Showing 45001 words to 48000 words out of 397328 words

Chapter 16 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70008

duk jajircewar iyayen ki, idan kuma ya so babu su sai ki zama abar kwatance..."

Ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da cewa" Kar ki ce babu anfanin rayuwar ki, a ƙalla ki sa a ran ki za ki rayu ko dan ƙanen ki da ya rage miki, ba ke kaɗai ce ba Yusrah, ke da ƙanin ki ne kwance, kuma ubangiji ne kaɗai ya san dalilin da ya sa lafiyar ki bata kassara kamar ta ɗan uwan ki ba, ni idan zan iya kintata daidai sai nace wataƙila rashin lafiyar ƙanin ki, wani babban mafari ne da zai koya miki *WATA TAFIYAR* mai cike da gwagwarmayar rayuwa, ki rayu dan ƙanin ki Yusrah, sannan ki tsaya tsayin daka dan kiga ya samu lafiya, wataƙila shiyasa kika rayu bayan duk wannan."

A zabure Yusrah ta ɗaga tana dubanta, a birkice ta ce" Auta? Ina autan Mamanmu? Yana ina? Ina yake? Me ya same babbanmu? Bai mutu ba shi? Yana ina?"

Nurse ɗin har sai da ta sauke ajiyar zuciya tana sake hankalta da yanayin Yusrah kar aje yarinyar ta samu taɓuwar hankali baiwar Allah, jiki a mace ta nuna mata ƙaninta dake kwance, barci yake yi ƙashirban dan sun saka masa ƙarin ruwa na ɗauke raɗaɗin ciwo da kuma allurar barci mai nauyi dan kuwa rigima yake ba ji ba gani , shi yasa ya samu barcin mai nauyin gaske.

A rikice ta kama ta miƙe, gaba ɗaya sai ta ji nauyin jikin da ya hanata tashi ɗazu yanzun bai hanata miƙewa ba, a saiɓance ta ƙarasa inda yake ta zube ƙafafuwanta idanuwanta tamkar zasu faɗo tana kallon ƙafafuwansa, ba'a riga aka ɗora shi ba kamar yadda ƙa'idar asibiti take amma an ɗaure dan a samu a ɗora ɗin zuwa an jima.

Muryarta har ta gama disashewa da wani kukan ta juyo tana dubanta ta ce" Me ya same shi? Innalilahi wa inna ilaihi raj'un, ya naga ƙafafun shi a haka? Kamar fa duka ƙafafuwansa basa yi? Ina file dinsa?"

Dafa kafaɗar ta nurse ɗin ta yi a tausashe tace" Idan za ki iya, zaki iya zuwa wajen Docter zai miki bayani, dan ba jimawa da rahoton lafiyar ku ke da ƙanin ki ya fito, kuma rahoton yana wajen shi, ki je sai ki ji me zai faɗa miki."

Da sauri ta miƙe ba ta tsaya ɓata lokaci ba, sai dai nurse ɗin dake bayan ta ce kawai ke kula da ƙarfin hali ne ya sa take takawa da sauri, amma tabbas jikin ta na mata ciwo ba kaɗan ba saboda yadda jikin nata ke motsa. Fitowar su kafin su isa corridor ɗin da zai sada su da office ɗin Docter suka haɗe da wata tsohuwa da kuma ɗaya daga cikin masu jinyar waɗanda wannan abu ya faru.

Yusrah na ganin tsohuwar ta gane ta, kamar Kaka take ga mahaifin su, ita ma tsohuwar tana ganin ta da sauri tace "Ke ƴar nan, ina kika koma da zama muke ta neman ki? Ba dan wannan ta taimaka min ba da ina zan laluboki a asibitin nan?"

Ƙala Yusrah ba ta ce ba sai ƙarasomawa da ta yi kusan tsohuwar ta dafa hannun ta tare da cije leɓe tana kuma dafe bayan ta da take jin yana mata wata muguwar tauna.





*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*14*




Cike da kulawa Iya Abu ta kalli Yusrah tana ƙara damƙe hannun ta tace "Yusrah, kina lafiya? Ke da ya kamata a same ki kan gado."

Nurse ɗin ce ta bata amsa da "Tsohuwa wajen likita ne za mu je da ita, yanzu za ta dawo."

Kallon nurse ɗin Yusrah ta yi a sanyaye tace "Ki nuna mata inda Safwan yake, zan je da kaina wajen Docter."

A wahalce ta saki hannun Iya Abu ta fara takawa, su ma ɗakin da Safwan ɗin yake suka nufa, ana Iya Abu ke ta salallami tunda ta ga Safwan har da kukan ta.

*Tana* ƙwanƙwasawa ya bayar da izinin shiga saboda yana ma tsaye ne yana tattare abun buƙatar shi zai tafi masallaci dan daf ake da fara kiran sallah magrib, yana ganin Yusrah ya saki wani murmushin gefen laɓɓa ya aje komai kan table ɗin ya koma ya zauna yana waina kujerar shi cike da izgili, a daddafe Yusrah ta ƙaraso kan ta ƙasa ta tsaya tace "Barka da aiki *yallaɓai*?"

Ɗan waro idanu ya yi kaɗan jin wai yallaɓai ba Docter da take cewa ba, amma sai ya share ta kawai ya nuna mata wurin zama da hannu, ba musu ta zauna dan ta rasa me yake damun ta da bayan ta ke mata wannan abu haka kamar wata mai tsohon cikin yan biyu, a nutse ta zauna sai dai ba sosai ba tana kallon table ɗin gaban shi da tausasawa tace "Yallaɓai, dama na zo ne akan rahoton lafiyar ƙanina, sunan shi Safwan Abdul-Hameed Turaki."

Da wani kallon shaƙiyanci yana murmusawa ya ɗago daga jinginar da ya yi ga kujera yace "Yusrah, ashe haka wannan abu ya faru?"

Satar kallon shi tayi cike da tsarguwa ta gyaɗa kai alamar e, taɓe baki ya yi yace "Allah ya kyauta."

A takaice ta amsa da "Ameen, na gode."

Abun mamaki, rahoto biyu ne a keɓe ta ga ya ɗauko dukan su ya aje gaban shi ya fara dubawa, ba ta damu ba tana dai jira ta ji me zai ce, can ya ɗago ya kalle ta yace "Yusrah, ina mai baki haƙuri akan sanar dake ɗan uwan ki ya samu matsala a ƙashin bayan shi da ta jawo wani ƙaramin tazgaro game da tafiyar sa, ga kuma karaya da ƙafafuwan suke ɗauke da ita, amma dai duka ba wata matsala bace, tunda bayan sallah magrib zamu shiga da shi a masa ɗori, wannan alfarma ce muka yi miki kasancewar ki ma'aikaciyar mu, amma tiyatar bayan nasa kuma..."

Sai kuma ya ƙura mata idanu ba alamar wasa yace" Ya danganta da yadda kika tsananin son ki ga ƙanin shi ya koma yadda ya ke."

Da mamaki da kuma rashin fahimtar kalaman sa tace" Ban gane ba yallaɓai?"

Komawa ya yi ya jingina a kujerar yana juya ta ba wani kwana-kwana yace" Yusrah, sharaɗi biyu, idan kin bi su zan wa ƙanin ki aiki ya samu lafiya, idan kuma kika bijire to a daren nan ki yi gaggawar ɗaukar ƙanin ki ku bar nan, ko kuma dai ku biya kuɗin aiki sai a masa, kuma sisin kwabo ba za'a rage miki ba."

Kallon shi tayi da kumburarrun idanun ta dake matuƙar buƙatar kulawa tace" Wane irin sharaɗi ne yallaɓai?"

Ba kunya ba tsoron Allah yace" Na farko shine, za ki ci gaba da yi min aiki anan asibitin, kuma za ki yi duk abinda na saka ki."

Gyara zama ya yi yace" Na biyu kuma, za ki bani haɗin kai, ni da ke mu rayu cikin farin ciki da soyayya."

Da matsanancin mamaki ta kalle shi sosai cikin rarrabe kalaman ta tace" Haɗin kai? Soyayya? Wace irin soyayya kenan?"

Wani banzan kallo ya mata yace" Ke yarinya ce? Ba ki da wayewar da za ki fahimci abin da nake nufi ne? Soyayya ina nufin ni da ke zamu dinga haɗuwa a wani wajen da ba asibiti, sannan ma...ba mamaki ta kai mu ga aure idan kin so hakan."

Ƙura masa idanu ta yi tana kallo, kawai ta rasa me za ta ce mishi, me yake shirin faruwa da ita? A doguwar *tafiyar* da ta yi tun daga matakin primaire (primary) har zuwa karatun likitanci ba ta samu wannan matsalar ba, me ya sa sai yanzu da take daf da fara cin moriyar abun? Wannan wane irin sheɗanin mutum ne a cikin riga mai daraja da ɗaukaka? Wace irin zuciya ce da shi da za ta iya cewa sam babu ɗigon imani a cikin ta? Ita kam ba ta manta alƙawarin da ta wa mahaifiyar ta a safiyar daren da abun nan zai faru ba, sun hore ta da kare mutumcin ta komai tsanani komai wuya, dan haka Safwan ko a gargarar mutuwa yake ba za ta siyar da mutumcin ta ba akan rayuwar da bata da tabbacin za ta ci gaba da numfasawa daga sanda ta since zariyar zanenta gaban wani da ba mijin auren ta ba har sanda za ta mayar ta ɗaura, ubangiji na sane da su ba kuma ba ya son su bane, dan haka za ta zuba idanu ta ga me zai faru a gaba.

Tsam ta miƙe ba tare da ta ce masa ci kan ka ba ta fice daga ofishin, saida ta ɓacewa ganin shi kaɗai ya yi wata ƴar dariya ya miƙe yana sake ɗaukar wayar shi da makulli yana faɗin "Yarinyar nan tana da taurin kai, amma na tabbata za ki dawo dan babu inda za ki je a taimaka miki, mu zuba mu gani." Shi ma fita ya yi daga ofishin ya nufi masallaci.

***Jiki ba ƙarfi ta koma ɗakin, ta samu Iya Abu na zaune saman sallaya, dan haka sai ta ƙarasa bayi ita ma ta ɗauro alwala ta dawo ta ɗauki hijabin da Iya Abu ta zo da shi ta saka ta kabarta sallah a saman mayafin da aka rufa mata, ba ta ma san ko mayafin wanene ba ita dai ta ganshi a jikinta.

A daddafe ta salamce sallolin dake kanta sai ta sada kai ta yi shiru ta ƙurawa waje ɗaya idanuwa, ta yi nisa a tunanin jiya da kuma yau, ta yi nisa wajen tsarkake buwayar Allah, ta yi nisa cikin ƙara durmiya da imani ga Allah mai ikon da babu wani mahaluki mai kwatankwacin sa, jiya tana tare da ahalin ta warhaka ko hadda ba su fara ba gaban mahaifin su, amma ta wayi gari babu su sai ita sai Auta, shikenan aunty Hannah ta tafi kenan? Har ranar auren ta da aka saka shikenan an rufe babin?

Kamar daga sama Iya Abu da ke kula da ita ta dubeta ta ce" Yusrah, taso ga koko mai zafi ki sha kin ji? In cikinki ya buɗe sai ki ci ƙosan nan."

Yusrah ta ɗaga jajayan idanuwanta ta sauke a fuskar Iya Abu, lokaci ɗaya fuskar mahaifiyarta ta faɗo cikin idanuwanta...A hankali ta buɗi baki muryarta shaƙe ta ce" Iya..., shikenan har an yiwa su Mama sutura? Da Baba? Da aunty Hannah? Jiya fa warhaka muna tare kuma lafiya lafiya cikin farin ciki, Iya shikenan yanzu sun tafi?"

Iya Abu ta sadda kai tana share hawayenta, ta sake ɗagowa tana kallonta a sanyaye ta ce" Yusrah, wa'adi idan ya kai, babu tsumi babu dabara sai an tafi, tabbas wannan mutuwa da wahala a gaban nan ki ga wata da zata maki gigitar ta, sai dai ko taki, ama a haka dole ki ɗauki dangana da haƙuri, ki yi ta yi wa iyayen ki addu'a Allah ya musu rahama, ke da ɗan uwan ki kuma Allah ya shiga lamarin ku."

Murza idanu tayi da niyyar ta daina kukan, amma sai wasu hawayen suka sake taho mata, hakan ya sa kawai ta ci gaba da rera sanyayyan kukan ta, duk da kuwa Iya Abu dake zaune tana ta bata haƙuri da rarrashi.



*AA ANZA*



Kamar kullum duk da ba da wuri zai fita ba sai da ya zo gaishe da iyayen shi, kuma yau falon daga shi sai Dad ko Anna tana nata ɗakin, dan hakane ma bayan sun gaisa Dad ya kalli AA ɗin da ya yi niyyar tashi yace "Zauna."

Da ladabi ya koma ya zauna yana kallon shi, shi ma kallon shi yake yi har yace "Aswan, na baka zaɓi biyu na aikin da kake so ka yi, amma ba ka ce min komai ba, haka Annar ka ma ta ce baka ce mata komai ba, ko me ya sa?"

Kallon Dad ɗin ya yi, sai kuma ya rusunar da kan shi yana tunanin amsar da zai bashi wacce ba za ta saka ya fara zargin shi da wani abun ba... Sai dai ya makaro, dan kuwa Dad ya masa tambayar ne ma saboda ya fara zargin akwai wani abu da yake shiryawa, idan ba haka ba yau kwana nawa? Amma bai sake masa maganar komawar sa aiki ba, sannan bai ga alama ko birbishin damuwa a tare da shi ba ko misƙala zarra, dan haka kawai akwai wani abu a ƙasa da AA yake shiryawa, dan shi ya fi kowa sanin sa.

Da tausasawa AA yana kallon zara-zaran yatsun hannayen shi da zoben azurfa da doguwar yatsar sa ke ɗauke da ita yace "Aba, dama ina ta tunanin wanda zan zaɓa ne, ina son tafi abroad saboda na manta da tsohon aikina, amma kuma ina son zama anan saboda *ku*."

Da ya fara magana a sheƙe Dad ke kallon sa irin ka gama zancen ka ba yarda zan yi ba, amma haruffan nan na ƙarshe *ku*, wato a duniyar AA babu wani abu da yake da mahimmanci sama da su, duk abun shi a bayan idanun su ne, a gaban su kuma tamkar zakin da bashi da haƙora. Da jin daɗin haka da kuma gamsuwa ya jinjina kai yace "Shikenan, ka nutsu ka yanke hukunci, nima kaina ba zan so ka min nisa ba."

Kallon Das ɗin ya yi murya ƙasa ƙasa yace "Amma kuma ai ku kuka bani zaɓi, har da cewa dole na ɗauki ɗaya."

Irin kamar bai ji ba ya yi yace "Me ka ce?"

Girgiza kai ya yi alamar ba komai, sannan ya miƙe yana masa sallama, saida ya kusa fita Dad ɗin yace "Kuma dole ka zaɓa ba, idan ba haka ba to ka yi aure a ƙarshen watan nan."

Juyowa ya yi ya kalli Dad ɗin da ya ɗage kai sama kamar ba shi ya yi maganar ba, wato su raba hali yake da buƙata ba? Sai kawai ya girgiza kai yace "Shi ma ɗin zan yi, in sha Allah."

Daga haka ya fice ya bar Dad da kallon ƙofa, murmushi ya yi yace "Allah ya nuna min ranar, Allah ya nuna min wannan babbar rana AA, na gaji da ganin ka haka kana ta ƙara girma ba aure."

AA kuma na fita wata sabgar ya fita mai mahimmanci da tunanin daga can zai wuce asibiti ganin mutumin nan da Mani dreba ya faɗa masa.

Yadda Mani dreba ya faɗa mishi zai same su haka ya same su bayan saukowar shi daga masallacin juma'a, sai dai wannan karan zaune ya yi kan bencin da suke zaune suma ya ce shayi yake so, kafin a dafa a bashi ya ɗan ɗauki lokacin da suka dinga taɓa hira shi da su, sai dai ya fi jefa bakin shi idan wannan mutumin ya yi magana, akasin haka kuma murmushi kawai yake yi bai ce wa uffan.

Dama su biyar ne a wurin, bai jima da zama ba ɗaya ya tashi, ana nan kuma aka kira motar ujila dole Mani ya fita daga asibitin da gaggawa, ɗaya mutumin da ya rage ne AA ya dube shi yace "Anan kusa ko za'a samu sigari?"

Wanda AA yake nema ne ya ƙura masa idanu, ba zai iya cewa ba ya sha ba ko bai taɓa sha ba, sai dai gaskiya yadda ya ga hannayen AA da tafukan hannayen da kuma laɓɓan shi kai har ma da haƙora, sai yake jin ko dai yana sha to irin asha ruwan tsintsaye yake mata, idan ka yi ra'ayi ka sha idan ba haka ba ko a kan ka dan kaga mai sha.

Shigar shi ce kaɗai ta sa suke bashi girma da kuma abun hawan da ya sauka a cikin shi, shiyasa mutumin da gaggawa ya miƙe yana bashi tabbacin zai samo, ko kuɗin da AA ke son cirowa ya bashi bai tsaya karɓa ba saboda targuet ɗin shi shine idan ya tashi tafiya ya musu gwaggwaɓar sallama duk da kuwa basu san wanene ba? Me ke kawo shi asibitin? Sannan me yake nema?

Cikin jin daɗin sararin da suka samu AA ya dube shi, sai ya ga har lokacin mutumin yana kallon shi ne, amma da suka haɗa idanu sai ya yi murmushi ya ci gaba da ziga shayin yana faɗin "Yallaɓai, ban va laifin ka ba fa, dan gaskiya ku baku da kwaramniyar da za ta saka ku hurawa kai hayaƙi kowane lokaci, dole sai dai ku sha kawai dan ta raya muku."

Wani malalacin murmushi AA ya yi ya ƙura masa idanu kawai, har mutumin ya cire rai da jin amsar shi ya ji yace" Hakane, a ƙalla na fi shekara biyu zuwa shida haka rabon da na sha, alƙawari na wa mahaifiyata akan na daina."

Da washe baki mutumin yace" Amma dai yallaɓai tun fil'azal dama ba hawan ƙawara ka ke mata ba, saboda alamun ka sun nuna haka."

Ɗan murmushin gefen laɓɓa AA ya yi saboda maganar ta so saka shi dariya, lokacin da yake shan sigari ai ko wani ya ga yana sha sha'awar ta yake yi, idan bai sha ba kuma sai ya ji har kan sa ke masa ciwo, amma


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login