Showing 237001 words to 240000 words out of 397328 words

Chapter 80 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70048

tunda ya ga za su aurar da Yusrah kowa na gidan ke bashi baƙin haushi, gashi ba wanda ya fahimci yana son ta bare ya agaza masssss...

Da sauri ya raruko idanu yana sake kallon yarinyar dake tare da AA ɗin za'a jefa su mota hannayen ta sanye da ankwa, wani gumi ya ji ya tsatsafo masa ya zabura ya miƙe tsaye, amma rashin ƙwarin jiki da girman abinda ya gani sai suka saka shi zubewa a gurin yana liƙe idanun shi saboda rawa jikin shi kawai ke yi, da gudu jami'in ya nufe shi, dake duk ya rame ɗaukar shi ya yi ya kwantar kan kujera, idanun shi biyu sai dai a rufe suke kawai ciwo ne ya ci ƙarfin shi. Haka jami'in nan ya fita ya gayawa mai gadi shi kuma ya sanar da maman Joli, amma fir ta kalle shi tace ya je ya bata wuri ya daɗe bai mutu ba, ganin yadda take kuka ranta ɓace ya san akwai wani abu, sai kawai ya dawo ya sanar da shi nan suka tattara shi jami'in ya ɗauki ɗaya daga cikin motar uncle Hamat ɗin ya yi asibiti da shi, saboda ya kasance mai barin makullin mota a hannun mai gadi idan ya wanke mota sai zai fita da ita yake karɓa.


*NABIHAT*


Tunda jama'a suka watse ya rage daga ita sai ƙawarta aminiyarta shaƙiƙiyarta da kuma Nabihat ɗin a ɗakin ta wacce tunda ƙawayenta suka ga kayan suka ƙunsa mata maganar ta sallame su ta ringa magiyar kar wanda ya ɗauki hoto ko vidio, amma wasu sun ɗauka a ɓoye ya zamo ta ajiye wayarta da aka turo mata wata vidio wai a kan Yusrah da hotuna dan kuwa a jiya jiya wani mutum ya mata dm suka yi magana ta bashi numbarta ta whatsup ya tabatar mata shi dai wannan fuskar ko da wancen a wancen karon ba kwalliya kuma ba fara'a wannan kuwa da fara'a sosai da dariya fuskar ba zata ɓace masa ba, ya taɓa ɗaukan matar nan da mijinta a bakin hanya, shine suka yi magana ya tura mata hoton a jiya a matsayin idan ka buɗe ɗin nan ya goge, shine fa ta saka aminiyarta ta tarda shi inda zasu haɗu suka tantance suka ga komai ta bashi saƙonsa ya bata sa ƙon ta waya ita kuma ta tura mata, bata iya bi ta kan saƙon ba dan tsabar ruɗewar da ta yi na maganar kuɗin kayan lefen da aka kawo mata har ta sallami kowa kamar yadda mahaifiyarta ta sallami wa'inda ba zasu kwana a gidan ba wa'inda zasu kwana kuwa ta bar su da halinsu da akwatunan a wajensu dan ko ta kan akwatunan bata bi ba.

Ƙawarta dake son tafiya gida amma yanayin ƙawar nata ya hanata ta sake sauke ajiyar zuciya, ita abin mamaki yake bata kuma duk tunani take yi wasa ne dan haka da kula ta kalli Hajiar ta ce" Hajia, me zai hana daughter ta yi kiransa ne ta ji abinda yake faruwa? Ina ji a jikina kamar ko baya so a ga tarin dukiyar auren ne ya sa ya yi haka, kin san fa yanzu duniya ta ƙi gaskiya, mutum ya yi ta kansa shi ya fi alkairi, ina kyautata zaton ido ya gujewa, haba jaka ɗari biyar ko kyauta zai yiwa wanda bai sani ba ai ya fi ƙarfin ya bashi haka balle ace kuɗin aurensa."

Hajia ta fitar da wani huci, Nabihat kuwa ta sake cusa hannayenta cikin kitson ta na atach da baya damunta a ɗazu amma yanzu ji take kamar ta yi aski dan duk ya sakar mata nauyi, idanuwanta sun yi jajir na abin kuka, ta kalli ƙawar mahaifiyarta ya fi a irga kamar ta ce da ita dan Allah tashi ki tafi, amma ta kasa dan haushi matar ke bata tun ɗazu ta nace sai ta yi kiran AA bayan mutumin basu taɓa kiran juna ba, ta yi kiransa ta ce masa me? Ta fara ta ina?

Itama mahaifiyar tata ta ƙi yin magana ne dan ta ciki na ciki, du da suna ƙawance sosai da ƙawar ta ta ba zata iya buɗar baki ta faɗa mata babu wani babbar jituwa tsakanin yaran, ba auren haɗi ne kawai, shi yasa yanzu ta fitar da numfashi bayan ta hangi ana buɗewa chef gida ta window ta saki murmushin yaƙe tace" Ƙawata kar ki damu fa, na tsayar da ke baiwar Allah ki tafi kawai ai ga chef nan yanzu ma je mu ji abinda yake faruwa, ta yiwu kuɗin lefen ma na wajensa dan kuwa nima na yarda da maganar ki da wahala in ba gudun a gani suka yi ba saboda tsaro, harkar iko ɗin nan ai sai su."

Ita ma hakan ya fi gyarata dan dare ya yi, duk da bata da ƴaƴa ƴan mata duk ta aurar da su amma akwai jikokinta biyu dake gidan suna jiranta, dan haka ta miƙe ta yi mata sallama ta tafi, tana tafiya Hajia ta dubi Nabihat bayan ta fitar da huci mai zafi ta ce" Bari ki ji, idan muka je wajen mahaifinki ki kula da abinda zan faɗa ki kiyaye kar ki zubda wani shirmen da zai sa ya gane ba zan taɓa lamuncewa a yi aurenki da wannan uwar arhar ba, dan kin sani sarai shi ba kuɗin ke gabansa ba, abinda yake gabansa ya aurawa soja ke, ni kuwa ba ruwana da wani soja dan wallahi ko soja ne in dai bashi da kuɗi ba zan iya kallonsa ba, rayuwar nan sai da ƴaƴan banki, duniyar nan idan baka da su kai ba kowa bane, dan haka ki kula, mu je mu ji in da abin arziki a baya zan duba, idan babu ko da sonsa zai kashe ki ki guji gwadawa zan ja maki girma ne har sai an maki abin kirki zaki tafi, idan kika ja min ɓacin rai zan iya yafe ki yadda na yafe Yayarki! Tashi mu je."

Miƙewa ta yi ta bi mahaifiyarta suka nufi ɓangaren chef, da suka je sun same shi yana zaune yana shan ruwa masu ɗumi, fuskarsa ƙawace da fara'a yana kallon tv, da fara'a ya amshe su, yana duban Nabihat ya ce" Baki kwanta ba ke?"

Nabihat ta sadda kanta bayan ta amsa mahaifinta da eh, zama Hajia ta yi tana dubansa da kula ta ce" Sannu da watsewar taro papa Nabihat, an sha taro."

Shi ma da fara'a sosai yace" Ai kam mun sha taro ma sha Allah, kai an yi mutane, yawwa ya ya maganar saka ranar nan, ina ce mun yi da ke tun ranar da na zo cewa sati uku sir yace ya dace a saka? Sai kuma kice da abu mai mahinmanci kar a jadadda ranar, me ya sa? Ga sadakin nan a cikin walet ɗina, ma sha Allah jaka hamsin ne sosai sir ya yi aiki da yadda addini ya nuna, sadaki madaidaici ya fi albarka, jaka hamsin ne sadakin."

Ita da kanta Nabihat yanzun sai da ta ɗago a zabure ta zubawa mahaifinta ido, sai kawai ta ji kuka na neman kubce mata, dan haka ta miƙe da sauri ta fita tana ɓarkewa da kuka ta nufi ɗakin ta da gudu ta faɗa kan gado zuciyarta kamar zata fashe, yanzu ace ita? Ita Nabihat dake iya yin kyautar kuɗa&en da suka fi wannan ko ita dake da ƙarancin dukiya a kansa ita ce ya bada kuɗin sadakinta jaka hamsin dan ya ƙasƙantar da ita ya nuna mata ita ba kowa bace? Ita Nabihat ce aka kawowa sadaki jaka hamsin? Ina, ba zai taɓa yiwuwa ba, ita ma ba zata taɓa iya amincewa da haka ba, ƙwarai da gaske ta yarda da maganar mahaifiyarta, zasu ja maganar har sai sun gane sun ƙara kuɗin, dan ita ma ba zata taɓa yarda a ɗaura mata aure da jaka hamsin matsayin kuɗin sadakinta ba.

A can ɗakin kuwa Hajia ta yi iya yinta ta sama zuciyarta nutsuwa da ƙyar kafin ta fuskanci mijinta da kissa sosai ta ce" Ma sha Allah, Aban Nabihat ya yi sosai, ka riƙe a wajenka, ga kuɗin lefen ma ka haɗa ka riƙe jaka ɗari biyar ce (million daya da dubu dari biyar a Naira), maganar saka ranar kuwa abinda yasa nace haka, aunty ce tace dan Allah a roƙe ka alfarmar a bari har a je aikin hajji, idan muka je sai mu dawo da ita a ɗaura auren nan da ita ta sada ƴar ta a ɗakin ta."

Ɗan jim ya yi sai kuma ya kalleta ya ce" Saboda wannan za'a matsa auren da suka so a ɗaura nan da sati uku har zuwa watanni shida? Haba dai."

Sosai ta marairaice fuska ta ce" Elhaji, ce mata zan yi a'a? Ka san fa rabonta da ƙasar nan tun rikicin da aka yi a kan yayar Nabihat, kuma yanzu ta ce a roƙar mata alfarmar nan sai ince a'a? Ka san fa irin yadda aunty keda ƙulafuci a kan ƴaƴan nan."

Ya sake yin shiru, sai kuma ya ce" Kin ga, zan dai ga sir, in kamar nan da wani wata biyu zai yiwu a ɗaura sai a ƙara yan satittika ma ba wai har wata shida ba, sai ki faɗa mata kawai ta shirya zuwa nan da wata biyu haka in sha Allah, aa aure ai ba'a jiransa Allah ya ba yarinya yaro mai daraja ai sai san barka a yi a bashi su je su yi zamansu da fatan alkairi, yau baki ga tayani murnar wannan abin farin ciki da ake yi ba, Allah ya yiwa Nabihat albarka, bani abinci in ci na kwaso yinwa fa."

Miƙewa ta yi ta nufi waje tana faɗin tana zuwa, dan ɗauko masa abincin, a ranta kuwa tana ayyana _'Ai sai ka yi, in sha Allah sai na ƙwatawa ƴata ƴanci ko da a yi auren nan, haka kawai duk kyansa bai kai cfa ba wallahi, gidan hutu nake so ba in kai ƴata ba in rasa hutun zuciya da na jiki, ka yi ka gama bari in yi kiran auntyn in faɗa mata da kaina zata sameka ne zaka matsa auren nan ko baka so, in yaso mu zo mu samu hanyar bi, dubi wasu ƴan iskan akwatuna da aka kawo wai na Nabihat.'_

A taƙaice daga Nabihat har mahaifiyarta sun ɗauki ɗamarar tanƙwasa zuciyar ango ta hanyar ƙin saka masa ranar aure da wuri da kuma hanyoyin da su suke da su dan ya kawo kansa da kansa ya nemi a saka masa ranar ɗaurin aurensa, wannan lamari ya saka Nabihat kwantar da hankalinta har ta samu barci ba tare da ta taɓa wayarta ba dan a gajiye take matuƙa ga ciwon kai da kuka ya haddasa mata.



*_SAJEERAH_*🖊️


*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:27 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*60*




Kwanaki biyu da suka gabata bayan an kai kuɗin Aswan, yanzu haka ana shirin karɓar kuɗin Yusrah ne a gidan su Anna, Aunty Furera da uncle Sulaimane su da kansu sai da suka ƙara yarda cewar e a yanzu fa da wahala su iya ba Yusrah irin gatan da take samu a gidan mariƙanta, domin duk wani condution da ya dace ace ta samu dan samun farin ciki da gata ta same shi gaba da baya a gidan nan, shiri suke yi da sake yin gayyata dan karɓar lefe da sadakin ƴar su, aunty Intisar a wuni biyun kusan kullum tana nan suna sake shiri da shawara ita da Anna a kan karɓar lefen, da kuma taya ƴan matan nasu shiri, idan ka ganta ta ɗauki babbar riga tana buga waya tana faɗin gobe ne a zo tana gayyatar amsar sadakin ƴar ta sai ka sha dariya da jinjina dan kuwa gayya ta yi sosai da sosai sai da dare ya yi ta koma gida ta bar su Anna ƙarama a gidan Anna wa'inda suke ta murnar ganin ana sabga a gidansu.

Da ta koma gida ta samu Yaya Mubarak na ɓangaren Hajia, dan haka ta je ta gaisar da Hajia ɗin ita ma, a can ta samu zaratan ƴaƴan Hajiar zaune a ƙasa su duka, ga dukkan alamu tattaunawa ake yi ta uwa da ƴaƴanta dan haka ta gaishe su gaba ɗaya ta basu waje ba tare da ta zauna ta jima ba.

Bayan wani lokaci sai gashi ya shigo, ita tuni tana saman gadon ta tana barci dan niyyarta gobe in sha Allah ta yi gida, su zasu amsa ba su zasu kai ba gaskiya, jikinta ya haye a hankali yana sinsinar wuyanta, muryarsa can ciki ya ce" Kin san me Hajia tace?"

A hankali ta juyo tana duban fuskarsa haɗi da lasar leɓensa ta ɗan shige jikinsa can ciki ta ce" Me mama tace?"

Shi ɗin ma a hankali yace" Tace wai a kai irin kuɗin da aka kai na babban Yaya, tun ɗazu lallaɓata ne muke yi ta ce ina mai kuɗi ma ya kai haka balle talaka wai duka duka aikin Bilal ɗin nawa ne? Mun nuna mata mu siyayya ce muka shirya daga kampanin na kowa chop, muna so idan safiya ta yi ne mu je mu kwaso saititikan da aka haɗa mana mu kawo mata, shi ne fa harda kuka wai a kan me za'a yi mata ɗanwaken zagaye a ci amanarta? Dole a dubeta a yi mata abinda ya dace ba wai a ci amanarta ba! Yanzu mun rasa yaya zamu yi, shi ne na ce masa ya kwantar da hankalinsa idan an kai ɗin sai ya yi transfer ya ƙara mata isassun
kuɗin da zata yi suturarta yadda take so."

Fuskarta ta ɗago tana kallon haɓarsa da bata da gashi ko ɗiz a jiki dan Yaya Mubarak baya tara gemu, a hankali ta ce" Yaya, a yi yadda Hajiar ta ce , kuma kar a ƙara kuɗin dan su Anna ba zasu amince ba, albarkar auren ai ake nema, ko nawa aka kai Alhamdulillah Allah ya sakawa abin albarka ya basu zaman lafiya."

Kasa magana ya yi, abin ya girmame shi sosai, tun ɗazu magiya ce suke yi wa Hajia suna rarrashin ta a kan maganar nan, ama ta kafe tace ai fa ba zai yiwu ba, kuma irin shirye shiryen nan da ake yi dan a tarbi baƙi su basu ga tana yi ba, sun ce mata me da me za'a kawo ta ce ba komai, gaba ɗaya Bilal sai rigima yake musu a kan lamarin, ya ɗaga masu hankali sosai ya ce shi fa ba zai yarda ba, kuma ba zai zauna a ɓangaren can ba, dan ta ƙi ya gyara ɓangaren wai a bar wajen hakanan ya yi ba sai an taɓa komai ba wai ai ta ma samu gata part ɗin ɗauke da ɗakuna huɗu ga kicin ga bayi a duk ɗaki ga babban falo, ta san su a gidan ubanta ne? Su kam basu san alƙiblar Hajia ba, ta nuna ta yarda da aure ta ƙi sakuwa a yi abinda ya dace, ko da yake su dukansu haka ta yi a aurensu, dan Yaya Mubarak sai da aka je ta rage abubuwa da yawa haka kuwa su Anna suka amsa da fara'a da murna da komai suka basu ƴar, to Yaya Mubarak mai haƙuri ne sosai a kan Bilal, Bilal sai rigima yake yi ya ƙi sauraron kowa ya ce shi fa ko duka abinda ya mallaka ya mallakawa Yusrah bai faɗi ba tunda yana son abinsa, wannan kalamai sun ɓatawa Hajia rai ainun, amma bata ce komai ba ta kore su daga ɓangaren ta.

Sai da ta bari ya yi barci sosai ta miƙe ta je ɗayan ɗakin ta yi kiran Anna, dan ta tabbata Anna ba mai yin barci da wuri bace balle idan tana da taro, a sanyaye ta sanarwa Anna komai, ta ɗora da faɗin" Anna, ina jin tsoron saka yarinyar nan a hannun Hajia in tafi, ban sani ba ko zata iya jure wasu abubuwan?"

Anna ɗin kanta ta yi jim na lokaci mai ɗan tsayi kafin ta buɗi baki a sanyaye ta ce" Intisar, ba kuɗin auren da za'a kawo bane damuwata, kin san a yanzu a matsayin da yarinyar nan ta taka ko ita sai ta yiwa kanta tufafi idan tana da matsalar su, balle Abanku fa tun jiya ya ce min a ina za'a yi mata siyayya a nan ƙasar ko fita za'a yi? Da na tambaye shi gadaje ? Sai ya ce komai da komai har da tufafi, maganar da nake maki ya yi transfer mai kaurin gaske wacce ba wai tufafi da gadajen ɗakunanta huɗu ba, ko me ye zamu iya siya, kuma na tabbata Yayanku zai motsa, ga na wajenku da Mubarak ya bada, ke dai in ƙarashe maki magana da kuɗin Abanku kaɗai za'a mata siyayyarta sauran dukiyarta sai komai ya lafa zan saka mata a banki sannan a nemi abinda zata yi wanda zai ƙara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login