Showing 252001 words to 255000 words out of 397328 words

Chapter 85 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70011

auren ta da shi bane, kawai dai na so abinda ya so ne, amma a wannan gaɓar kam ba zan zama shashashar uwa ba gaskiya."

Tana gama maganar ta kaɗe kai irin ta gama magana kenan, ƙwarai Aba ya ji zafin kalaman nata, amma saboda neman maslaha musamman idan ya tuna Yusrah da maraicin ta, sai ya sake haƙurƙurtar da kan shi yace" Dan girman Allah Hajia kar ki saka marainiyar Allah zubar da hawayen baƙin ciki, na tabbata yarinyar da tana da wani aibu da ta ɓoye mana da Aswan ya jima da gano mana shi, ko karen gadinmu bai yarda ya zauna a gidan mu ba saida ya san asalin ba kare mai mugun dafi bane, da kuma tana da wani abun ba zai duba alaƙarta da ɗan shi Safwan ba, tsaf zai yakiceta daga jikin mu, kai idan har duka danginta ya gano suna da wani aibun da ya san zai iya shafar mu, har Safwan zai iya haƙura da shi saboda yana sonmu fiye da komai a duniyar nan, da wannan nake sake roƙon ku kar ki yi abinda rayuka za su ɓace, ƙarshe wani zumuncin ya wargaje."

A ɗan zafafe Hajia ta juya gefen ta ta ɗauko wayar nan da ba ta rabuwa da ita gudun ma kar wanda ya turo mata ita ya ɗauke ko cikin yaran gidan ya buɗe sai kuwa akan vidion, da ƙyar ta taso daga kan kujera ta miƙo masa wayar tana faɗin" Duba fa ka gani Alhaji, dubi ka ga taron da aka y, dubi tarin jami'an da suka zagaye su, ka dubi shigar ta sannan ka dubi jikin wanda ke ikrarin matar sa ce, shin kuna da tabbacin ko ba matar sa bace babu wata mummunar alaƙa tsakanin su, yaran na yau Alhaji? Ɗan na yau da ka haife shi ne baka haifi halin shi ba, Alhaji wanda ka haifa ma a cikin ka kuke kwana a gida ɗaya sannan ku wayi gari gida ɗaya, zai iya yin abinda zai sumar da kai, bare wacce a titi kawai aka tsinto muku ita, shin iftila'in nan da ya faru ita kaɗai ya sama? Amma me ya sa ita kaɗai ce ke gararanba a garin nan ta gagara zama a cikin dangin ta ko gidan su? Na tabbata ak..."

Tunda Aba ya tsurawa vidion idanu yake kallo yana ƙara maida shi baya, muryar ɗan daban, da kamannin ɗan daban... Sun fi ƙarfin ya ce kamanni ne kawai, tunda har zuciyar sa ta doka da ƙarfin da sai ta ga masoyi kuma makusanci kaɗai take wannan bugun, sassan jikin shi suka karɓa, tsigar jikin sa ta tashi sannan jinin sa ya ƙara gudu a kowace magudana ta jikin shi, take a loakcin ya ji wata zufa ta karyo masa da tun shigowar shi dama yake jin zafin amma bai ji gumi a jikin shi ba sai yanzu, duk maganar da Hajia ke yi ko sauraren ta ba ya yi ya miƙe tsaye, ko a ina? Ko a ya ya? Ko a wane hali? Ko a wane irin canji ya ga Aswan zai iya gane shi, shi ya haifi abun sa, shi ya rene kayan shi, a gaban idanun shi ya girma, Allah ya tsare yau ko mummunan haɗari ɗan sa Aswan ya samu da za'a nemi tantance gangar jikin sa, cikin sauƙi zai fito da shi dan babu wata gaɓa dake bayyana a fili da bai sani ba ta jikin Aswan, uwa uba tsayar da vidion da ya yi a daidai inda ya ɗaga hannu ya ɗan kare fuskar shi sanda ya kula ana ɗaukar su, tabbas zoben dake yatsar sa ta tsakiya ne ya mayar a ƙaramar yatsa, kuma wannan zoben kusan shekarun su ɗaya da Aswan, dan su al'adar su ce ba ka haihuwar yaro ka zube shi kara zube dole sai ka saka masa ingantacciyar azurfa da babu sirki a cikin ta, dan har kariya tana yi daga sheɗanu ma, wannan ya sa tun kafin a yi sunan shi yake sanye da wannan zoben, idan ya ƙaru kuma akan cire ne a ƙara buɗa masa shi, har aka kai lokacin da shi yake zuwa ya bayar a buɗa masa kayan sa, dan haka ba ya cire shi a kowane hali.

A rikice sosai hankali tashe Aba ya furta " *ASWAN*?"

Hannun shi na rawa rawa ya miƙawa Hajia wayar yana duban ta da idanun shi da suka kaɗa suka yi ja tsabar ɓacin rai da gigita, cikin wata murya da ɗazu ba da ita yake mata magana ba yace "Magana ɗaya ta dattako nake so na ji, za'a yi auren ko ba za'a yi ba?"

Saida ta wani karkace kai sannan tace "Ba za'ayi ba gaskiya, shine magana."

Jinjina kai Aba ya yi yace "Shikenan, mun gode, Allah ya saka da alkairi, gobe za'a dawowa da Bilal abinda ya kai wa Yusrah in sha Allah."

Yana faɗin haka ya juya a fusace ya fice a falon ranshi ya matuƙar ɓaci da maganar Hajiar, dan gaskiya ba dan ya san ba daidai bane, da yau ya nuna mata iyakar ta ta hanyar dawo da Intisar gida ko dan ta ga yadda ƴaƴan ta za su kasance, amma ba komai ai rayuwa ce, ba za ta bar duniyar nan ba har sai ta samu da daidai ita.

Tunda ya shiga mota ya ji jikin shi kamar ba daɗi, dan haka ya miƙowa Sk wayar shi yace "Kira min jikan Anza."

Da ladabi ya karɓa ya nemo lambar Aswan ɗin sannan ya miƙo masa, a speaker Aba ya sa dan hannayen sa har yanzu rawa suke masa ta yadda ba zai iya daidaita wayar a kunnen shi ba, Aswan na ɗagawa yace "Kana ina?"

Saida ya ji wani tsammm! A jikin shi saboda jin yanayin muryar Aba, amma sai bai kawo komai a ransa ba yace "Ina tare da Mukhtar ne."

"Ka sameni gida yanzun nan." Aba ya faɗa tare da gimtse wayar ya cilla kan kujerar motar ya sake rufe idanun shi.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
07/06/2024, 18:12 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*63*



Duk da dare ya yi amma haka ya tarar da su Anna a falo kacaniya kawai suke yi, Anna da Abrar suna ɗuɗɗura turakun ruwa a mazuban su irin masu shegiyar tsadar nan da kyau da na wuta, su Nawal kuma nata ninke kayan Yusrah suna sakawa a akwatina saboda gobe sammakon gyaran ɗaki za su je su yi, aunty Fureira kuma tana ciro musu kwalaben a tsanake tana basu, idan suka zuba sai ta rufe ta ajiye a hankali, duk da tana farin cikin zaman ta da su, amma dai ta matsu gobe ta yi ƴan Funtuwa su zo dan su koma gidan su Yusrah tare sa Yusrahn, ba ƙaramin daɗi ta ji ba da suka karɓi buƙatar nan ta su, ko ba komai suna son keɓewa da Yusrahn dan suma akwai kayan gyaran da zasu zo da su wanda basu raina ba duk da bai kai wanda ake mata anan tsada ba, sannan suna so a ɗauketa daga inda aka birne cibiyar ta zuwa gidan mijin ta, duk da kwana ɗaya ne rak za su yi amma suna son haka ɗin, musamman da tuni Aba ya sa aka tayar da duk inda ya zube.

Gaishe da su ya yi da girmamawa sannan ya wuce wurin Aba, hakan ya sa Anna raka shi da kallo, dan shekaru ne masu yawa rabon da ta bi bayan shi idan ya shigo amma ya ce ta je su ci gaba da aikin su kawai, bayan ga damuwa ta gani a tare da shi amma ya nuna mata ba komai.

Daga yadda ya samu Aba a tsaye hannun shi ɗaya a baya ɗaya kume riƙe da waya, ba ya tiktok, amma yanzun nan ya sauke ta sannan ya samo vidion a sunan mutumin da ya ga ya ɗora vidion, kallo yake yana ƙara tabbatarwa kan shi *shine fa*, AA na shigowa Aba ya juyo a hassale tare da mayar da duk wata wasa a gefe duk da kuwa ya gane kallon da AA din ke masa na mamakin yanayin shi, amma shi ya san bai ga komai ba ma har sai ya tabbatar masa da gaskiyar shine a hoton nan zai ga asalin ɓacin rai.

Wayar ya nuna mishi tare da kausasa murya yace "Wa ye a vidion nan?"

"To fa." Ya ambata yana wara idanun shi kan screen ɗin wayar, shi kan shi duk jarumtar shi saida gaban shi ya faɗi a lokacin, kallo ɗaya ya ma vidion ya fahimci komai, dan haka a nutse ya ɗaga idanun shi ya kalli Aba da irin yanayin marairaicewa da aika saƙon _'Aba ka min rai, ka zauna muyi magana.'_

Wata muguwar tsawa Aba ya daka masa ya sake faɗin "Aswan da kai nake magana, na ce wa ye nan? Me ka sani game da wannan ɗaukar? Ka bani amsa ko ran ka ya ɓace yanzun nan."

Take jikin shi ya yi sanyi ya fahimci girman abinda ke jiran shi a gaba daga gurin Aban, sai kawai ya sadda kan shi ƙasa a ladabce sosai murya a tausashe cike da tarin nadama yace" Ka yi haƙuri Aba, ni ne."

A dai shekarun da zai ce bai manta wani abu da ya faru da shi ba, ba zai iya tuna ranar da Aban ya ɗaga hannu a kan sa ba, amma sai gashi yau Aba ya ɗaga hannu ya wanke fuskar shi da mahaukacin marin da ya saka shi rintse idanu tamau tare da tangaɗawa ya yi baya sannan ya koma ya tsaya kan ƙafafun shi, bai kuma buɗa idanun shi ba sai ma sulalewa da ya yi ya gurfana a guiwoyin shi, yana jiran ya ji yadda Aba zai yi da shi ba shi da ta cewa yau kam, sama sama ya dinga jin muryar Aba na magana saboda ya maru fa, har jin shi saida ya samu naƙasu, amma a haka yake tsintar faɗan Aban cikin zafin ran da bai ta;a kwatanta yi masa ba yana faɗin "Ashe ƙin jin ka har ya wuce inda nake tunanin shi Aswan? Ashe za ka iya aikata duk wani ta'addanci da aka ce min ka yi babu kokonto? Aswan dama kaine wanda ya lalata rayuwar yarinyar nan, sannan kake ci gaba da lalata mata rayuwa a kowace daƙiƙa? Yanzu ka san me kuskuren ka ya haifar? Ka san me wautar ka da banzan tunanin ka ya saka mutane a ciki? Saboda k..."

Sai kuma Aba ya shaƙo wuyan rigar shi ya miƙar da shi tsaye yana nuna shi da yatsa yace" Maganar da nake maka yanzu uwar Bilal ta ce ba za ta taɓa bari a yi auren ta da shi ba saboda wannan vidion, saboda tunanin ta shine wannan na hoton abokin iskancin yarinyar ne ko dai wani abu daban, yanzu me ka aikata kenan? Akan wane dalili za ka saka ƴar mutane a jafa'i?"

Shiru ya yi ya kasa cewa komai, dan haka Aba ya sake daka masa tsawa da cewa" Ba da kai nake magana ba? Me ye duk wannan abun? A ina ne? Yaushe aka yi? Akan me hakan ya faru? Sannan wace shigar banza ce wannan ka yi?"

A raunane ya ɗago yana buɗa idanun shi ya kalli Aban, a tausashe sosai yana jin jikin shi na ƙara rikice masa yace" Ka yi haƙuri Aba, kar ka jawo wa kan ka wata matsalar, idan ka nutsu zan sanar da kai komai, na yi alƙawari."

A tsawace Aba yace" Maganar banza, ka san maganganun da na sha yanzu a wajen tsohuwar nan saboda wannan vidion? Shine kake faɗa min sai na nutsu za ka min bayani? Aswan dama haka ka rainani?"

Idanun sa ne suka cika taf da ƙwalla ya girgizawa Aba kai kamar zai fashe da kuka, muryar sa na neman shaƙewa yace" A'a Aba, dan Allah ka sassauta, kar wani abu ya same ka a d..."

Katse shi Aba ya yi da faɗin" Tashi ka ɓace min da gani..." Sai kuma ya juya masa baya a dake sosai ya ɗora da" Kar na sake ganin ƙafar ka a gidan nan har sai ka ji hukuncina a kan ka."

Duk abinda yake yi yana yi dan iyayen sa da ƴan uwan sa ne, ba abinda Allah ya jarabce shi da so kamar waɗannan ahali, ya kenan yanzu da Aba ke neman raba shi da su? Lumshe idanun da ya yi ya sa hawayen da bai san sun taru haka a gurbin idanuwan shi ba suka gangaro masa a saman kumatu har cikin gemun shi, kallon ƙeyar Aban ya yi a raunane yace "Aba..., dan All..al..."

"Ka tashi na ce kafin ka ji wani mummunan furuci daga bakina da zai ɗaiɗata rayuwar ka." Aba ya faɗa ba alamar wasa, jiki a saɓule ya miƙe yana kallon Aban ya juya zai fice Aban ya sake cewa "Har yanzu baka ga komai ba, har sai wani mummunan abu ya faru da Yusrah, a lokacin ne za ka tabbatar da ɗan Aliyu ba tsaran wasan ka bane, uba ne a gare ka."

Dakatawa ya yi, sai kuma ya sa hannu ya share ƙwallar nan sannan ya ci gaba da tafiya har ya fice daga ɗakin zuciyar sa ta masa wani bala'in nauyi marar misaltuwa. Yana fita Aba ya kira wayar Anna dan ba zai iya leƙawa ya mata magana a wannan yanayin nashi ba, tana ɗaga kiran a daƙile yace "A shirya akwatin nan da yaron nan ya kawo wa Yusrah ki kawo min su ɗakina yanzu."

Ko da ya faɗi haka ya yanke kiran, hakan ya sa Anna bin wayar da kallo sannan sannan ta miƙe tana so ta ji wai me yake faruwa ne, Aswan ya fito ko kallon inda suke bai yi ba bayan tasan dole zai zo gaban ta ya rusuna ya mata saida safe, idan ba gizo idanun ta ke mata ba sai ta ga kamar yana share hawaye ma a idanun shi fa.

Tana shiga ɗaki kuma ta samu Aba na waya da Chef, shima a taƙaicen ta ji yace masa "Please, ka daure ka zo da safe ina son ganin ka."

Ba ta ji me Chef ɗin ya ce ba kawai ya yanke kiran, da kulawa sosai hankalin ta na ƙara tashi tace "Aban Aswan, lafiya? Me yake faruwa ne?"

Juyowa ya yi ya zuba mata idanu, da ƙoƙarin kwantar mata da hankali yace "Ina Yusrah take?"

Da mamakin tambayar ita kuma tace "Yusrah tana ɗakin ta, da magriba ne ta ce kanta na ciwo, tasha magani sai ta kwanta."

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yace "Ki daure ki ƙara duba jikin nata, ni zan shiga na kwanta, saida safe."

Daga haka ya juya ya barta nan tsaye, tabbas yanzu kam ta yarda akwai matsala kuma babba, amma me yake faruwa? Akwatina fa ya ce wanda Bilal ya kawo? Me zai yi da su? Kuma yadda aka kawo su? Kenan su cire kayayyakin da suka zuba musu?

Ga dai ƙannan Anna da wasu daga cikin ƴan uwa sun mata kara sun zo dan tafiya gyaran ɗakin Yusrah, aunty Fureira ma ta shirya suna jiran umarnin Anna kafin ta ɗauki Yusrah su tafi, sai Nawal da Abrar da suka wuce saloon tuni za'a musu ƙunshi da kitso, aunty Intisar kuma ta baro su da yara dan ita za ta jagoranci gyaran ɗakin. Amma fa tunda safiyar ta waye duk suka kasa gane wa Anna, wacce baiwar Allah ita ma abinda take gani daga wajen Aban ne duk ya gigita ta, musamman da ta kai masa akwatin a yadda aka kawo su ta samu an shigo masa da goro ta ƙofar baya sak yadda aka kawo, tana aje akwatin kuma ya shiga ɗaki ko da ya fito ta ga ya ɗora kuɗi kan akwatin nan, irin dai...kamar dai zai mayar da ma masu su kayan su? Kai subhanallah! Hankalin ta a tashe yake matuƙa, ta so zuwa ta zauna su yi maganar, amma sai Chef ya zo dole ta basu wuri su gama zantawa.

*Chef* ma ya jima yana kallon shi bai ce komai ba, kafin daga bisani ya dubi kayan sannan ya kalli Chef ɗin yace "Chef, wannan sune kayan da aka kawo na auren Yusrah da Bilal, dan Allah ka min alfarmar kai musu kayan nan, saboda an fasa ɗaurin auren."

Zaro idanu Chef ya yi da ɗan ƙarfi yace "Me? An fasa ɗaura auran? Jibi ne fa?"

Jinjina kai ya yi yana ciccije fuska yace "Umm! An fasa."

"Subhanallah! Me ya faru haka Elhaj? Lafiya kuwa?" Chef ya tambaya da sigar tashin hankali.

Girgiza kai ya fara yi bai ce komai ba, kafin daga bisani ya ɗauko wayar sa ya nemo vidion sannan ya miƙo mishi yace "Ka duba ka ga abinda ɗan ka ya mana? Dalilin wannan ɗaukar ne aka fasa auren yarinyar nan, me ya shiga kan Aswan haka? Me ya haɗa shi da yi wa yarinyar mutane irin wannan baƙin fantin? Yanzu wa ya san ya rayuwar ta za ta kasance, shin idan ta ƙara samun wani mijin fa shima


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login