Showing 303001 words to 306000 words out of 397328 words
ajiyar zuciya da take ta saukewa a kai a kai tace "Ann..a, ni zan...shiga n...a kwan...ta, saida safen...ku."
Nawal ce ta dube ta tace "Tun yanzu?"
Kallon Nawal ɗin Anna ta yi tace "Ki bar ta mana, sai dai baki ci komai ba fa, bana so ki kwanta da yunwa gaskiya..." Ta yi maganar tana kallon Yusrah, dan kar ta sa Anna ta ji ba daɗi sai kawai ta ɗauki wani yalolon plate marar nauyi tace "A'a Anna, zan...ɗauki wa...ni abu."
Tuffa ta ɗauka da ayaba, sai gorar yaghourt ɗaya da ƙananan robar ruwa guda shi ma sannan ta sake yi musu sai da safe ta juya ba ta sake kallon inda yake ba. Hakan sai ya taɓa shi sosai, dan shi a lokacin babbar damuwar sa ita ce ya san me ya saka ta kuka, gaba ɗaya sai ya manta da abinda ya kawo shi gidan, sai dalilin sa na biyu ya gabatar ta hanyar faɗawa Anna "Sai da safe Anna."
Da mamakin haka Anna ta dube shi duba da ba dare ya yi ba kuma Aba ma tunda ya fita masallaci ya wuce asibiti ganin uncle Hamat, shine zai ce musu saida safe suna cin abinci? A saiɓance ta amsa tunda ita dai bata ga damuwa a tare da shi ba ko alamar rashin lafiya, lokacin Manal ta kawowa uncle Sulaiman ruwan ya karɓa yana mata godiya sai kawai ya juya suka fita tare da shi.
*Lamarin zuciya* babba ne, kana sane ko baka sane ta kan zo maka da abinda baka yi tsammanin shi ba, wani zubin ma ba ya cikin tsarin ka, sau tari idan ka ga wanda so yake wahalarwa sai ka ji ko ya baka haushi ko kana takaicin hakan, alhali akwai dayawa da su kansu sukan so cire kawunan su daga wannan rayuwar, sai dai laifin daga zuciyar su ne. Kusan hakane yanzun yake faruwa da mutanen nan biyu da su a wajen su babu maganar so, kawai sun ɗauki hakan a matsayin damuwar kai baka son haka, wani lokaci kuma sai a yi ƙoƙarin basar da abun ta hanyar nuna me ye haɗina da wane ko wance? Amma minti biyu ba'ayi cikakke abun yake sake ɗarsuwa a zuciyar a ci gaba da tunanin, sai gashi Yusrah tana ta tuna abubuwan da duk suke ta faruwa tsakanin shi da Nabihat waɗanda ta gani tana lissafa su a matsayin ci mata fuska da yake kuma bata so gaskiya, bacci ya ƙauracewa idanun ta sai dai ta juya ta gyara kwanciya tana kallon Safwan dake baccin shi a nutse, ta yi tsaki, ta yi ƙyaci, ta yi ƙwafa, ta yi zunɗe ya fi bila adadin amma ba wata mafita. Haka shi ma Aswan sam ya kasa bacci saboda son sanin dalilin kukan Y. Turaki, shin shine ya mata laifin? Ko wani ne ya mata? Shi dai sam bai kawo cewa wai tafiyar Intisar ce ta saka ta zubar da hawaye ba, daga ƙarshe dai da kayan baccin jikin shi ya ɗauki makullayen gidan Aban da yake da su saboda halin rayuwa sannan ya fito ya hau ƙaton babur ɗin shi ya nufi gidan zuciyar sa cike da wasi-wasin me zai yi idan ya je? Abu ɗaya da ya sani shine sai ya gan ta ko da bacci take kuwa, dan shi mutum ne da bai iya saka damuwa a ran sa ba, yin hakan na haifar masa da rashin lafiya, shiyasa idan abun ya so tsaya masa to kawai zai fuskance ka ne ku yi sulhu kowa ya san matsayar sa.
A sauƙaƙe ya shiga ta ƙofar gidan, sai dai kamar yadda ya yi tunani gidan shiru da alama kowa ya kwanta, har ya saka makullin hannun shi zai buɗe babban falon ya shiga kawai ya ga gilmawar Anna da flask ɗin Anna, dake ƙofar ta gmas ce za ta iya ganin ko da inuwar mutum ne ita ma, sai kawai ya gaggauta kaucewa yana ayyana _"'Anna ho! Anya ma Anna tana bacci kuwa ita da Aba? Shan shayi yanzu?'_
Take kawai ya sauya shawara ta shiga falon ta ƙofa, baya baya ya dawo yana kallon saman gidan, lissafawa ya dinga yi ɗakin Goggo Tidin, ɗakin Abrar, ɗakin twins, na su kuma ke kusa da na Y. Turaki, ko da ya tabbatar da windown sai kawai ya soka makullayen a aljihu, cike da jaraba da gogewa ta aikin soja da ya samu horo ma kan shi matattakala ta bangon da duk wani da ba shi ba kallon abun kwalliya zai ma wurin har ya yi nasarar ɗanewa saman windown ɗakin Yusrah dake rufe, kusan duka windown ma a rufe suke sai dai ita nata ta saki labule ta rufe ga kuma fitila a kashe.
Saida ya tabbatar ya tsaya da kyau sannan ya ƙwanƙwasa tagar a nutse dan ya so ɗagata ta nan ya ji alamar an saka sakatar da ke jikin su ne irin mai kyan nan. Kamar daga sama ta ji an ƙwanƙwasa tagar ta ta, dama tana kwance ne tana fuskantar tagar, tashi ta yi zaune tana zazzare idanu tsoro na neman kamata, jinkirtawar da ta yi ya sa ya sake bubbugawa a hankali, cike da ƙarfin hali ta sauka daga kan gadon tana saka lallausan takalmin ta masu gashi tare da jan dogon wandon ta da ya tattare, saida ta fara ɗaukar ƴar wuƙar dake cikin set ɗin akwatin gyaran farce sannan ta matsa kusa da tagar, a tsorace sosai tana ja baya-baya ta fara yaye labulen.
Hasken jan fitilun dake ƙawata gidan irin na kwalliya ne suka taimaka suka haska mata fuskar shi, tana ganin fuskar tashi ta ƙara ja baya ta hana kanta ihu ta hanyar rufe bakin ta tana rarako idanu, da yatsa ya mata alamar ta buɗe mana, ba dan ta yarda shi bane tace "Wa ye kai? Ta ina ka biyo? Me ya kawo ka nan bawan Allah?"
Harara ya wurgo mata cikin raɗa yace "Y. Turaki buɗe min ƙofar nan?"
Galala ta yi tana duban shi ba ta kuma yi niyyar buɗe ƙofar ba, hakan ya sa shi jinjina kai alamar shikenan tare da gyara ɗanewar da ya yi a saman tagar ya ɗaga guiwar hannun shi sosai ya bangaji madubin, da sauri ta zaro idanu tare da rufe bakin ta da tafin hannu, ganin ya sake ɗaga guiwar zai mangari ƙofar ya sa ta saurin takowa ɗaya biyu zuwa na uku dan ta buɗe mishi cikin salama, sai dai kafin ta isa har ya sake bankaɗar kofar wanda hakan ya sa madubin gabcewa ya fito daga jikin ainahin ƙarfen da yake maƙale mai kama da roba ya faɗo ɗakin da ƙarfi, da ƙarfin bala'i ita ma ta ja baya har hular baccin dake kanta ta faɗi saboda dama ta yi kusa da faɗuwa saboda juye juyen da take ba bacci, kasa motsawa ta yi, tunani take daga nan tsaye, me ya kawo shi wannan lokacin? Ta ya ya hauro nan kamar wani yaro ko ƙadangare? Yanzu me za ta faɗawa mutane akan wannan ɓarnar?
Tana tsayen nan ya shigo gaba ɗayan sa yana wani batse fuska da gyara rigar shi ta baya kamar wanda ya yi wani abun arziƙi, kallon shi take yi da maɗaukakin mamakin lamarin shi, ita kam zuwa yanzu ita ma sai dai ta ba wani labarin shi gaskiya. Saida ya gama kallon Safwan dake bacci sannan ya kalle ta da niyyar tambayar me ya sa ba za ta bar shi ya kwanta ɗakin shi ba dan ya walala? Amma ganin ta a shigar da bai taɓa gani ba sai ya gagara furta abinda ya so faɗa ɗin, a nutse ya shiga ƙare mata kallo daga ƙasa har zuwa saman kumkumin ta da surar shi ta bayyana a cikin wandon baccin ta, da tunanin ina Y. Turaki ta samo wannan faɗin kumkumi ya gaggauta cira idanuwan shi saman fuskar ta dan ya mata kallon tambayar wannan fa? Daga ina yake? Shafe-shafe take yi ko?
Sai Yusrah da ta ga kallon da yake bin ta da shi tayi saurin duƙawa ta ɗauki hular kan ta da ta faɗi ta ɗora akan nata tana wani kakkare jikin ta tana sakar masa hararar ƙasa-ƙasa, ɗauke kan shi ya yi tare da taɓe baki irin me zan kalla ɗin nan? Ita ma sai ta nufi gadon ta da niyyar komawa ta zauna ta zuba mishi idanu ta ga me ya kawo shi, dan ta yi niyyar ba za ta masa magana a yanzu ba, idan kuma ta mishi to abinda ke ranta ne za ta furzo. Da kallo ya biyota yace "Magana na zo mu yi fa."
Da mamakin jin haka ta juyo tana yatsina fuska ta kalle shi, fuskar ta a haɗe kamar mai raɗa tace "Magana? A wannan lokacin? Bayan ka hauro min ɗaki?"
Sai kawai ta sake juyawa za ta ci gaba da tafiyar ta, da ƙarfi ta dakata da tafiyar ta rintse idanun ta saboda hannun ta na dama da ya riƙe irin sanyayyan riƙon nan da ya gaurayar da tafukan hannayen su a cikin na juna, wata irin harbawa ƙirjin ta ya shiga yi da ƙarfi take ta ji jikin ta na neman macewa ba tare da tasan dalilin hakan ba.
Shi kan shi bugun ƙirjin shi saida ya tsanan ta, amma haka ya daure ya yi ƙarfin halin dawowa da baya tunda ita ta ƙi ko da juyowa ya fuskance ta, fuskarta ya tsare da idanu saboda bata buɗe idanun ta ba har lokacin, ko sharrin shaiɗan ne? Ko kuma dan yana dare ne? Shi dai sai ya ga bai taɓa ganin wani irin nutsatse da sahihin salihin kyan dake kan fuskar nan ta ta ba sai yanzu, hakan ya bashi damar kallon kowace gaɓa dake fuskar ta cikin wata raunanniyar murya kamar mai son sakata bacci yace "Me ya saka ki kuka ɗazu?"
A hankali ta buɗa idanun ta sai kuwa wasu hawayen da tunda ta ji ya dawo gaban ta suka sake cika mata idanu da tunanin haka yake wa yarinyar nan ko? Idan ba ya ƙaunar ta ya sake ta mana? Ita ma ai bata aure shi dan ta zauna da shi ba, ganin wannan sabbin hawaye sai hankalin shi ya sake tashi duk ya yatsina fuska cike sa damuwa ya riƙo ɗaya hannun nata, hakan yasa duka hannayen su na cikin na juna ne, da tsantsar kulawa da tausasawa yace "Ban san me ya sa ba, amma ina so na san dalilin kukan ki? Ni ne? Ko Anna ta miki wani abu da baki so ba? Ko kuma su Nawal ne? Ki faɗa min mana?"
A hankali ta dinga mitsitsika hannayen ta dake cikin nashi har ta ƙwace hannayen ta sannan ta sa ta share hawayen ta, saida ta kalli tsakiyar idanun shi cikin muryar kuka tace" Ba abinda aka min, dan Allah ka tafi."
Raɓa shi ta yi za ta wuce kawai ya figo damtsen ta ya sake dawo da ita gaban shi wannan karan da kusanci sosai, bai kuma saki damtsen nata ba fuskar shi a ɗan haɗe da kakkausar murya yace" Hakan damuna yake, me ya sa ba zaki fahimta ba?"
Ƙoƙarin ƙwatar hannun ta tayi amma ya ƙi sakin ta, sai kawai ta kalle shi tana cije fuska dan ya riƙe ta sosai yace" Ba zan fahimta ba *Aswan*, ka sakeni mana, ka daina taɓani dan Allah."
Yau ne na farko da ya ji sunan shi daga bakin ta, kuma na farko da ya ji sunan shi bayan ya haura shekara ashirin a duniya bayan ga bakin iyayen shi da malaman shi, hakan ba ƙaramin ɗaɗashi ya yi ga ƙasa ba, amma hautsina masa lissafi da take son yi yasa ya aje maganar a gefe ya sake tsareta da idanu yace "Zan sake ki, amma da sharaɗin zaki daina ɗaga min hankalina, kin fahimta?"
Da tafasar zuci na abinda ke ranta ta kalle shi har da ɗaga murya tace "Ban fahimci komai ba, ni ce zan ce ka daina ɗaga min hankalina, sannan idan ka yi haƙuri nan da ɗan lokaci ni da ƙanina zamu fita a rayuwar ku gaba ɗaya, dan dole za ka dawo min da ƙanina ko kana so ko baka so."
Sai kuma ta duƙar da kanta ta furta "Sakeni ko na maka ihu?"
Yadda ta yi maganar alamar e ta gama magana kenan, ƙwarai bai san me ke damun shi ba, shi dai ya san ya saki hannun nata a hassale tare da juyawa da ƙarfi ya naushi bango, naushin da ya saka Yusrah jan wani numfashi ta liƙe idanu gam gabanta ya shiga wata irin dokawa, shakka babu da ita ya nausa to ta zama gawa, da kuma wani abu mai rauni ne to tuni ya lalace, amma da ta kalli bayan shi taga bai juyo ba ya dafe bangon kanshi sadde kamar mai tunani, sai kawai ta taka da niyyar kwanciyar ta ya jima bai yankata ba mana, amma sai ta sauke duban ta kan hannun nashi da ya naushi bango har ya ɓalle da jini, haka kawai ta ji tana neman shiga halin rashin jin daɗi duk da kuwa hushi take da shi wallahi.
Ƙarasawa ta yi kusan gadon ta ɗauki tissue dake cikin kwalin shi ta tsaya bayan shi ta miƙo masa tissue ɗin, sai dai bai ma san tana yi ba saboda bai ko waiwayo ba, ƙara haɗe fuska ta yi sannan ta matsa kusa da hannun, a hankali ta kamo hannun nashi ta fara laulaya masa tissue ɗin, saida ta ɗaure masa ta juya ta haye gadon ta har da jawo zani ta rufe har kan ta bata sake bi ta kan shi ba.
Ba ƙaramin gumurzo ya sha ba dan kawai ya daidaita nutsuwar shi ta yadda ba zai illata ta ba, haka kawai yake jin ba zai iya cutar da ko wani mai mahimmanci a rayuwar ta ba bare ita, shiyasa ma ya ƙyaleta ta ɗaura masa tissue ɗin nan bai ko juyo ba bare ya sake hassala, saida ta gama ya juyo sai ya ga dan rainin hankali ta yi kwanciyar ta ta bar shi a tsaye, ya ɗauki sakanni yana kallon ta kafin ya bi ta inda ya biyo a hassale yana jerawa kanshi tambayoyin _"Wai me ya sa ya damu ma? Rayuwar ta ce mana, dan ta yi kuka sai me? Ta yi ta yi mana, amma har shi ne za ta ma haka? Har tana kama sunan shi kai tsaye ba ko jin kunya a tare da ita? Shi fa? Hmmmm!"_
Da wannan yanayin ya koma gidan shi ya sakar wa kanshi ruwa, yana fitowa ya kashe acn ɗakin dan yanzu sanyin zai haɗe ya jawo masa jarfar da bai shirya mata ba, sai dai a wannan dare kam ba wanda ya yi bacci a cikin su saboda wannan baƙon yanayi da ba wanda ya san ainahin menene a cikin su.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*76*
Tun ranar za ta iya rantsewa ba ta sake saka shi a idanun ta ba, ko dan shirin da Anna ta sake duƙufa akan ta ake mata mai cin lokaci da kashin kuɗi? Amma dai tana da yaƙinin yana zuwa tunda a washe gari ma ya ɗauki Safwan ai suka koma gidan sa, ga tashik hankalin da su Anna ke ƙara mata idan ta ji ana maganar kayan ɗakin ta ko gyara, sai ta yi saƙo tana tambayar kanta _"Da gaske ni za su kai gida ɗaya tare sa shi? Bayan kuma ma kamar ya fi son fiance ɗin sa a kaina? Mutumin da nake da tabbacin zai iya murɗe min wuya a gidan nan? Aswan fa?"_
To amma ya za ta yi, irin kashedi da gargaɗi da jan kunnen da su aunty Fureira suka mata sanda duk suka koma Funtuwa, da wanda uncle Sulaiman yake mata sanda ya ƙudiri komawa karatu wai yana so ya samu takardar Bac, shi kaɗai ma ya ishe ta taja baki ta yi shiru ta haƙura ta zauna da shi, idan ajalinta ne ke kiran ta ai sai su bita da addu'a ita ma kamar yadda suke wa iyayen ta da Yayar ta.
Kwanci tashi har an yi sati biyu da ɗaurin auren su Yusrah, a cikin kwanakin nan an yi gyaran gida ne ba ji ba gani, kuma an zuba kaya a ciki an gama komai, a yanzu ranar da Anna ta ware zata tare take jira, ta saka har wasu sati biyun a sama, ta saka Yusrah a gaba sai zuba mata gyara take yi kamar ba gobe, a gaskiya kowa ya ga irin gyaran da Yusrah ke samu zai gane cewar ana yin lamari ne na ɗan gata, domin gyaran nan ba kowa zai mora ba sai ɗan gata.
Nabihat har yanzu tana gidan dan naci da rashin magayi tsayayye, da farko mahaifinta ya nuna dalilin da yasa har yanzu take can? Sai mahaifiyarta ta nuna ai ba wani abu bane kafin a ƙulla alaƙa tsakaninsu ta auren yara ma