kwatsama wani irin salati ta taho da sauri saboda ƙibar ta ba zata barta tayi gudu ba tana faɗin" Hure ni kika zubarwa da kunu, in na yarda Allah ya tsine min, Billahillazi sai kin biyani kowace asara, in hauka ne a kan ki wallahi yau zan sauke miki shi Hurera dan kutum..."

Riƙe hannun ta mijin nata ya yi yana faɗin" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hindatu wai kuna da hankali kuwa? Me ye haka?"

Wani kallo ta masa tana son ƙwatar hannun ta tace" Sakeni dan Allah malam, ban da hankali, kai baka ga abinda ta min ba, sanin da ka min ina yarda da asara ne ko ta sisin kwabo? Bare na fara ɗaukar ta yau ɗin nan."

Kallon aunty Fureira ya yi yace" Fureira, ki yi haƙuri dan Allah, ni kaina saida na gaya mata bata kyauta ba abinda ta ma yaran nan, amma ta ce babu ruwana ba abinda ya shafeni bane, ki yi haƙuri dan Allah ki je, na miki alƙawarin ni da kaina zan kiraki idan aka samu ko da labarin su Yusrah ne."

Kallon shi tayi duk da tana girmama shi amma tace" Baban Khadi, zan tafi, amma idan kaga na fita daga nan to ta kwatanta min gidan su Maryam ne kawai."

Goggo da takaici ke neman kasheta ta saki baki tace" Iyehhh! Lallai ma."

Mijin Goggo kuma cewa ya yi" Wace Maryam kuma?"

A tausashe aunty Fureira tace" Ƙawar Yusrah ce, da na haihu tare suka je har Funtuwa kuma suka dawo tare, ita ta yiwu ta san wani abun da ba kowa ya sani ba."

Kallon Goggon ya yi yace" Hinda, kin san gidan ne? Kwatanta mata dan Allah?"

Kamar za ta fasa gidan tace" In na kwatanta mata kar na matsa daga nan, kai har ni za'a wa buru'uba? Ni Hinda dake cin Jibiya da Kano, kaf ƴan tasha ba wanda bai san Hinda sana'a goma ba."

Tsaki aunty Fureira tayi da wani shaƙiyin murmushi tace" Shiyasa dama nace miki a shirye na zo gidan ki yau, dan abinda yake saman kan ki nake son sauke miki dan in baki tabbacin ba ke kaɗai kika iya buru'ubar ba."

Kishiyar Goggo ya kalla yace" Hafsatu, ke baki san gidan su Maryam ɗin ba?"

Girgiza kai tayi a sanyaye tace" Wallahi ban ma san Maryam ɗin ba."

Tana ajiye maganar ta Safiya da ƙannan ta suna shigowa daga islamiyya, dan haka ya dubi Safiyar yace" Ke Safiya, kin san gidan Maryam ƙawar Yusrah?"

Tana kallon aunty Fureira da Maman ta da taga kamar ba lafiya ba tace" Maryam? Wannan ƴar makarantar su? Na san gidan."

Da wani irin farin ciki yace" Yawwa, Alhamdulillah, Fureira, ga Safiya nan ta kwatanta miki, ke kwatanta mata gidan."

Nan Safiya ta kwatanta ma aunty Fureira gidan ta juya ta fita ko sallama ba ta ma kowa ba ta dai ɗauki kayan ta kawai, Goggo kam ai kamar za ta yi kuka an zubar mata da kunu, hakan ya jawo ma duka gidan wani masifaffen wuni, dan har yaro mai rarrafe yau ya shaida ranta ɓace yake, motsi kawai da bai mata ba za ka yi za ta zagi uban ka har da kakanin ka, in la ka san su ko baka san su ba labarin su ka ji, waɗanda ke kusa da ita kuma duka ba laifi sun sha daidai gwargwado.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*34*




Aunty Fureira duk da ba gari ta sani sosai ba, amma haka da jakar kayan ta ko gidan Aminu da take cewa za ta je ta kwana bata je ta kai kayan ba, burin ta ta ji ina su Yusrah? Haka ta kama hanyar gidan su Maryam kamar yadda Safiya ta kwatanta mata, kuma bata sha wahalar ganewa ba, yaro ɗaya ta tambaya ya nuna mata har ƙofar gidan.

Da sallama ta shiga Maman su Maryam ta amsa da Maryam ɗin kan ta da yau ita aikin gadi ne za ta yi, Maryam ce ta gane ta sosai ta tarbe ta da farin ciki, kafin ta gaya wa maman ta alaƙar aunty Fureira da Yusrah ita ma ta shiga yi mata sannu da zuwa, tabarma suka shinfiɗa mata Maryam ta aje mata ruwa har da kunu aka saka ƙanƙara a ciki ya yi sanyi saboda ko ba ta faɗa ba an san ta ɗauko rana tunda kwana biyu ba'ayi ruwa ba saboda watan markan ya ja baya sosai.

Ruwan kaɗai ta iya sha sannan ta aje ta kalli Maryam da ta tambaye ta ina baby da suka je biki? Cikin nutsuwa ta bata amsa da "Maryam Iman tana gida na barota, dake ƙonewa tayi da koko a safiyar da zamu taho nan, hakan ya dakatar da zuwana ni sai yanzu."

Da jimami suka shiga jajanta mata tana amsawa, can daga bisani ta sake duban Maryam sosai tace "Maryam, neman ƙawar ki na fito, ina fata ko ban samu labarin Yusrah a ko ina ba na samu a wajen ki, dan Allah ina Yusrah take? Me kuma ya faru da har ita da Safwan suka rabu?"

Da farin ciki Maryam saboda tana da amsar tambayar aunty tace "Aunty Fureira, abinda ya raba Safwan da Yusrah babba ne, sai dai daga baya mu kanmu mun fahimci kuskure ta aikata, nan t zo da dare ta ce mana..." Duk labarin abinda ya faru har ya janyo rasa Safwan ta faɗa mata, sannan ta ɗora da "Yusrah kuma aunty jiya warhaka ma ina tare da ita a gidan da take zaune."

Da sauri aunty Fureira ta riƙo hannun Maryam tace "Da gaske Maryam? Yanzu haka kinsan inda Yusrah take? Kuma a garin nan?"

Jinjina mata kai tayi tace "Tabbas aunty Fureira, Yusrah tana garin nan, jiya muna tare da ita har bayan sallah isha'i kafin na zo gida."

Lumshe idanu aunty Fureira ta yi tare da sauke nauyayyar ajiyar zuciya ta furta "Alhamdulillah! Allah na gode maka."

Sai kuma ta kalli Maryam sannan ta kalli Maman su dake murmushi tace "Maryam ba kuskuren Yusrah bane ita kaɗai, har da ke ma da kuma mahaifiyar ki, dan Hindatu ma da ƴaƴan ta abar maganar su, amma zan faɗa muku gaskiya ko da ba zaku ji daɗi ba."

Sosai ta kalli Maman Maryam tace "A sanina Baban su Maryam baya raye, sannan baki da matsala ta tunanin barin gida a hannun wa? Maryam Yayun ta maza biyu ita ta uku ga kuma ƙannan ta, ko iya hannun Yayun Maryam kika bar gidan nan na shekara ɗaya wallahi na tabbata ba zaki je ki dawo ki tarar da abinda ran ki zai ɓace ba, da Yusrah ta sanar da ke halin da ake ciki, shin da ba ƴan uwan ki bane shiyasa kika gagara zuwa ki karɓa mata Safwan a hannun Iya Abu? Idan ke baki je ba, a cikin Yayun Maryam biyu babu ɗaya da zaki iya umarta ya je ya zauna da shi kafin ita ta kammala? Bayan ma duk wannan, a matsayin ki na uwa gare ta, me ya sa baki nuna mata hakan kuskure bane? Zai fi ki nuna mata ko da iya kuɗin da ta samu ne ta je ta kai, a wace rayuwa ce ba'a alfarma da su likitocin ba zasu karɓi abinda ta kawo ba? Sannan ke Maryam..."

Ta faɗa tana kallon Maryam tace" Tun washe garin ranar da kika je asibiti kika duba shi kika sanar da ita har ta ji daɗi, shin kin sake yin gaban kan ki kin leƙa Safwan?"

Sai kuma ta ja numfashi tana kallon ƙofar shigowa tace" A gaskiya ba zan ɓoye muku ba, wallahi ban ji daɗin abinda kuka yi ba, sai naga kamar babu zaman tare a lamarin, sannan na sake yarda lallai su Yusrah sun riga da sun zama marayu tunda har suka rasa iyayen da suka haife su, yanzu gashi nan, Safwan ba wanda zai ce ga inda yake, sannan ita ma tana can tana garari a gidan mutane kamar wata almajira, saboda ita kunya da kawaici sun hanata neman taimakon ku akan wani ya je ya zauna mata, ku kuma kun kasa yi mata kara da kawaici ku zauna mata da ƙanin nata na kwanan da bai fi biyu ko uku ba."

Maryam ta kalla tace" Za ki iya rakani gidan idan babu abinda kike yi?"

Jiki a sanyaye Maryam ta gyaɗa kai da cewa" To, tun safe ma nake ta kiran ta dan naji ya suka kwana, saboda matar wanda ya taimake ta wata irin jarababbiya ce, wallahi jiya ma da ƙyar muka sha, dan ta yi yunƙurin sai ta ƙona Yusrah, sai da na samu na bulbule mata fetur ɗin da ta zo da shi a jiki kaɗai muka samu lafiya."

Zazzaro idanu aunty Fureira tayi tace" Me? Yusrahn da za ta ƙona? Akan me to? Yusrah dai."

Da jimami Maryam tace" Wallahi wai tana zargin ko mijin ta yana son Yusrah ne, shine dai take ta kiran ta karuwa da ɓatanci kala kala."

Yunƙurawa aunty Fureira ta yi tace" Maza maza Maryam, tashi muje ban ga ta zama ba, Yusrahn ce za ta ƙona da fetur? Wannan zaman ta a gidan ma ai haɗari ne."

Miƙewa Maryam ta yi da sauri ta shiga ɗaki dan ɗauko hijabin ta, inda aunty Fureira kuma ta sake duban Maman Maryam tace" Hmmmm! Na tabbata dai Maryam ta baki labarin haɗarin da Yusrah ke ciki, amma na zo na same ku hankalin ku kwance ba wani yunƙuri na cewa za ki je ki taho da Yusrah nan..."

Girgiza kai tayi cike da takaici tace" Maman Maryam rayuwar nan fa bata da tabbas, mutuwa kuma dole ce akan kowa, jiya Maman Yusrah ce, wataƙila kuma gobe maman Maryam, shin wane tabbaci kike da shi na ke naki iyalin zasu tsira daga wannan ha'ula'in da Yusrah ke ciki? Kina da garanti ne akan ƴan uwan ki za su riƙe miki su? Iyayen Yusrah ma babu wanda ya yi tsammanin za'a rasa mai tallafawa ƴaƴan su, shin kina ganin a maƙwabta ko abokan arziki akwai wanda za su tsaya kan damuwar su ne? Duka baki da wannan tabbacin, kamar yadda baki isa ki ce zaki kai anjima ba bare ki shiryawa yaran ki rayuwa mai kyau da ko bayan ran ki ba zasu tagayyara ba, alƙawari ne idan har ka taimaki maraya to Allah zai taimaki naka ƴaƴan sa'ilin da suka shiga maraici, amma ba ma tuna wannan a yanzu."

Jakar ta ta ɗauka kawai ta fice daga gidan dan ba za ta so jin wani abu daga bakin maman Maryam ɗin ba, dan ƙarara ta nuna ita nata kawai ta sani, Yusrah kuma idan an haɗu ne a yi dariya a yaƙe ma juna baki, bayan wannan ba wani taimako ko tallafi da za'a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login