Showing 387001 words to 390000 words out of 397328 words

Chapter 130 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70015

lafiya ai ba na jawo abinda zai ɗaga mata hankali ba."

Ƙasa da sama ya sake kallon ta sannan ya ɗauke kai yace "Idan kika saie cewa maman ki in ban kirata ba yanzu ta zo nan na mata gashin rana ba ki ce har yanzu Anza bai rasu ba."

Dariya ta yi amma ba ta ce komai ba dan kar ta jawa aunty Intisar, in dama ace bata zo ƙasar bane dan bikin ƙannan ta da sai ta ƙalubalance shi dan ta san ai ba za'a goyi da bayan shi kan ta zo ƙasar ba, dan haka ta canza shawara gwara ta bishi da irin salon shi kafin ta jawo ra'ayin sa gare ta ya manta da abinda yake damun shi.

Duban shi ta sake yi a tausashe tace "Rohi, ba dai siyo indomie ka yi a dafe ba? Bayan kuma akwai a gida."

A hankali ya ɗago ya jingina a kujerar dake bayan shi ya zuba mata idanun shi yace "Dan akwai, shiyasa na dafa da kaina."

Daga yadda ya mata magana da yadda ta ga fuskar shi ya nuna mata ƙiris yake jira ya goranta mata, sai kawai ta basar ta saki murmushi tace "Ayya, ka yi ƙoƙari, ashe ka iya girki? Shine ba ka taɓa yi min ba?"

Ɗan kawar da kai ya yi yana shafa ƙeyar shi yana ayyana _'Kai! Wato maza za'a ƙure? Dan an ga ba fannin da suka ƙware bane?'_

Basarwa ya yi shima ya ɗan turɓune fuska ba tare da ya kalle ta ba yace" Yanzu ma sai a girka miki ai, me ye a ciki dan ka dafawa wanda ya kamata ace shine ya baka kake ci?"

"Tooo." Ta faɗa tana ajiye jakar ta gefeb ta a hankali ta sauko daga kan kujerar ta rarrafa kusan shi ta kai hannu za ta ɗauki plate ɗin gaban shi, da sauri ya ɗauke plate ɗin yana sakar mata wani kallon bangane ba, hakan ya sa tace "A'a, ɗanɗanawa fa kawai zan yi AA."

Girgiza kai ya yi a tsaurare yace "Ga hanyar madafar can..." Ya faɗa yana nuna mata tare da ɗorawa da "Babu abinda babu a ciki, da indomien, da albasar, da tarugun, da jajjagen, har ma da kazar akwai a fridge."

Gyara zama ta yi tana duban shi tace "Ina ce dai duka abinda ka lissafa a gidana suke, kuma mallakina ne? Sannan ita ma kazar ai ni na soya abata kafin na fita...kuma ma wallahi Haidar ne ya ji yana sha'awar indomien."

Kallon fuskarta ya yi da niyyar ƙwalla mata harara idan ya so ɗan Anza ya sa a rufe shi na kwanaki, amma dake shi mutumin kirki ne, shi ɗin bawan Allah ne na gari, yana da zuciya ne irin wacce ake so bawa ya kasance da ita, suna haɗa idanu da ta mishi takwaf takwaf da fuskar nan ta ta irin ta waɗanda ba ruwan su, wallahi sai yanzu wani irin tausayin baiwar Allahn nan ya kama shi, take ma ya ji duniyar ta fice masa a rai idan har bai ba wa wannan ƴar yarinya indomie ta ci ba, me ye a ciki dan ya dafa? Shin wata nawa ta kwashe tana masa girki yana sharɓa? Ta ciyar da shi ta ciyar da ƴaƴan shi? Kai jama'a me ye duniyar? Y. Turaki ce fa, ba ruwan ta ai.

Dan kar ta ɗauka ko tsoron ta ne ya sa zai bata sai da ya ɗauke kai yana wani harare harare sannan ya turo mata plate ɗin gaban ta yana faɗin "Karɓi ki ci, kuma mu ai imani gadon shi mukayi, ko ba'a yi wa jinin Haidar sharri ba zan iya sadaukar da indomie ai."

Dariya ta yi tana girgiza kai, ba dan tana jin yunwa ba sai dan yadda ta ga ya dafa indomien da ruwa sosai ne ya birge ta kawai za ta ci, gyara zama ta yi kam sosai ta zare zif ɗin siket ɗin ta da yanzu ma ta daina sakawa, fitar nan ce ta yau kaɗai ta sa ta saka shi sannan ta ɗebo lomar farko za ta kai baki ita ma ta maida mishi magana da cewa "Idan ma ba da zuciya ɗaya aka bamu ba ci zamuyi, kuma mu ma ai mun gaji imanin a wurin kakanin mu, tunda har muka iya yafe kwanan da aka ja mana a cell ba tare da mun yi laifin komai ba."

Kallon ta ya yi, amma sai bai ce komai ba ya taɓe baki yana rayawa a ran shi _'Da ace Chef bai sa aka ƙara ƙaramin matsayi ba da ba abinda zai hana mu daku dake a gidan nan, amma ni yanzu ba sa'an ki bane, wallahi dokina ma ya isheki wa'azi ai.'_

Ci ta yi sosai amma ban da naman dan ko lasawa ba ta yi ba, kamar yadda ɗazu sha'awa ta sa ta gyarashi amma ya fita a ranta, haka yanzu ma bata ji tana son ci ba kawai ta miƙe ƙafafun ta tana yin zama sosai na masu ciki, filon kujerar ta ɗauko ta aje bayan ta yadda za ta jingina da kyau sannan ta saɓule rigar ta saboda wata zufa dake ta karyo mata bayan gama cin abincin, hakan ya sa saida ta yi ƙasa da rigar gaba ɗaya har ta zo kan ƙugun ta saboda gaba ɗaya ta ji kayan suna takura ta.

Hakan ya sa saman ta ya rage daga cikin ta da ya fito tana ta shafa shi sai bleu ɗin bras ɗin ta data mata kyau a jiki ta fito da fatar ta, sanyin acn da ya fara ratsa ko ina na jikin ta yasa ta shiga lumshe idanuwa tana faɗin "Alhamdulillah kasiran, Allah ka bamu na gobe."

A ɗan hassalen nan ya juyo da niyyar ce mata "Idan kin dafa ne za ki ci gobe."

Amma sai ya sauke duban shi kan ƙirjin ta, a hankali kuma zuwa cikin ta, ya ɗauki kusan sakan goma yana kallon su yana taune leɓe, sai kuma ya ɗan ƙyabta idanun shi tare da sunkuyar da kai, a hankali ya shiga faɗawa kan shi _'Ita duniya ai ƴar haƙuri ce jikan Anza, matsayin ka na babba sai kana haƙuri da yara, idan ka duba ai ita ma ƴar ka ce ta wani fannin ko? Sannan ta tabbata mata na shiga halin aikata wauta idan suna da juna biyu, dan haka komai aka maka ka yafe jikan Anza, da izinin Allah ladar za ta tabbata gare ka ta haƙuri da ka yi.'_

Da sauri ya ɗauko ruwa masu sanyin dake gefen shi ya buɗe bidon ya ɗan rarrafo ya miƙo mata yana faɗin "Sha budurwata, ni wallahi tun ɗazu ma wani duru-duru nake gani ko shaida mutanen dake tsaye kaina bana yi, Allah ya sa dai ban miki ba daidai ba ko?"

Karɓan ruwan tayi tana son hana kanta dariya tare da matse fuska sosai ta aje ruwan gefe tace "Alhamdulillah, idan na tashi zan ɗauko da kaina."

Gyara zaman shi ya yi sosai kusan ta tare da saka hannayen shi biyu yana tausa mata ƙafafu sannu sannu yana cewa "Sannu, me da me Anna ta saka ki yau? Amma dai gobe za ki huta ba zaki fita ba ko?"

Ɗan janye ƙafa ɗayan ta yi tace "Ka barshi fa na gode, fita kam ai gobe ma wajibi ce."

A hankali kuma ya fara shafa cikin ta har ya yi nasarar yin sama da shi ya fara murza su, a sanyaye ta ture hannun shi tana yunƙurin tashi tana cewa "Akan indomie me ye ba'a gaya min ba? Yau kowa ya kwana a gadon shi."

A ran shi ya ayyana _'In kin isa Allah gafarta min, akan me? Ai yanzu aikin soja ma a shirye nake da na ajiye shi akan na raba shinfiɗa dake *uwar Aliyu*.'_

A zahiri kuma sai ya riƙe hannun ta yana jawo wayar shi yace" Tsaya ki ji bab, Billahillazi Arif ne shaidata kan yau bana hayyacina, tsaya ki ji daga bakin shi..."

Arif na ɗaga kiran kafin AA ya yi magana yace _"A'uzubillah! Oga yau kuma sheɗanun club suka kai ka? In ce kana da babban speaker a gi..."_

Da sauri AA ya katse shi da cewa _" Kai dallah dakata! Ka faɗi gaskiya tsakanin ka da Allah yau ba hayaƙin wiwi muka shaƙa a layin ƴan tasha ba da naje kamo wani zan masa warning?"_

Arif ya yi shiru bai fahimci zancen shi ba yace _" Oga in dai kai ne kullum ba'a cikin shaƙar ta kake ba?"_

Yusrah ya kalla dake ta ɓoye dariyar ta ya sake cewa Arif _" Kai banza ne, to tsakanin ka da Allah yau ban maka gulmar Y. Turaki ba? Na ce maka saliha ce ita kuma mumina sannan uwar marayu, ko ban faɗi haka a kan ta ba yau?"_

Take Arif ya gano me yake faruwa, ai kuwa ɗan ƙarawa aya zaƙi sai ya kashe murya yace _" Tabbas, har raina ya ɓace nace matar ka tafi tawa ne? To ai kai oga ma ba'a haɗuwa baka yabi aunty Yussy ba, ai ka faɗi ka ƙara ba uwar marayu bace kaɗai, mai uwar ma ita ce gatan sa."_

Ƙitt! Ya yanke kiran tare da kawota ya zaunar kan cinyar shi yana ci gaba da shafa ƴan biyun shi yace" Kin ji ko? Haba my lady, wai ni me ma ya haɗamu ne yau?"

Kallon shi ta yi a marairaice ta shafo kumatun shi cikin wani irin salo tace" Muje ko?"

A hankali ya gyaɗ mata kai yana sumbatar ƙirjin ta yace" Umm, ban san me ya sa ba kya isata ba?"

Murmushi ta yi bata amsa mishi ba sai ƙoƙarin haɗa bakinta da nashi da take yi, dan a haka mijin ta ya hore ta, kuma an yi sa'a tana karɓan karatun shi sala-sala, wataƙila ko a gaba, amma cikin ta baya bata matsala ta wannan fannin, duk da yanzu girman shi ya sa dole wani abun suke haƙura da shi, amma dai ita ma bata jin wai bata ra'ayin shi a yanzu dai kam.


*BAYAN KWANA BIYU*


Cikin hukuncin Allah aka ɗaura auren ƴan matan uku kowace ta tare a ɗakin ta a gida mabambamta juna, sai dai Manal za su zauna na sati ɗaya ne sai ya ɗauketa zuwa inda yake karatun shi kafin ya kammala a shekarar, anyi hidima ta gani ta kuma bugawa a mujalla, daga amaren har angayen kowa ya sha kyau har ya gaji, inda kowace amarya ta dace da nata angon da tun a wajen shagulgula suke nuna musu zallar tuzuranci da haukan gaurantaka, musamman ma uncle Sul da Mukhtar da idan sukayi wani abun sai AA ya kalle su ya taɓe baki yace "Kun ji kunya wallahi, kun auri ƙananan yara kuna musu iskanci."

Uncle Sul dariya yake yi yace "Kura ake ramawa aniyar ta."

Inda Mukhtar ke maida martani da "Daga na gabanmu muka gani muka koya, ai sawun ka muke ba *ya babba*."

Arif ne ke musu alƙalanci, wani zubin ya goyi bayan angayen ta hanyar faɗin "Ku ai nafila ma kuke yi, oga fa farilla yake aikatawa."

Wani lokacin kuma ya koma bayan AA ta hanyar cewa "To shi ai ba sa'an ku bane, kuma aunty Yussy ba tsaran matan ku bace, dan haka harkan su ta manya ce."

Su dai babu mai kula shi har sanda aka gama komai aka fara haramar ɗaukar amare zuwa gidan su, fir ya ce babu inda za shi wallahi, gandandan da shi zai wani je ɗakin ƙannan shi? Mukhtar kuwa ya dage ai ko ba bashi akwai rankon tafiya, dan haka shima sai ya raka masa amaryar sa har gida yadda ya raka tashi, daga ƙarshe dai ya kaɗe kai yana gyara zama yace "Ko Anza kuka taso ba zai tasheni daga nan ba, idan kuma cikin ku akwai wanda ya isa to bismillah."

Cike da shaƙiyanci Arif ya dafa kafaɗar Mukhtar yace "Yallaɓai Anza ai babba ne, Allah dai ya jiƙan shi da rahama, amma ga aunty Yussy, kira ɗaya da ta maka fa yanzu za ka je a dolen ka."

Sheƙeƙe ya dube shi yace "Ai tsoron ta ka ga ina yi ko?"

Girgiza mishi kai ya yi yace "A'a, amma dai tana da abunda kake so a tare da ita, kuma dole muke musu biyayya idan har muna son kyautatuwar dararen mu."

Harara ya galla mishi yace "Ka kirata ka ce ta daina bani, shekara nawa ina rayuwa babu abun? Me ya sameni? Ɗan Annar sa fa ne ni da kake gani, shekara biyu ta yi tana shayar da ni, shiyasa nake da ƙarko."

Ashe duk hirar nan da suke uncle Sul ya kira lambar Yusrah, tana ɗagawa sai ji sukayi yace" Ƴata, nace har kun shirya ne?"

Yusrah da bata san ya saka ta a speaker ba ta amsa da" E uncle, da wani abun da kuke so?"

Murmushi ya yi yace" A'a ba komai ƴar albarka, amma dai Abrar za ki raka ko? Saboda mijin ki ma can zai nufa saboda kusan ita ce a hamɓare."

A sanyaye Yusrah tace" E uncle, ai da ni da aunty Intisar gidan Abrar muka nufa in sha Allah."

Amsa mata ya yi da" To shikenan, sai anjima."

Yana kashe wayar ya kalli AA da ke kallon shi ƙasa ƙasa, irin kallon da wataƙila da sun jima tare da shi da ya gane ma'anar kallon, amma sai bai fahimci komai ba ya dubi su Mukhtar yace" Ku wuce mu tafi, ƴata dai za ta nufi gidan matar Mukhtar ne, kuma naga yau kwalliya ta caɓa ga mayafi da ta ɗora, tubarkallah ta fito sak kamar ita ma Annarmu ce ta haife ta."

Duk juyawa sukayi suna barin falon nashi na tsohon gidan shi da sukayi zaman bikin su anan, amma har lokacin bai daina yi wa uncle Sul wannan kallon ba, saida suka fita daga ɗakin ya gyara zaman shi ya maka musu harara dukan su yace" Ka ji kunya wallahi Sulaiman, kana uba amma kana lalata tarbiyyar ƴar ka, to ta tafi mana sai me? Ba inda zan je."

Wayar shi ya zaro daga aljihu ya fara dannawa, sai kuma ya yi cak ya kafe wayar da idanu, ya ɗan ɗauki sakanni yana tunani sai kawai ya miƙe da sauri tare da zaran hular shi da makullin mota ya soka wayar aljihu ya nufi ƙofa yana faɗin" Ka ji haushi Sulaiman, hutun da maraya zai samu ne ka ke hassada da shi? Allah ya shirya ku kai da mahaukaciyar ƴar ka da ke biye maka."

Ba dan ya so ba ya bisu wannan raka amarya wanda sam Yusrah bata ji daɗin haka ba, dan kowa dake wajen indai har ya shiga ɗakin Abrar to ya shaida Aswan Aliyu mijin Yusrah ne, ya kuma gane girman ta da darajar ta a gun shi, sannan ya fahimci tsananin kishin sa akan matar sa, dan kowane motsin ta akan idanun shi ne, kowane juyawar ta a kusa da jikin shi take, bai yarda sun yi nisa da ita ba, yana riƙe da hannun ta ne duk inda ta ce za ta nufa yana biye da ita, da ma ta kyaɓe fuska ta kalli aunty Intisar tace "Aunty Into, dan Allah ki masa magana..."

Wangale baki aunty Intisar tayi da mamakin ya Yusrah za ta mata haka mana? Wane irin ta masa magana kuma? Sai kawai ta ɗaga idanun ta da nufin ta kalle shi tace _"Shareta kawai Akhi, ai matar ka ce."_

Sai dai tuni ta makaro, dan bai ma gane kallon me aunty Intisar ta masa ba ya wurga mata harara ba tare da ya duba tsohon cikin jikin ta ba yace" Na...zan ci uw..."

Da sauri Yusrah ta rufe mishi baki, hakan ya sa ya maida jan kallon ga fuskar ta cike da gargaɗin wallahi da Intisar ɗin, da mijin Intisar ɗin Mubarak, kai har ma da angon duk sai ya haɗa ya nannarka musu ba daɗi, dan haka ki kiyaye.

Aunty Intisar ma kallon kin kyauta min ta bita da shi tare da yin gaba ta bar su tana ayyana _'Ai ba dole sai da ke zan yi ta yawo ba, haka kawai ya zane ni da tsohon cikina, alhalin mijina haƙƙin sa ma na kwanciya ya yafe min ya ce har sai na haihu, haba.'_

Basu bar gidan Abrar ba saida suka yi faɗa shi da ita, dan kuwa duk sanda ya zo zasuyi hannun riga da uncle Sul saboda sai sun gama da gidan Abrar zasu wuce gidan shi, haka kawai sai ya harare shi yace masa "Ka ji kunya kai kam."

Sau uku aka yi haka, shine fa ta tambaye shi wai kunyar me kawun ta ya ji? Kawun ta ne fa? Ƙanin mahaifin ta? Ya zai dinga raina mata uba a gaban ta kuma? Haka dai sukayi ta muzurai ita da shi amma bai saki hannun ta ba, haka ya hana ta zuwa gidan Manal da ta so wucewa daga nan tare da su ya kwasheta sukayi gida.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*99*



Yau da gobe kayan Allah, kwana tashi har yau cikin Yusrah ya shiga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login