Showing 138001 words to 141000 words out of 397328 words
ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*37*
Dare ya tsala sosai, a dole ya je gidansa ya kwanta da nufin garin Allah na wayewa zai ɗauki hanyar garin su Mani dreba, gashi kuma yana ta kiran lambar rikitacciyar nurse ɗin nan ba ya shiga, wa ma ya sani yanzu wane jejin ta faɗa? Tabbas yana son tattaunawa da ita, amma kuma yana yawan tuna yadda tattaunawar tasu za ta kasance, dan abu ne mai matuƙar wahala hira tsakanin mai hankali da marar shi, musamman ma muhimmiyar hira.
*Washe gari* tunda sanyin safiya kiran Aba ya same shi kan ya shirya zai biyo ya ɗauke shi su je wajen gari gidan wani tsohon aminin Aban da matarsa ta rasu, a dole ya dakatar da nufinsa na yin sammako zuwa wajen Mani dreba, balle irin yadda Aba ke ɗan sakama duk wani motsinsa ido a yanzu, ba zai so ya gane baya kusa ba a samu wata matsalar.
Sun samu sutura, sannan sun jima wajen makokin kafin su juyo gida, suna zuwa gidan kuma a dole ya tsaya domin lokacin cin abincin rana ya wuce tuni, suka ci abinci da Aba suka shiga fira, Aban na sake yi masa tambayoyi da sake hankalta da yanayinsa dan baya wasa ko kaɗan da lamarin ƴaƴansa balle kuma Aswan da ya fi kowa nuna alamun rashin ji, gashi soja, yakan yi taka tsantsan da lamarinsa sosai, ga aukin yi masa nasiha da wa'azi, domin ko a yanzun da suke falon Aba zaune, Anna na daga cen gefe ta gama waya da Intisar tana cike da mamakin Intisar ɗin Aba ya katse mata yunƙuri da ta yi da nufin yin magana a lokacin da ya ce" Son, a duniya mutum ya guji zina, ka ga ita mugun saɓo ce da farata ke da daɗi da sauƙi, amma barinta kuma ke da wahala sosai."
A nutse Aswan ya ce" Na sani Aba."
Shiru ya biyo bayan maganar sakamakon faɗin ya sani da ya yi, Ana ta dubi Aba da sauri, shi kuwa ya tsatsare Aswan da ido ya ce" Ka san me jikan Anza?"
Aswan ya ɗago ya kalli Aba sanadiyar jin muryar ta Aba kamar ta ƙara gaggawa a kan yadda yake da, idan kuwa ka ji muryarsa a haka ko yana cikin yanayin firgici ko yana daf da ɓallewa da faɗa, sai yanzu ya maimaita abinda aka yi yanzu yanzu a ƙwaƙwalwarsa, sai ya samu kansa da yin murmushi ya kai dubansa kan Ana, ai kam ya ga ta yi tsuru baiwar Allah ita ma amsar take jira, sai ya samu kansa da sake yin murmushin a ransa ya ayya _"Ayya, to hausar ta Aba da amsar tawa ce basu zo daidai ba ina ga, amma ina zan san daɗin abin ni da ban taɓa ɗanɗanawa ba? Uhum."_
A bayyane kuwa a tausashe ya ce" Ina nufin, na san cewa ita zina farata ke da sauƙi, dainata kuma wahala gare shi, kuma zina ai tana cinye duk wani aikin alkhairi dake iya raɓar bawa, duk dukiyar mutum kuwa tsaf zai wayi gari ba ko sisi dan bata da albarka ita."
Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, Anna ta girgiza kai, Aba kuwa ya ɗora da faɗin" Hakane son, verry good, ashe duk ka san irin munanan ayyukanta? Allah dai ya tsare dukkan ƴaƴan musulmi da kusantarta ya nuna min na maka aure lafiya lau."
Ƙasa ƙasa ya amsa da amen amen, Anna kuwa ta ce" Uhum! Intisar an dage, wata yarinya take so a bata ka ga yanzu ta kashe kiran tace in dai abin ya ja dunga in sanar maka zata so ka saka baki da yayansu a bata riƙon yarinyar."
"Sai kace ƙwallon mangwaro? Iyayenta basa sonta ne zasu ɗauki ƴa sukutum su bayar?" AA ya faɗa yana kallon Anna.
Anna ta yi murmushi tana kallonsa ta ce" Yarinyar marainiya ce Aswan, kuma ina ga dai tana da buƙatar taimakon ne."
Aba ya ce" Ayya, to ina danginta? Me yake faruwa ne?"
Anna ta ce" Nima ban gama gane abinda take nufi ba, yarinyar dai mahaifiyarta da mahaifinta sun rasu ne, kuma tana so ta amsheta a wajen danginta ne ina ga ko bata samun kulawar da ya dace a wajen dangin nata ne? Ta ce dai yau zasu zauna da dangin nata in ji Mubarack, wai idan an hana mata tana so ku shiga maganar kai da yayansu."
"To amma, ita ya ya zata iya raino bayan bata da lafiyar ita ma? Annarsu ko dai Intisar na da buƙatar ƴaƴanta ne ta yi shiru bata sanar ba? Ba fa na so a tauye yaro fa, idan har tana da buƙatar ƴaƴanta su dawo inda take ya dace a sanar min ni kuwa zan je da kaina in dawo da ƴaƴanta." Aba ya faɗa da ƙara bada yanayin tabbacin gaskiyarsa kenan.
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Abansu, kaima ka san dole akwai kewa, sai dai tana da haƙuri sosai dan bata nunawa ko kaɗan, kuma ka ga mijinta yana yin bakin ƙoƙarinsa, yanzu haka ina ga sun kusa samun tafiya can ɗin fa, kuma yarinyar da take so a bata ɗin ai ba ƙarama bace budurwa ce."
Aswan ya kalli Anna, ya kalli Aba, sai kuma ya yi shiru bai ce komai ba, ƙarshe ma duba yanayin lokaci ya saka shi miƙewa yana gyara rigar jikinsa ta lallausan yadi ya ce" Aba bari in je, sai na shigo in anjima in sha Allah."
Aba ya ɗago yana kallonsa da kyau ya ce" Son, yanzu ina zaka je? Kawai ka ƙi faɗa min aikin da kake so ko? Sai dai ka yi barci ka motsa jiki ko?"
Aswan ya yi murmushi yana sake rage tsayinsa ya ce" Zan faɗa Aba, bari in je in ba su Meem abinci, Meem ɗin ke mura."
Aba ya yi masa addu'a, Annama ta raka shi da addu'a ya juya ya fice a ɗakin yana murmushi ya baro su suna ci gaba da firar budurwar ƴar da Intisar ke so a bata riƙo, ita ma ko yaushe aka haifeta? Ƴaƴan yanzu sai son girman tsiya.
Yana saukowa falo Abrar ta ɗauko abin wanke hannu zata kaiwa mahaifiyarta da ta sha mango ta ɗan ɓata hannunta kaɗan, sai da ta ajiye abin dan girmamawa ta ɗan rage tsayinta ta gaishe shi.
Har ya saka ƙafa ɗaya zai yi gaba sai ya dakata, ya juyo inda take ya yi ɗan murmushi sannan ya amsa gaisuwarta cikakkiya kafin ya kalli Goggon sa ya aika mata nata gaisuwar kamar haka "Hi." Ya juya ya fice a falon.
Da matsanancin mamaki suka raka bayansa da kallo, ba ma kamar Abrar wacce hakan ya matuƙar neman sumar da ita a tsaye, domin tunda suke a kullum gaisuwar nan da ta yi masa yau ita take yi masa, sai dai amsar ɗaya ce yake bata "Barka." Amma a yau sai gashi ya amsa gaisuwarta a cike harda saƙon murmushi? ya ilahi!
Tana juyowa suka yi ido huɗu da mamanta, Mamanta ta taɓe baki ta ce" Me kennan? Uhum! Koma meye kya yi ki gama shirmenki dan a shirme na ɗauka, ko duƙawa ya yi ya gaishe ki ni ai kin ga hi yace da ni irin na saƙo da saƙo."
Abrar ta sadda kanta ta ɗauko abin wanke hannun ta kawo ta tsiyaya mata ta wanke sumul ta ɗauka ta kai wajen masu aiki da gudu gudu ta haye ta nufi ɗakin su, dan burinta ta je ta ɓuya ta yi ihu iya ihu na farin cikin wannan lamari, tabbas sai ta yi farin cikin nan sosai da sosai.
ASWAN kuwa yana fita da motarsa dake gidan wacce tunda suka shigo ya saka a fitar da ita a dubata da komai, yana fitowa ya tardata har wanke ta aka yi sumul, dan haka ya amshi ky ɗin ya yiwa wanda ya masa hidimar kyauta, domin wannan ɗan ihsani nasa ya sa duka kaf ma'aikatan gidan ke matuƙar girmama shi da son ganin ya zo gidan, dan ko bai saka ka aiki ba in Allah ya cidaka sai aljihunka ya cika, kai in dai ya zo da wahala ya tafi bai duba su ba, sai in ransa a ɓace, abinda basa fata ko kaɗan a ɓata masa wato rai.
Hanya ya kama, ya tsaya ya idasa cike tankin motar a gidan man sa sannan ya ɗauki hanyar garin su Mani dreba, domin yana son ganawa da Mani dreba kuma yana so ya ga ko yana lafiya? Da wannan ya ɗauki hanya hankali kwance, hanya dai ya santa ciki da bai, shi soja ne, a bayan motarsu ta sojawa babu inda basu ratsa ba.
Kasantuwar garin su Mani gari ne ƙarami sosai wanda yake ƙauye ne amma wanda ya samu ci gaban rayuwa daidai misali, domin ƙauye ne mai ni'ima sosai , amma kuma sunansa ƙauye domin kowa ya san kowa duk wanda ka faɗi sunansa an san wanene balle a lokacin da ya tsaya ƙofar mai shago ya ƙure kiɗa a shagon samarin ƙauyen duk yawanci nan suke tarewa ana baza gayu, yana tsayawa mai kantin ya tardo shi da kansa yana tambayarsa abinda yake da buƙata, kasantuwar ya gama yin ilimi na zamantakewa da ɗan adam mai hasken kai da mai duhun kai, sai ya fara yin siyaya har ya sa aka rabawa samarin dake nan yan canji sannan ya yiwa mai kantin tambayar gidan Mani?
Ai kam kusan duk in ka ga baƙo daga birni dama yawanci in dai ba gidan mai gari ba sai gidan malam Mani ake zuwa tambaya, ɗaya daga cikin samarin nan ne ya miƙe da ƙarfin sa yana faɗin" Yau ni zan kai baƙon nan gidan malam Mani, na rigayi kowa."
Ai kam shi dai yana kallon ikon Allah saurayin ya shiga motar nan ya hakimce yana masa kwatance har suka ƙaraso ƙofar gidan Mani dreba, sannan ya sauka yana ta murnar ƙarin wani abin ihsanin da ya samu daga nan ya yi gidansa dan kuwa da aurensa duk da ƙarancin shekarunsa ya je dan ya shirya ya yi birni, yau dole ya yiwa matarsa siyayyar kayan daɗi na birni.
AA ya jima a ƙofar zaune cikin mota, tunda saurayin nan ya shiga ya sanar da ana magana da Mani shiru kake ji bai fito ba har sai da ya fara tunanin to ko baya nan ne? Sai ya ga ana ɗan buɗe ƙofar gidan kaɗan ana leƙowa amma kuma ba'a fito ba gaba ɗaya.
Shi ma ido ya tsurawa mai leƙowar cike da mamaki, sai kuma ya buɗe ya fito ya tsaya dan kuwa ya tabbata tamkar Mani so yake ya gane waye a cikin motar.
Hankalin Mani ya ƙara tashi, ya fito gaba ɗayan sa, sai dai a mugun firgice, a tsorace ainun ya shiga faɗin" Yallaɓai, kai ne? Yaushe ka zo? Ya ya aka yi ka zo? Wa ya kawo ka nan ɗin? Kai da wa kuka zo?"
Mamaki ya ƙara kama AA, firgicin Mani a bayyane yake, har ya manta da gaisuwa wacce ita ya dace su fara yi kamar yadda suka saba haka kuma suke girmama juna, har suka da AA ɗin ya kama hannunsa yana kallonsa ya ce" Mani, bamu gaisa ba, kai kuwa ka san wahalar sanin sunan garinka in dai na sani ganinka ai ba zai yi wuya ba, na je neman ka sau biyu bana samun ka, shine na binciko garinku dan na ga wayar ka ma bata shiga, ina fatan lafiya dai?"
Mani gaba ɗaya ya kasa nutsuwa, ya kasa amsa shi da lafiya ko babu, ya juya ya nufi ciki hankalinsa duk a tashe, AA bai yi wata wata ba ya mara masa baya, suna shiga suka samu iyalinsa tsaye da hijabinta har ƙasa ita ma yanayinta a firgice, sai ƴaƴa hudu dake leƙowa suna komawa su ɗin ma a firgicen suke.
Da mamaki ya dan ja baya kadan dan ba neman izini ya yi ba ya ce" Wai me yake faruwa ne?"
Mani ya dan duka yana dafe kansa da hannayensa biyu, sai kuma ya mike ya aro duk wata jarumtar da yake da ita ya karaso yana fadin a basu tabarma
Nan da nan matarsa ta dauko da kanta ta kai soron kofar gidan ta shinfida masu ta koma ta nemi kwanon shan ruwan mijinta ta cika da ruwan tulu d'anta ya kai masu ya dawo
Mani ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Sir ba komai fa, babu abinda ya faru, kawai dai na zata ko wasu ne ba kai ba"
Kallonsa kawai ASWAN ke yi, karantarsa yake ƙara yi, yanayinsa ya nuna a tsorace yake ainun, sannan a bayyane ya gane akwai abinda ke damunsa domin Mani ai ba haka yake ba, mutum ne mai faɗin abinda ke ransa in dai ya sani kansa tsaye, dan haka ya ce"Dama na dawo ne a kan ƴan tambayoyin da nake yi maka, sai na samu baka nan."
Cike da tsoron nan dai Mani ya ce" Yallaɓai, ka ganni nan babu abinda na sani, gaba ɗaya komai da nake faɗa maka ma canka nake yi, ka ƙaddara ƙarya nake faɗa maka kuma ka daina tambayata dan Allah."
Cike da jin haushin yanayinsa Aswan ya ce" Ka dawo hayyacinka, kar ka yi wasa da ni Mani, ban zo nan dan mu yi wasa a kan abinda na ɗauka da mahimmanci ba, ko me kake ɓoyewa ka san da zan sani, kuma ko wa kake tsoro yana gaba da mahaliccinka ne? Idan ka saka ni a hanyar da ta dace na kai ga cimma burina kai ka san har wajen ubangijinka ka taimaki rayuka ne, amma ba komai tunda haka ka zaɓa shikenan."
Ya ƙarashe cike da ƙoƙarin miƙewa dan abin ya fara kai masa karo, ya tabbata akwai abinda ya firgita Mani, amma bai yi tunanin zai kai shi ƙasa haka ba, bai cika son ganin jarumi ya faɗi wanwar irin haka ba.
Jiki a saɓule sosai Mani ya ce" Elhaji, ba zaka gane irin firgicin da aka sakani dan kawai na zanta da kai sau ɗaya ko sau biyu ba, ban taɓa tunanin haka ba sai da aka gwada min matata da ƴaƴana a duƙe kawunansu a ƙasa bindiga a kawunansu aka ce idan na saki na sake waiwayar birni a bakin rayukansu da ni baki ɗaya, ni kuwa na ga tabbas idan ban yi bankwana da birnin a kan ɗan albashin da ba kowani wata ake bani ba , ba kuma isata ciyar da iyalina yake yi ba har zan ɗauki wannan kasadar ta saka rayukansu a hatsari? Sai kawai na zaɓi dangana da shiga birnin na karya layina a gabansa na yar."
Aswan ya zuba masa ido kafin ya rintse idanuwansa cike da tashin hankalin dake kunno masa, wato irin gargaɗin da aka yi masa a prison ne aka yiwa Mani? Subhanallah! Dole zai tsorata bawan Allah dole zai shiga wani hali.
Sai da ya fara bashi haƙuri sosai na halin da ya saka shi, sannan ya ɗora da faɗin" Wato Mani a hankali binciken neman inda dukiya mai yawa ke fitowa na son kaini wajen da bana tunani, domin lamarin nan ƙwarai da gaske babba ne a bayyane, kuma waɗanda muke buga wasan nan da su suna ƙara nuna min girman darajar wasan namu wanda na lashi takobi sai dai idan raina ya fita daga gangar jikina, amma zaren da na ja sai na lauya shi a wuyan duk wani mai hannu a cikin lamarin nan, in har sun zo na tabbata ba zasu gaza barin mai duba masu kai ba, abinda nake so da kai shine zan fita ina faɗa kamar dai mun samu matsala da kai haka, kai ma ka biyo ni sama sama kana nuna babu ni babu kai, daga nan zan shiga mota in tafi, zan tsaya a wajen gari in yi jira, gaba ɗaya ahalin ka ka tabbatar da sun fito wajen gari, kar wanda ya ɗauki komai sai takardun anfani masu mahinmanci idan akwai..."
Numfashi ya ja ya sauke sannan ya ci gaba da cewa" Da ɗaiɗaya da dabara nake so ku fita, zan jiraku a motar cikin gonakin nan na shigowar garin nan, sannan zan yi zagaye zan barta a buɗe, duk wanda ya zo ya shige, ni kuwa zan kama mai kula da leƙen asirin waɗanda yake yiwa aiki, daga nan zan kai ku wani gidana dake daji dan in je cikin gari in sama maku hanyar tafiya babban gari, akwai yarona soja ne babba, zai ɗauke ku ya kai ku wani gidana a can da suke bawa tsaro, babu abinda zaku nema ku rasa na ɗan lokaci, idan komai ya lafa sai ka zaɓa a cikin garin nan zaka zauna ko a ina, zan sama maka aiki da dukkan abinda ya dace da muhalli, zan yi haka domin Allah da kuma taimakon da ka min sannan dan na kuɓutar da kai daga wannan ɗaurin da aka yi maka, amma ina roƙon ka ka sanar da ni waye ya yi maka wannan kashedin?"
Sosai Mani dreba ya ji ya gamsu da wannan lamarin, ya sani inma maganar tsaron za'a yi tabbas AA ya dame wanda ya tsorata shi, ya san waye AA, kuma yana girmama hakan ainun, dan haka ya dube shi ya ce" *OGA* ne."
AA ya yi wani kiskirim yana kallonsa, dan har ga Allah tamkar bai ji me yace ba, har sai da ya ga ƙwarai haka ɗin yake nufi ya ce" Oga ne me?"
Mani ya ce" Oga ne ya aikata hakan, a tafiyar nan da aka yi da ni dama dan a yi haka da ni ne."
"OGA? OGA? KANA NUFIN HAMMAT ANZA?" Ya sake tambaya da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa yana tsatsare shi da idanu da kallo kamar na bai yarda da shi ba haka.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*