Showing 54001 words to 57000 words out of 397328 words
Ta tambaya cike da jimami, nan ma amsawa ta yi da sauƙi, kafin aunty Khadin ta dafa kafaɗar ta tace "Yusrah haka wannan abu ya faru daɗa? Ki yi haƙuri kin ji, Allah ya baki dangana, Allah ya jiƙan su Baba, Allah ya musu rahama, ku kuma Allah ya baku lafiya ya rayaku, sannu kin ji."
Da jin daɗin kulawar ta gare ta sosai ta amsa da ameen, Goggo dake ta yatsina fuska ta kalli aunty Khadi tace" Ki tashi ki zuba mata abincin ta tafi da shi."
Da sauri tace" To, amma komawa zakiyi yanzu?"
Jinjina mata kai Yusrah ta yi alamar e, miƙewa ta yi da sauri ta nemi kwano ta wanke ta zuba mata sosai har da man sannan ta kawo mata, karɓa ta yi bayan ta miƙe tsaye tace" To Goggo ni na tafi."
A taƙaice tace mata" A gaida Iya."
"Za ta ji." Ita ma ta faɗa tana nufa ƙofa, bayan ta aunty Khadi ta biyo cikin raɗa tana faɗin "Nima in sha Allah zan leƙo ko zuwa gobe ne na ga jikin Safwan ɗin."
Amsa mata ta yi har suka kai soro, tsayar da ita ta yi ta shiga kiciniyar ciro ƙaramar jakar hannun ta dake matse a rigar ta, zif ɗin jakar ta zuge ta ciro jaka biyu ta miƙo mata tace "Karɓi wannan Yusrah ya muku anfani, kuma na san ba lalle kina da kuɗin komawa asibiti ba."
Murmushi Yusrah ta yi ba tare da ta ce a'a ba ta sa hannaye biyu ta karɓa tana mata godiya, har ƙofar gidan ta rakota sannan ta koma ciki ita kuma ta tafi. Tun a hanya ta yanke shawarar ba za ta koma asibitin ba, ta ɗauka idan ta je ta faɗawa Goggo za ta samu wani abu a gurin ta ko da wanda za su ci gaba da biyan kuɗin gado ne da sauran ƙananan abubuwa, amma sai ta yi burus da lamarin kamar ba ta san su ba, tana zuwa asibitin ɗan kurma dake kama ma mahaifin na shi aiki ta ba kwanon tare da kaso biyu na ukun kuɗin hannun ta tace "Dan Allah ka kai ma tsohuwar nan da muke jinyar Safwan tare, ka ce mata na je na dawo yanzu, su ci abinci kar su jira ni."
Da sauri ya juya ya tafi dn cika umarnin ta ita kuma ta shiga takawa a ƙafa, ko mahaifin ta dake ɗawainiya da su ba ta taɓa jin ya tafi roƙo ko neman taimako wajen wani ba, sai dai ita a yau za ta tafi, wulaƙancin da Docter Hamat yake son yi mata na kawai ta ƙi bashi haɗin kai take so ta dakatar ta hanyar ɗaukar duk wani caji da zai mata na kuɗi, duk da ɓangaren da suke yanzu na masu matsakaicin ƙarfi ne irin su, amma dai duk kwanan duniya akwai kuɗin gado da ake biya, gashi ko ruwa ya ce kar a ƙarawa Safwan idan ba kuɗi ta biya ba, dan haka za ta tafi gidan Alhaji Bubakar tresorie da ta ji ana faɗa cewa ya na taimako sosai, shiyasa za ta je ta jaraba ta gani ko za ta dace.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*16*
Tana isa ƙofar gidan bayan sun gaisa da mai gadi take tambayar shi "Dan Allah ko Alhaji yana nan?"
Kallon ta ya yi sama da ƙasa sannan yace "Baiwar Allah lafiya kike neman Alhaji?"
A sanyaye tace "Lafiya lau wallahi, na zo wajen shi ne dai."
Da kulawa yace "Yarinya Alhaji baya nan, ba ya ma gari gaba ɗaya, tunda suka tafi aikin Hajd shi da iyalin sa basu dawowa ba saboda ganin likita da zasuyi, amma dai an ce satin sama in sha Allah za su shigo."
Tunda ya furta ba ya gari ta lumshe idanun ta tana karanta _"Hasbunallah wani'imal wakil."_
Saida ya gama bayanin shi sannan ta kalle shi a tausashe jiki ba karsashi tace" Shikenan Baba, na gode sosai, sai anjima."
Gyaɗa ya yi yana kallon ta, har ta juya yace" Yarinya."
Da sauri ta juyo ta amsa da" Na'am Baba."
Ɗorawa ya yi da" Da alama taimako kika zo nema, Alhaji mai taimakawa ne fisabilillah, ki dawo sati na saman in sha Allah zai taimaka miki, da kaina zan miki iso har wajen shi."
Murmushi ta yi, sati na sama zuwa lokacin idan ta samu abinda take so ai Safwan ya fara samun lafiya, amma dan kar ta gwasale shi sai tace" To Baba, in sha Allah zan dawo, na gode sosai da wannan taimakon."
Murmushi shi ma ya yi yace" Ba komai, Allah ya kyauta."
"Ameen." Ta faɗa tana sake juyawa, saida ta karya kwana ta zauna bakin wata itaciya dan ta yi tunanin abun yi, gidan Hajia Fauziyya da ya zo a ran ta yasa ta miƙe zunbur ta ɗauki hanyar ba tunanin komai. Matar gidan ta yana kusa da makarantar su ta likitanci ne, suna shiga ne kawai suna shan ruwa ko alwala da sallah ko ma wata buƙatar daban, tana da tsananin kirki haka ma mijin ta bai da matsala, a ƙalla ta san in dai tana da ko ba komai za ta samu ko da wani kaso ne na abinda take nema.
Da ƙyar adaidaita sahu ya ɗauketa saboda kuɗin hannun ta sun ƙare. Amma alhamdulillah, tunda tana zuwa tun a ƙofar gidan mai gadi ya buɗe mata ƙofa dan ya san su farin sani, haka ma ciki da ta shiga tayi karo da yaran ta suna wasa, duk da murna suka tarbe ta kamar wata ƴar uwar su ta jini, haka ta gaisa da su sannan ta wuce falon maman nasu.
Aka ce wai shinfiɗar fuska ta fi ta tabarma, ƙwarai hakane dan yadda ta karɓe ta saboda tunda aka turasu service ba su haɗu ko a hanya ba, tun bata yi niyyar sanar da ita abinda ya kawo ta ba ta shiga ƙwallawa mai aikin ta kira, tana fitowa tace mata "Yawwa, dan Allah ki kawo wa Yusrah abinci da abun sha."
Da "To." Mai aikin ta amsa ta juya zuwa madafa, kallon ta Yusrah ta yi tna murmushi tace "Aunty Fauziyya wallahi da kin bar shi, ba zan iya cin komai ba."
Ɗan hararan ta tayi da wasa tace "Iyeh! Saboda me kuma? A gidan nawa ne za'a ƙi cin abinci kuma Yusrah?"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan tace "Ba haka bane aunty Fauziyya, ban da lafiya ne ga kuma uzurin da ke gabana, ba zai barni na ci abinci ba yanzu dan ba zan gane ɗanɗanon shi ba."
Tsam! Aunty Fauziyya ta yi ta zuba mata idanu saboda serious ta yi maganar, a tausashe tace "Subhanallah! Me ya same ki Yusrah? Tabbas na ga duk kin faɗa ba kamar yadda kike ba, me yake faruwa da ke?"
Ita ma zubawa aunty Fauziyya idanu tayi tace "Aunty Fauziyya, na san ba zaki rasa jin rushewar gidajen da ya faru a unguwarmu ba wajen zarya, a cikin wannan rushewar har da gidan mu."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil! Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!" Shine abinda ta yi ta maimaitawa tana tafa hannaye kafin daga bisani tace "Yusrah na samu labari, sai dai wallahi ban san da ke a hatsarin ba, Yusrah har da gidan ku?"
Jinjina kai ta yi a sanyaye tace "Har da gidan mu aunty."
Da sauri ta ce "Amma dai kowa lafiya ko?"
Kallon ta Yusrah ta yi ta ɗan ƙaƙaro murmushi, sai kuma ta kawar da kan ta gefe hawaye na ziraro mata, saida ta haɗiye wani abu mai nauyi da ya tokare mata maƙoshi kafin ta sake kallon ta tace "Aunty Fauziyya da Mamanmu, da Babanmu, da aunty Hannah..."
Sai kuma ta huro iska daga bakin ta sannan ta ce "Duk sun rasu, Mamanmu da Hannah ko shurawa ba su yi ba, Babanmu ne ma ya rasu a asibiti."
Dafe goshi aunty Fauziyya ta yi ta shiga jeranta salallami tana share hawaye cike da tausayin ta, ƙwarai ta shiga jimamin da ya sa dole Yusrah ta ɗora da "Ni da Safwan ne a asibiti, ni kam ban da matsalar komai a jikina, amma Safwan..."
Da sauri ta ɗago ta kalle ta tace "Me ya samu ƙanin naki?"
A nutse tana sadda kan ta tace "Karaya ya samu a cinya, sai ƙashin bayan shi da ya taɓa duka ƙafafun shi yanzu haka ba ya iya tafiya, kuma a asibiti sun tabbatar mana da idan ba'a masa aiki da gaggagawa ba zai iya rasa ƙafafun shi na har abada."
Sai kuma ta ɗaga kai ta kalle ta tace "Aunty Fauziyya, kuɗin aikin da za'a ma Safwan suna dayawa, nema nake yi saboda bana so ya rasa ƙafafun shi, yanzu haka akwai filin su Babanmu da aka saka a kasuwa, idan aka siyar za'a bamu kason su mu biya kuɗin aikin, sai dai na san ba za su isa ba saboda su uku ne da filin, shiyasa aunty na zo da sa ran za ki taimaka min da wani abu, dan Allah aunty Fauziyya ko bani ne ki yi na biya, idan ya so na samu aiki na dindindin sai na dinga biyan ki."
Girgiza kai aunty Fauziyya ta yi da jin ba daɗi sosai tace" Haba Yusrah, tsakanina da ke ai babu haka, kinga matsalar babu kuɗi ne dayawa a hannuna wallahi, gashi kuma Baban yara sai yau ne yake shigowa gari, amma bari ina zuwa..."
Ta faɗa tana miƙewa ta yi hanyar falon mijin ta, gyara zama Yusrah ta yi tana sake kallon ɗakin da aka sauyawa jere, wataƙila dan mai gidan zai zo ne, ta ɗan ɗauki mintin da ya fi sha biyar kafin ta ji motsin fitowar aunty Fauziyya.
Tana zuwa kusan ta ta zauna sosai tare da miƙa mata enveloppe tace "Karɓi wannan Yusrah ba yawa, sai dai na kira Baban yara na sanar da shi abinda ya faru, ya ce ba damuwa idan ya shigo in dai bai yi dare na, to ki bar lamba da za'a same ki sai ki zo, idan kuma ya yi dare to gobe da safe kawai ki zo, in sha Allah Yusrah ƙanin ki ba zai rasa ƙafafuwan sa ba."
Tana kuka ta karɓa tana godiya, da ta sake mata maganar lamba ne tace" Aunty tunda na farka ban san a ina wayata take ba, na san kuma da an gan su da za'a bani."
Da rashin damuwa tace mata" To shikenan, ina ga kawai goben da safe ki zo."
Jinjina kai ta yi alamar to, da haka ta miƙe tana sake yi mata godiya, rakota ta yi har bakin ƙofa sannan ta koma cike da jimamin wannan lamari da tausaya mata.
Tana fitowa ta bi ta hanyar da take ganin za ta fi sauƙin samun adaidaita sahu, anan ma har ta ciro kuɗin nan ta shiga ƙidayawa, ta yi mamaki sosai da ta ga adadin kuɗin, dan ba ta ɗauka za ta samu ko jaka arba'in ba, amma sai ga shi ta samu har kusan jaka ɗari a wajen matar da ba su da haɗin komai, kawai zumunci ne na hanya amma ta mata wannan alkairin ba tare da tunanin ta biya ta a gaba ba? Lallai aunty Fauziyya ta daban ce a cikin mutane.
Niyyar ta shine daga nan gidan su Maryam za ta wuce, amma da hanya ta ɗaukota ta biyo ta gaban irin ma'aikatun nan masu aikin sa kai wanda ke zaman kan su, sai ta ga mata da samari na fitowa daga ciki kuma mafi aksarin matan ƴan mata ne da riguna iri ɗaya na aiki da suke ɗauke da tambari da sunan ƙungiyar da kuma wasu irin jakunkuna har biyu a kafaɗun su, da mamaki take ta kallon su saboda gaskiya ba su yi kama da masu rigakafin shan inna ba, kuma ta sani irin ma'aikatun nan kullum suna cikin ƙirƙiro abinda za su taimaki mutane ne, dan ba ta mantawa watannin baya an je unguwar su duk aka ɗauki sunayen mata aka dinga basu jari, Mamansu ma ta samu nata kwason dan dai kawai gida ya cinye ne, dan haka wasu ƴan mata biyu da suka fito a a jere ta tsaida su da cewa "Sannun ku ƴan uwa?"
Amsawa sukayi da "Yawwa, sannu."
A nutse tace "Dan Allah me ake anan naga kuna ta fitowa kamar za ku je wani aiki?"
Ɗaya daga ciki ce tace "E, aiki zamu je, projet ce ta bamu aiki."
"Wane iri?" Cewar Yusrah da gaggawa, amsa ɗaya daga ciki ta bata da "Gidan sauro ne za'a rarraba unguwannin gangare da irin can ƙuryar gari da kuma su zarya haka dai, kin gane? Saboda bincike ya nuna ana ta samun mace mace da rashin lafiya wanda cizon sauro ke haddasawa, shine zamu fita rabawa yanzu."
Da gamsuwa tace "Kuma biyan ku za'a yi?"
Murmushi ɗayar ta yi tace "Projet ai ba'a musu aikin banza, biyanmu zasuyi mana, yau ne da gobe da jibi an gama, da ka kai musu wannan katin da adadin mutanen da ka ɗauko sunayen su, mu yanzu aikinmu shine mu ɗauki sunayen mutane da adadin dake cikin gida da kuma gidan sauro nawa ake da buƙata, su kuma zasu tura ma'aikatansu su raba musu."
Cike da gamsuwa dai Yusrah tace" To nawa za'a biya?"
Amsa ta bata da" In dai kin iya rubutu, to a kwana ukun nan kin ci jaka sittin."
Da mamakin kuɗin Yusrah ta buɗe baki, amma sai ta ɓoye mamakin ta tace" Yanzu nima za su iya daukata? Wane takardu suke karɓa kafin su ɗauke ka?"
Girgiza kai ɗayar ta yi tace" Ko ɗaya, ke dai ki basu cikakken bayanin ki kawai ki kuma san kin yi karatu za ki iya rubutawa da karantawa, to shikenan."
Murmushi sosai Yusrah ta yi tace" Na gode sosai, na gode ƴan uwa."
Da sauri ta raɓa su ta shige ta ƙofar da masu gadi biyu ke tsaro ba tare da sun hana ba saboda yau ƙofar buɗe take ga kowa.
*MENSION ANZA*
A cikin ɗakin baccin su Manal ta yada zango tun da ta zo gidan, yanzu haka hira suke ba ji ba gani kuma ba ta da niyyar tafiya gida duk da yamma ta yi lis, Abrar na fitowa daga wanka Nawal ta miƙe ita ma za ta shiga tana faɗin "Bari na yi alwala idan mukayi sallah zan nuna miki hotunan."
Da kallo Nabihat ta bita, ita akwai abinda ke ran ta take kuma so ta tambaye su, amma kallon da zasu mata ya sa take ta dannewa, ba ta so su fahimceta da wuri bare har su fallasa sirrin da ke ran ta, yanzun ma tambayar da take so ta yi daban, amma sai ta share tace "To shikenan."
Kallon Abrar ta yi tace "Ke kin yi ankon bikin gidan su aunty Inti?"
Abrar dake shafa turare a jikin ta ta amsa mata da "Wallahi na siya, da zamu je mu kai ɗinki yau, to sai aunty (Anna) ta ce sun yi waya da aunty Inti wai jaririyar ma suna asibiti an riƙe su, shiyasa muka ɗan dakata har mu gani."
Da kulawa Nabihat tace "Subhanallah, ba ta lafiya?"
"Um wallahi." Ta bata amsa, dan haka tace "To Allah ya bata lafiya, nima na siya saboda aunty Inti ta ce idan ban yi ba to za ta ɓata min rai, na ce ai ba za ta kaimu ga haka ba ma."
Dariya Abrar ta yi ita da Manal tace "Ai kam za ki sha mita."
Sai Manal da ta ɗora da "Ita f a a dole bata so ta ga ƴan gidan su a baya bayan kuma akwai abun a yin."
Kallon Manal Nabihat tayi tace "Ban ga laifin aunty Inti ba, za ta ƙara kece raini a cikin dangin mijinta a gane ba ƙananan mutane bane, sannan a fahimci sharar fage muke, dan wannan karan dole a bar mana aunty Inti ta haihu a ƙasar nan dan mu bada mamaki."
Abrar ce tace "Gaskiya kam, dan nima abinda nake fata kenan."
Nawal da ta ɗauro alwala ce ta yi katsalandan a maganar tasu da cewa "To ku tayata fatan ta samu cikin."
Nabihat ce tace "In sha Allah ma tana da shi, dan rashin lafiyar da ta yi kwanan baya nake ji a jiki ciki ne."
"Allah ya sa to." Cewar Nawal da Abrar a tare, Manal ma ban ɗaki ta shiga, Nawal kuma ta kabbara sallah magrib da aka kira ba jimawa, Abrar ma na saka hijab Nabihat ta miƙe ta matsa kusa da ita, cikin raɗa saboda ganin ai ita cousine ɗin su ce tace "Sis, wai Yaya AA baya nan ne? Ni tunda na zo ban gan shi ba, ko za ki rakani gidan shi na gaishe shi ba tare da twins sun sani ba?"
Darammmm! Shine sautin bugawar ƙirjin Abrar da ya sakata kallon Nabihat a zabure, dakatawa ta yi daga saka hijab ɗin ta ta shiga ƙare ma fuskar ta kallo kamar mai son gano munin ta ko wani abun ta da ya ɓata a fuskar Nabihat din. Abun da ke mata yawo shine... Ba wata dangantaka