Showing 201001 words to 204000 words out of 397328 words
shagwaɓa Nabihat tace _" Mama ni gida zan zo, dan Allah ki kira maman su Manal ki ce mata kina nemana yanzu, ni kawai gidan nake so na bari wallahi na gaji."_
Da tausasawa tace mata _" Ki fara nutsuwa sannan ki gaya min abinda yake faruwa, kin san bana son iskancin banza ni za ki wani sakani gaba kina kuka."_
Ƙara fashewa ta yi da kuka tace _" To Mama ba Yaya AA bane, tunda na zo gidan nan fa ganin ma ban yi ba sai sau ɗaya..."_ Kaf abinda ya faru ta sanar da ita sannan ta ɗora da _Shiyasa nake so na bar gidan Mama, dan in ba haka ba zan iya kashe Abrar ɗin nan kowa ma ya huta, Mama ina tsoron Yaya AA ya dubi yarinyar nan tunda ta fi ni abubuwa dayawa sannan ita ƴar uwar sa ce ta jini, idan ba haka ba ta ya zai dinga yi mata murmushi yana kallon ta, ɗazu ma amsar saƙon shi na gani a wayar ta tana tambayar jikin musakin yaron nan, kuma fa ya bata amsa, amma ni na tura masa da saƙonni sun fi ashirin daga tafiyar shi zuwa yau, amma kamar ma bai san tsiyar da nake yi ba."_
Da irin jin haushin nan mahaifiyar ta tace mata _" Kuma shine za ki taho ki bar mata gidan? Dan kawai ki nuna mata ba zaki iya yaƙi da ita ba kenan? Wacece Abrar? Wacece uwar ta ma balle ita? Kinga saurareni Nabihat, ban turaki gidan nan dan ki je kina kirana kina faɗa min matsaltsalu bane, na tura ki ne dan ki cika mana burin mu da Yayar ki Fauziyya ta kasa cika mana, ki zauna a gidan babu inda za ki je, sannan ki jira dawowar sa dan ya zama naki ke kaɗai, ɗan sa ma ki nuna masa ƙauna a zahiri tunda haka yake so, da zaran kin zama matar sa kina ɗaukar ciki sai yadda kika ga damar yi da shi, dan na tabbata shi kan shi zai so ganin abinda za ki haifa, duk da wasu lokuta yaran dake zuwa da matsala sun fi shiga ran iyaye, amma wannan karan labari zai canza daga sanda kika samu cikin Aswan, kin fahimce ni?"_
A shagwaɓe Nabihat tace _" To ni Mama ya zan masa? Ba fa ya zuwa gidan sai da sassafe, kuma ba kai tsaye yake shigowa ta babban falon da zamu iya ganin shi ba sai kace wani saraki, da dare kuma wani lokaci ma sai munyi bacci yake zuwa, gidan sa kuma ko ƙannen sa ba sa zuwa."_
Taɓe baki tayi kamar suna kallon juna tace _" Kinga yanzu Abban ki yana kirana, kashe zan ɗaga kiran nashi sai na sake kiran ki, ni nan zan gaya miki yadda zakiyi ki jawo hankalin sa gare ki, yo kina mace har ya nuna miki jan aji?"_
Amsawa Nabihat ta yi tana kashe kiran ta zauna zaman jiran sake kiran daga mahaihiyar ta dan ta ji ta inda za ta farmaki AA sannan ta yaƙi Abrar duk a lokaci ɗaya.
Har Nabihat ta cire rai da Maman za ta sake kiran ta sai kuma ga kira a daren nan, tana ɗauka da murnar ta da shewar ta ta shiga faɗin _"Ke albishirin ki?"_
Jiki a sanyaye har tana aikawa bango harara ta amsa da _" Mama bana yanayin daɗi fa kin sani."_
Dariya Maman ta ƙyalƙyale da ita tace _" Ba dai Aswan ne matsalar ki ba?"_
Shiru Nabihat ta yi dan sai take jin kamar Maman ma ta ɗauki matsalar ta a shirme, dan haka maman ta mata tsawa da cewa _" Ke amsa min mana, ba dai shine matsalar ba? To kwantar da hankalin ki yarinya kin samu Aswan."_
A gajarce ta furta _" Ta ya ya Mama?"_
Nan ta labarta mata abinda Chef ya sanar da ita, dan da ya kira ya ɗan fara tsegunta mata ne tsabar farin ciki sannan ya ce ta jira ya ƙaraso gida, yana zuwa suka shiga zantawa shine fa ita saida ma ta gama kiran ƙawayen ta tana shaida musu da wasu daga cikin ƴan uwa cewa fa to ƴar su ta yi babban kamun da za ta cire su a kunya, dan haka kowa ya shirya da kyau kula ba dogon lokaci za'a saka ba, masu farin ciki har zuciya sun yi, masu baƙin ciki kuma daga zuciyar su suma sun yi yayin da suka bayyana farin cikin akan laɓunan su.
Nabihat saida ta ji kamar za ta suma dan farin ciki, ta aniya tsalle a ɗakin ta sai dai bata ui ihun da kowa zai ji ta ba, nan suka dinga kitsawa suna warwarewa ita da uwar da alwashin yadda za'a muzgunawa Abrar ta gane ruwa ba sa'an kwando bane, sun jima suna waya har da faɗan _"Yawwa Mama, kinga dama na nuna miki kayan ɗakin Bushra nace miki irin su nake so, yanzu sai a min su ko?"_
A tsawace uwar tace _" Ke tafi can mahaukaciya, ana maganar auren ki da babban ɗa ga Aliyu Anza, kina wani maganar banzayen kayan ƙawar ki? Wacece Bushra? Nawa kayan nata suke gaba ɗaya? Nabihat, darajar ki yanzu ta kai a zuba miki kayan da suka ba wa milyan goma baya, idan ɗaki ashirin ne a gidan Aswan, to ni nan zan siyar da duk kadarata a haɗa da na mahaifin ki a cireki kunya, an faɗa miki Aswan ɗin wasa ne? To ko iya noma da kiwo da yaron nan ya saka a gaba sun ishe ku rayuwa, kina dai gani, mahaifin ki duk abinda ya shafi kayan marmari ba ya siyan shi sai dai a je a ciro komai a lambun shi, arzikin da yake samu ta shanu, raƙuma, awaki da tsintsaye da su kifi kuwa Allah kaɗai ya san adadin shi, bar maganar wasu sabgogin nashi da basu san gaban su ba ma, dan haka ki shiga hankalin ki bana son buru'uba."_
Daga haka Maman ta kashe kiran tana jan tsaki dan ran ta ya ɓace ita ba kaɗan ba, yo ban da aikin banza wacece wata Bushra? Uban ta fa ma'aikacin banki ne, uwar ta kuma malamar asibiti, shine take ganin an mata fitatta anan? Yo me aka mata idan aka haɗa da ita wanda take da burin yi yanzu idan auren Nabihat ya tashi da Aswan, ai biki ne take so ta yi na kece raini da fitowa cikin tsara, takaici da baƙin cikin da Yayar ta Fauziyya ta saka musu duk sai sun huce shi a bikin Nabihat.
*U.S*
Duk da kwanan yaran biyu ne amma sun saba suk safe ya kan buga ƙofar su su gaisa, wani lokacin ya tafi asibiti shi kaɗai sai da yamma ko dare ya ɗauke su suje suma, sannan ba sa kwantawa bai tabbatar sun kwanta lafiya lau ba. Amma sai suka wayi gari yau shiru babu motsin shi babu alamar sa, Yusrah ce kaɗai abun ya dama, dan ko ba zai tafi asibiti da ita ba tun kafin ma yaran su zo ya kan leƙo ne ya datsa mata maganar da ranta zai ɓace irin su kar ki fita a gari ki ɓace ki sakani haukan neman ki, ko ki yi odern duk abinda kike so, amma kar ki ci abinda zai halakaki, ko saura ki je ki shiga ruwa dan kin hangi wasu na shiga, idan bindiga zakiyi ki fashe ba zan ciroki ba, dan ni bana harka da sanyi komai ƙanƙantar sa.
Abun kamar sabo sai ya zamana yau duk ta damu da rashin jin motsin na shi, kuma hankalin ta na kan ɗakin shi bata ji ya fita ba tun asuba da ta tashi, ta so tafiya ta bubbuga ta ga ko lafiya? Tunda shi ɗin ya kasance rainon carfet ne rarrafe tiles ba wani ƙarko a jiki, abu kaɗan ya kwanta ba lafiya saboda kawai jar fata ce sannan girman biscuit da indomie, amma kafin ta je ta buga ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofar su, da sauri ta sauke akan gado ta je ta buɗe ƙofar bayan ta ga mai kula da ɗakin AA ɗin ne, ko gaisawa ba su yi ba ya faɗa mata ya buga ɗakin oga ne ya ji shiru sai ya shiga dan kar a zo ko bai da lafiya ne, shine ya same shi kamar dai ranar da zazzaɓi a jikin shi, shin za ta duba shi ko ya kira likita?
Da hanzari ta sanar masa za ta duba shi sannan ta dawo ɗakin ta ɗauki jakar ta mai magunguna ta ja yaran suka fice dan kar ta barsu su kaɗai, kai tsaye suka shiga ɗakin nashi Yusrah na ƙare masa kallo akan gado, amma ko da ta ga jikin shi ba ya rawa kamar ranar sannan ba ya wannan nishin ta san ba lallai irin zazzaɓin ranar bane. Wani coffre dake gefen gadon ta jawo ta zauna tasa yaran suka zauna kan sofa ɗin dake ɗakin suna kallon shi da tausayawa dan fuskar shi a fili take, abun auna zafi ta fara cirowa dan ta auna, ta kama zanin rufar ta ja za ta taimaka mishi dan ya saka ta gane zafin AA ya wurgo mata idanuwan shi da suka yi jajir sosai fiye da ranar.
Hakan bai tsorata ta sai kawai ta sake zura hannu za ta taɓa nashi, da wani irin ƙarfi ya riƙe yatsun ta uku sannan ya sake ƙura mata idanu, a matuƙar wahalce cikin jin haushin za ta ƙara kunna shi bayan kuma mace ce matsalar da tsawa tsawa yace "Leave me alone, please, get out."
Ɗan jawo hannun ta tayi dan ta ƙwace, amma ta ji ya riƙe ta gam da ƙarfi, fizge hannun ta yi da ƙarfi tana faɗin "Malam taimaka maka kawai zan yi, dole sai na auna zafin sannan na sake duba zazzaɓin me ka ke yi."
Rintse idanu ya yi yana yunƙurin tashi zaune yace "Saboda ke wacece? Uwata Anna? Malama ki fitar min a ɗaki nace...!"
Yadda ya sake yin tsawar ya sa su Anna ƙarama miƙewa da sauri, Yusrah kuma karon farko a tarayyar ta da shi da taji tsawar sa da ɓacin ran sa ba'a bakin komai ba, kawai ta rasa dalilin da ya sa yaji a yau za'a fara likitar da zata tursasa mutum dan ta masa magani.
Hawayen da suka ɓalle mata da ta rasa ko na me ye tasa tafin hannu ta share, da irin saurin nan na ɓacin rai ta mayar da abun awon zafin ta ɗauko kwalin abun ɗaukar jini, da ma taso hutar da shi ne ta hanyar auna zafin a sauƙaƙe anan, amma abun ɗaukar jinin babba ne da har zafin zai nuna mata, kai har ciwon sugar yana nunawa kawai ta buɗe kwalin da sauri hawaye kuma na gangaro mata da ita kan ta tasan ba na tsawar da ya mata bane, dan ya mata fiye da haka, sannan ba na ya mata gaban su Uka bane, ya tozarta ta ma a gaban dubannin al'uma, kawai dai... Kawai dai irin yanayin nan take ji na wani naka haka sosai ba lafiyar nan kai kuma ka damu sosai, shiyasa ma har take jin yau za ta ƙurewa taurin kansa gudu, zai gane wallahi ita ma renon zamani ce.
AA na kallon ta bayan ya daidaita zaman shi da takaici ganin bata da niyyar tashi sai ma wasu tarikitai da take cirowa daga jaka, amma dan ya ga iya gudun ruwan ta sai yake ta hararen ta dan ya ga me za ta yi to? Ai kuwa bai tamtamce ba ya ji Yusrah ta fizgo yatsar ta tsakiya doguwa da ya aje hannun kan gado yana ɗan yatsina baki da jin haushin sun hana shi ya yi ta juye juyen shi a gado har babbar masarautar taga damar shafa masa lafiya. Kafin ya farga ta daidaita yatsar ta soka tsinin ƴar allurar nan tana jan majina tana kuma magana da faɗa faɗa "Idan ba ka damu da lafiyar ka ba ai ka damu da wanda suke tare sa kai, ba za ka barni da kula da yara ba sannan ka kwanta ba lafiya, idan aka bigeni aka ɗauke su kuma ni ce abar tuhuma ko? Gwara a ce *ni na mutu* amma *kai ka rayu* dan nasan za ka sada duka yaran nan da gida in sha Allah."
Sai kuma ta yi ƙasa ƙasa da murya sosai tace" A yi mutum sai taurin kai kamar ba'a riski islama ba."
Duk fa tana faɗan ne tana matse yatsar sa har jini ya ɗasu a inda take da buƙata ga abun awon sannan ta shiga zubawa abun idanu tana jiran sakamako... *Lallai* Yusrah ta kafa masa tarihin da babu wani mahaluki da ya taɓa kafa masa a rayuwa, ko Aba bai taɓa kiran sa da mai taurin kai ba haka dai kai tsaye, sai dai ya ce masa ka daina rigima, ko ka bar kafiya jikan Anza, uwa uba kuma Anna ita ma bata taɓa ba, amma yau wata ƴar yarinya tsaran su Manal tana gaban shi tana kuma faɗa masa sai taurin kai, bayan haka tana nuna masa fin ƙarfi wajen yi masa abinda ya mata tsawa ya ce ba ya so? *Wacece ita*? *Me ya sa bata tsoron sa*? Me kuma ya sa *bai ji ransa ya sake ɓaci ba*???
Zuba mata idanun da ya yi yana wannan tunanin ya sa har Yusrah ta gama haɗa allurar da ta dace da zafin jikin shi ta soka masa ita a damtsen shi bai ma sani ba, sai da ya ji zafin ne a bazata ya ɗan lumshe idanu ya furta "Shhhhhh."
Wannan yajin da ya ja yasa ta ɗaga idanuwan ta ta dube shi har lokacin hawaye take yi da ya saka shi tsurawa idanun nata idanu yana so ya ji kukan me take to? Bayan shi aka ma allura, amma sai yaji muryar ta cikin yanayin kuka sosai ta furta masa" Sorry, shikenan."
Tana gama tattara kayan ba tare da ta dubi fuskar shi ba ta miƙe tsaye tana kama zanin rufar tace" Oya kwanta, nan da minti goma zazzɓin zai sauka in sha Allah, sannan ka daina duk wani abu da ka san yana jawo maka zazzaɓin nan."
Bai kwanta ɗin ba sai dai binta da idanu kawai ya rasa gane me yake ji game da umarnin da take ta bashi kamar wata uwatai, dan haka ta ɗan ja zanin ta rufa masa har kusan ƙirjin sa sannan ta juya inda su Uku suke zazzaune suna kallon su ita ma ta zauna amma ta ƙi haɗa idanu da shi.
Ita dai bata sake kallon shi ba har sai da ta ji kamar numfashin shi na fita irin dai mutum bacci yake yi, tana kallon in da yake ta ga e baccin yake a zaunen nan, girgiza kai ta yi kawai ta taso ta ɗan saka yatsu biyu a goshin shi ta ji babu zafi sai ma gumi da yake tsatsafo masa, komawa ta yi ta zauna tare da kunna acn da ke kashe tun shigowar su tana kallon su Anna ƙarama dake game da wayar ta.
Daga nan zaune ita ma baccin ya ɗauke ta saboda tun asuba da ta farka bata koma ba, har mai kula da ɗakin ya kawo abinci sai Uka ce ta buɗe sannan ta rufe da ya fita amma daga shi har Yusrah ba wanda ya san an yi...
Awa ɗaya da rabi suka kwashe a ɗakin nan ba wanda ya farkar da su sai da shi zaman ya ishe shi sannan ya farka yana dafe wuyan shi da ya ji ya masa sanyi sosai, kan su Uka ya fara sauke duban shi, sannan ita ma data ɗora kan ta a hannun sofar tana ta sharar bacci har kallabin rigar ta ya faɗi a saman wuyan ta. Ya so tashi dan ya shiga ban ɗaki, amma dake wandon sa gajere ne ko yaran ba zai so su gan shi haka ba bare kuma wannan mai shirin zama uwar tasa da ta wani tsare shi a ɗaki kamar jariri, sai ya dubi Uka cikin muryar bacci yace "Baby, ku tashi auntyn ku ta je ta kwanta."
Da gimamawa Uka ta amsa sannan ta shiga daddaɓa Yusrah a nutse, tana farkawa da sauri ta tashi zaune tana zare idanu tare da kallon inda marar lafiyan ta yake, suna haɗa ido sai ta kawar da kai tana miƙewa tsaye haɗe da jawo kallabin ta gaba tana rufe gashin ta da ya ƙurawa idanu yana ayyana _"Kaga jaraba ya yaran yau ko? Wato zaman ta da Intisar ne zai saka ta ƙare-ƙaren gashi na banza, mtsssss!"_
Inda yake ta nufo ta ɗauki jakar ta tana kallon fuskar shi, yatsu ta sake kaiwa ta saman goshin shi ta taɓa, da kallo kawai ya bita tunda dai ta zame masa kutuwar uwa zama da ita dole, to wannan idan ya yi wasa ma sai ta tsinke fuskar sa da tafi, tunda lamari na masu jinnu mata ma sai ta daki mijinta ai a rashin sani, bare shi ƙaton banza da ba wani tsoron sa take ji ba, hmmmm! Wannan tafiya, wannan tafiya shi kam ai ba zai manta da ita ba, ko yana manta wasu tafiyoyin ban da wannan *WATA TAFIYA* da godiya kawai zai yi ga Allahn da ya halicce sa.
Ba ta ce masa ƙala ba ta ja yaran suka fice daga ɗakin shi ma ya miƙe ya shige ban ɗaki cike da ɗauran niyya ba zai sake yin wankan daren nan ba kuma ya kunna ac, dole sai dai ya yi ɗaya gaskiya, in ba haka ba aure zai kama shi a satin nan, shi kuma bai shirya ba.
*Kwanci* tashi har kwanakin da suka ɗibo suka ƙare, kuma Alhamdulillah sosai ake ganin sauƙi a tare da Safwan har ya zamo gobe zasu juya gida shi yasa yau tunda Yusrah ta zo take ciki tare da likitansa yana yi mata dukkan bayanan da ya dace a kan kula da lafiyar Safwan tun daga nan har zuwansu gida da tsayin wata ɗaya da ya bada idan bai miƙe yana yawonsa ko ina ba dole za'a dawo da shi, in dai an bashi dukkan kular da ta dace.
Zuwa yanzu da kansa yake ɗaga kansa