Showing 75001 words to 78000 words out of 397328 words
shirin juyowa ma, inda ta ji karan mota na ta kwaroronto Katsina Katsina ta nufa, suka yi magana da ciniki gaba ɗaya ta ciro jaka za ta biya tace "Amma ya naga kamar ba'a tafiya yau?"
Amsa ya bata da "E Hajia, amma yanzu za'a tashi in sha Allah, dake akwai matsala ne a hanya, shiyasa ake so mota kamar goma haka ta tashi gaba ɗaya."
Da mamaki tace "Matsala? A hanyar?"
Kallonta ya yi yace "A'a, jiya ne aka bma wani police dukan tsiya har ya suma, sannan aka ɗauke katin shaidar sa da kuma bindigar sa ta aiki kuma babbar bindiga, yanzu haka an ce yana asibiti rai a hannun Allah, to tun daren jiya ma aka baza jami'ai ana ta sintiri da binciken mutane, yau kuma tun da asuba an baza jami'ai a duk wata hanya ta wucewa sai sun ma kowa binciken ƙwaƙwaf."
Jin haka sai kawai hankalin ta ya kwanta saboda a ganin ta wannan matsala ai bata shafe ta ba ko alama, dan haka ta zauna daga cikin motar tana jiran lokacin tashi ya yi.
Wasa wasa sai da ta share awa kusan biyu zaune, su kansu drebobi yau abun bai musu ba, saboda wani da yanzu ya sake juyawa, amma haka aka yi haƙuri dole sai da aka tashi gaba ɗaya sannan aka ɗauki hanya lokacin Yusrah ta gaji, ta matsu iya matsuwa, da aka fara tafiya ne kaɗai ta sauke ajiyar zuciya...
Mota kusan shida ce gaba ta su motar, kuma motar da take ciki akwai mazaunin mutum ɗaya da ba'a cika ba dama, suna shirin hawa titi wani karan mota ya dinga faɗin wurin fasinja ɗaya Katsina, ai ko sai dreban ya dakata Yusrah na kallo ta ga wa zai shigo... Sai *AA* ta hanga yana zagayowa ta inda take zaune dan nan kwandastan nan ya buɗe mishi, ɓata rai ta yi saboda kayan jikin shi na jiya da wannan arnan shirin a jikin shi, sai wata baƙar jaka dake rataye a kafaɗar sa irin ta jita haka.
Ko da ta ga ya zagayo ta ɗauke kai tana matse fuska, kwandastan ne yace "Hajia ɗan matsa mana oga zai shiga."
A wani yangance ta juyo ta kalle shi tace "A nan ɗin?"
"E, sosai ma." Ya bata amsa, ɗan gajeran tsaki tayi tare da matsawa duk ta takure wuri ɗaya, AA da ba wannan ne gaban shi ba ya fara sauke jitar daga kafaɗar sa sannan ya shigo da ƙyar saboda a matse suke sosai, saida AA ya ɗan sake ɗaga rabin mazaunan shi ya kallo inda Yusrah take da nufin ta gyara mana ya zauna duk ta wani babbake kamar motar gadon su...amma sai ya ga ba ta yi niyyar gyarawa dinba, sai kawai ya zauna sosai yana wani bubbuɗe kafaɗu ya wara ƙafafun shi ya aje jakar jitar shi tsakiya sannan ya rufo motar.
Tafiya aka fara, Yusrah da baƙin cikin zama da mutumin ke ciciyar ta haka ta ɗan saci kallon shi, wani irin shegen gashi haka birci birci uwa hanjin mayya, wani banzan ɗamammen wando cinya a fili, ga wasu zobuna har uku a hannun shi na dama har da mai kan fatalwa ce ko aljana, mtsssss! Abun haushi da ba ya ƙarewa a duniya, kuma mutumin ba irin ma ƙananan samarin nan ba, a ƙalla fa ya kwarari wata arba'in haka, idan ko bai yi ba dai a talatin da biyar watanni kaɗan ne babu.
Hannun shi ya zuro zai kai ga aljihu ya ciro sigari, da wani irin saurin bala'i Yusrah ta damƙi jakar kuɗin ta tana wani kallon shi irin bata gane ba fa, shi ma kallon ta y yi da son gano me take nufi da shi? Da ya fahimta wato ɓoye jakar ta take yi sai kawai ya taɓe baki ya shiga lalubo karan sigarin da ƙyar da jaraba saboda ba ƙaramin takura ya yi a wandon nan ba... Har ya kai sigarin a bakin shi ya fara neman maƙyasta, sai kawai ya yi wani irin duƙowa yana leƙa fuskar Yusrah da son gano wai tsaya? Wannan kuwa bai san ta ba a wani wurin? Dake so yake ya nuna shi ɗin tantiri ne, madadin ya mata magana sai kawai ya sa yatsa ya ɗan laƙato kafaɗar ta, da sauri ta juyo a hassale ganin shine ya taɓa ta cike da masifa tace "Malam me ye haka? Ba fa na son ƙananan iskanci."
Tsaki ta ja ta sake juya kan ta tana kallon ɗaya ɓangaren tana faɗin "In ba jarabar mota ba ma mai kwashe kwashen haɗa ka da kowa, me zai haɗani wannan zaman kata'in da kai."
Magana ta gaskiya jarabar da take yi dariya ta so bashi, wato likitar nan ce mahaukaciya har anan tasha? Me ya kawota nan? Anya kuwa ba tserewa ta yi ba? Wataƙila ana can ana neman ta, sai kuma ya kawar da kan shi ya taɓe baki kawai ya karkata sigarin a gefen bakin shi amma bai kunna ba, saboda dama ba niyyar kunnawar gare shi ba ko dan jama'a.
*Tafiya* tayi *tafiya* tun suna wuce inda ba wani caje caje sosai, har suka kawo inda sojwa ne ke tsaro musamman saboda abinda ya faru jiya, AA na hangen haka ya gyara zaman shi yana murmushi, haka jerin motocin suka dakata kowa ya fita ana ta bincike tun daga jikin mutum, kayan mutum dake cikin koma menene zuwa bayan mota da saman ta. Suma dama duk sun fita, amma Yusna ciki zaune sai hararen AA take dake tsaye jikin motar yana shan sigarin da ya jima rabon shi da ita, sojawa biyu ne suka tunkaro motar su ya gyara tsayuwa yana jefar da sigarin ƙasan ƙafar shi, ya ɗan juyo kan shi da nufin saka ƙafa ya murje kawai suka haɗa idanu da Yusrah tana masa kallon banza, da yanayin fitsara yace mata "Sorry fa, ban miki bismillah ba, amma ki ban kwatancen inda za ki sauka, akwai ƴar murje, akwai wiwi, akwai tabar gume, sannan akwai irin wannan, duk zan haɗa na kawo miki gida."
Wani takaici ne ya kunnota, za ta yi magana sojawan nan suka ƙaraso inda suke, ɗayan wasu ya fara bincika, inda ɗayan ya shiga ƙarewa AA kallo da yanayin shi, sai kawai ya tara masa hannu yace" Katin shaidar ka?"
A wani gadarance AA yana kallon sojan cike da raini yace" Tsayuwata anan bai shaida ko ni wanene ba? Ko hakan bai ya isa ya nuna nima ɗan ƙasa bane?"
A mugun kausashe police ɗin ya wni ƙara riƙe bindigar shi tare da murtuke fuska yace "Maganar banza, wa ye kai anan? Malam kar ka ɓata mana lokaci ka ji, aiki ne a gabanmu ja, idan kuma tashen rashin kunya ne kake ji muna daidai da zamanin irin ku, bani katin ka nace?"
Ya faɗa yana tara masa hannu. Yusrah ta jima da tsorata, tun daga tambayar kati da aka yi ita kuma bata san ina nata yake ba, da dai niyyar ta shine ta faɗi yadda aka yi ta rasa katin nata, idan dai suna jin labarai ai sun gasgata ta, to amma ta ga alamar wannan rikitaccen yana neman hassala su har su ƙi karɓan uzirin ta, wanene shi? Me yake ji da shi jama'a? Ita wallahi a ƙage take da taje inda Safwan yake, dan haka ta fito saga motar jikin ta na neman kwasar ɓari baki na rawa rawa tace "Yyyallaɓ...ai, n..."
Kallon ta police ɗin ya yi a tsawace yace "Madam ban zo gare ki ba ki jirani dan Allah."
Ai kuwa sai AA ya juya ya kalle ta, me ya shiga kan shi? Shi kawai tsoro da firgicin da ya gani a tare sa ita sai ya ji yana neman zama masa abun nishaɗi, sai kuwa ya daddage ya cira jakar hannun shi da hannu ya miƙawa Yusrah, bai jira ta amsa ba ya aje kan jikin ta yana kallon ta yace "Yanzu hankalin ki ya kwanta *ƙoramata*? Wa ya ce ki sa baki a maganar mu? Ai kinsan dai mijin ki ba sakarai bane ko?"
Yana gama faɗa ya juya kan sojan yace "Me ka ce in baka?"
Wata uwar harara ya watsa mishi yace "Katin shaida da farko."
Laluba aljihun shi ya fara yi yana kallon Yusrah da kamar ta suma daga zaune sam bata gane kalaman sa ba yace "Allah ya sa baki manta min shi ba garin azalzalar mu zo, wato ke dai in biki ya zama na danginku ne to ba wani esxuce kawai a je."
Da wani matsiyacin mamaki Yusrah ta nemi tashi tsaye tana shirin aje jakar da ya ɗora mata tace "Wai kan ka ɗaya kuwa? Me kake magana a kai?"
"Katina na shaida." Ya bata amsa kai tsaye yana ciro walet da kwalin sigari, duba walet ɗin ya yi sai kawai ya sake ajeta saman jikin Yusrah yace "Yallaɓai ban ga katin nan ba fa, ya zamuyi yanzu? Nawa ne farashin ka?"
Wata mahaukaciyar tsawa ya daka masa da cewa "Kai, ka shiga hankalin ka wallahi..." Sai kuma ya sagala kafaɗar shi a kafaɗa ya matsa kaɗan ya zura hannu ya ɗauki walet ɗin da AA ɗin ya aje jikin Yusrah yana faɗin "Wallahi yau zaka yabawa aya zaƙin ta, ana hanaku shaye shayen nan, idan kuma ya zama dole sai kun yi ku sha wacce za ta iya ɗaukar kan ku mana, amma ku ja rikicin da y..."
Katin police ɗin nan da ya bayyana a walet ɗin ya sa shi ɗauke wuta daga abinda yake faɗa, haba wa! Ai sai ya damƙe wallet ɗin ya shiga shaidawa sauran jami'an an samu wani abun zargi anan, da gudu duk sauran suka dawo nan tare da zagaye AA suna nuna shi da bindiga, amma duk da haka bai razana ba sai wani basarwa da ya yi ya kalli Yusrah "Fisabilillah akwai abinda na musu anan ƙoramata?"
Jefar da kayan da ya zuba jikin ta tayi ta nunoshi da yatsa tace "Ka ƙara sakani a maganar ku da su yallaɓai wallahi zan maka hauka."
Wani shaƙiyin murmushi ya yi ya kalli jami'in da ya fi kusa da shi cikin raɗa yace masa "Wasu lokuta ciwon ta ya kan motsa dama irin haka, shiyasa aka ce *so jarabta* ne."
Wanda tun farko yake tuhumar AA ne ya kalli ɗaya daga ciki yace "Duba mana wannan kayan sa ne."
Da sauri ya duƙa kusa da AA ɗin ya ɗauki kwalin sigarin da Yusrah ta jefar ya zazzage sogarin ya jefar AA kuma na faɗin "Kai daina jefar min da kayata ƙasa, kuɗi na sa na siya fa, ka ji almubazzarancin b..."
Sa'ilin da jami'in ya buɗa jakar jitar nan ya ga bindiga ɓaro ɓaro wacce suke nema, shiyasa ba su bar shi ya ƙarasa maganar ba wani daga ciki ya daki tsakiyar guiwar AA, hakane ya tilasta masa durƙusawa da guiwar da aka daka ɗin, cikin tsawa da tashin hankali jami'in yace mishi "Hannun ka saman kan ka, kar ka sake f..."
Shi ma d zafin nama bai yarda ya gama maganar sa ba cike da takaici da sauka a aikin shi ya miƙe kamar wani zaki ya damiƙi wuyan matashin police ɗin nan wanda ko banza ya girme shi ya kuma girmi jikin shi, wannan ne dalilin da ya sa take police ɗin nan ya ji wannan shaƙa ba kaɗan ba har kamar yana tafiya gangara zai wulla.
Da gudu sauran jami'an suka rufu akan AA suna nuna shi da bakin bindigogin su suna umartar shi da ya sake jami'in su ko su buɗe mishi wuta? Da ƙarfi ya yi cilli da shi gefe har saida ya kai ƙasa dandaɓar, nan suka sake umartar shi da guiwar shi ƙasa.
Ganin ana mutane nata ƙoƙarin ɗaukar videon abinda ke faruwa ya sa ya duƙa ɗin yana ta ƙoƙarin sinne kan shi, suma jami'an sun yi ƙoƙarin su wajen hana ɗaukar hotunan tunda ba'a tabbatar da laifin sa ba tukuna.
Ba musu ya yi yadda ya ce, nan take aka umarci wani jami'in da ya ƙaraso da mota, inda wani ya juya ta baya yana sarƙafa masa ankwa a hannu, AA kuma hankalin shi na kan Yusrah da ta jima da miƙewa tsaye tsabar tsoro jikin ta rawa yake, kusan kamar ta fi kowa tsorata da lamarin duk da kuwa sauran mutane ma duk a ɗarare suke, wasu kuma har sun fara ɗauka da wayoyin su dan ma jami'an na hanawa.
Kallon Yusrah ya yi kamar wata kakar shi yace " *Sweety*, kinga da zaki min hallaci sai ki biyoni muje duk inda zasu kaini, kinga ba mai baki abinci idan kin koma gida ke ɗaya, wallahi yunwa c..."
Da ɗaga sanda motar ta iso wani ya nuna Yusrah da bakin bindiga yace "Wacece ita?"
Da sauri AA ya kalle shi yace " *Matata ce*, me ya sa ka tambaya?"
Kallon wani jami'i ya yi yace "Tare ka gan su?"
Jinjina kai ya yi yace "E yallaɓai, jakar ma a hannun ta take."
Da mugun tartsatsi yace ma Yusrah "Maza malama, guiwanki ƙasa, kai saka mata ankwa ita ma, ina kayan ta?"
Jakar ta ta jefar ta ɗora hannayen ta biyu a kai ta kwamtsa wani irin salati da cewa "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! La'ilaha ilallahu Muhammad Rasulillahi sallalahu alaihi wa sallam! Na shiga uku ni Yusrah."
Sai kuma ta nemi matsawa kusan ogan tare da aje jakar kayanta da ba wani yawa ne da su ba tana faɗin "Yallaɓai, dube ni da hijabina, da mutumcina, da darajata ta ƴa mace, a ce na rasa mijin aure sai wannan *abun*? Allahumma ajirni fi musibati, waklufli kairan minha, yallaɓai ku duba jakata ku gani, ni wallahi har karatu ma nayi."
Ai kuwa da gaske gurfanar da ita sukayi suka ƙaƙaba mata ankwa kafin a saka ɗaya ya fara bincika jakar ta, duk da sun ga takardun ta na makaranta masu mahimmanci har da ta shaidar makarantar likitanci da ta yi, sai dai babu katin shaida, mayar da kayan sukayi amma babu alamar zai ce ta tashi ko a ƙyaleta, dole ta fashe da kuka tana rantsuwa da faɗin" Yallaɓai, na rantse da girman Allah, na rantse da Allahn da ya halicceni ban san wannan ƙazamin bawan ba, wallahi tallahi bani da wani haɗi da shi yallaɓai, ku tambayi kowa ku ji zai faɗa muku gaskiya."
A tsawace jami'in yace" Ke shiru! Ba abinda bamu sani ba game da irin ku, tare kuke shirya duk wani bala'i da mazajen ku ko ƴan uwan ku, nan wane irin case ne bamu gani ba da ranmu?"
Wata irin shegiyar dariya AA ya bushe da ita yana kallon ta yace" Ka ji rainin wayo, ita nan fa ta ɗauka yanka mu zakuyi? Har da wani cewa da hijabi, to ba da hijabin ba har ƙunar baƙin wake mun shirya da ke, makamai nawa kika wuce mana da su a cikin hijabi *Wifeyna*?"
Miƙar da su akayi tsaye amma Yusrah ta dinga tirjewa kamar ragon da ya ga wuƙar yankar shi, rikici irin na jikan Anza sai kuwa ya daka mata tsawa da cewa" Billahillazi wifey kika ɗaga bujen ki a gurin nan kotu ce kaɗai za ta rabamu."
Har da wani jinjina kai ɗin nan irin barki ɗin nan ya ci gaba da tafiya a zafafe yana cewa" Ni ga sakaran banza tsaye kina ta ware ƙafafu gaban dubbanin kwarata, duk lalacewata ai nasan mahimmancin gonata ko? Haba dan Allah."
Cikin kuka da tashin hankali Yusrah ke duban ƙeyar shi tace" Ka rantse da kwarankwatsa ta faɗo saman kan ka ni matar ka ce? Ka rantse musu da doguwa mana."
Turus! Ya tsaya ya juyo kamar dai mijin da zai tsawatawa matar sa yace" Ban hana ki yi min rantsuwar banzan nan ba idan ba da Allah za ki yi ba? Tomm!"
Ya faɗa yana ci gaba da tafiyar shi saida ya zo ɗaga ƙafa shiga motar ya fahimci illar da samarin da suke son saka irin wanɗunan nan matsatsu suke ma kan su, dan kuwa tsaf ya gagara haurawa motar saida ya kalli jami'an dake bayan shi yace" Ku cicciɓoni dan Allah? Wandon ne ya soma yi min kaɗan."
Cicciɓa shin sukayi ya shiga ya zauna, Yusrah kuwa da ta dage akan saidai su kasheta ba inda za ta je cirata sukayi suka wulla cikin motar sannan suka rufe aka tayar da motocin suka bar nan dan dama abinda ya kawo su kenan.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*21*
Da gudun tsiya motar ta shigo cikin babban ofishin sojawa, wanda ake kira da PG, tunda suka shigo ya sinne kansa, domin ya sani da wahala ya shigo nan ya fita bai haɗu da mazaje ba, ɗaya ya gane shi duk kuwa da irin shigar da ya yi, da askin da ya yi, da irin yanayin da ya shigo, daɗin sa ɗaya a irin yadda garin nan ya girma a yanzu haka ire irin PG din sun kai goma manya manyan banda maganar ƙannanu waɗanda duk anguwa akwai dan kwantar da tarzoma da kawo tsaro.
Kama wuyansa polise ɗin nan ya so