Showing 168001 words to 171000 words out of 397328 words
su, in dai suna shiga guri kuwa ko yayane za'a gane, ba wai zargin ɗansa yake yi ba, uba ne shi dake fatan ganin ɗansa baya aikata wani saɓo, kuma binciken da yin kafa ƙafan ba laifi bane.
Sun ƙaraso babban farfajiyar gidan, wani soja da hular sanyi wacce ta rufe har kumatunsa ta bar iya ƙofofin hancinsa da idanuwansa, ɗauke da bindigarsa ya ƙaraso ya buɗe gefen da Aba yake ya sara masa dan bashi girma sannan ya ce " Barka da zuwa sir, sir Aswan na jiran ku a babban falon sa."
Aba ya gyaɗa kai ya fara yin gaba sauran duk suka rufa masa baya, ya zamo yau kowa cikin ƴan matan kallon gidan yake yi domin dare ne an kunna fitilu da duk wani abin da zai ƙawata gidan idan dare ya yi, sai ya zamo ya ƙara kyau fiye da rana. A wajen shiga babbar ƙofar Aba ya ɗora ƴar yatsarsa babba, ƙofar ta buɗe da digital ɗin sa, dama da nasa da na Anna da na Aswan ɗin ne kawai ke buɗe ta, yanzu ne ya sa a ƙara na Safwan.
Nabihat bata nemi gigicewa ba sai da suka shigo babban falon, inna lillahi! Yarinya ta nemi haukacewa, ta nemi fita a hayyacinta, da ƙyar da siɗin goshi ta iya hana kanta juyewa ya dubi baya tsabar son ta ga komai a lokaci guda, sai da ya zamo ta nanuƙu inda Abrar ta zauna bata ankara ba, abu ɗaya dai ta sani idan iyayen na zaune a saman kujera harda Aba, to a gidan Anna ba'a zama a saman kujerar nan, dan haka yanzun ma dai ta kai ƙasa ta zauna ba tare da ta gane komai ba, idanuwanta a kansu shi da Aba, inna lillahi, idanuwanta a kan su, da Aba, da shi, da Anna, da kuma wannan yaro da Allah ya taimake shi har uban ya samo shi, kai jama'a wannan yaro akwai rabo fa, ga yaro dai an samu ɗan gaba da fatiha amma kuma tsabar tashin hankali irin na mai kuɗi gayanan ana yi masa tamkar za'a haɗiye a cinye dan so.
Aba ya kama kujerar ta Safwan, wacce tun jiya Docter da shi Aswan ɗin suka amsota a aeroport, wacce aka turo ce daga cen US ɗin, irin kujerar nan ce da ake ɗora mai matsalar takawa da kansa tana tura shi duk inda ya zo shiga, mugun tsada ne da ita gaskiya, ya zamo da aka kawota docter ya gyarata ya daidaita komai aka ɗora Safwan, a jiya irin yawon da ya sha tsakanin ɗakin sa da falo, tare da su meem, tun suna masa jan aji sai da suka ringa binsa duk inda zai shiga suna masa yan kokensu na nuna sabo su da shi har uban ya je anguwa ya yi duka kaf abubuwan dake gabansa ya daidaita komai sannan ya dawo gidan ya tarda shi a falo ya yi barci saman kujerar, domin ya gaza sauka , yana saman dai a kwance sai da ya zo ne ya ɗauke shi ya kai shi gadonsa yana murmushin ganin farin cikin da yaron nasa ke ciki tunda aka kawo kujerar nan, har faɗi yake yi zai iya yawo da ita ko ina, zai iya fita ko ina da ita, shi kuma ya nuna masa ƙwarai kuwa, domin idan suka je aka yi aikin ma a kwana goma bai isa takawa ba sai ya warke sumul a nan kafin ya fara takawa, kwanaki goman zasu yi observation ne su ga idan ana samun ci gaba na ƙashin bayan da aka gyara in yana gyaruwar, sannan su sake shi idan sun dawo za'a ci gaba da bashi kulawa a asibiti har sai komai ya daidaita sannan a sallame shi.
Aba bayan ya shiga tura shi da kujerar ya ce" Aboki, wai ni tafiyar nan kamar a yita da ni, zuwa zaka yi ka more ka bar ni?"
Anna na yar dariya tana kallon su, yan matan kuwa sai a lokacin suka samu gaisar da yayan nasu bayan sun gaisa da Aba da Anna da kuma Humed da matarsa, Humed na yi masu hoto yana dariyar Safwan da ya ɗago kansa ya ce" Papy kenan garin akwai mugun daɗi?"
Humed ya ce" Ku ji min baki muimui, garin akwai mugun daɗi kamar wani boss, sak irin babanka son." Aba ya juyo da shi ya dawo da shi daf da Anna ya ce" Yana da daɗi sosai aboki, balle ga babanka a gefe na san zaka more, ku zauna a yi addu'a, Allah ya sa a yi farar tafiya, ya bada lafiya jikana."
Gaba ɗaya suka amsa da amen, Aba ya ja addu'ar, suna amsawa, ita kuwa Nabihat hannayen kawai ta iya ɗagawa idanuwanta a kan AA ko ɗaukewa bata yi, wanda hakan kowa ya gani ya kuma ga inda take kallo banda shi da tunda ya amsa gaisuwar su bai kuma yi masu kallon da ya wuce ƙa'ida ba, hasalima ya shiga zantawa da Abansa ne har aka shiga yin addu'a, Abrar kanta ta ga irin kallon nan ya yi yawa ta girgiza kai a ranta tana ayyana _"Baki san yayanmu ba, Allah ya sa ya kama idanuwanki a kansa haka, zaki gane baki da wayo, idan kin yiwa wani rashin mutumci wani ya wuce gaban ki wulaƙanta shi ne ai."_
Da aka gama aka shafa addu'ar Safwan ya danna kujerarsa ya ƙarasa wajen auntys ɗin sa, tagwaye da Abrar suka ɓalle da fira, su tagwaye har gardama suke yi wai ya yi jiki a'a fari ya ƙara dai da sauran su, Abrar kuwa gift ta zo masa da shi a jakarta ta buɗe ta cire ɗan ɗaurin ta bashi tana murmushi ta ce" Ka ga abinda nace maka?"
Safwan ya zaro ido da mamaki da murna ya juya ya ce" Dad, wow! Dad kalli?"
Abin mamaki gare su baki ɗaya sai gani suka yi Aswan ya taso da kansa ya nufi inda suke ya duƙa gaban kujerar ta Safwan ya amshi abinda yake nuna masa, Safwan da murnarsa ya ce" Dady ba nace maka ina son azurfa ba? Dama a asibiti aunty Abrar tace zata yi min abin hannu da sunana na azurfa, Dady ka san a gida can wanda ya faɗo mana aunty Yussy kaɗai take da azurfa a ɗan yatsarta na biyu, kullum sai na cire mata sai ta amshe abinta ta mayar, ka ga nima na yi nawa yau ba zan ɓata ba kowa ba Dady."
Aswan sai da ya gyara masa ƙafafuwansa da kyau a saman kujerar ya buɗe abin ya ciro masa, shi ma ya yiwa fuskarsa wata expression ta mamaki ya ce" Wow! Kai kai kai ma sha Allah, ka cewa aunty Abrar thank you? Oya mu cewa aunty Abrar thank you."
Da murmushi a fuskokinsu shi da Safwan ɗin suka dubu Abrar suka furta mata kalmar godiyar da ta daskareta a zaune, ba wai ita kaɗai ba, har da tagwaye da Nabihat, wacce tashin hankalin ganin kallon kirki bata samu ba a wajen yayan nasu, duk irin wankan da ta ɗauka da kwalliyar da ta yi da wankan da ta yi da turare dan kawai ya zamo ta fi kowa fitowa a cikinsu ta fi kowa fizga ya zamo dole zai kalleta sai gashi kallo ɗaya ma bai yi mata ba na mutumci wanda zai sa ta gane tana da dama a tare da shi, sai wannan abin hannun ne ya saka shi farin ciki haka harda godewa wannan banzar? Tun daga lokacin zuciyarta ke tuƙuƙi, ta kasa gane komai sai kallon da take binsa da shi wanda zuwa yanzu Aba ma ya gane dan kuwa tsaf ya ga kallon nata ya wuce misali shi kuwa har da ɗan murmushin sa, domin zai fi kowa farin cikin ganin haka, Nabihat ƴar wajen chef ce ai, kuma yarinyar bata da laifi, gashi tana girmama su sosai, zai ji daɗin ta zamo sarakuwarsa.
Sun ɗan jima kaɗan sannan suka fito su dukansu, amma Aba zai zauna ne har Aswan ya je ya dawo saboda idon Safwan biyu ba zai barshi shi kaɗai ba, da yace Humed ya zauna, sai Aban ya nuna a'a su je da matarsa bari shi ya zauna in ya dawo sai a ɗauki mota a maida shi gida.
Bayan sun shishiga mota su kuwa su uku suna tsaye daga nesa kaɗan Aba na murmushi ƙasa ƙasa ya ce" yaya ka ga yarinyar?"
Aswan ya kalli Aba, ya ga irin murmushin da yake yi da kuma motar su tagwaye da Abrar da Nabihat ya tsurawa ido sai yayi murmushi shima yace" Ma sha Allah, tana da kula sosai, ka ga yadda take saka Safwan farin ciki? Dubi abin hannun da ta masa."
Aba ya kalle shi yana faɗin" Kai ba Abrar nake nufi ba, Nabihat fa, ba na ga irin kallon da kuke yiwa juna ba na soyaya?"
Da mamaki ya zaro ido ya dafa ƙirjinsa ya ce"...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
27/05/2024, 12:08 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕??❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*44*
Da mamaki ya zaro ido ya dafa ƙirjinsa ya ce" Ni?"
Aba ya ce" A'a ba kai ba ni. "
Aswan ya saka hannayensa ya rufe idanuwan Safwan da ya ɗago yana kallon su duk wanda ya ɗauki magana ƙasa ƙasa ya ce" Aba a gaban ɗana zaka yi maganar soyaya? Jinjiri ne fa, kuma bayan wannan ni ai ba sa'an ta bane gaskiya, Aba bari in je in dawo freind sai kirana yake yi, in sha Allah ba zan jima ba."
Aba baki buɗe ya raka shi da kallo har ya haye ƙaton babur ɗin sa ya saka casque ɗin mashin ɗin ya tayar ya fice a gidan da gudun babur ɗin wanda bai matse gudun ba kamar yadda ya saba saboda Aba da ya kasa ya tsare sai da ya fita ya matse abinsa ya ɗauki hanyar gidan su Barista Muktar.
Aba kuwa girgiza kai ya yi ya saddo dubansa ya ga Safwan danna tap ɗin sa kawai yake yana game sai kawai ya tura shi suka koma a ransa yana ayyana _"To ko dai ni na fassara kallon? Kai kallon nan na Nabihat ba na lafiya bane gaskiya, to ko dai ba kallon da nake tunani bane? Ni yanzu bana iya gane kallon soyayyar ma, ƴan matan yanzu sun maida kallon kamar harara kamar masu kamun farfaɗiya abu dai kamar faɗa zaka gani a tv wai sai Annar yara tace soyayya ce, Allah shi kyauta."_
Aswan kuwa sai da ya isa har ƙofar gidan su Barista ya tsayar da babur ɗin, a lokacin da Barista da su Samir suna ƙofar gida suna saman kujeru suna shan shayi suna fira, tun ɗazu burinsa ya ga zuwan AA ya ƙi sanar masu wanda zai zo dan baya so su gudu su bar gidan.
AA ya sauka daga babur ɗin ya nufi inda suke zazzaune, dama tunda babur ɗin ya tsaya suka zuba masa ido, abin duhu duhun ya hana masu gane ko waye kai tsaye, amma girman babur ɗin ya sa suka kasa ɗauke idanuwansu sai Yaya Muktar da ya tashi yana ta murmushi ya ɗan tarbo shin nan suka gaisa, kafin ya ƙarasa kusan fitilun ƙofar gidan haske ya haske shi da kyau ya shiga miƙa masu hannu sannan amon muryarsa ta bayyanar masu da wanene.
Da sauri Dauda ya kalli Attahir shi ma ya kalli Dauda da Samir suka sake kallon AA dake cewa Yaya Muktar ya raka shi ya gaisar da Hajia, jikin samarin nan ya yi sanyi ƙalau, suka haɗe waje ɗaya suka yi shiru kamar ba yanzu suke shan fira da ihu da dariya ba suna kallon bayan shi har ya shige gida kafin Samir ya kwantar da kansa a jikin Dauda ya ce" Jikina duk ya mutu, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! Kai wai makashin mahaukacin soja ne? Me ya kawo shi nan kuma? Me muka yi to mu? Wayyo Allahna kar dai ya mayar da mu wajen can?"
Da sauri Dauda ya bige kansa ya ce" A'uzubillah mina shiaɗanin rajim, falyaƙul khairan au liyasmut Samir, ku tashi mu je mu gaishe shi, hannu fa muka bashi, sa'anmu ne shi?"
Da sauri suke girgiza kai, amsar ba sa'ansu bane ɗin, kuma suka miƙe suka jeru ɗaya na bin ɗaya suka yi cikin gidan, dan kuwa ba zasu iya jira daga an fito a yi gaba da su ba Hajia bata yafe musu ba, da suka shiga suka samu yana saman kujera suna ta ɗan taɓa fira da Hajia ita ma a saman kujerar da hijabinta a jirge ga gumba ta dama zata ɗirka gefe guda kuwa ya matanta na faman kwaɗa salak, ɗayar kuwa tana ciki ta kunna kiɗa sai casu take yi, tsakiyar ɗakin kuwa hijabansu ne, riga ce, tarkace dai wajen da zai zauna ma sai da aka kwashe kaya sannan ya zauna.
Daga bakin ƙofar suka duƙa su dukansu murya a sanyaye ƙalau suka ce" Baba ina yini."
AA ya yi kamar bai ji su ba, Yaya Muktar kuwa ya kai hannayensa ya gumtse bakinsa tamau dan kar ya bushe da mahaukaciyar dariya, Samir ya miƙe da sauri ya shige ɗakin sa ya ɗauko jallabiya ya ɗora saman rigarsa mai jankaken hannu ya dawo ya sake duƙawar kusan ƴan uwansa.
Hajia ta ɗauki tocila ɗin ta ta kunna tana rage girman idanuwanta ta ce" Muntari, muryar su waye na ji suna gaishe da baba? Babanku ya shigo ne?"
Yaya Muktar ya ce" Uhum, su Auta ne."
Hajia ta haske su, ta ga sun yi tsamo tsamo a duƙe, ga wanda suka duƙawa ɗin dai a ganewarta, ta ƙara ƙanƙance ido ta ce" Attahiru? Kai uban menene ne wannan tsuguno da murya a lauye? Wani sabon salon ne kuka fito da shi? Wannan fa abokin yayanku ne ai ba rashin kunya zaku masa ba ko?"
Hankalin Attahir ya tashi, yaya Hajia zata kama sunansa ta danganta da rashin kunya a gaban makashin mahaukacin soja? Rashin kunya? inna lillahi! Dauda ya yi gaggawar cewa" A'a Hajia wa Billahillazi ba rashin kunya zamu yi ba gaishe shi muka zo yi, kuma muka ce a haɗa mana wankin Baba da naki da na su Rhaisa zamu yi yanzu yanzu, kuma a bamu makullan motoci suma mu wanke su yanzu yanzu."
"To fa, ka ga wani salon cutar ko? Kai yanzu Dauda ka zata na shirufce halan? Ɗan ƙaniya ni zaka yiwa wankin harda su Rhaisa? Mota kuwa in ba fita zaku yi da ita ba kun taɓa wankewa? Ni dai bana son munafurci Alkur'ani, Muntari ka ji wata lalatar ko?" Hajia ta tare tana janye jakarta mai makullayen motocin gidan, bata saki domin ɗauka suke yi su yi tafiyarsu yawo, duk da yanzu an jima bata ga ko jin sun tambayi mota ba, amma bata saken da zasu gani har su ɗauka.
Rhaisa da mamaki ta ɗaga labule ta leƙo ta kalli ƴaƴan Hajia, ta gyaɗa kai ta ce" Tabɗijam! Lallai."
Sai kuma ta komawarta, dattin jikinta ma ya ishe ta sai fama take yi da waya tana waya da saurayi, ita ma Iman dake ɗirkar rawar a ciki saman kayan dake zube ne take yin rawar cikin kuwa sai yanar tautau, haka ma falon, kai wacce ke falon tana kwaɗa salak ɗin kanta ba zata yi girki shi dai ya ci ba, zanin jikinta har ya cenza kala dan wahala, zaunen da yake yana dai jin muryar Hajiar ne, amma gaba ɗaya hankalinsa a kan kowa na gidan yake yana karantar su.
Ƙasa ƙasa ya ce" Kai ku tashi mana ku je waje ku zauna."
Kamar zasu fashe da kuka suna kallon Hajia dan ta gane wallahi har cikin ƙoƙon ransu da gaske suke a basu aikin gidan nan kaf yau su yi da su je su yi jiransa daga su sai shi, amma Hajia ta ɗauka salon danfara ne? Inna lillahi! Wai su abinda ya fi ɗaure masu kai daga ina yake? Ya rasa inda zai zo sai gidan nan? Kuma wa ya bashi shiga mai kyau haka? Yaushe ya yi aski? Wa ya bashi babur ɗin can? Kai jama'a, abu dai in zai samu bawa baya taɓa yi masa shawara ai da mutum ya kimtsa kansa ya daidaita zamansa, haka suka miƙe suka fice gaba ɗayansu, shi kuwa ya gama karantar kowa sannan ya miƙe yana murmushi ya duƙa gaban Hajia ya ajiye cheik ɗin da ya rubuto dan bashi da kashhhh kuma ba zai iya shiga bai yi alkairin ba, sannan ya miƙe ya saukewa mai kwaɗa salak ɗin kallon da ya sa ta ɗan yi tsuru tana kallonsa da tunanin anya ba harararta ya yi ba? To amma me ta yi masa? Sai dai bata ƙarasa wannan tunanin ba ya tsallaka ya ɗage labulen nan da kyau ya bi ɗakin da kallo, da su ɗin dake sha'anin su, warin ɗakin nasu in har ya shiga ya tabbata sai paralyse ta kama shi, har gashin hammata yake hange daga gefen hannun yarinyar