Showing 15001 words to 18000 words out of 397328 words

Chapter 6 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

69996

fatar baki.

Duk wannan gaisuwa ba wacce ya amsa a ciki, sai ma ƙarasawa da ya yi kusa da kujerar da Anna ke zaune shima ya zauna a mugun nutse yana ɗora Islam a cinyar sa... Abrar da dole take jira sai ya kalle ta kafin za ta gaishe shi, sakamakon gargaɗin da Mahaifiyar ta tayi mata, sai dai ta ga hakan ba za ta faru ba, domin kuwa kusurwar da take ma bai kalla ba bare ta saka ran ya san da zaman ta a wurin.

Ba ita ba, mahaifiyar ta kanta taga bai kalli inda take ba, gashi kuma bata neman abinda zai yi sanadiyar kwantar da ita asibiti, ba wai ya kai ga jikin ta ba, ba ma zai kai ɗin ba dan baya rigima ko ta kallon juna ce da mace, amma akwai furucin da zai furta mata da za ta ji ina ma bata zo duniyar nan ba, dan magana kawai AA zai faɗa maka a tausashe amma ka rufe kan ka a ɗaki ka sha kuka. Wannan dalilin ya sa dole ta basar da umarnin mahaifiyar ta Tidin tana mai tsare dukkan gaɓɓan shi da kallo tace "Ina kwana Yaya AA?"

Wani kallon sakanni ya mata, gashi dai ya kalle ta, amma sai taji ta tsargi kan ta ba tare da sanin ainahin dalili ba kuma. Manal da farin cikin ganin alert yake nuƙurƙusarta ce cikin raɗatake faɗawa Nawal cewa "U see my half, na gaya miki ai Dad ya ce albashin mu zai ƙaru tunda zamu koma makaranta, kin gani ko? Over 10% ya ƙara mana."

Rumgume juna sukayi suna murna wanda hakan ya faru sarai a idanun shi da kuma kunnuwan shi, hatta Tidin murmushi ne a fuskar ta saboda ita ma nata albashin wannan watan ya ɗan ƙaru, ga kuma albashin aikin da take yi na gumin ta, shi ya sa ba ta ji baƙin ciki akan na kowa ba, duk da tasan na Asalama ya dame nasu sau ninkin ba ninkin mai ninki ma, amma dai ba ta damu ba. Manal da ta ga Anna ta ɗan duba wayar ta ne ta dube ta sosai tace "Anna, ke ma naki ya shigo?"

Murmushi Anna tayi wacce hankalinta ke kan AA tana ta nazartar shi da son gano yau waɗanne kala ne a kan shi dan tasan ta yadda zata tarbe shi ba tare da an ji kansu ba ta girgiza mata kai alamar a'a saboda saƙo ne daga Excellence yana neman ta ɗakin shi, duk da ba ɗaga murya take ba saboda gudun yin laifin da zai jefe ta da _Abujahal_ ɗin kallo, amma bai hana Manal ta miƙe ta nufi Anna tana faɗin "Please Anna, nuna mana mu gani mana, ke ma na san an ƙara miki fa yanzu, saboda nasan an samu gwagwaɓɓan riba sosai a masana'antun mai wannan watan."

Aswan dake zaune dai ɗauke da Islam har yanzu bai tankawa kowa ba, sai madaga bisani daya yatsina fuska ya ɗan fizgi kallon inda Goggon su take yace" Barka da safiya."

Fahimtar cewa da ita yake, ba kuma fuskar da za ta iya kasa amsawa ya sa ita ma a fizge ta amsa da" Barka, antashi lafiya?"

Anna ya kalli ba tare da ya amsa ba, ko shakka babu albashin wannan watan suke magana a kai, duk wani dake ahalin nan duk wata ana biyanshi daga asusun gwamnati har shi kan shi, kuma fa ba wai dan suna wa gwamnati aiki bane, bayan ci, sha, sutura, wuta da ruwa da duk gwamnati ta ɗauke musu, amma a haka ana biyan su duk wata kuɗin da sai babba babban ma'aikacin da takardun shi suka cancanta ne sannan zai samu wannan kuÉmɗin. *Karo* na farko kenan a rayuwar shi da ya ji yana so ma ya san wai daga ina kuɗin ke fitowa ne a cikin gwamnatin? Dad dai ya jima yana taɓa harkar siyasa, ya kuma san yana bada gudummuwa sosai saboda tun kafin ya shiga siyasar mutum ne da ya tara tarin dukiyar da ta zarta misali, to amma me ya sa shi baya biyan nasu daga asusun shi idan biyan ya zama dole? Tun fa da ya shiga makarantar soja aka buɗe mishi count ake tura masa wannan albashin, gashi ba ka rasa komai ba na rayuwa, dan haka babu abinda yake da kuɗin face siyan mai tsada ya hau ko ya saka ko ya shafa. Albashin shi kuma yana ƙara bunƙasa harkar noma da kiwon shi ne da har ya gawurta a harkar yanzu haka.

Anna ya sake duba da tausasawa yace " Anna Ina Dad?"

Da sanyayyan murmushi a fuskar ta ta bashi amsa da "Yana falon shi." Jinjina kai yayi kafin ya ɗan miƙe yana aje Islam, saida ya yi tsaye sannan ya kalli Anna yace "Anna, wai daga wane asusu ne kuɗin nan ke fita?"

Wani kallo duk suka mishi musamman ma Anna, sai kuma ta kawar da kai tana wani murmushi tace "Me ya sa ka tambaya? Kai ba'a tura maka naka bane?"

Sai da tayi maganar ma ya ɗan laluba aljihun wandon shi, jin bbu waya sai kawai yace "Tambaya ce nayi."

Sai da ta girgiza kai irin ba zaka ƙureni ɗin nan ba sannan tace "To ban sani ba dai nima."

Ta faɗa tana wucewa dan zuwa kiran Dad ɗin, bayan ta ya bi a nutse zuwa falon, Meem da Angel da suke wasa tare da Islam ƙura masa idanu sukayi, amma suna ganin sun nufi ɗakin Dad sai suka ci gaba da wasar su sun fahimci ba nan zai bar su ba kenan, Manal ce tayi murmushi ta duƙo tana shafa kan Angel tana cewa "Cute baby, idan zan tafi America da ku zan tafi, na san Bro zai sake samo wasu daga Paris idan ya tafi, za ku bi ni?"

Humed da ya miƙe tare da matar shi *Hafsata* yana faɗin "Ba zasu iya rayuwa babu shi ba."

Nawal ce tace "Shi ma kuma haka ba." Taɓe baki Abrar tayi saboda takaicin yadda ita ko kallon ta ma Aswan bai yi ba ya tafiyar shi, ita bata san me ta tsare masa ba? Ko ba ya ƙaunar zaman ta gidan ne ko me? Amma dai gaskiya tana jin haushin shareta da yake yi ƙwarai da gaske. Da sallama suka shiga falon Dad dake shirin fita ya amsa musu har da yin murmushin ganin Aswan a bayan Anna, gaishe shi yayi ya amsa da kulawa kafin suka ɗan zubawa juna idanu na sakanni, kawar da kai Dad yayi yana ƙarasa daidaita zaman hular shi da wani irin murmushin nan saboda ya gane da magana a bakin Aswan yace "Uhum! Ina jin ka?"

Ba tare da kwalo kwalo ba ya ɗan matsa gefen Anna ya zauna kan kujera a ladabce yana duban Dad ɗin yace "Dad, minti biyu dan Allah, zamu iya yin magana?"

Ba tare da Dad ɗin ya kalle shi ba yace "Akan me? Faɗi ina jin ka, ina da fitar gaggawa ne da take da buƙatar sammako."

Sai kuma ya kalli Anna yace "Ni zan fita madame, ba komai?"

Murmushi tayi tana ɗan girgiza kai tace "Ba komai mon Excellence, Allah ya tsare."

Jinjina kai yayi yace "Ok, ba ni agogona a ɗaki?"

Da girmamawa ta nufi ɗakin, sannan yayi tsaye yana fuskantar Aswan ya sake cewa "Ina jin ka?"

Saida ya sauke numfashi ya dubi Dad ɗin yace "Dad, dan Allah ka wa Chef magana, su sassauta hukuncin da suka min, Dad, ba zan iya jurar tashi da safe ba tare da zan tafi CEN ba, please."

Ƙura masa idanu Dad yayi na lokaci, sai kuma ya girgiza kai ya na sakin wani malalacin murmushi ya ɗan juyawa gefen shi yace" Aswan, ni tun jiya na nemi irin wannan alfarmar da kake nemana da ita yanzu a gaban Chef ɗin, amma bai min ba."

Ɗan haɗe fuska Aswan yayi da alamar tashin hankali yace" Dad kai ɗin ma? Amma fa kai da Chef aminai ne, zai iya yi maka komai."

Ba tare da Dad ya daina murmushin nan ba yana ɗan gyara zaman babbar rigar tsadaddiyar shaddar dake jikin shi kalar maroon sai ƙyalli take cikin tausasawa a nutse yace" Yess, ba zai iya bane da ya min, amma da tuni ka samu wata matsayar ba wannan ba."

Gyara zama Aswan yayi cikin kujerar yana ƙanƙance idanu a tausashe sosai yace" Dad, ban fahimta ba? Wace alfarma ka nema a wajen Chef?"

Saida Dad ya kalle shi sosai daidai da fitowar Anna sannan yace" Ce wa nayi ya koreka daga aikin soja kora ta har abada."

A hargitse Aswan ya miƙe tsaye ya furta" What!" Agogon da Anna ta miƙowa Dad ya miƙa mata hannu tana sagala mishi, a rikice ya ƙara matsawa kusa da su yana faɗin" Dad, ba zan iya wani aiki ba aikin soja ba, na fi son shi saboda shi ne rayuwata, Anna..."

Ya kira sunan ta yana kallon ta kamar zaiyi kuka yace" Anna ina son aikin nan, ki wa Dad magana kar ya sa baki a rabani da aikina, ni sam ba zan iya rayuwa ba tare da ina zuwa compg. ba, ba zan iya zuwa wani wurin aikin ba tare da ina jiyo muryoyin mazan da suka amsa sunan maza suna waƙe a lokacin da suke raha ko kuma suna hargagi yayin tashin hankalin su ba, Dad, ba zan iya jurar na shafe wani lokaci ba tare da ina jin sautin fitar harsashi daga bindiga ba, a taƙaice ma Dad, ni fa ina ganin kamar zan cika namiji ne kawai idan ina aikin nan."

Tunda ya fara maganar nan Dad da Anna ke kallon shi kamar baƙo, sai da ya dasa aya Dad ya sauke numfashi yana jinjina kai a nutse sosai yace" E! Na gane, kenan duk mu nan mata ne da bamu saka kakin soja ba Aswan?"

Da sauri ya girgiza kai da ladabi yana ɗan ja baya kaɗan cikin wata kasalalliyar murya yace" Ba haka nake nufi ba Dad, am so sorry."

Tana gama saka mishi agogon ya dube shi da kyau ba alamar wasa yace" Aswan, saurareni da kyau ka ji, an dakatar da kai aiki na wata biyar, ba zaka zauna min haka ba har wannan lokacin, dole ne ka kama wani aikin, zan baka zaɓi uku, kuma dole ka zaɓi ɗaya a cikin su, na farko, akwai matsayin DG na kamfanonina dake ƙasashen waje wanda duk kun ƙi zama can kai da Humed, na biyu kuma akwai matsayi na duk wata babbar kwangila da za ta fito daga gwamnati, to kai ne mai bayar da ita ga wanda ka so, sai kuma na uku shine ka zama DG na masana'antar mai na ƙasa baki ɗaya."

Anna ya kalla dake tsaye tana duban su yace" Idan ya zaɓi ɗaya a ciki ki sanar da ni, kafin magrib matsayin zai hau kan shi da izinin Allah."

Ficewa yayi ya barshi dafe da gaban goshin shi har yana ɗan taune leɓen shi na ƙasa, saida Anna ta kalle shi tace "Tom kaji, wane zan faɗa masa ka zaɓa kenan?"

Da ɗan sauri ya kalli Anna, sai fuskar ta da yanayin ta suka nuna mishi kamar tana son ƙular da shi, dan haka ya rikbceo hannayen ta biyu a cikin nashi yana kallon fuskar ta yace "Anna, idan ba aikin soja ba bana son kowane aiki, son da nake masa ne ma ya sa na kasa yarda wata mace ta shiga rayuwata, saboda idan na fara haɗa aikina da mace to zan fara samun matsala, ina so ne nayi aikin soja da gaba ɗaya rayuwata, idan na tafi aikina to ya zama kune kawai zan kira na gaishe ku, amma ba nauyin macen da kana fagen daga ba za ta iya haɗa maka lissafi da sabgar cefanai, lalle, kitso, fita unguwa, uwa uba kuma ƙorafi akan rashin bata lokaci, wannan ya sa Anna har yanzu na kasa cika miki burin ki akan aure."

Sakin hannayen ta ya yi yana rusuna kallon shi daga gare ta yace" Zan samawa kaina wani aikin Anna, ba sai ya sama min da kan shi ba, sannan, ki gaya masa ya daina roƙon Chef akan ya kore ni a aikin nan, please."

Juyawa ya yi ya fita da sauri zuciyar shi na tafasa sosai yana jin kamar ya naushi wani, magunan shi na hango fitar shi kuma ya nufi ƙofar fita suka bi bayan shi a sukwane, haka ya bar gidan ya koma na shi ya shiga tunanin abubuwa da dama, daga bisani maganar motar asibitin nan ce ta sake dawo masa a lisafi da Col. Garba y yi, wayar da ya bari nan ya ɗauka ya kira ɗaya daga cikin jami'an da sukayi gadi a wannan ranar wanda shi ya saka su, nan jami'in ya tabbatar mishi lallai motar ta wuce amma ta asibitin mahaifin sa ce, sai dai gaskiya su basu san me ye a ciki ba tunda ba su duba ba dan sun gan ta cikin ujila da alama ta ɗauko marar lafiya dake buƙatar agaji. Ya jima wurin nan zaune yana aiki kira da tambaya kan wasu abubuwa da suka shige masa duhu har da kan albashin da ake musu biya shi da ɗan uwan shi da mahaifiyar su da ƙanwar mahaifin su da shi sai yau ne ma ya ji yana so ya san biyan nasu na me ye ake yi? Sannan daga wane asusu ake biyan na su? Yana so ya sani? Dole ne ya sani, dan ba zai juri ganin talakawa na rayuwar ƙunci da neman abinda za su ci ido rufe, amma su da suke da shi kuma ana sake loda musu, ƙarshe sai banzatar da dukiyar suke saboda ba su suka nema da gumin su ba sannan ba su san me za su yi da ita ba?



*YUSRAH TURAKI*



Hannunsa ta kama tana masa murmushi ƙasa ƙasa ta ce" Malamin gidan mu, Autan Mama how far?"

Shima ya yi mata murmushi yana cewa" Sannu da aiki aunty Yussy, bari in kawo miki ruwa."

Duk ya yi maganar ne yana ajiye jakarta a ɗakin su sannan ya nufi tulu ya ciko mata moɗa da ruwa mai sanyi ya kawo mata ɗakin Mama a lokacin da suke gaisawa da Maman, a sanyaye ta gyara zaman ta tare da kamawa Maman ninkin da take yi na mayafanta, kallo ɗaya ta mata ta karanci yanayinta ta ce" Kin yi sallah kuwa?"

Girgiza mama kai tayi tana jiyo muryar Hannah daga ɗakin su dake faɗin" Yussy, rigar ki tayi datti ne na haɗa da ita na wanke miki?"

Yusrah kallon ƙofar ɗakin tayi cikin murya kamar mai jin bacci tace" E aunty, bari na cire."

Sai bayan ta bata amsa ne ta kula da kallon da Mama ke mata, ma'ana tana jiran amsar tambayar ta, dan haka ta sake girgiza kai tace" Yanzu zan yi Mamanmu."

Yunƙurawa tayi za ta miƙe, sai kuma Mama da ta fahimci kamar akwai damuwa a fuskar ta tace" YUSRAH lafiyarki kuwa?"

YUSRAH ta kalli Mama wannan karon ma da kula, ba su saba ɓoyewa mahaifiyar su komai ba, saboda tun suna yara ta yarda ta zama ƙawar su, dan haka ko da suna da ƙawa to bayan aminiyar su (Mahaifiyar) ne, nutse ta ce" Mama, wani abu ya ɗaure min kai, yau wata mata aka kawo, ni na dubata, tabbas tana iya haihuwa da kanta har ma tana daf da haihuwar, sai kawai aka ce ba zata iya haihuwa da kanta ba, kuma kin san mu yara ne a cikin likitocin ba lalle ne a sanar mana abinda ba lalle sai mun sani ba, treatment ɗin ta kawai ya shafe mu, shi aka sanar mana shikenan, sai kawai aka shige da ita ɗakin tiyata, shine abin ya ɗaure min kai..."

Sai kuma ta ƙarasa miƙewa tana ɗan gajeran tsaki tace" Ko da yake yanzu matan masu kuɗin nan basa son wahala, sun fi ganewa aiki fiye da su haihu da kansu."

Da ɗan mamaki Mama ta ce" A'a fa Yussy, in ba ciwo ba anya akwai wanda zai zaɓi a fasa shi a ciro masa yaro? Bayan ance fasawar nan sosai yake taɓa lafiyar mutum? da zarar an fara yiwa mace aiki aka ce ba ita ba aikin wahala in ba haka ba sai ciwon baya, wata ta haɗu da ciwon kai mai tsanani kenan har ta bar duniya, wata hawan jini, ko sutura fa aka ce mace bata isa ta ci gaba da sakawa yadda take sakawa a da ba, saboda wajen da aka yi mata aikin, nan maman su Sudais cewa ta yi shekara uku kenan da aka yi mata aikin nan amma har yanzu bata dawo daidai ba? Dan kawai gudun ciwon naƙuda ko fitowar kan ɗa abu na ɗan lokaci mutum zai siyawa kansa abinda zai zauna masa har ƙarshen rayuwarsa kuwa? Inaga tabbas akwai dalilin da ya sa aka shiga da matar, Allah dai ya bata lafiya."

Yusrah ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Hakane kuma mama, ameen ya Allah, bari in fara yin sallah sai na yi wanka yi wanka, yau muna da hadda wurin Baba."

Ɗakin nasu ta shige ta samu Hannah na ciro kayan da zata yi wanki, kuma ba nata kaɗai ba har da na Safwan da ita kan ta Yusrah, kayan ta ta fara cirewa ta ɗauki zane ta ɗaura a ƙirji ta lulluɓa kallabi sannan ta fito dan ɗiban ruwa.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login