Showing 60001 words to 63000 words out of 397328 words
ko ƙofa kar ya buɗe min, ni ko ƴaƴana ko mijina, shiyasa na zaɓi taimakawa mutane, wataƙila idan dan Allah nake yin haka ya dubi buƙatata ya shirya tsakanina da iyayena, Yusrah shiyasa nake ɗaukar kowa a matsayin dangina, kema kuma kamar ƙanwa nake kallon ki, dan baki fi tsarar ƙanwata ta biyu ba *Nabihat*."
Cike da jimami da girmama lamarin Yusrah ta jinjina kai tana sako hawaye da murmushi a fuskar ta tace" Allah sarki, kowa ka gani a rayuwar nan da akwai abinda yake damun shi, sai dai na wani ya fi na wani, in sha Allah aunty iyayen ki zasu neme ki watarana, da izinin Allah ni da ire-irena ba zamu gaji da yi miki addu'a ba."
Murmushi kawai ta yi tare da jawo jakar ta a gefe ta buɗe zif ta ciro wata enveloppe ta miƙo mata tace" Tun da safen da ya farka ya ga baki zo ba, ya so ya ganki dan ya jajanta miki, daga ƙarshe zai fita dole ya bani ya ce idan kin zo na baki wannan, idan kuma akwai wata buƙatar ki zo Yusrah kar ki ji nauyi ki sanar dani ni kuma zan faɗa masa."
Yusrah na kuka ta sa hannu ta karɓi kuɗin tana mata godiya, ba tare da ta amsa godiyar ba ta bata tabbata anjima zasu je asibitin suma su ga jikin Safwan, amsa mata kawai ta yi amma ba ta ce ba zata je asibitin yanzu ba sai gobe ta sake haɗa kan kuɗin aikin ta, kuma Iya Abu ita ce dalilin ta na ƙin komawa, yanzu ai ta san tana can dole ba yadda za ta yi, amma da ta tafi tun jiya da yanzu Iya Abu ta wuni gida tunda da la'sar za su tafi.
Daga nan gidan adaidaita sahu ta ɗauka wasu masallatan ma ana sallah isha'i dan saida ta yi magrib gidan aunty Fauziyya ta fito, bata zame ko ina ba sai gidan Goggon su Hindatu dan ta ji inda aka kwana...
Tun daga ƙofar gidan za ka shaida lallai Goggo ƴar zafin nema ce, dan kuwa unguwar nan ta su dake da mutane sosai babu wanda bai san ta ba, yanzu haka a ƙofar gidan biyu daga cikin yaran ta ne ke kula mata da kaya kamar haka, kunu, taiba da awara, wake mai shinkafa da marar shinkafa, pure water mai sanyi da kuma lemu na leda mai ƙanƙara kala har uku.
Gaisawa sukayi da yaran ta wuce ciki bayan sun tabbatar mata e Goggon tana nan, tana shiga ma daga soro take jiyo muryar Goggon tana faɗin "Na rantse da Allah Fadila kika sa ya zubar min da ƙwai sai na ci kakan..."
Lumshe idanu Yusrah ta yi tana ayyana yadda za su kwashe yanzu ma, haka ta shigo da sallama yara na ta hayaniya su manyan haka, Goggon kuma na magana da wata mata da alama amsar kaya ta zo dan har jibiya da katsina tana ci duk ranar lahadi, da kulawa Yusrah ta gaishe da kishiyar Goggon tana zaune can gefe tana ƙulla mata ruwa na ƙanƙara da take na siyarwa, cike da tausaya mata Yusrah ta juyo tana auna rashin imani irin na Goggon su, kishiyar ki amma ki mayar da ita ƴar aikin ki, kuma ita babu ruwan ta baiwar Allah, haka shi ma mijin tunda ana ɗauke masa wasu ɗawainiyar to komai Goggon ta yi daidai ne.
Da ƙyar ta samu kujera ta zauna dan gidan a kacame yake da kaya a barbaje ko ina kuma duk na sana'ar Goggon ne, tana zaune tana kallo bayan ta gaisheta ta amsa tana mata wani kallon sama da ƙasa, saida ta gama da matar nan ta bata ƙwai har cret takwas yara suka shiga fitar mata da shi waje.
Tana kallon Yusrah ba tare da ta nemi su sirrnta ba tace "Daga ina kike? An ce ana ta zuwa asibiti ba kya nan, kuma kinsan Iya Abu ita ma marar lafiya gare ta za ta koma inda ta fito, haka yau duk ƴan garin su suka tafi suka bar ta."
Da ladabi Yusrah tana matsar hannu da enveloppe ɗin da take da tabbacin kuɗin sun fi wanda aunty Fauziyya ta bata saboda kaurin su har take Allah Allah ta je gida ta ƙidaya ta ga nawa ne tace" Goggo naje wata projet ne muka yi musu aiki, saboda ina so na tara kuɗin aikin Safwan, yanzu ma daga can nake na biyo in ji yadda ake ciki game da maganar mu."
Wani irin ƙara haɗe fuska ta yi ta taɓe baki tace" Hmmmm! An yi cinikin filin, tunda kin matsa shiyasa ba yadda zamuyi muka karyar da filin mu a banza, milyan uku da ɗari da hamsin aka siya, aka ba wa dillali hamsin ɗin saboda a fita haƙƙin shi, yanzu kuɗin wanda ya siyi gidan ya yi alƙawarin kawo su gobe bayan sallah magrib, sai mu jira shi kuma."
Idan ta haɗa da wanda ke gare ta, aka bata na gobe da kuma na aikin ta, da izinin Allah kuɗin aikin Safwan sun kammala, dan haka da frin ciki ta amsa da" Shikenan Goggo, Allah ya kaimu goben."
Ko amsa mata ba ta yi ba ta fara lissafin kuɗin dake jimƙe a hannun ta masu yawa, cikin nutsuwa Yusrah ta sake cexa" Goggo, nace dan Allah ba za'a samu lambar wani a wajen ku ba daga wajen su Mamanmu? Su fa ina ga basu san halin da ake ciki ba."
Shiru Goggon ta yi, sai kawai ta juya tana kallon ɗakin ta ta shiga kiran" Safiya, Safiya."
Safiya ta amsa tace" Ɗauko min wayata?"
Ba jimawa Safiya ta fito da wayar ta ba wa Goggo, kallo ɗaya su ka wa juna da Yusrah tace" Sannu."
Ita ma da" Sannu." Ta amsa tana ɗauke kai, tana buɗe tsaron wayar ta miƙawa Yusrah wayar tace" Ki duba a jerin lambobin akwai lambar auntyn ku *Fureira*."
Da mamaki ta kalli Goggon tace" Goggo ku baku kira su ba?"
Ba tare da ta ko kalle ta ba tace" An ce min idan nasa dala ɗari ma ba lallai mu gaisa ba kuɗin za su ƙare, shiyasa."
Wani abu ne ya taho ma Yusrah maƙoshi ya tokare ta, amma sai ta haɗe kukan ta da komai ta karɓi wayar ta duba lambar, dake lambar da ɗan tsayi sai na nemi cikin yara suka kawo mata alƙalami da takarda ta rubuta, daga nan ma har ta ɗauki lambar kawun su dake ƙasar waje wato autan su Goggo ɗin, wataƙila shima ba ta sanar da shi halin da suke ciki ba, kuma idan ta ce ta bata lambar shi ba za ta bata ba ta sani ne, dan ko Baban su sanda ya rasa wayar shi da ya yi ƙaramar waya ai da ƙyar ta bashi lambar tana ta masa hanya hanya, shiyasa kullum ita ke cin arziƙin shi ban da kowa saboda ya ɗauke ta kamar uwa.
Miƙa mata wayar ta yi ta miƙe ta mata sallama da cewa sai goben, da a taƙaice kawai tace "Ki gaida su."
Kasa riƙe hawayen ta tayi tana fita soro ta sako su suka sauko mata masu zafin gaske, amma sai ta share su tayi gaba abun ta, daɗin ta ɗaya tana da kuɗin adaidaita ba ta buƙata daga gare ta, sai dai gaskiya duk yadda take son zama garin nan ba za ta iya zama wajen Goggon su ba, gwara ta koma *Funtuwa* ya fi mata alkairi wajen dangin Mamanta, amma ba za ta ɗorawa aunty Fauziyya nauyin komai ba, wanda ta mata ba a baya da yanzu ya isa haka.
*Duk* da Maryam ta faɗa mata da ta je ta samu Safwan na bacci, dan kuwa zuwan safe ne ta yi ta samu Iya Abu ta bashi maganin bacci da rage raɗaɗi, dan haka iya abinda ta faɗa mata kenan sai yadda Iya ta faɗa mata cewa jikin shi da sauƙi, murmushi ta yi na jin daɗin haka tace "Na godewa Allah, in sha Allah gobe warhaka komai ya kusa zuwa ƙarshe, wataƙila ma an shiga da shi ɗakin tiyata."
Sai kuma a zuciyar ta ta ayyana _"Docter Hamat za ka sha kunya, ai Allah ba azzalumin bayin sa bane, kuma wallahi za ka ga ƙarshen ka, mugu kawai."_
Da haka Maryam da Mamanta suka taya ta ƙidaya kuɗin mijin aunty Fauziyya *Salman*, ai kuwa kuɗin ruɓin na auntyn ne uku, addu'a dai kam sun sha ta a gurin su har suka yi shinfiɗa suka kwanta bacci da tunanin wayewar gari lafiya su ɗora in da suka tsaya.
*Sai dai* ina? Tunanin Yusrah ya gaya mata ƙarya, tana cikin kuskure ba ta sani ba da wauta da rashin hankali irin na mace wani sa'ilin, tunda Iya Abu ta ji labarin kowa fa na garin su ya tafi nata hankalin ya koma gida ita ma, ita ma dai sai ta aikata wani ɗanyen aikin wanda a ganin ta daidai ne. Anata tunanin Safwan asibiti yake, ita kuma majinyacinta gida yake, Safwan ba ya iya zuwa ko ina, nata tsohon kuma idan ya kubce ya fita da ƙyar ake samo shi bayan wasu kwanaki, sannan Safwan zai iya samun samu kulawa da shi, tsohon ta kuma babu kpwa tare da shi sai jikokinta biyu dake tare da ita su biyu ƴan mata, babbar cikin su ita ce ke da shekara tara a duniya, ba za su iya kula da shi ba ko kaɗan.
Dan haka ta haɗa kayan ta Safwan na bacci ta ƙarasa gadon dake kusa da su ta ce wa matar dake jinyar wata tsohuwa "Dan Allah ƴata ga ɗan jikina nan ki kula min da shi kafin Yayar sa ta dawo, tabbas duk inda Yusrah take magriba ba za ta yi ba za ta zo nan, nima majinyacin gareni a gida da ya fi wannan."
Kallonta matar ta yi, dama fa su zaman tsohuwar da Safwan duk ya ishe su saboda yawan koke-koke da yake musu, ya za ta wani bata kula da shi? Ita ta yi ya da nata jinyar, amma dan kar ta ce a'a sai kawai ta gyaɗa mata kai tace" To shikenan."
Godiya Iya Abu ta mata ta juya ta kalli Safwan dake bacci, yanzun ma wani maganin ta ɗibga masa dan ta samu ta tafiyar ta, yayin da matar nan kuma su fa kowane lokaci sallama suke jira, da da safe ma zasu sallame su sai aka ƙara sakawa tsohuwar ruwan da zai sauke mata zazzabi, shiyasa har suke nan i warhaka ma... Iya ta juya ta tafi zuwa ƙauyen su ba tare da tunanin komai ba ko ƙoƙarin sada Safwan da inda ya fi kula, a ƙalla ko da Goggo dafa shi za ta yi da ko ita da ke dolen su ta kai shi can tunda dama ba kulawar da ake basu, sai dai duk bata yi wannan tunani ba ta kama gaban ta da tunanin ai za ta baro amanar tsohon ne ita ma sannan ta dawo ga yaran ta ga yadda za'a yi aikin da sauran abubuwa dai.
Tun da yammar nurse ɗin nan ta dawo dan faɗawa Iya Abu saƙon Docter na cewa su bar asibitin nan, imma su koma wata ko su koma gida duk matsalar su ce ba tashi ba, amma sai ta samu babu kowa tare da shi, matar nan ma da Iya Abu ta ce ta kula da shi kafin zuwa Yusrah an sallame su, dan haka Safwan sai shi kaɗai a ɗakin da wata dattijuwa tana jinyar wani saurayi suma kuma yau ne suka zo wataƙila ma zazzaɓi ne da ruwan sun ƙare za'a sallame su.
Wasa farin girki, sai gashi bayan sallah isha'i da nurse ɗin ta dawo Yusrah dai ba ta zo ba, kuma lokacin Safwan kuka yake yi saboda rashin ganin kowa a tare da shi ga tsinanniyar yunwar da yake ji, sai ta sake komawa ta sanar wa Docter da ya gama wata tiyata yan shirin tafiya gida, ai kuwa ya ce ta samu kurma ya ɗauki yaron su fitar da shi nan waje, idan yayar tashi ta zo ta ganshi a nan sai ta ƙarasa tattara shi su bar masa asibiti, idan ba haka ba har ita nurse ɗin zai kora fa.
Jiki na rawa ta samu kurma ta sanar da shi umarnin Docter ɗin, ba sani, ba sabo, ba tsoron Allah, ba tausayi haka suka fito da Safwan daga ɗakin nan aka aje shi cikin rumfar da masu jinyar mutum ke zama suna hutawa wasu ma har suyi bacci, haka kula suka juya suka bar shi nan sai dai nurse ɗin na mamakin yadda ta ga kamar Docter ɗin na nuna tsanar yaron a fili.
Asibiti kowa ta kan shi yake, duk kukan nan da Safwan ke yi ɗaiɗaiku ne suka iya tambayar sa lafiya? Abinda shi kuma yake faɗa shine "Yayata ce da Iya Abu suka gudu suka bar ni nan, ban san ina zan je ba kuma."
Iya magana kaɗai mutane ke iya fesowa, amma ko yunwar da yaron ke ji ba wanda ya iya fahimtar haka bare ya samu ko da abinci, wannan magana sai ta zama abar da ake ta tattaunawa a asibitin har dare ya yi, anan ɗaya daga cikin ƴaƴan mai gadi ya jiyo labarin shima cewa wasu masu jinyar yaro sun gudu sun bar shi a asibiti, anan ne mai gadi ma na tattauna maganar har Mani dreba ya ji, shi kam da tausayi da kulawa ya zo rumfar ya samu Safwan, rarrashin shi ya yi tare da ɗaukar shi ya nufi inda yake zama shi kaɗai idan dare ya tsala tunda nan yake kwana iyalinsa kuma na wani garin.
Abinci ya bashi da tunanin ba lallai ya ci ba saboda kukan aunty Yussy kawai yake, amma cikin ikon Allah dake yana jin yunwa sosai sai kuwa ya kama cin shinkafar nan da miya har saida ya ƙoshi... Daga nan yana ajiyar zuciya har bacci ya ɗauke shi bayan dubara da Mani dreba ya masa ta hanyar faɗa masa da safe zasu je wajen aunty Yussy ɗin, shi kuma niyyar sa ita ce idan gari ya waye baya da aiki ya nemi alfarma ya je unguwar su yaron ya sada shi da wani nashi, idan kuma bai da kowa sai ya riƙe shi ya haɗa da ƴaƴan sa, yaro ai na kowa ne.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*18*
Yana nan zaune saƙon AA ya same shi cewar yanzu zai shigo, dan haka ya sanar masa inda yake zama dan gujewa idanun mutane, domin ya gama gane cewar AA na bincike ne, shi kuwa bincike ko na menene in dai na ƙasa ne zai baɗa haɗin kai in sha Allah. Kamar yadda suka saba gaisawa da mutunta juna hakan ce yau ma, AA ya zo ne dan ya yi masa wata tambayar, sai dai tunda ya fito daga motarsa ya ƙaraso wajen tabarmar Mani direba idanuwansa suka sauka a kan yaron dake kwance wani irin kwanci a takure, ga ɗori a ƙafafuwansa sai ajiyar zuciya yake saukewa alamun ya wahala, kuma yana cikin wahalar sai ya samu kansa da faɗin" Wannan ɗanka ne ba lafiya?"
Mani direba ya kalli Safwan, ya juyo ya kalli AA fuska da alamun tashin hankali ya girgiza kai yana fitar da huci a sanyaye ya ce" A'a, ba ɗana bane, nima ɗauko shi na yi a cen wajen majinyata, yau kwana uku da iftila'i ya faɗa anguwarsu aka yi zubewar gidaje, mahaifiyarsa, da mahaifinsa da Yayarsa guda sun rasu sai Yayarsa ɗaya ta rage da shi, to ni dai ban san ya ya aka yi ba, ko ta fita a hayyacin ta ne ko menene? Ance wai da ita da wata dattijuwa sun gudu sun barshi, ka ganshi nan bawan Allah yunwar cikinsa ma ta ishe shi, ga ciwo, ka san kuma yadda asibitin tamu take ba sani ba sabo idan har baka daidaita harkar biya ba ana yin waje da kai ne, shine na kawo shi nan har in ga me gobe zata yi in sha Allah in nemi yayar tasa, idan na ga ban samu ba kuma ni sai in rike Allah ya tayani riƙo."
Gaba ɗaya AA sai ya ji hankalinsa ya ƙara tashi, a nutse ya ƙarasa inda yaron ke kwance, kumburin da ƙafafuwansa suka ɗauka na abin ɗori sun yi sundum, kumburin kuma har fuskarsa ya haye sundum, a nutse ya zubawa fuskarsa ido, hawaye bushe a saman fuskar tasa sai ajiyar zuciya yake saukewa akai akai ya riƙe rigar jikinsa tam.
A hankali ya janye dubansa daga yaron ƙirjinsa na wani irin matsanancin dokawa, wani irin tausayi mai girman gaske ya ratsa ƙirjinsa har ya saka shi manta tambayar da ta kawo shi wajen Mani, a hankali ya taka ya ƙarasa wajen motarsa ya buɗe ya shiga, Mani na biye da shi, daidai lokacin ne kuma Mani ya samu kira daga offishin oga aka sanar masa gobe da yamma zasu yi tafiya shi da ogan, dan haka yana saukewa shi ma juyawa ya yi