Showing 24001 words to 27000 words out of 397328 words
masa wannan, amma ace hakan bai ishe su ba, sai kuma ana wawurar kuɗin al'umma ana basu? Shin idan suka ce musu Allah ya isa, ana ganin ba za ta kama su bane?
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*8*
Cike da jimami da sanyin jiki Yusrah ta wuce wurin zaman su, Ustaz ne ta samu yana auna nauyin mata masu ciki da kuma dp ɗin su, zaunen da tayi ta dafe kai ba tare da ta karɓi aikin ba ya ba Ustaz tabbacin ko dai bata jin daɗi, ko kuma akwai abinda ya faru, amma a ƙaramin sanin da ya ma Yusrah sam bata son zama babu aiki a asibitin nan, dake awo ne matan suka zo kuma ba wani yawa ne da su ba kasancewar asibitin kuɗi ce, hakan ya sa yana gama bawa kowace sakamakon da zasu kai gaba dan a ƙarasa musu awon ya zauna yana fuskantar ta.
Cike da kulawa yace "Malama Yusrah, lafiya dai? Ko baki da lafiya ne?"
A hankali ta ɗago kanta tana sauke numfashi, saida ta fara girgiza kai alamar a'a sannan ta ɗauke hannun ta daga saman kan ta tace "Ba komai ustaz, har ka gama ne?"
B tare da ya daina kallonta ba yace "Um, sai kuma na gaba."
Shiru tayi ba amsa, shi ma kuma ya ɗan yi shirun, sai dai yanayinta ya nuna masa akwai wani abu, ba haka take ba gaskiya, dan haka ya sake cewa "Yusrah, kamar akwai abinda yake damun ki ko? Kar ki bar damuwa a ran ki mana, ki tattauna da wani zaki samu sassauci."
Kallonshi tayi tare da zuba tagumi tana tunanin ta faɗa masa ko ta yi shiru, amma dake sun saba tattauna duk wata matsalar su da mahaifiyar su, sai kawai ta gyara zaman ta akan kujerar ƙarfen tana dubanshi tace" Ustaz ka gane? Wasu abubuwa ne suke ban mamaki a asibitin nan, kafin jiya waɗannan abubuwan sune a raina, amma basu taɓa ɗaga min hankali ba kasancewar nasan ko a makaranta ko a asibiti ko a kasuwa ko masana'anta, a ko ina ma aka tara mutane dole za ka ga abinda zai baka mamaki, dan ƙiri-ƙiri za ka ga wani yana tauye doka kuma ba mai taka masa birki, amma jiya..."
Numfashi ta sauke mai nauyi tana girgiza kai cike da ruɗu tace" Jiya sai naga abinda ya dame duk waɗanda nake gani, mata na daf da..."
Kamar wacce aka ba tsoro sai kuma tayi shiru tare da saurin jujjuyawa bayanta dan taga ko babu kowa, kafin ta sake kallon shi tana mai sassauta murya cikin raɗa tace" Matar fa na daf da haihuwa, kan ɗanta ya fara fitowa kawai aka ce wai ba za ta haihu ba sai dai a mata aiki, kuma ba fa daga ƙananan likitoci ba, daga babban Docter dan shi ya mata aikin ma, to kuma ɗazu ma haka ce ta sake faruwa, ita ma matar za ta iya haihuwa amma ya hanata numfasawa sannan ya kwantar mata da naƙuda har ya mata aiki, gaskiya ni shine na kasa fahimta."
Tunda ta fara magana Ustaz ke kallon ta, shi kam bai san ya zai ce mata ba yanzu, shi da ya rigata fara aiki anan ya san hakan na faruwa ba tun yanzu ba, dan haka yake jira ya wata takardar da ya tura ta neman aiki ta fito yana cikin masu samun nasara ya yi gaba, riƙon shi da addini da gemun da ya tsayar irin na sunna ya sa ake kiran shi ustaz, wannan dalilin ya sa shi kanshi har kunya yake ji a ce anan yake aiki, dan gaskiya akwai abubuwan kauce ƙa'ida sosai anan sai dai idan ka kawar da kan ka kawai.
Numfashi ya sauke yana ci gaba da kallon farar fuskarta yace "Malama Yusrah, abinda kika sani kenan kawai, kuma jiya kika fara gani, ki roƙi Allah ya sa iya abinda za ki gani kenan har ki bar asibitin nan, dan wasu abubuwan kan ki ba zai ɗauka ba."
Da matsanancin mamaki ta zaro idanu tace "Kana nufin wannan ɗin ba komai bane idan an haɗa da wasu abubuwan?"
Gyaɗa mata kai yayi alamar e, da sauri ta sosa gaban goshin ta da yatsa ɗaya bayan ta sauke ta sake cewa "Kuma haka zamu zuba idanu muna gani ana yanka matan mutane ba zamu ce komai ba?"
"Me za ki ce to?" Cewar Ustaz yana ƙureta da idanu, cikin sassauta murya yace "Yusrah kin san akan wa kike magana? Docter *Hamat Anza* fa, ɗiyan Anza dai kika sani ko da a labarai ne, ƙani ga Aliyu Anza da ko kokonto babu shekara biyu masu zuwa shi zai ɗane kujerar shugaban ƙasa, baya ga mahaukata kuma bijirarru sannan gawurtattun bilyoyin da ya tara, dan haka babu abinda ke ko wanin ki zai iya aikatawa, ki ja baki kawai kiyi shiru ki gama abinda ya kawo ki, kar ki manta hanya ce ta kawo ki asibitin nan bautar ƙasa, ba dan haka ba ai kema kin san asibitin gwamnati ake yi, idan ma ba zaki yi fatan samun aiki na dindindin ba, to ki gama wannan lafiya ki kama gaban ki kawai."
Yatsina fuska ta yi tana girgiza kai tace "Allah ya kyauta, to ko dai ita ma Sakina duk irin su? Dan na kula bata cika mayar da hankali akan aikinta ba idan ba mace ta ga an kawo haihuwa ba musamman idan suna da alamar kuɗi a tare da su."
Irin murmushin nan na yaro da babba ya mata yana ɗaukar alƙalamin gabanshi yace" Hmmm! Sakina ai kamasho take samu a kowane sufuri da motar ujila zatayi, sannan ga kuɗin da ake biyan ta wajen ajiye mahaifa (uwa)."
Zazzaro idanu Yusrah tayi cike da tsoro har da ɗan dafe ƙirji tace" Mahaifa? Kamar ya? Ban gane ba?"
Bayan ya faɗi maganar sannan ya tuna katoɓarar da ya yi, da ta jefo masa wannan tambayoyin kuma sai ya basar tare da miƙewa tsaye yana ɗaukar wasu abubuwan aiki yana cewa" Ammm... Malama Yusrah, ni zan je can sashen, akwai waɗanda zan duba, sai mun sake haɗuwa."
Da sauri Yusrah ta miƙe dan ta ƙara tambayar shi me yake nufi? Amma tuni Ustaz ya fice daga gurin dan ba zai yarda ta ji mutuwar sarki a bakin shi ba. Danƙari! Ya sake jefata wata cakwakiyar kuma, mahaifa? Kamar ya ita ke ajiye mahaifa ana biyan ta? Dama biya ake anan ana ajewa? Ita mahaifar da ba a asibiti ake tarawa sai a birne ba, daga bisani saboda lura ana cutuwa da haka sai ake ba wa mata suna rufewa a gida, a ina ma ake ajiye ta ɗin? Kuma me ya sa ake biya?
Dafe goshin ta ta sake yi tare da furta "Hasbunallah wani'imal wakil!"
Shigowar mata biyu riƙe da mai naƙuda da kuma wani saurayi daga bayan su yana waya yasa Yusrah miƙewa ta tarbe su, kama matashiyar tayi suka nufi ɗakin haihuwa tana tabbatar musu komai zai zo da sauƙi da izinin Allah.
Ko da suka shiga ciki ta saka safar hannu ta duba ta tabbatar haihuwa ce dan sai ruwa take zubarwa, fitowa ta yi ta karɓi katin matar a hannun surukar ta da yayar ta duk ta yi abinda ya kamata sannan ta koma kan ta bayan ta karɓi kayan da suka zo da su dan buƙata.
Wani iko na Allah Yusrah na komawa ɗakin haohuwar nan ta samu matar nan sai wani irin nishi take yi mai kama da kamar abin da ke cikin ta ya fara fitowa, da gudu ta ƙarasa saboda a lokacin matashiyar tana ɗan yawo ne dan kwal ɗin ta ya ƙara buɗewa, da sauri ta kamata tana faɗin "Sannu, kin fara jin nishi wanda k..."
Tana maganar ne tana ƙoƙarin mayar da ita kan gado, amma kafin ta gama tambayar ta sai matashiyar ta daddafe gadon tare da yin durƙushe, tabbas ba dubarar mace ke fito da yaro zuwa duniya ba, dan kuwa matashiyar nan haihuwa ce ta taho mata gadan gadan da babu tsumi babu dubara, ƙoƙarin taimaka mata Yusrah ta fara yi sai dai ina... Tana dubata jaririyar ta na shirin faɗowa ƙasan tiles, da mugun sauri mai tattare da mamaki Yusrah ta cabki yarinyar a hannayen ta tana kallon fuskar matashiyar da bata fi tsarar ba ko ma ta ɗan girme ta da shekara ɗaya ko biyu.
Wannan abu ya zama na farko da ya fara ba wa Yusrah mamaki, da zuwa asibiti da haihuwa ita kam a ɗan zaman da tayi nan bata gani ba sai yanzu, kuma ma yarinya wacce ko kokonto bata yi haihuwar farko ce. Da kulawa ta kwantar da matashiyar a ƙasan tiles ɗin dan bata san ya zatayi da su ba haka, sannan ta tattare rigar ta sama ta ɗora mata ƴar ta akan cikin ta kafin ta ɗauko abun yanke cibiya da sikelin da zata ɗora yarinyar, bayan ta gama hakane ta kira Mama unguwar-zoma wacce yanzu ita ce zata kula da matar ita kuma yarinyar har a tabbatar da lafiyar su.
Saida ta tura Mama ɗakin kafin ta fito ga ahalin matar bakin ta washe cike da murnar da take tamtama anya ba ta fito su? Da burin ace duk wacce ta zo da kanta ta haihu tace "Mama, albishirin ku?"
Da fara'ar jin haka duk suka zuba mata idanu sarakuwar tace "Goro fari ƴar nan."
Ba tare da murmushin fuskar ta ya ɗauke ba tace "Mama t..."
Daga bayan matar suka ji muryar saurayin nan yace "A'a Mama, goron ya kasance kyakyawa kamar dai wacce za ta faɗi albishir ɗin."
Duk kallon shi sukayi har da Yusrah da ta kalle shi tana haɗe fara'ar ta, irin kallon da yake mata na ƙurillar nan ɗauke da sahihin murmushi ya sa ta sake duban dattijuwar tace" Mama, ƴar ku ta haihu, ta samu ƴar ta mace, nan da awa ɗaya za'a kaita ɗakin hutu."
Farin ciki ne ya sake kaurewa tsakanin matan, yayin da saurayin kuma yake kallon Yusrah yace" Kin mana albishir mai daɗi malama likita, mun gode sosai."
Ba tare da fara'a ba tana kallonshi sama da ƙasa tace" Ba komai, aikina ne."
Sai kuma ta kalli matan tace" Zaku bamu sabon zane da za'a canza mata, da kuma wanda za'a saka jaririya ciki."
Da sauri dattijuwar ta juya inda kayan su suke, sai yayar mijin mai haihuwar da tace" Ƙanwata, dan Allah nace ko akwai ɗaki a sashen manya? Zamu fi so a kwantar da ita can kafin a sallame mu, tunda kinga la'asar ta fara gabatowa nasan sai gobe a sallame mu ko?"
Jinjina kai Yusrah tayi tace" Ba damuwa, ba za'a rasa ɗaki a V. I. P, sai dai kun san da ƴar tsada."
Maganar da ta yi tasa saurayin nan yin murmushi yana tsare bakinta da kallo mai birgewa, yayin da Yayar tace" Kar ki damu ƙanwata, wannan ba matsala bane, ni kaina anan ake ajiye ni idan na haihu."
Da ƙwarin guiwa ta sake gyaɗa mata kai alamar to sannan ta karɓi kayan ta juya, dattijuwar ce ta juya ta kalli saurayin tace" *Bilal*, ka kira Yayan naka ne?"
Wayar hannun shi ya nuno mata yace" Momma shine nake kira yanzu, yawwa ya ɗaga..."
Ya yi maganar yana ɗora wayar a kunne da cewa _" Hello Yaya *Marwan*, albishirin ka?"_
Amsa mishi aka yi daga can ɓangaren kafin da fara'a bakinshi har kunne yace _" Yaya Marwan, aunty *Zahra'u* ta haihu lafiya ta samu ƴar ta mace, to aban goron albishir ɗina?"_
Jim ya yi sai kuma ya sunkuyar da kai alamar girmamawa yace _" Godiya nake Yaya Marwan, Allah ƙara girma da arziƙi, Allah dawo da kai lafiya."_
Kashe wayar ya yi ya kalli Yayar shi yace" Aunty *Bilkisu*, idan Yaya Marwan ya turo min canjin nan zan baki jaka hamsin a ciki."
Zaro idanu tayi da murna tace" Kai Bilal, kuɗin da za ka iya bayar da jaka hamsin kake kira canji? Har nawa ya baka shi kam?"
Dariya ya yi yace" Sirri ne."
Haka suka ci gaba da murna inda Yusrah ma suke cin gaba da nasu aikin suma, kafin daga bisani Yusrah ta kawo takardar maganin da za'a siyo dan uwar ta kuma fito musu da ƴar dan lafiyar ta ƙalau.
A lokacin ne ta cike a littafin asibiti sunan wacce ta haihu da lokaci da adreshi, ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin ko za ta yi laifi a wurin likita? Dan doka ce kafin a duba mai haihuwa sai an sanar da shi, cike da wofantar da lamarin shi dan gaskiya tsarin sa bai mata ba ta nufi ofishin dan sanar da shi.
*AA ANZA*
Cikin wani ɗanyen yadi ya fito baƙi wulik da ya gama karɓan jikin sa, haɗe da takalmin shi ƙafa ciki baƙaƙe da ɗan golding ɗin tambayi (H) daga saman su, babu hula a kan shi dan haka molon shi ba ya ɓoyuwa, duk da ƙananan gashi ya fara tsirowa saboda dama jinsu na masu gashin nan ga kuma mai da ake ƙarawa da shi, hannun hagun shi ɗauke yake da agogo ta zallar azurfa da babu sirki a ciki, dama kuma mundun shi ya fi saka shi idan yana bakin aiki.
H colors ɗin crv honda ya shiga bayan ya gama sumbatar magunan shi da faɗa musu zai dawo, da ƙyar ya rabu da Meem dan ita ta fahimci shirin shi zai iya kaishi ga yin nesa da su, haka ya fice daga gidan yana kallon su bayan ya bar wa mai kula da gidan alhakin kula da su da komai ya nufi gidan su.
Kai tsaye yau ya samu ganin Dad ɗin a falon shi da bai fara shirin fita ba, Anna dake shirin fita a falon bayan ta miƙa masa shayin sa ya kalla yace "Anna, Humed fa?"
Da kulawa ta amsa shi da "Bai riga ya fita ba, na sa a turo maka shi ne?"
Da idanu ya amsa da e ta hanyar lumshe su a ladabce, ficewa ta yi shi kuma ya ƙara narkewa cikin kujera yana kallon Dad ɗin ƙasa ƙasa dake kallon shi shima yana wani murmushin gayya mai tattare da magana a cikin shi, ba wanda dai ya ce wa kowa komai dan sun riga da sun gaisa.
Ƙarar da wayar Dad ta yi ce tasa shi kallon wayar dake gabanshi saman ƙaramin table ya zura hannu ya ɗauka, a taƙaice AA ya ji ya amsa da _"E, ban fita ba."_
Jim ya yi sai kuma yace _" Ba damuwa, shigo, ina falona."_
Daga haka ya ajiye wayar, take kuma AA ya fahimci Goggonshi ce suka yi waya, dan haka ya ƙara gyara zaman shi yana jiran shigowar ta, ba jimawa ko ta buɗo ƙofa da sallama, ta ƙasan idanu a sakanni ƙalila ya gane irin adon dake jikin ta, ba abun mamaki bane, haka take kullum cikin kashewa jiki kuɗi, har ta ƙarasa ta zauna kujerar dake fuskantar Dad ta zauna, ba ta yi sallama ba, sai dai bayan ta zauna ta kalli Yayan nata tace "Barka da safiya Akhi?"
Da kulawa sosai ya dubeta yace "Barka, fita zakiyi?"
Gyaɗa kai ta fara yi, lokacin ne kuma AA cikin tsumammiyar murya yace "Ina kwana?"
Kallon inda yake tayi tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"
A taƙaice ya amsa da "Lafiya ƙalau."
Sai Dad da yace "Kin ce kina son ganina, da wata matsala ne?"
A hankali ta ɗan kalli sashen da AA ke zaune yana latsa wayar shi, sai kuma ta kalli Yayan nata irin kallon ka umarce shi ya bar nan mana, sai dai ta san ba zai iya ba, abinda ke haɗata da su kenan akan AA, wani lokaci sai ta ga kamar suna tsoron shi ma wallahi!
Kafin ta kai ga yin magana Humed ma ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin, shirun da aka yi ya sa ya ɗan buɗo ƙofar ya leƙo yana sallama, Dad ne ya amsa da fara'a suka gaisa da shi sosai, kusa da AA ya nufa yana ɗan rusunawa dan shirin gaishe shi, sai kuma AA ɗin ya miƙa masa hannu suka gaisa yana amsa gaisuwar shi, kujerar kusa da shi ya zauna da mugun taushi yace "Yaya kana nemana ne?"
AA ya ɗago sosai ya gyara zamansa daidai lokacin da Anna ta dawo da kula ta yiwa gogonsu sannu sannan ta zauna dan ta tabbata zaman nan na AA akwai magana a tare da shi, yanayinsa baya taɓa barin gangar jikinsa, a duk lokacin da zai furta magana mai mahinmanci ko da bashi da rigar kaki a jikinsa to kuwa izza da mulki na fita a motsinsa da harrufan sa, babban abinda ya sa mahaifinsa ke yawan yin murmushi idan yana kallonsa yana da hira kenan.
A nutse AA ya dubi mahaifinsa, da duba na mutumci da girmamawa sannan ya sake risinar da kansa ɗan ƙara nuni da furucin wa mai girma a duniyarsa ne zai yi sannan ya buɗa bakinsa a tausashe ya ce" Dad, na dawo kan maganar kuɗin da ake fitarwa famillyn nan ne daga asusun gwamnati duk ƙarshen