Showing 297001 words to 300000 words out of 397328 words
kaɗai, kin ga in ba haka ba ko? Za'ace a zuba maki kowace shara a kanki ne a wuce, oya goge hawayenki ina tare da ku na san halin kowa, kowa shi ke fitar da halinsa fili a gane waye shi, kar ki damu je ki cenza ki dawo mu yi aikin tare suma na tashe su daga barcin ai, yau baban ku ma doyar zai ci tunda na bashi zaɓin me zai ci yace abinda zamu ci."
Yusrah ta sauke ajiyar zuciya ta fice tana jin wata yar salama na shiga zuciyarta tana kuma jin eh lalle zata zagine ɗin ta iya ƙwatar kanta, tunda har zasu gilla mata sharri a gaban idanuwanta ba kunya ba jin tsoron Allah tabbas zata iya kare kanta cikin hikima ba tare da sun gane komai ba.
Tana komawa wanka ta sake shiga dole ta wanke rigar nan sumul sannan ta fito ɗaure da tawul ta ƙaraso wajen bed ɗin ta ya ɗauki wayarta dake ta ruri ya kara a kunne tana faɗin" Malama ya da kira da sassafe haka?"
Maryam ta yi dariya tana faɗin" Allah ya shirye ki, ko dai yau jaruminmu a kusa da ke ya kwana?"
Yusrah ta dafe kai tana faɗin" Yaushe kika lalace?"
Maryam ta ce" Tunda kike min faɗan kiran safe bayan na san baki tare ba, ke ko kewata ba kya ji ko Yussy?"
Yusrah ta yi ƴar dariya ta zauna tana faɗin" Ina kewarki sosai ƙawata, ya gida ya su Mama?"
Maryam ta ce" Alhamdulilah, ke jiya fa kasa barci na yi, shine nake ta addu'ar safiya ta yi dan in yi kiranki mu zanta, wai kin san wani tashin hankali kuwa? Jiya fa su Hajia suka zo ita da yaya Jafar wai so suke yi a yi maganar aure wai kwana kusa suke so a yi komai a gama."
Yusrah ta faɗaɗa faraarta tana faɗin" Alhamdulilah alhamdulilah, to meye na kasa barcin bayan abin farin ciki ne? Ko kina da wani da kike so ne?"
Maryam ta yi ɗan tsai sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Yusrah, ni gaba ɗaya gani nake yi anya zai iya tsawatarwa a gidansa kuwa? Ji fa abubuwan da na gani, ni gaba ɗaya tsoro ne nake ji kar aje zama ya zame min masifa, kin ga tsoron matarsa yake ji fa, kuma ta yiwu baya haɗa soyayyarta da kowa, uwar ƴaƴansa ce fa."
Yusrah ta ɗan lumshe manyan idanuwanta a tausashe ta ce" Shine kawai damuwarki?"
Maryam ta gyaɗa kai tana faɗin" Eh, gaskiya shine babbar damuwar."
Yusrah ta yi murmushi ta ce" Kin san Allah, Tasneem ƙaddarar yaya Jafar ce kawai, irin ƙadarorin nan da baka isa ka zagaye musu ba sai sun cin maka, bayan wannan ki ɗauka cewar ƴaƴan dake tsakanin su rabo ne da babu damar ya je ko'ina sai ya fito daga tsatson mahaifiyarsu, daga wannan ki yi shagalinki hajiata ki barwa Allah zaɓi, amma yaya Jafar kam ba maganar wai soyayyar matar nan a ransa har ta hana masa sukuni, idan a da ya sota ba zan yi musu ba, amma a yanzu wallahi gaba ɗaya ta kankare duk wata darajatata a idanuwansa da zuciyarsa, ko da zai sake yin wani zama da ita saboda ƴaƴansa ne kawai, bayan wannan wallahi ba wani abu, trust me."
Maryam ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Suna nufin fa ƙarshen watan nan za'a yi zama ɗaya a kawo komai da komai da Yusrah."
Yusrah ta ce" Alhamdulilah, to ba shikenan ba ta faɗi gidan sauƙi? Yau duka duka huɗu ga watan ai Maryam, kafin nan ko menene ya tabbata, zamu yi ta faɗawa Allah in sha Allah alkairi zai riske mu kin ji? Kar ki wani damu."
Maryam ta ce" In sha Allah besty, sai na shigo, ba'a saka ranar tarewa bane?"
Yusrah ta yi jim kafin ta ce" Uhum."
Maryam ta ce" Uhum ba amsa ba malama, wallahi ki kiyayemu a kan auren nan sai in zane ki tam."
Yusrah ta yi ɗan murmushi tana faɗin" Ke dilla ni sai anjima bari in je kicin zan sauka fa."
Maryam ta ce" Na ji, duk irin yadda kike kiyaye maganar nan dole mu yi ta, zaki dawo ne ai, sai na shigo ke dai."
Daga nan suka yi sallama Yusrah ta sake shiryawa cikin riga da sket na atamfa ta yane kanta da mayafi mai ɗan faɗi sannan ta fice ta nufi ɗakin tagwaye tana faɗin" Kai wai me kuke yi a ɗakin nan ne har yanzu?"
Ayyukansu suka yi tare da Anna cikin farin ciki suka jere komai sannan suka zauna suka karya Anna kuwa ta kai na Aba da nata ɓangaren Aba, Manal kuwa ta kai na uncle Sulaimane ta dawo, Nabihat na zaune tana kaɗa ƙafa bata ci ba dan wallahi ba zata ci doyar nan da Yusrah ta sakawa mutanen gidan ra'ayin cinta ba, gaba ɗayama muryoyin yaran Intisar ke ƙara ɓata mata rai, sai kawai ta yi zamanta a nan tana waya da mamanta.
Kusan ƙarfe goma sha biyu yaya Mubarak ya ajiye Intisar ya gaishe da Anna ya sanar mata maganar tafiyar sannan ya wuce ya barsu suka shiga shirye shiryen tafiyar ta su Aunty Intisar ta hanyar yi mata dake daken su kayan yaji, su miyar yauƙi, kai harda su daddawa Manal kuwa na tsefe mata kai saboda gobe kitso zasu je da yaran idan Allah ya nufa, a ranar dai sai da yamma Akhi ya shigo tare da uncle Sulaimane da Safwan yana sanar masa daga makarantar da zai saka Safwan yake sun tabbatar masa yana iya zuwa ya ci gaba da ɗaukan lesson in dai yana da kwonya zai kamo su ne.
A lokacin su Yusrah suna can ɗayan falon, gaishe gaishhe kawai suka yi, sai Nabihat da ta ringa jera abin sha sannan ta ɗan zauna sai jan Aswan da fira take yi har aunty Intisar ta zunguri Yusrah ta nuna mata, Yusrah ta zuba musu ido har ya ɗago suka yi ido huɗu, da sauri ƴaƴan Anna suka sadda kawunnansu ita kuwa ta samu kanta da sakar masa harara ta ɗauke kanta.
Ido ya ɗan zarro bayan ya zuba mata ido yace" Ka san me aboki?"
Uncle Sulaiman ya ce " sai ka faɗa aboki."
AA ya girgiza kai ya ce" yarinyar can fitsararriya ce sosai."
Uncle Sulaiman ya juya ya kalli matan wajen kaf sannan ya kalle shi ya ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
24/06/2024, 23:55 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕??❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*74*
Uncle Sulaimane ya juya ya kalli matan gaba ɗayan su ya juyo ya ce" Wace a ciki fa?"
AA ya ɗan taɓe yana ɗan tallabe haɓa yace" Wace kuwa ban da Y Turaki? Hararena take yi na rantse maka."
Uncle Sulaiman ya yi ƴar dariya ya ce" Ayya! Kun fi kusa ai, na zata mai tsada ka ke nufin bata da kunya da in ce kar fa mu yi haka da kai."
AA ya zuba masa ido, ya sake juyawa ya ƙarewa ƴan matan kaf kallo ya sake juyowa ƙasa ƙasa ya ce" Amma wace mai tsada da ta kai Y. Turaki a can? Ai a can da nan kaf babu wacce ta kaita tsada gaskiyar magana kenan fa Freind."
Nabihat ta ɗago ta sake zuba masa ido, a maganarsa babu abinda bata ji ba, sai ta ga hakan wani salon cin fuska ne da wulaƙancin, shi da kansa uncle Sulaiman sai ya yi murmushi kawai ya ɗauko wata maganar dan ya riga ya gane AA ba tsoron uban wani zai ji ba abinda ke zuciyarsa zai faɗa kai tsaye idan ta kama dan haka gwara shi ya yi shiru kar yarinyar nan da ta zo ta saka su a gaba ta ga ana ana wulaƙantata, kiraye kirayen magriba ya sa kowa ya tashi ya kama gabansa dan zuwa jin sallah, bayan sun dawo ya wuce wajen Aba suka tattauna kafin ya bar gidan, inda aunty Intisar ma ta gaggauta haɗa abubuwan da zata tafi da su Yaya Mubarak na zuwa suka wuce da bankwanar sai gobe idan sun haɗu dan tafiyar su.
*WASHE GARI*
Duk da tana cikin jimamin tafiyar ta su aunty Intisar wacce take jin kamar ta dakatar da su daga tafiyar, amma kuma a haka ta riga kowa shiryawa dan tafiya raka su aeroport, su Manal ma da take ganin kamar ba shiri suke da gaggawa ba haka take ta azalzalar su, Abrar na mata dariya suna shiryawa har suka gama. Gaba ɗayan su suka sauko ƙasa kai tsaye kuma falon Anna suka nufa, fitowar ta kenan ita ma daga falo cikin shirin haɗaɗɗiyar atamfa, da walwala a fuskar ta tace "Har kun fito kuma?"
Da ladabi suka amsa ta da e, dan haka ta dubi Nawal tace "Nawal, kinga to ko ki karɓi makullin mota a hannun Shatima sai ki tuƙa su ku tafi, dan dreban har yanzu bai dawo daga ɗaukar kifin da ya tafi ba, kuma ku sai kun biya ta gidan ta sannan za ku wuce, to kawai ku tafi ɗin ni sai na jira shi."
Da murna sosai Nawal da Manal suka tafa suna faɗin" Yawwa Anna, hakan ma ya fi."
Wani kallon tuhuma ta jefe su da shi tace" Uhum? Ina fata dai ba wani abun kuke shiryawa ba?"
Girgiza kai Manal ta yi tace" Wallahi ba komai Anna, kawai dai mun fi so muna tuƙi ne da kan mu."
Taɓe baki ta yi tace" Tom, idan ma da wani abun dai kar ku manta har da matar Akhin ku a tafiyar, dan haka sai ku kiyaye."
Kallon Anna Yusrah ta yi, sai kuma ta sadda kai cike da jin kunyar da ta kasa gane wai su su Anna ba sa jin nauyin kiran ta matar shi? Hmmmm! Aswan ko? Aswan dai ko? Wallahi zai zo ya same ta gidan nan, ba dai ita ta sake kama shi jiya yana kallon yarinyar nan shi da uncle Sulaiman ba sannan suna ƙusƙus ko? Ita fa magana ta gaskiya ta tsani Nabihat ɗin nan wallahi, ba ta san dalili ba amma ba ta ƙaunar ta sam, kawai suna faɗan su ita da shi mai daɗi na hararen juna, shikenan yarinyar nan ta wani zo tana karairaiya da turo masa ƙirji wai tana kawo abin ci da sha, kai Astagfirullah! Dan haka yau a ƙufule ta wuni wallahi, kuma shi take jira su haɗu ta amayar masa ba fa ta son haka da yake mata, sam ba ta so kawai ya daina a zauna lafiya.
Har sun juya za su tafi Anna tace da su "Ina Nabihat kuma?"
Nawal ce ta taɓe baki ta bata amsa da "Ohon mata Anna! Kinsan ba fita take so tare da mutane ba, idan ma an fita ba wata tsiya da take tsinana mana."
Da sigar gargaɗi Anna tace "Nawaaaalll."
Da gudu ta juya ta fice tana faɗin "Sorry Anna, sai kun iso, love u."
Da murmushi kawai ta bisu da kallo har suka fita sannan ta zauna kan kujera dan ci gaba da jiran dreba. Suna fita daga gidan sukayi hannun hagun su, hakan ya sa basu haɗe da motar AA da shi kuma ya hangi ta su motar ba kuma wallahi sarai ya ga Nawal ce ke tuƙi sannan ya hangi Y. Turaki a baya ta hakimce saboda rashin tsoron Allah, shi kam lamarin yarinyar na neman hargitsa masa lissafi, kai sai ta yi ta abubuwa kawai gasu nan dai, yanzu ita ko kunya bata ji Nawal ta tuƙa ta a mota? Ta ya ma za'a bar ƴan mata haka su shiga gari wai ba wani babba a tare da su? Shi kam bai san me su Anna suka ɗauke shi ba, sai su yi ta bata izinin fita, idan ya mata magana ta ce ai Anna ta ce ta tafi, to kenan Anna ke bada umarni ko?
Da wannan saƙe-saƙen ya shiga har falon Anna, dan ko da ya ga bata babban falo ya wuce can kai tsaye, sallamar da ya yi ta amsa tana ɗan gimtse fuskar ta dan bata son ƙorafe ƙorafen nan da yake yawan kawo mata kan Y. Turaki tayi kaza, me ya sa aka bari ta yi kaza? Me ya sa kaza kaza? Gaisawa sukayi yana ɗorawa da "Anna Aba bai dawo ba? Ban ga motocin su ba?"
Da sakin fuska ta bashi amsa da "Bai dawo ba, da yana nan ma ai da shi ya tuƙani yau, gani na ƙare da jiran dreba."
Da mamaki ya ɗan waro idanu yace "Anna Aban?"
Da kyau ta kalle shi tace "Aban mana, a ganin ka ya manta yadda ake tuƙi ne yanzu?"
Ƙara zuba mata idanu ya yi, sai kawai ya yi murmushi yana hasaso ta yadda Elhaj Aliyu Anza zai yi tuƙin mota, shi dai rabon da ya ga haka ai an ɗauki shekaru, to amma tunda Annar su ce, zai iya yi tsaf ko da ya manta ɗin ma, sai kawai ya sassauta murya da ladabi sosai yace "Anna, to ni na kai ki inda za ki je mana."
Kallon shi tayi tace "Fansar sa ka yi wai?"
Girgiza kai ya yi alamar a'a tare da zuba tagumi yana ayyana _"Kawai mu rabu lafiya, amma wannan abun da Anna ke yi rigima ce yau fal tare da ita, idan ma nace zan ja rigimar uwani za ta ci."_
Miƙewa ta yi tana faɗin" To, bari na ɗauko jakata da mayafi."
Gyara zama ya yi dan jiran fitowar ta, ba laifi kuma ta ɗan ɗauki mintuna kafin ta fito, tana gaba yana binta a baya suka fito ta babban falon, nan sukayi kiciɓis da Nabihat ta fito tana soka wayar ta da makullin mota a jaka ita ma za ta tafi rakiyar aunty Intisar ɗin, dan ma tana ita ce ba dan haka ba babu inda za ta je wallahi da yammar nan.
Tana ganin shi bata wani damu da ganin Anna ba ta shiga sakar masa murmushi da rawar kai tace "Yaya AA barka da yammaci?"
Waina idanu ya yi tare da yin kamar bai ganta ba bare ya ji ta, idan har ba za ta girmama masa iyaye ba to tabbas shi da ita zasu saka ƙafar wando ɗaya, ƙanwar uban sa ma ya shareta kan lamarin Babar shi bare wata banzar bazara. Kamar ta san me yake tunani ya ji muryar ta tana cewa Anna "Anna har kun fito? Ai na ɗauka tare da su Manal kuka tafi?"
Da sakin fuska Anna duk da kuwa ta jima da fita a sabgar ta Nabihat, kawai tana dai zaune da ita ne dan ba za ta kore ta ba, amma tana dai kallon ta ne taga yaushe za ta koma gidan su, da ƴar fara'a ta amsa mata da" Ba tare muka tafi ba Nabihat, dreba na tsaya jira kuma bai zo ba, amma shi zai kaini."
Ta faɗa tana nuna AA da ya ɗan yi gaba, da wani irin zumuɗi Nabihat tace" Lah! To Anna ko na biyo ku nima, wallahi dama tuƙin ne nake ta jinjinawa a raina, na gaji sosai."
Ba alamar damuwa Anna tace" Ba komai, muje."
Kamar za ta kifa ƙasa dan sauri take bin Anna a baya tana murnar yau za ta shiga mota ɗaya da shi, kai ina ma Anna za ta zauna baya ita kuma a gaba? Ta sani ne dole sai an dinga kallon su har ma wasu su shaida wannan fita ta su, duba da motocin shi sanannu ne da yana ɗaya daga cikin tsirarun mutanen da ana ganin motocin ake lissafa shi a ciki, to aka gane shine aka kuma gan ta a kusa da shi ai lafiyar ta ƙalau wallahi, iya haka ma tasan za ta iya cin alfarmar AA a garin nan.
Suna fitowa kuma ashe dreba shi ma ya dawo har ma an shigar da kifin ta ƙofar madafar dake farfajiya yana shirin shigowa ya sanar da Anna ya dawo sai kuma ga su sun fito, da girmamawa ya musu barka da fitowa, amsawa AA ya yi tare da yin gaba sai Anna da ta dube shi tace "Ka dawo ashe?"
Cikin rusunawa yace "Na dawo Hajia, zan shiga ma na sanar da ku ne ai, zamu iya tafiya yanzun?"
Kallon AA ta yi dake amsa waya nesa da su kaɗan tace "E to...ko ku..."
Sai kuma ta canza maganar ta hanyar faɗin "E, ina zuwa."
Matsawa ta yi kusan AA ɗin da yana ganin haka ya yanke kiran da niyyar buɗe mata mazaunin kusa da shi, a tausashe tace masa "Ka bar shi ma jikan Anza, tunda ga dreban ya dawo, ka tafi da Nabihat kawai sai ka sauke ta gidan Intisar ɗin, kaga kaima ka mata bankwana daga nan, ni kuma sai na biya na ɗauki Safwan wajen Fureira, kai tsaye sai na wuce can, zuwa lokacin dai nasan sun ƙarasa aeroport ɗin, k ji?"
Nabihat ya juyo ya kalla wacce ke tsaye nesa da su sai faman murmushi take yi kamar bata da lafiyar kai, sai kuma ya kalli Anna yace" Amma Anna da waccen