Showing 39001 words to 42000 words out of 397328 words

Chapter 14 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70009

kuma har kuma da kuke gani kuna yin shiru ba kwa magana."

Juyawa ta yi a hassale ta ƙarasa sauka daga matakalar dake gurin ta fice, kalamanta ne suka daskarar da shi saboda wannan ya fi ƙarfin *jirwaye*, sai dai ace fitila ta sa ta haska masa wani duhu da wataƙila aka jima ana tafiya a cikin sa a wannan asibitin, beban nan da ya juya zai tafi ya yi gaggawar riƙe hannun shi yana kallon hanyar da ta bi yace "Wacece ita?"

Cikin ɗaga murya beban yace "Yallaɓai ai anan take aiki ita ma, amma bata jima da zuwa ba, dan ko wata ba ta yi ba."

Sakin hannun shi ya yi da mamaki ya furta "Ba ta yi wata ɗaya ba? Kuma za ta bar aikin ta? Akan wane dalili to?"

Mata masu cikin dake gefen shi zazzaune ya ɗan kalle su, sai kawai ya shiga takawa dan barin wurin amma tunanin Yusrah da maganganun ta ne fal a kwanyar kan shi, asibitin su? Asibitin mahaifin shi? Me ake aikatawa haka? Me ya saka yarinyar can kuka bayan ta fito daga ofishin uncle ɗin shi? Dan shakka babu daga nan take dan ofishin shi kaɗai ke wurin sai bangon da zai sa dole ka dawo baya, me take nufi da ana cin zalin al'umma? Me ake aikatawa? Wane bala'in ake ɓoyewa a asibitin nan? Shin da sanin Aba ne haka ke faruwa? Kuma da sanin uncle ɗin sa?

"Ya salam." Ya furta a fili yana nufa inda zai samu Mani dreba yana jin kanshi kamar zai fashe, ga binciken da ya fara ɗaura ɗamba akan shi, ga kuma wasu abubuwan na kunno ma sa kai da bai yi tunanin zai same su a tsarin sa ba.





*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍??🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*12*




Yana zuwa inda ya samu Mani dreba ya tarar bayanan, sai dai kafin ya bar wurin ya shigo asibiti da motar ujila da mugun gudu ya ɗauko wani mai kuɗi da ya samu bugawar zuciya, shine aka kira da gaggawa aka ɗauko shi daga kamfanin shi, yana tsaye yana kallo har aka fito da shi aka shiga ɗakin gaggawa, lokacin ne shi kan shi Mani hankalin sa ya dawo gare shi har ya kula da AA dake gefe yana kallon su.

Ƙarasawa ya yi kusan shi da girmamawa dan duk da baisan shi ba ya san ba ɗan ƙaramin gida bane, yana zuwa suka gaisa kafin AA ya yace masa "Ka ga na dawo ko? Kar ka damu, dama jiya na je asibitin da ka faɗa min ka kai motar nan, sai dai an tabbatar min da ba ta kwana asibitin ba, kana bada baya aka ɗauketa daga nan."

Da tsantsar mamaki Mani dreba ya riƙe haɓa yana jajanta lamarin da bashi tabbacin bai sani ba wallahi, bai kula da zancenshi ba yace masa" Ina so ka faɗa min wa ya dawo da motar nan asibitin? Ko ba'a maidota ba?"

Da tabbaci Mani dreba yace" An maidota..." Sai kuma ya nuna mishi motar da ya shigo da ita yanzu yace" Ai ita ce wannan ma."

Jinjina kai AA ya yi yace" Hmmmm! Wa ya kawo ta?"

Da irin shakku ba karsashi yace" Ɗaya daga cikin mutanen da na faɗa maka ne suna zuwa wajen oga, shi ya dawo da motar da sassafe."

Ba alamar wasa yace" Yana nan? Ko kasan inda zan iya samun shi?"

Girgiza kai ya yi yace" Gaskiya ban san komai akan su ba, idan dai suka zo mu kan zauna nan har mu ɗora shayi tare da su mu sha, sai dai duk ranar juma'a wannan dahir ne idan ka zo nan daga sallah juma'a zuwa yamma za ka same su nan."

Shiru AA ya yi kafin ya gyaɗa kai yace" Shikenan, ai gobe juma'a."

Jinjina kai ya yi yace" Hakane yallaɓai."

Hannu ya bashi suka yi sallama da niyyar gobe ma zai dawo, dole sai ya san daga ina kuɗin nan suka fito? Sannan na wanene? Kuma suna ina yanzu? Bayan ya san wannan kuma zai nemi sanin *wacece wannan ashirin ba ɗaya* ɗin? Dan duk da an faɗa masa ita ma ma'aikaciya ce, gaskiya bai gama yarda ɗari bisa ɗari ba, idan ma hakane to sai dai idan kawai irin waɗanda ake ma hanyar abu ne basu cancance shi ba, amma dai maganar sahihin hankali a gurin nan kam babu shi. To zai ƙoƙarta ya samu bayanan abinda take nufi da abinda ta faɗa ko da hakan na nufin ya ɗan ari irin rigar ta ta marasa cikakken hankali ne dan ya samu abun da yake so.



*YUSRAH*



Tunda ta dawo gida a gajiye tsabar tafiya tambayar farko da Mama ta mata ita ce "Me ya dawo dake gida kuma yanzu? Har kin tashi ne?"

A taƙaice tana kumbura baki tace "A'a Mama."

Zuba mata idanuwa Maman tayi tana jiran ta ji to me ya maido ta? Amma sai Yusrah tayi shiru, hakan ya sa maman cewa "Ina jin ki? Lafiya?"

A hankalce ta kalli Maman cike da son danne ɓacin ran da ta ƙunso tace "Mama, na daina aiki a asibitin nan ne kawai, ba zan iya ba ko kaɗan Mama, akwai wasu abubuwa da ake aikatawa da sam basu dace da tsari ba, sannan Docter ɗin gaba ɗaya ba mutumin kirki bane, shiyasa kawai na tahowata."

Saida ta dasa aya Maman ta numfasa tace" Me ye hujjar ki ta barin aikin Yusrah? Ina ce burin ki shine ki samu aiki ki taimaki mahaifin ki? Shin munin zaman ki a asibitin har yafi munin ki sanar da mahaifin ki cewa kin daina aiki Yusrah?"

Da sauri ta kalli Maman tace" Mama, idan na ci gaba da zama a asibitin nan ban san me zai faru dani ba watarana, Mama yau ina zuwa na samu wata tsohuwa na faɗa akan tun jiya jikanyar ta ta haihu amma ba'a basu uwa sun rufe ba, kuma dama Ustaz ya fara faɗa min akwai wata mummunar hanya da ake shiga da uwar matan mutane idan suka haihu, sannan...kuma..."

Shiru tayi tare da sadda kan ta, hakan ya sa Maman riƙo hannun ta cike da kulawa tace" Yussy, ƙawaye ne ni da ke da ma ƴar uwar ki, na rene ku ne a turban dazaku iya faɗa min komai ya dame ku komai ƙanƙantar sa, faɗa min sannan kuma me?"

Idanuwan ta ta zuba cikin na mahaifiyar ta tace" Mama, abinda ya sa na baro asibitin yanzu, Doctern ne da ya kirani ofishin shi ya fara taɓa jikina, na tsorata Mama sosai, shiyasa na ce masa na haƙura da aikin dan na tseratar da mutumcina."

Ƙura mata idanuwa Maman tayi tana kallo tsawon sakanni, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan dafa kanta tace" Kin yi abinda ya dace, Allah ya miki albarka."

Asanyaye ta amsa da" Ameen Mama."

Sannan kuma cike da gargaɗi ta ɗora mata da" Sannan, ko wane hali za ki shiga a rayuwa, komai buƙata ko larura da zaki samu kan ki a ciki, ko girman wata alfarma ko taimako da za'a miki, indai sai kin salwantar da darajar ki ta ƴa mace, to ki haramtawa kan ki wannan aikin komai alfanun shi, dan shi kuskuren zubar da kima sau ɗaya tak idan ka aikata shi ba ya taɓa gyaruwa, kin fahimce ni?"

Gyaɗa kai tayi tace" Na fahimta Mama, in sha Allah ba zan taɓa baki kunya ba."

A sanyaye Mama tace" Shiga ciki, idan Abban ki ya shigo zan sanar da shi."

Miƙewa tayi daga kan tabarmar ta nufi ɗakin su, kayan jikin ta ta cire sannan ta fito, cikin sa'a kuma sai ga yaro Baba ya aiko daga kasuwa ya kawo musu masara da kuma shinkafa, ba ɓata lokaci Yusrah ta kunna wutar gawayi daga baki bakin ƙofar falo dan ta kama wutar saboda yayyafin da ake ta yi, rumfar su kuma ba ta tare ruwa saboda zana ne kuma ta tsufa sosai.

Haka ta wuni gidan su tare da ƴan uwan ta cikin farin ciki da nishaɗi, ƙawar ta Maryam ma da take son kira amma babu kati a wayar ta sai da wayar aunty Hannah ta kira ta, basu ja doguwar gaisuwa ba duk da aiki ya ɓatar da dukansu sun kwana biyu ba su haɗu ba, dama makaranta ke haɗasu kullum, sai ita aka tura ta babbar asibitin gwamnati ita kuma Yusrah ta kuɗi, ta kuɗin ma ta masu kumbar susa, wataƙila shiyasa ma Docter ɗin ke yadda ya ga dama a asibitin.

Daga bisani ne Yusrah ke tambayar Maryam ɗin _"Maryam, wai dan Allah kina ganin yanzu idan na je wajen Docter Saddi na ce masa a canza min gurin aiki na kuma bashi ƙwaƙwaran dalilin da ya sa bana son waccen, kina ganin zai amince?"_

Amsa Maryam ɗin ta bata _" Zai iya mana Yusrah, tunda dama kinga ai asibitin gwamnati ya kamata kiyi bautar ƙasar ki amma sukayi cuku-cuku suka tura ki can, amma dama ai ko asibitin ƙauye aka kaiki kuma bai miki ba misali, ai kina iya neman alfarma a canza miki, matsalar ɗaya ce kawai idan baki da wanda zai shige miki gaba."_

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tace _" Shikenan Maryam, zan jaraba na gani."_

Da sauri Marya tace _" Dakata wai, na ji kina wannan tambayar lafiya? Ba kya son asibitin ne?"_

A taƙaice ta amsa mata da _" E, har ma na daina aikin."_

Da mamaki Maryam tace _" Ke Yusrah, kina da hankali kuwa? Ki samu aikin da ake ta raɗe-raɗin ɗaukar ki za'ayi ma, sannan asibiti kamar wannan ki ce kin daina, me ya sa to?"_

Aunty Hannah ta kalla da ke ta mata alama kuɗin ta kar su ƙara basu da yawa sannan tace _" Kinga zamuyi magana idan mun haɗu, katin ya kusa ƙarewa, sai anjima."_

Da haka suka rabu ta shiga tunani da kuma niyyar in sha Allah gari na wayewa za ta je makarantar su ta sanar da Docter, a dai dattijantakar shi da ta sani idan ya yi niyya ya kuma fahimce ta zai mata wannan alfarmar.

Haka dare ya riske su har Baba ya dawo kuma Mama ta faɗa mishi abinda ya faru, shi ma dai bayan ta ya goya tare da mata addu'ar samun wani aikin da ya fi waccen, har ya je masallaci ya dawo suka yi haddar su da dama ba kullum bane suke yi rana ɗaya ake tsallake, har suka gama karatu dare ya ƙara yi suka kwanta gari ana ta yayyafi ko sau ɗaya ba'a ɗauke ba, haka aka kwanta da tunanin wayewar gari a ɗora daga inda aka tsaya.

Can kusan ƙarfe ɗaya na dare mahaifiyarsu ta buɗe idanuwanta da suka yi mata mugun nauyi ta ɗan sake duban gefen da mijinta ke kwance, so take yi ta tashi ta leƙa wajen su Yusrah dan ta san halin Yusrah da shegen son sanyi, ta sha bari sai kowa ya kwanta ta shige ruwa ta sha jiƙa jikinta kafin ta kwanta, bare a zamanin damina idan ka ga an yi ruwa ta kwana a ɗaki to kuwa ana tsaye a kanta ne, in ba wannan ba ba zata taɓa kwanciya a ɗaki ba komai ruwan.

Sai dai duk yadda ta so tashin ta gaza, tamkar an danneta da wani ɗungumemen dutse, a dole ta mayar da kanta tana ta addu'a ta sake mayar da idanuwanta ta lumshe dan ta tabbata gajiya ce ke damunta ba komai ba sai mutuwar jikin da take fama da shi wanda Baban su Yusrah ya tabbatar mata ba komai bane face zazzaɓi harma ya kawo mata maganin zazzaɓin.

Dare na ƙara yi, asubahi na gabatowa ya zamo an kusa kiraye kirayen sallar asuba, gari kuwa ya ɗauki shiru irin shirun nan da ƙaramin motsi ke zuwa nesa, wani irin ƙarar zubewar gini ya saka duk wani magidanci zabura wanda abun bai shafa ba a lokacin, ido a waje sannan ya kaɗo waje dan ganin a inda ginin ya zube, ba wai iya mazan ba har da mata da yara duk an fito a rikice ana hailala da neman inda abin ya faru domin zubar ginar nan tabbas ba ƙarama bace.

"Innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, jama'a a kawo ɗaukin gagawa, gidan Inna mai koko, gidan Habu na ƙetare, gidan tagwaye da gidan Malan Abdul Hameed a nan ne garu suka zube."

Muryar liman ta karaɗe anguwar da lasifika, hakan ya sa da gaggawa duk jama'a suka ɗugunzuma kowa na nufar inda ya fi kusa da shi dan bada taimakon gaggawa.

Lahaula wala ƙuwwata illa billah, gidaje ne suka rushe tashi ɗaya domin wata na zubewa wata ke binta ciki harda na gidan su Yusrah domin zubewar ɗaki biyu ne a kan iyalan Abdul Hameed, a lokacin da suke cikin ɗaki cikin nauyayyan barci, wato garun da ya haɗa ɗakunan biyu ne ya rufta hakan ya sa sauran ginin zubuwa a kan su.

Hankalin duk wani wanda ke wajen nan ya gama tashi gaba ɗaya anguwar ta rikice, an yi kiran motar kwana kwana, nan da nan kuma motar polisai ta bakin titi ta ƙaraso saboda Liman dake da kyakkyawar alaƙa da mutanen dan duk yawanci sukan yi sallah a nan masallacin tare da shi, sun bazama gidajen ana ta kokowar fitowa da mutanen waɗanda nan take kake jin an kwashi kuka domin abin ya yi muni, an samu mace mace sosai.

Ƴan anguwa tun daga kan dattijai har zuwa yara yaran maza fama suke yi kansu da ƙafafuwansu suna fitar da duk wani abu da yake dutse ko ƙasa dan su samu hanyar ceton maƙotansu, har masu motar kwana kwanan suka ƙaraso aka shiga ƙoƙarin ganin an ceci rayukansu baki ɗaya.

Tsofaffin dake gidan Inna mai koko babu wacce ta fita da ranta, a gidan su tagwaye kuwa samari biyu suma lokaci ya yi, sauran kuwa suna cikin hali na muguwar jigatuwa.

A gidan su Yusrah an samu an fara fitar da su Baba, wanda jini ke tsiyaya a jikinsa tamkar gawa idanuwansa a rufe ruf, jikinsa kuwa burtuk da ƙura , sai Mama wacce ana fitar da ita aka shiga dannar ƙirjinta ana ta faman a ga numfashinta ya dawo jikinta, amma ina? Mama ta riga da ta rigayemu gidan gaskiya, a haka aka fitar da Yusrah wacce ke yashe a filin Allah dan kuwa ita ba'a ɗakin ba ma take amma kuma gaba ɗaya ƙasa ita ma ta rufeta haka kuma tamkar a summe take domin idanuwanta a kakkafe suke kuma bata jan numfashi, ƙarshe aka samu aka ciro Hannah da Auta, Hannah bata numfashi dan kanta ya lotsa gaba ɗayan shi, Auta kuwa yana fuzga tamkar mai fitar rai.

Ban da hailalar maza da kukan mata baka jiyo komai, gaba ɗaya anguwar ta rikice ya zamo babu mai ba dan uwansa haƙuri, asibiti aka wuce da su, nan da nan aka karɓe su likitoci suka shiga gabatar da nasu aikin suma, nan take suka tabbatarwa da su Liman cewar Mama ta rasu ita da Hannah, Baba yana cikin mawuyacin hali domin bai san inda kansa yake ba, abu dama da girma ga tashin hankalin ga ciwo, Auta ya samu muguwar karaya ta ƙaffafuwansa baki ɗaya har cinya ga manyan raunuka, Yusrah ce ta farfaɗo sai dai tana fahimtar abinda ya faru ta suma, amma ita a jikinta ƴan raunuka ne kawai aka gani, amma ana jiran hoton kai da za'a yi mata zuwa an jima.

Wasa farin girki, kafin ake cewa ƙarfe tara na safe ta yi gigita mafi girma da tashin hankali ta gama mamaye wannan ahali, firgici ya gama turnuƙe zuƙatan ƴan anguwan su a lokacin da aka sake basu gawar Abba, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une kawai liman ke maimaitawa hankalinsa tashe, kansa a ƙasa yana sauraron bayanin babban polise ɗin dake tare da su.

A raunane sosai ya ce" Yanzu ya zamu yi kenan? Zamu yiwa sauran sutura ne su kuma iyalan Marigayin nan mu yi jira har ta farka yarinyar nan kafin a rufe iyayenta da yayarta?"

Shima polise ɗin jikinsa tamkar babu jinin kirki dan irin yadda juwa ke kwasarsa ya ce " Babu jiran da zamu yi Akaramakallah, yau juma'a ce, in sha Allah zamu sallacesu idan mun gama sallah sai a yi masu sutura, Allah ya jiƙansu Allah ya amshi shahadar su, ita kuma da ƙaninta da sauran jama'ar dake cikin wani hali Allah ya tashi kafaɗun su, dan ka ji bayanin likita sun yi mata allura mai nauyin gaske, saboda gudun shiga mugun yannayi na bugawar ƙwaƙwalwa saboda chock ko zuciya."

Malam Yusuf ya girgiza kai yana share hawaye ya dubi polise ɗin nan da liman ya ce" Ni abinda nake tunani a yanzun wannan asibitin da aka kawo jama'armu, malam liman asibitin kuɗi ce mai tsadar gaske ban san ko zamu iya daidaita lamarin kuɗaɗen majinyatan duba da bamu san adadin lokacin da zasu iya ɗauka ba, amma idan tashin hankalin ya ɗan ragu sai mu zo a maida mana su ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login