Showing 339001 words to 342000 words out of 397328 words

Chapter 114 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69992

yi sai kawai dariya ta kubce masa, dan ya san abun nan da tayi har da gayya ta masa, wataƙila dan ta yi alfahari, ko kuma tana so ta huce takaicin bai tuntuɓe ta ba wajen saka ranar ya yi gaban kan shi, duk da kuɗin sun so su fi ƙarfin shi, ba dan ma rufin asirin Allah ba kana wasu hulɗoɗin na arziki da kuma tarayya da manya irin su Aba, amma albashin nasu na wata nawa ne? E manya ne su kuma suna ɗauka da kauri sosai, amma hidimar gida ai ita take cinye komai, dan kar ya nuna mata gazawar shi sannan kar su fara da ɓacin rai da cacar baki sai kawai ya tanƙwashe takardar ya ajiye kusa da shi yace "Ba damuwa dan wannan madame, in sha Allah ba zai gagara ba, idan na dawo anjima zan baki ko da rabi ne, kafin lokacin sai na cika sauran ko? Hakan ya miki?"

Da dariya a fuskar ta tace "Ba komai Papan Nabihat, Allah ya amince."

"Ameen." Ya fara amsawa da shi kafin ya ɗora da "Ba wani abun kuma?"

Girgiza kai ta yi tace "Ba kom..." Wayar ta dake cikin tafin hannun ta ce ta yi ƙara, dan haka ta dakata da maganar tana duba allon wayar, ganin lambar da ta jima da hardacewa saboda nacin kiran ta da mai lambar ta dinga yi a lokutan baya yasa saida ta ji wani sanyayyan faɗuwar gaban da ya sakata lumshe idanuwa kafin ya jimƙe wayar a hannu sosai ta buɗa idanuwan ta tana mai jan tsaki ta yanke kiran, sannan ta sake maida duban ta ga Chef dake kula da ita sosai tace "Papan Nabihat, nace anan zan kawo maka abincin ka? Ko na bar..."

Wani kiran da ya sake shigowa ya sake katse mata maganar ta, da yanayin hassala ta dubi wayar tana sake katse kiran da jan wani wawan tsaki ta furta "A'a, yau ga jaraba."

Da kulawa Chef dake kallonta yace "Ya dai? Wa ye yake kiran ki haka? Ki ɗaga mana."

Kallonshi ta yi cike da wofantarwa tace "Wannan banzar Fauziyyar ce, kasan mun haɗu da ita gidan Aswan ta je raka amarya ɗazu, kar ka so kaga shishigi wajen yarinyar nan, za ka rantse da Allah bata da labarin Aswan zai auri ƙanwar ta, amma dan baƙin ciki da baƙin hali haka take ta wani shige ma amaryar har da tayata shiryawa, duk da ma naji tana faɗin ai ita tasan Yusrah ne ba tun yau ba, wai ko tun Yusrah na makarantar koyon likitanci suka san juna, wa ye wa ye dai haka, aikin banza kawai, shine zata dameni da kira dan taga ni ko kallon Allah ya isa ban mata ba."

Saida ta yi shiru sannan Chef ya numfasa bayan tunanin da ya wuni yana yi akan babbar ƴar sa da Aba ya sake yi masa maganar ya tausasa mata tun safe, da abun ya wuni a rai har ya fita da shi ya kuma dawo da shi, a ganinsa lokaci ne ya yi da zasu jawo ƴar su ga jiki kamar yadda ya faɗa, yau dai ko raba auren ta sukayi da mijin ta ai basu da wata riba, sannan duk inda aka je aka dawo Jamil dai ya zama nasu shima tunda har Fauziyya ta haifa masa yara ɗaiɗaya har guda biyar, shin da basu yi auren ba ma da ina wannan zazzafan rabo zai kai su? Da su da suke iyayen ta yanzu suna ina? Baya ga haka ya lalata zumuncin shi da ƙanin shi, wanda shi da shi sai dai gaisuwa irin ta sama saman nan kawai dan wannan abu, duk me ya yi zafi? Tsawon wane lokaci za su iya ɗauka suna hushin da ita? Suna rayen amma bata bar mijin ta ba ta dawo gare su, shin idan suka kwanta dama fa shikenan Jamil ya fi su cin ribar haihuwar Fauz...

Shima nasa tunanin ne ya katse da maman Nabihat ta ɗaga murya tace "Papan Nabihat..."

Ɗan zabura ya yi ya kalle ta, hakan ya sa ta nuna mishi wayar shi dake kusa da shi tace "Wayar ka ce ake kira, duba kaga ko wannan mayatacciyar ce?"

Dubawa ya yi yana ɗaukar wayar a sanyaye yace "Ita ce kuwa."

Da sauri ta ɗago daga zaman ta tare da zuro hannu za ta karɓi wayar tana faɗin "Bani wayar nan, idan ta gaji ai dole ta shafawa mutane lafiya..."

Da sauri ya jaye hannun nashi yana aiko mata da wani kakkausan kallo, ita ma kallon shi ta yi sai ta koma ta zauna tana jira ta ga me zai yi, shi ma dai tasan ba ɗaga kiran ta yake yi ba, amma abun mamaki sai ta ga ya danna ok ya kuma kara wayar a kunne...

Daga wajen Fauzy shiru ta yi tana so ta tantance shin da gaske Abban nata ne ya ɗauka, sun kwashi sakanni kusan sha biyar a haka babu ko sautin numfashi, kafin ta yi ƙarfin hali murya na rawa tace _"Assalama alaikum Abba."_

Saida ya lumshe idanuwan shi saboda wani abu da ya tsarga masa lokaci ɗaya, a tausashe ya amsa da _" Wa'alaiki salam, ma fille (ƴata)."_

Wani irin kuka Fauzy ta fashe da shi, dan ko bai gaya mata ba alamu ne na ya fara saukowa daga dokin zuciyar sa, kasa furta komai ta yi sai wannan kukan kamar an mata mutuwa, shima saida ƙwalla ta fito mishi ya share, yana kallon fuskar Maman ta dake binshi da wani kallon ban gane ba? Sannan yace ma Fauzy _"Ki daina kukan haka ya isa, kin san wani abu? Ya kamata ki zo gida dan a yi shirin bikin ƙanwar ki da ke, ki zo kin ji? Ina son ganin ki a kusa damu a wannan lokacin."_

Cikin shasheƙar kuka Fauzy tace _" To Abba, in sha Allah, Abba na gode, Abba ka daina hushi dani kenan? Abba ka yafe min dan Allah, ba zan sake aikata irin wannan kuskuren ba, Abba ku yafe min dan Allah?"_

Cike da tausayin ta yace _" Kar ki damu ma fille, ba komai, ni da mahaifiyar ki mun yafe miki, ke dai ki zo kin ji, sannan ki zo har da mijin ki da yaran ki duka, kin ji ko?"_

Da ladabi ta amsa da _" To Abba, in sha Allah zamu zo, Abba ina Mama? Mama bata ɗaukar wayata har yanzu."_

Fuskar maman nasu ya kalla da tunda ya ce sun yafe mata ta miƙe tsaye ta dafe ƙugu tana kallon shi, murmushi ya yi yace _" Kar ki damu da wannan, za ta ɗauki kiran ki idan ta koma ɗakin ta."_

_"To Abba, na gode Abbana, Allah ya saka da alkairi."_ Ta faɗa a sanyaye, amsawa ya yi da _" Ameen, sai anjima."_

Ɗauke wayar ya yi daga kunne ya aje gefe, hakak ya ba Maman su Nabihat damar faɗin" Papan Nabi..."

Miƙewa ya yi tare da ɗaga mata hannu alamar ta masa shiru, idanun shi cikin nata fuska a ɗaure murya a kausashe yace" Kina ji na Hajia, Fauziyya ƴata ce ta cikina ke ma kuma haka, laifi ne ta aikata mun kuma hukunta ta daidai da abinda ta yi, shekara goma sha huɗu ba kwana goma sha huɗu bane, dan haka ƴata za ta zo nan a yi shagulgulan bikin ƙanwar ta a gaban ta, ni dai daga wajena na yafe mata duniya da lahira, kema kuma ina baki shawara da ki yafe mata kafin wacce kika ƙwallafa rai a kan ta wata rana ta saka ki jin kunya ko ba daɗi, ba baki na miki ba, amma ai duniya ta iya koyawa kowa hankali, daga ƙarshe... Idan Fauziyya da iyalin ta suka zo gidan nan wallahi aka musu ko da kallon da bai min ba, to ran uban kowa zai ɓace a gidan nan, ki rubuta ki ajiye wannan maganar tawa."

Yana gama faɗin haka ya waiwaya inda wayar sa take ya ɗauka ya sake kallonta yace" Ki bar abincin ki, na ci a waje."

Daga haka ya fice ya bar mata falon, sororo ya bar ta kamar wata gawa, ba yadda za ta yi ko ta iya da ya wuce fita daga ɗakin ita ma tana ta tunanin wannan lamari, amma daga bisani sai ta yarda da shawarar da sheɗan ya mata kan ta saki fuskar ita ma ta yarda Fauzy ɗin ta zo ko dan ta ga yadda za'a sha bidiri a bikin na Nabihat abinda ita bata samu ba a nata bikin, to ina ma ta samu wannan gatan?


*AA MENSION*


Da wannan yanayin ya shiga gida yana ƙoƙarin danne damuwar sa da kan sa da yake jin ya fara masa ciwo, yau ma kamar jiya yana shiga ƙamshin turarukan wuta ne suka tarbe shi, kafin ya hange ta tana shirin shiga ɗakin ta riƙe da kaskon turaren za ta mayar da shi can, tana ganin shi ta aje kaskon ta taho a nutse... Inda a kowane takon ta yake ƙare mata kallo daga ƙasan ta har sama, rigar less ce yanzu ma a jikin ta kalar pink ɗinkin rigar ya karɓe ta sosai, sai mayafin ta babba da take ta fama da shi har lokacin ta ƙi ta aje.

Jan lallen da ya ƙara fito da hasken ta, kwalliyar da ke fuskar ta irin mai sauƙin nan, dan bakin ta ma ba jan baki bane aka shafa mata da zai fito da kalar shi har a gane, ƙwarai ta masa kyau ba kaɗan ba, ya kuma shagala da kallon ta har ta ƙaraso ta tsaya kusa da shi kanta sadde a ƙasa murya da tausasawa tace "Sannu da zuwa oga."

Jikin sanyin jiki ya saka duka hannayen shi biyu ya jawo nata hannayen ta a kasalance bai ce mata uffan ba, sai kawai wata kyakyawar rumguma da ya bata a cikin jikin shi da ta saka ta yin tsammm! Sai kuma ta ɗan dafa bayan shi a hankali tana noƙe kan ta tace "Kana lafiya?"

Idanun shi a rufe ya matse ta sosai yana jin wata nutsuwa na saukar masa da kuma wani abu mai kama da kuka kuka na taso masa daga ƙasan zuciyar sa, saboda kalaman kawun sa ne ke ta zuwa masa a kai har yanzu, ya sake ta ya aura! Ya fi shi son ta! Ya san bai taɓa ta ba har yanzu! Da aure yak...

Da ƙarfi ya ja numfashi ya sake rufe idanuwan shi gam gam ya fizgi amsa da ƙyar ya bata da cewa "Umm..ina lafiya."

Shiru suka sake yi a haka kowa da abinda zuciyar sa ke raya masa da kuma kalar bugawar da take, sun jima a haka kafin ya sake ɓamɓaro wasu kalaman cikin raɗa yace "Muje ki rakani in yi wanka, kwance nake so nayi my lady."

A hankali ta ɗago kanta ta kalle shi tace "Ba za ka ci abinci ba?"

A nutse ya girgiza mata kai tare da cewa "Um um."

Kafin ta ce wani abu ya ja ta zuwa ɗakin shi, tsaruwar ɗakin ta sa saida ta waigawa ta sake juyawa tana kallon ɗakin, dan gaskiya tsarin shi ya birge ta sosai, inda take tunanin drower ce ta ga ya buɗe, ta zuba masa idanu da son ganin kayan da zai ɗauko, amma sai ta ga ya shige ciki ya kuma rufo ƙofar, mamakin hakan ya sa ta sakin haɓa tana kallo har bata ankara ba ya sake fitowa sanye da singlet da lallausan wando dogo sai towel a saman kafaɗar shi.

Yana kallon fuskar ta ya ga da sauri ta kawar da kai kamar marar gaskiya saboda saida gaban ta ya faɗi da ta ga damtsen shi, har ya shige ban ɗaki bayan ya sakar mata murmushi bata sake kallon shi ba, dake shi ya nemi da ta shigo, sai ta nemi wata irin sofa ta zauna a kai tana ta ci gaba da kalle kalle a ɗakin.

Minti ashirin da biyar ta kwashe zaune anan kafin ya fito ɗaure da rigar wanka, cikin drower nan ya sake shigewa bayan wani lokaci ƙamshin shi ya fara sanar da ita zai fito sannan ya fito sanye da kayan bacci. Hannun ta ya kama yana faɗin "Muje ke ma na rakaki ki yi wanka ki canza kaya, sai mu kwana a ɗakin ki ko?"

Ƙura masa idanu tayi, amma tuni ya ja ta suka fita suka kuma kama hanyar ɗakin nata, da gaske yake? Ta shiga uku? Kar fa ya mata irin na jiya? Wallahi tsoron sa take ji ita kam, ya za ta yi ne? Suna kusan kai wa ɗakin ta ɗan cije tace" Ammm... AA, aiki fa nake, ina so na kammala da kicin ne sai na zo nayi wankan, ka je ka kwanta kawai zan shigo yanzu."

Zuba mata idanu ya yi cike da birge shi da take yi a tausashe yace" AA, ni ne AA ko?"

Ɗan turo baki ta yi da fatan su yi faɗan da zai daki garu ya koma ɗakin shi ya bar ta a nata ita ma tace" E mana, kai ma ba kai bane ka ke kirana da sunan Kakana."

Kamar zai yi murmushi ya tsare bakin ta da idanu yace" Shine ke ma sai kike haɗa nawa sunan da na ɗan Anza ko?"

Sake turo bakin ta yi tana kawar da kai tace" To ai dai ni A... A kawai na faɗa, kai kuma fa? Turaki fa kake cewa, bayan sunan matsirinmu zuwa duniya ne."

Sakin hannun ta ya yi ya rumgume nashi hannayen yana murmushi yace" Kin san wani abu? Turaki ya iya dasa shuka, ke...da kuma Safwan, ina son kallon fuskar ku."

Da yanayin jin rigima ta kalle shi tace" Ka sake faɗa kan ka tsaye ko AA?"

Sai kawai ta nemi raɓa shi ta wuce tana faɗin" Ƙwalelen ka to."

Jawota ya yi da ƙarfin da ya sakata kawo masa karo, kallon fuskar shi ta yi shi ma kuma yana kallon fuskar ta ya dinga zura hannayen shi cikin gyalen ta yace" Idan ma ni an min ƙwalelen, ai ba'a isa a wa shukar da zan yi ba yau, dan na tabbata bugun farko jikan Aliyu Anza zai ɗauko kamannin ki ne sak."

Ɗan zaro idanu ta yi sai kuma kunya ta saka ta sadda kai tana girgizawa, hannayen shi da ya ɗora saman faffaɗa kuma kakkauran ɗuwawun ta yasa ta zazzaro idanu gaba ɗaya, lokaci ɗaya kuma ta liƙe su ta ja wani numfashi da ƙarfi kamar mai shirin fitar rai duk tsigar jikin ta a tashe.

Shi kuma ci gaba ya yi da matsa su yana shafawa ya haɗa goshin shi da nata yana faɗin "Y. Turaki kema acucin kike yi ma waɗannan abubuwan ne? Kinsan da halittar nan tana birgeni? Yau dai za ki barni na kwana saman..."

Kuka irin na bilhaƙƙin nan ta fashe da shi tana son ƙwatar jikin ta, sororo ya yi yana kallon ta yace "Y. Turaki wai lafiyar ki ƙalau kuwa? Ko dai aljanun kema gare ki da ba sa son aure? Me ye to?"

Tutturo baki ta yi tana faɗin "Dan Allah ni dai ka daina min wannan abubuwan, ka sake ni ka ji A...."

Riƙo leɓenta na ƙasa ya yi da yatsu biyu ya matse sosai matsar da ta saka ƙwalla gangaro mata na gaske ta rintse idanun ta tace "Shhhhhhhh, zafiiiiii."

A kausashe ya dube ta yace "Kar ki sake faɗin wai in sake ki? Ke halaliyata ce Yusrah, zan kuma iya yin komai akan ki, ba zan taɓa sakin ki wasu kurayen su cabke ba, jamais (ba zai yiwu ba)."

Saida ya saki leɓen nata ya ga hawayen da take zubar wa sannan ya jawota ya ƙara rumgumewa yace" Sorry my lady, muje ki yi wankan..."

Yana faɗa ya ci gaba da jan ta har zuwa ɗakin ta da shima saida ya kalli yadda aka ƙawata ɗakin, tsaye ya yi ya tura ta yace" Je ki fito?"

Tana shasheƙa ta kama hanya ta shige ban ɗakin tunda ta san tana da towel da rigunan wanka kala kala a ciki, kafin ta fito ya fita zuwa wajen fridge, cake da ya gani ya yanko musu a plate da madara mai sanyi ya dawo ɗakin.

Ita ma saida ta ɗauki lokacin ta sosai kafin ta fito tana ta ƙumbiya ƙumbiya ta saka doguwar rigar bacci mai taushi da suturta jiki, da ƙyar ta iya fesa turare dan duk wani motsin ta kallon ta yake yi yana sako mata kalaman kunya, daga bisani haka ya zaunar da ita ya dinga bata cake ɗin a baki da masarar saida ta ji cikin ta kamar zai fashe dan dama ta ci abinci, ko da suka gama suka sake kuskure bakunan su sannan ya ja ta kan gado wai su yi bacci bayan ya kashe musu wuta.

Ita ba ta yi baccin ba saboda fargaban abinda zai iya samun ta ko dan rumgumar da ya mata, shi ma kuma bai yi baccin ba saboda gaba ɗaya hankalin sa yana wajen Aba, kawai ƙarfin hali yake yana mata dariyar nan da hira dan kar ta fara ganin damuwar sa ko kwana uku ba ta yi a gidan shi ba. Bacci ya fara ɗaukar ta ya lalubo wayar sa da ya fito da ita ya kira wayar Anna, sama sama dai haka take jin kamar yana magana yana tambayar ya jikin Aba? Amma kuma lokacin ta sakankance sai bacci ya yi awon gaba da ita, shi ma da Anna ta tabbatar masa ba fa komai wallahi ya ci abinci ma ya jima da kwantawa ya ce anjima ta tashe shi zai yi sallah, sai ya ɗan samu nutsuwa kaɗan har bacci ya ɗauke shi yana manne da Yusrah a jikin shi.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
30/06/2024, 23:13 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login